← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 163

Sashe 151

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Bata rai Hannah tayi tace " Haba-haba ke kuwa, ki daure ki bashi dan Allah, ke baki ganin irin kukan daya ke yi ne?
Tun fa a safe baki bashi yasha ba, kina ganin kyauta kenan?
Ko irin tausayin shin nan bakijji ne ke?"

Teemah kam sai cewa tayi " d'auke shi Hannah please ki bashi ko zam-zan 'din ma yasha may be zai yi shiru"
Ta fa'da cikin hawaye.

Tsaki Hannah ta ja tare da sa hannu ta 'dauke shi a zuciye tayi waje da shi.
Gani take yi kamar rashin imani Teemahn ya zarce misali ne da har bata iya tausayin 'dan jinjirin dako kwanaki bai ma fara irgawa ba a duniya.

Da idanu Teemah ta bisu har suka fice, inda suna fita ta kifa jikin ta a kan gadon tana kuka da hawaye, ita da kanta haushin kanta takeji akan abinda tayi.

B'angaren Hannah kuwa koda ta fita da babyn jijjiga shi taci gaba dayi tana tafiya, sai sukayi kici6us da shi a corridor, shogowar kenan yajiyo kukan baby ya cika ko'ina agidan hakan yasa ya 'karaso nan 'din da gaggawa.

Da 'dan hanzarin sa ya iso kusa da Hannah.
Hannah ja tayi ta tsaya sai ya sa hannu ya kar6i babyn tare da fa'din " me ya same shi ne haka yake ta faman kuka?"

Amsa Hannah ta bashi da fa'din " tun safe bai sha komai ba sai zam-zam da ruwa inajin yunwa ce ke damun sa"

Yana jijjiga babyn yace mata
" ina Fateemahn kuma take me yasa ta barshi haka?"

Hannah sai tace
" tsoro takeji wai maman na mata zafi".

"Where is she now?"
ya tambaye ta sai ta bashi amsa da fa'din " tana dak'i na"

Tafiya ya fara yi da Babyn a hannun sa ba tare da ya sake fa'din komai ba ya nufi hanyar 'dakin Hannah 'din.

Hannah ma 'karasawa tayi 'bangaren Ummah ta dubo ta jin bata fito ba duk wannan uban ihun sai ta tarar ma ashe sallah take yi shiyasa.

Tambayar ta Ummah tayi wai " tabashi ne?"
Sai Hannah tace " ina kuwa ta bashi, har fa ta ciro kamar zata bashin kuma sai tace wai zafi yake yi mata"
Ummah cewa tayi
" To ai da kin taho min da shi nan d'in...."

Taranta Hannah tayi da fa'din " Yayah ne ya kar6e shi ai, yanzun nan inajin isowar shi ma"

" ai kuwa ba mamaki dan ko ni ma bansan da zuwan nashi ba".
Ummah tayi maganar tana mai cire hijab 'din data yi sallah dashi a kanta.

Teemah kam kasa zama tayi a 'dakin dan yanda take iya jiyo tashin kukan babyn gaba 'daya ya kara'de gidan nasu, ga shi maghrib tayi sam hankalin ta sai ya kasa kwanciya, dan haka sai ta yun'kura ta taso da niyyar bin bayan Hannah, tana 'ko'karin bu'de 'kofa sai kuma taji kukan babyn na sake tunkaro 'kofan daga waje.

Kafin ma ta bu'de sai ya riga ta bu'de wa sai suka tsaya kallon kallo.

Ita kallon mamakin ganin sa takeyi musamman da ta gansa rungume da Babyn, yayin da shi kuma yake yi mata kallon " kin kyauta ai"
Amma fuskar sa wasai babu wani alamun 6acin rai akai sai ma wani 6oyayyen sihirtacce kuma 'kayataccen murmushi.

*Only one☝🏻 page to go insha Allah.......* 👌🏻

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍
[10/13, 8:01 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated 2_
*Maman Ahmad &*
*Anty Maimounath o.g ( Mahnoor).*
*Mungode da 'kaunar da kuke nuna mana Allah Ubangiji ya bar mana ku (Ameeen)*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_U can’t change what happened in ur past, so b4 u let it destroy ur future, learn to live with it...._

🅿 *91*

Ganin kamar zata 6ata mai lokaci ne sai yayi hanzarin wucewa da kansa ya za6o mata doguwar riga da hijab.

Da taimakon sa ta sanya kayan a jikin ta tare da rufawa kanta hijab 'din still tana zubda hawaye suka fita zuwa clinic dake cikin barrack 'din nasu.

Daya ke ma koda wani lokaci kaje suna aiki basa yankewa so ba tare da wata damuwa ba suka isa ga babban Doctor 'din dake kan aiki a lokacin.

Abbas da kansa ya yiwa Doctor bayanin abinda ya kawo su Teemah kam sai hawaye take tana faman rarraba musu idanu daga gefe.

Wata nurse likitan ya 'kira yayi mata bayanin abinda zatayi sannan ya ha'da su da Teemah suka je ta 'dibi jinin ta sannan ta bata wani 'dan k'aramin abu tasa ta yin fitsari a ciki.

Teemah kam duk da tana cikin wani yanayi na tsananin damuwa amma hakan bai hanata ta6e baki da " mitar wai banda 'kazanta to me ze sa ta haka, a hakan ne wai Yayah zai ce itama ta zama likita" sake kallon robar tayi tana sake jinjina rashin kunya da 'kazanta irin ta likita.

