← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 163

Sashe 83

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunowa yayi da maganar Umar inda yace wai anmata barazana da kisa ne idan har tashigo da wani cikin lamarin, kenan hakan ne dalilin daya sanya ta'ki ta sanar dani, in hakane kuwa lallai mutanen nan basu da hankali, har yaushe zaka sa yarinya 'karama irin Fateemah agaba, meyasa bazasu je su cigaba da yin sha'aninsu a iya junansu da suka saba ba har se sun shigar da innocent soul irin wannan a haukansu.

Fita yayi haraban gidan ya ringa gwada 'kiran wayar Umar amma baya 'dagawa haushin haka ya 'kara sa shi jin suya acikin azuciyarsa, jiyake badan dare bane yanzun da babu abinda zai hana shi zuwa wajen Umar 'din ya tuhume shi sai ya sanar dashi kosuwaye ne, dan yanada ya'kinin Umar ze san wani abu akai tunda har labarin ya iso kunnansa, sai de ayanzun shikanshi baya so ya rin'ka garajen barinta agida saboda rashin sanin me ze iya biyo bayan hakan.

Haushin kansa ma yake ji da shi da kansan be tsanantawa ransa tunanin dalilin dake hana Fateema zama agida ba, ya tabbata daya nutsu ya bincika da kansa wata'kila da tuni ya san meke faruwa,
amma bakomai ko yanzun ma lokaci be 'kure masa ba, da iznin Allah zai bincika 'din kuma zai samo su dakansa koda Umar be fa'da masa ba.

Wannan karan kam ba ze yi shiru ba Abbah zai samu yafa'da masa abinda ke faruwa inyaso sai yayi magana a division sukawo masa security ana yi masa gadin gidan a 6oye, kodan ayi saurin kama wa'danda ke da hannu akan lamarin cikin sau'ki.

Umar kuwa ya 6oye wa Mahmud sunan dayaji ne akan lamarin badan komai ba sai dan saboda gudun kuskure, kar yaje kuma bayan yafa'a masa bincike yazo ya nuna bahakan bane yaji kunya daga baya shiyasa ya 6oye masa sunan yafi so idan ma su'din ne toh binciken sa ya nuna masa base yaji daga bakinsa ba, kuma idan ya bincika dakansa yaganecgaskiya zefi yadda da batun sa6anin idan aka sanar dashi baze yadda ba sai kaida ka fa'dan idan kayi wasa kanka fushin zai dawo.

*****
*MAIDUGURI BORNO* *STATE*

Rayuwa yanzu tayiwa Abbas zafi, sam baya ta6a jin da'din duk wani abu dayakeyi, wanda tun farkon auren Mahmud da Fateemah ya tsinci kansa a wannan yanayin, dalilin ma daya sanya shi neman hanya ya taho Barno kenan amma still ya kasa saita al'amuransa, wanda ada yake ganin kamar yin hakan ze 'dabe masa kaso mafi yawa daga cikin damuwarsa amma sai yaga hakan ya kasa yiwuwa agareshi, be tashi fahimtar Fateemah ce rayuwarsa ba har se da ya tabbatar da cewa yarasa ta, shikanshi be san iya adadin soyayyar da yake mata ba sai da yaji labarin za'abawa Mahmud auren ta sannan ya farga da hakan.

Rayuwarsa bayan auren Fateemah ta kasance ne gaba 'daya ajuye alokacin komai yakeyi Fateemah ce kawai ke zuwa tunaninsa da idanunsa akowani lokaci, ganinta yakeyi tare da wani da sunan mijinta ne wanda shida kansa shaida ne akan haka.

Ya kan 6ata lokaci yana tunaninta ko kuma yayita kallon pictures 'dinta dake cikin wayarsa wanda ita kanta ma bata san da zamansu ba, musamman yake yawan zama da wayarsa agefensa saboda yawan 'dagowa yaga hotonta daya keyi akan lokaci sam baya gajiya, wani write up data ta6a rubutawa ranar da hutunsa ya'kare a Damaturu wannan ma baya ta6a gajiya da karantashi idan yana karantawan kuwa harji yake kamar muryan ta ne ke karatun azuciyarsa tsaban yanda yasata aransa, idan kuwa yazauna yana tuno childish behaviourn ta shi ka 'dai se de kaga yana murmushi duk kuwa da 'kuncin da zuciyarsa take ciki amma baya ta6a denying murmushi akan tunaninta, yagama bawa ransa tabbacin cewa Fateema daban take agurinsa, bayaga mahaifiyarsa da Hannah arayuwarsa be ta6a bawa wata mace muhimmanci ba kamar Fateema shikansa ya yadda cewa irin soyayyar dayake matan nan ba me yankewa bace har abada domin ko bayan auren nata ma be ta6a jin soyayyar ta taragu acikin zuciyarsa ba koda da 'digo 'daya ne.

Ganin kamar abin na neman illata masa future 'dinsa ne yasa yanemi hanyar zuwa Borno alokacin har angama cire list ma amma ya nemi asaka shi, wanda kusan kowa idan yaji yana mamaki domin dayawan mutane basu so koka'dan ace sunan su yafito ajerin masu zuwa borno sai gashi shikuma dakansa ma ya nemi asakaya shi, ogansa yaso ya'ki amincewa amma Abbas 'din yadage ya kwantar da kansa yace ko na 5months ne pls akaishi yagaji da zama anan 'dinne kuma shima yanaso adama dashi cikin masu karawa da 'yan ta'addan.
Da hakan yasamu aka sanya sunanshi aciki.

Bayan bikin Fateemah da sati uku Abbas ya gudu Maiduguri, tunda yazo kuwa abubuwa suka so shan kanshi domin har alokacin dai-dai da kwayar zarra zuciyarsa bata sarara masa daga tunanin Fateemah ba, inda yasami sau'ki ma yanzun baya waya da Mahmud saboda rashin network dan Mahmud baya kwana hu'du me kyau batare da ya 'kira sa ba, wani lokacin sai yaga kamar da gangan Mahmud 'din keyi masa hakan, domin he can't deny it, ba'karamin kishin Mahmud yakeji ba har zuciyarsa ya tsani ganin 'kiran Mahmud awayarsa amma ahakan yake daurewa wani lokacin har shima yake 'kiransa kafin yadawo Maidugurin kenan.

Rashin hanyoyin sadarwan dake Jihar Borno yasa ya'danji dama dama yanzun yarage masa ne tsakaninsa da zuciyarsa kawai tunda ba zaiji labarin komai daga wurin kowa ba.

Yakan yiwa wayarsa caji duk da batada anfani saboda ba 'kira yakeyi da ita ba kuma shima babu damar a'kirashi amma dan kawai ya ringa kallonta aciki yasa sam wayar bata rabo da caji, duk da idan ya farga da abinda yakeyi 'din yakan yi gaggawan bari tare da neman yafiyar ubangijinsa saboda ayanzu amatsayin matar waninsa take, amma he can't help it baya sanin lokacin da yake zurfafawa atunanin nata ko kuma duba hotunanta da har yau yakasa maye gurbinta azuciyarsa da wa ta.

Yanaji tamkar yagama da al'amarin mata arayuwarsa, tun rabuwarsa da Fateemah be 'kara kallon wata mace sau biyu bama balle har yamata kallon mata.

Bayaga mahaifinsa dake ta matsa masa akan aure shi kan baya jin kamar ze iya zama da wata mace amatsayin matarsa, ita ka'dai yaso ta ya 'kaunace ta ita ka'dai yabawa muhimmanci arayuwarsa, ita ka'dai take da gurbi da matsayi babba azuciyarsa kuma baya jin akwai wacce zata maye wannan gurbin har abada.

Wani sa'in yakanyi mamaki domin kafin rabuwarsa da ita yasan already Fateemah nada feelings akansa, amma be san meyasa ta ta amince da auren Mahmud ba, ko dayake wasu soyayyarsu ba guda bace takan rarraba kanta zuwa wani 6angaren daban.

Da yawan lokuta Fateemah yake 'daurawa laifi dan shi aganinsa da amincewarta ne komai ya wakana badan ta amince ba da yasan daddy bazai ta6a 'daura mata aure da Mahmud ba, wani lokaci sai yaga kamar da gangan ne taza6i Mahmud akansa danta muzant shi.