Zuwa tayi ta mi'ka ma Nurse 'din tana sake kallon 'kwayar idanun ta amma sai taga bata wani nuna komai ba ta kar6a ta wuce laboratory da shi, bin bayan ta Teemah tayi da idanu har ta 6acewa ganin ta, ita kam wurin tap taje ta ringa dirzan hannun ta kamar zata sille shi sai da ta tabbatar ya wanku tas sannan ta bari ta koma office inda ta baro shi.

Zaune ta same shi shika'dai yana amsa waya ga dukkan alamu Doctor 'din ma ya fita ne.
A hankali ta 'karasa jikin sa ta zauna tayi luf, sai da ya kammala da wayar kafin ya tambaye ta har an gama ne kai ta 'daga masa tare da fa'din " Yayah wurin ma zafi yake min sosai"
Tayi maganar tare da nuna masa gurbin da aka ja jinin.
Hannu Abbas ya kai yana shafa mata a hankali yace " Vry sorry...zai daina zafin ai kinji"
Cikin sakalci da marairaita ta d'age kanta sama tare da fa'din " har da fitsarina fa ta kar6a Yayah".
Abbas duban fuskar ta yayi sannan ya ce mata " ba komai ai test za'a yi da shi".
Sai ya kai hannu jikin ta ya ta6a yanayin zafin jikin sannan ya 'kara da fa'din " har yanzu cikin na miki motsin ne?"
Teemah sai tace " Ah'ah.......ya daina amma Yayah ni tsoro nake ji"

Taran ta yayi da fa'din " Nima inajin hakan Zahra.. but Doctor yace min 'kila abin alkhairi ne zai same mu, amma bari dai mu jira ganin result 'din ko sai muga ko menene?"

Teemah sai ta 'daga kai alamar "to" tayi luf a jikin sa amma abin sai yana bata mamaki, kasa jurewa tayi sai 'dago tare da sake fa'din " Yayah dama akwai alkhairi a cuta ne?"
Abbas sai yayi murmushi sannana yace " akwai mana Zahra komai ai da irin 'kaddarar da yake zuwa dashi wani mai kyau wani kuwa akasin haka, inajin tamkar wani gagarumin farin ciki ne zai same ni, i feeel ths in my heart kuma ina fatan hakan ya kasance ki kwanatar da hankalin ki kinji ko insha Allahu ba abin damuwa bane".

Mai da kanta tayi ta kwantar a jikin san sannan a hankali tace " Allah yasa hakan ne to amma.... ni tsoro...nake ji Yayah bana son in.......".
Sai tayi shiru.
Abbas ne ya 'karasa mata maganar da fa'din " bakya so ki rasa ni ko?"
Murmushi tayi ta 6oye kanta a 'kirjinsa tare da tukuikuye hijab d'inta.

Shima Abbas murmushin yayi A saman la66an sa ya furta " silly girl". sannan ya kai hannun sa ya sau'ke shi a bayan ta a kunne ya ra'da mata " babu abinda zai raba mu kinji, sai dai mutuwa insha Allahu".

Shigowan likita ne yasa Teemah ta bar jikin sa ta zauna amma still kanta na jingine da gefen hannun sa tana wasa da hannayen ta, Doctor ha'kuri ya bawa Abbas na barin sa da yayi shi ka'dai inda Abbas yace dashi ba komai kar ya damu daganan suka 'dan fara ta6a hira da Doctor 'din sama-sama.

Sunyi jiran a 'kalla 30mins kafin result ya fito, a hannun Doctor aka mi'ka result 'din wanda hakan yasa Abbas zuba masa idanu danjin me ke faruwa, Doctor kuwa yana saka idanun sa kan result 'din take sai fuskar sa ta fa'da'da da fara'a Abbas kam binsa da idanu kawai yake binsa wanda fara'ar data sau'ka kan fuskar tasa yasa Abbas 'kaguwa yaji sakamakon dake ciki.

Tsaye likitan ya mi'ke tare da mi'kawa Abbas hannu, Abbas ma mi'kewan yayi sannan ya bashi hannun shima Doctor yana murmushi yace "Congratulations sir"
Abbas bu'de idanu yayi a kansa shima da alamar tambaya tare da fatan Allah ya tabbatar masa da zaton sa.
Juyawa yayi ya kallo Teemah da ke ta binsu da nata idanun ganin kalar game 'din da suke yi akan result 'din test 'din da akayi mata.

Abinda dukkan su kunnuwan su ya jiyo musu shine ".......ur madam is pregnant...."
Daga bakin likitan.

Ba Abbas ba hatta Teemah sai da ta bu'de idanu a kansa tana sake kallon bakin sa daya furta hakan sannan ta dawo da kallon ta kan Abbas cike da mamaki, Abbas kam ido kawai ya waro a kansa da alamar wata tambayar Doctor sai ya lumshe idanu ya kuma bu'dewa alamar tabbatar masa da gaskiyar sa sannan ya 'dago 'dayan hannun sa ya mi'kawa Abbas papern result 'din ya kar6a ya duba.
*Fateema Kabir* ya fara gani a sama daga shi sai
*Positive* idanun sa ya 'kara sau'ka a kai bayan sunan ta dake saman.

Kan sa ya 'daga ya kalli likitan yana murmushi duk da yanzu yagama tabbatar da hakan musamman daya tuno 'dan 'dagowa da cikin nata yai ga kuma motsin da ta ji wannan kadai ma ansawer ne amma duk da haka sai ya sake tambayar likitan cewa dagaske ne Fateemahn sa ne 'dauke da ciki?
Tambayar bai yita dan neman amsa ba face tsaban farin cikin daya cika zuciyar sa.
Chapter 151 · 0% Book details