Bayan zuwan sa Maiduguri da 'yan kwanaki ne ya 'dan fara jin dama-dama azuciyarsa game da Fateemahn badan komai ba sai dan yariga yasawa ransa cewar tabarshi kenan har abada, kuma sai yake ga dama haka 'kaddarar rayuwarsu tazo kaddara kuwa dolen kowani musulmi ne ko ya so ko ya'ki sannan aikin daya kawo shi maiduguri ma sai ya 'kara 'dauke hankalinsa gaba 'daya daga kan mafi yawan abubuwan rayuwarsa,
abubuwa duk suka rinca6e masa, komai na rayuwarsa yaja baya, be fiya samun lokacin da ze zauna yayi tunanin rayuwarsa ba ko wani abu daban, abinda kawai yasa agaba shine ta'addacin dake bawa jahar borno kashi yake kuma sasu rayuwa cikin 'kunci da tashin hankali akowani lokaci.

Wannan dalilin ne yasanya komai ma yabar kansa hatta Fateeman yakan wuni ya kwana bata shigo cikin tunaninsa ba, sai yake jin ma hakan yafi masa gara ya fuskanci rayuwarsa ya manta da duk wani abinda ya wuce tunda bashi da ikon canja komai, sai de dukda haka al'kawarin daya yiwa daddy kullun yana cikin ransa so yake abubuwa su 'dan tsagaita masa yasamu damar cikawa daddyn al'kwarinsa kamar yadda ya 'dauka, lokaci ne basamu ba amma be ta6a mantawa da hakan ba, yariga yasawa ransa zuwan duk da zuciyarsa bataso amma dole ne yaje Lagos saboda Daddy yafi 'karfin wasa arayuwarsa.

*****
*LAGOS STATE NIGERIA*

_8:21am_
Munnira ce zaune agefen a kan dinning table Anty yayinda ke siffing tea ka'dan-ka'dan at d same time kuma Anty ke bata ha'kuri tare da sake jaddada mata cewa takusan samun Mahmud a hannu domin Chiddy nasamun abinda takeso komai zai zama tarihi.

Dariya Munniran tayi tace " _ai na dena damuwa Anty, tunda naje ni aka_ ' _kara duba min cewa har yanzu aikina na jikinsu hankalina yakwanta_, _dan nasan kowan nan ka'dai na dogara dashi ma makami_ _ne babba balle kuma ke da kanki kinsa min hannu_ "

Anty ma murmushi tayi tace " _ke kuwa 'yar nan wani irin aiki kikayi haka_ ?.

Munnira kwashe komai tayi ta sanar da Anty.
Tace " _ai tun ranar dinner 'din auren su_ _nayi_ _maganinsu, kinsan yanda nake son Mahmud haka nake kishin sa, toh taya zan bari inagani ya_ _ra6i wata mace daban ni ina nan........._

Kaita ta juya ka'dan tace
" _zuciyata bazata iya 'dauka ba Anty, shiyasa nasaka akayi musu_ _katanga wanda bazai ta6a bari su anfani juna ba , ita nasa akasawa_ ' _karfin sha'awa wanda idan ya 'debe ta dole sai ta nemi atallafa mata....._ _amma fah Anty da 'kyar nasamu aikin yayiwu......._
" _Mtheww wai su adole masu rotson Allah, kinsan kuwa wanda nayi mata ranar dinnern_ _ma ko kamata beyi ba, sai da na koma shine bokan yace min wai sede atura mata aljani wanda zai ri'ka sata jin_ _sha'awar ammafa bakowani lokaci ba, sai in lokacin daya samu kanta_ _tukunna sannan se sakata, shi 'dinma Anty da 'kyar yasamu yashigeta_ _inji bokan, amma jiya dana koma yace min komai_ _normal, shirina yana tafiya akan_ _tsari banda_ _matsalar komai_ ".

Kallon Anty tayi wacce tabaza kunnuwa take jin tsaban shu'umanci irin na Munniran sai ma taji ta 'kara birgeta data yi maganinsu, ai ita da farko ma tunaninta beje ga hakan ba tazauna sa'ka'ka kawai tana jiran rabuwarsu ashe hauka tayi, inbadan Munniran ta yun'kura bama ai tanajin abun nasu sai yafi haka.
Chapter 83 · 0% Book details