Sashe 133
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannah dake 'ko'karin shigowa tace " _ehh na dawo ai ban bi gida ba kawai na taho nan, bana ma sam inje ni ta rin'ka kora 'din_ _nan wai ita a dole ina barin ki ke ka'dai a gida_"
Teemah cewa tayi
" _Hmm, gaskiyar ta ne ai Hannah ba 'karya bane....._ "
Hannah da sauri ta tare ta da fa'din
" _Ba wani nan naga kona zauna 'din ma baccinki kike sha ki barni ina gadinki, kuma Allah ki daina_ _baccin la'asar 'din nan kin ganki ne yanzun yanda kika zama tamkar mara lafiya fa"_
Hannah ce tayi gaba sai Teemah tabiyo bayan tana me fa'din
" _ai ba lafiyar ce dani ba Hannah ko dan ban fa'da miki bane shiyasa, Allah yau ban jin da'di........._ "
Maganar tata tsayawa tayi dalilin cafko hannun ta da taji Hannah tayi sai ta nuno takalman data gani a parlourn a mamakance 'kasa-'kasa tace " _ya dawo ne_ ?
Da kai Teemah ta bata amsa alamar " _ehh_ "
Hararar ta Hannah tayi tare da sakin hannun ta, Teemah kuwa sai tayi murmushi.
" _ina yake to_ ?"
Hannah ta tambaya.
Teemah ma sai ta bata amsa da fa'din " _d'akinsa_ "
A takaice
Hannah sai tace
" _Ki sanar dani cewa mijin ki ya dawo ne mana kika wani barni nake ta zabgawa bacci sharri_ "
" _Ke kika sani ai_ "
Teemah tace tare da wucewa cikin parlourn ta kwashi takalman nasa tayi gaba dasu zuwa d'akin sa.
Hannah ma d'akin Teemah ta shige da niyyan tattara kayanta ta koma gida tunda ya dawo.
Shigan Teemah d'akin nasa sai ta tarar dashi har yashiga bathroom,
kayan daya cire 'din ta kwashe ta fitar masa da wasu marasa nauyi riga arm less da 3quarter trouser dan taga idan yana gida da ire-iren su yafiya amfani.
Fita tayi ta koma wurin Hannah anan ta same ta tana kan ha'da kayan ta.
Turus taja ta tsaya tana kallon ikon Allah, data ga cewa dagaske take yi kaya take ha'dawa sai ta 'dan matso tare da fa'din " _Hannah wai miye hakan kike yi ne dan Allah_ ?"
Hannah bata 'dago ba tace da ita " _inda nafi wayo zan koma ko so kike in zauna har sai mijin ki ya_ _korani kafin in tafi_ ?"
Amsa Teemah tabata da fa'din
" _Ce miki akayi zai koreki? Ko kin ta6a jin ya kori wani ma agidan sa ballantana kuma ke_ ?"
" _ke nifah 'kyaleni Teemah gara na ware yafi, ya za'ayi gandamemiya dani kuma in zauna agidan amare_ ?"
Hannah na maganar tana zuge zip 'din akwatin kayanta.
Teemah kam tsaki tayi cike da haushi ta koma parlour Hannah ta rakata da murmushi tana murnar yau sai kwana a gida wurin Ummah.
Teemah zama tayi a parlourn ranta duk ajagule, Bata da'de da zama a wurin ba sai gashi shima yafito cikin shigar kayan data fitar masa yana amsa waya.
Sosai taji da'din hakan domin yau ne karo na farko data ta6a aikata masa irin hakan kuma tayi sa'a bai gwale ta ba.
Dinning ya nufa da wayar a kunnan sa itama sai ta tashi ta bishi abaya.
Koda ya isa wurin ma bai zauna ba har sai daya kammala da wayar kafin yaja kujera ya zauna.
Teemah kam bata zauna ba abincin tafara zuba masa dai-dai nan Hannah ta fito.
A hankali ta 'karaso wurin tayi masa barka da zuwa,
Suna ha'da idanu da Teemah sai ta banka mata harara, sannan taci gaba da abinda takeyi. Hannah kam dariya ma Teemah ke bata .
Abbas gaisuwar datayi masa yayi tare da tambayar ta ya makaranta.
Inda ta amsa da " _Alhamdulillah_ ".
" _Allah ya taimaka_ "
Yace 'kasa-'kasa.
Zama sukayi dukkan su bayan Teemah tagama serving nasu kafin su fara ci sai tace " _Yayah kaga Hannah ba! wai tafiya zatayi dan ka dawo har ta_ _gama ha'da kayan ta ma_ "
" _Ah ah ba yau ba_ "
Yace atakaice tare da saka abinci abakin sa.
Teemah kam murmushi tayi itama tayi bismillah tare da fara cin abincin.
Tana murmushin ta kallo Hannah da suka ha'da ido sai Hannah ma ta harareta ita kuwa Teemah tayi mata gwaliyo.
Hannah bata wani ci na kirki ba ta tashi ta koma 'dakin Teemah ta turo 'kofar.
Shiru sukayi kowa nacin abincin a hankali, Abbas kam ma daina cin nashi yazo yayi ya tsaya kallon ta ganin yanda take cin abincin, duk da bata ci ko rabin plate ba amma sosai yake 'kara ganin sauyi ta wannan 6angaren tattare da ita.
Saboda kwanaki ba haka take yi ba.
Yana ganin ta gama sai ya mi'ke tsaye ya koma parlour ya zauna, Teemah kam sai da ta tattare komai kafin ta bar wurin taje tana shirin wucewa 'dakin ta wurin Hannah sai yace da ita ta dubo masa 'dayan wayar sa a 'dakinsa.
D'akin ta wuce ta fara dubawa amma bata gani ba, shima 'din yasan bazata gani ba saboda bai ajiye inda zata yi saurin ganin ba dama dagangan ya turatan dan so yake yaji 'dumin matar sa, dan haka sai ya tashi ya bi bayan ta.
Ko yanzun ma waya yake amsawa wanda take kyautata zaton da abokin aikin sa ne saboda yanayin maganar dataji yakeyi, aranta tace " _wannan dai yau inajin cutar amsa wayace takama shi_ "
Tsayawa tayi tana kallo da jin yanda yake maganar da ta'kama tamkar wani sarki sai kace dole aka saka shi, tana ganin ya gama sai ta kauda kanta gefe da sauri.
Yana cire wayar a kunnan sa yace da ita " _come on, zo nan ki gaya min how u missed me_ "
A hankali ta taho sai ta zauna agefen sa 'dan nesa ka'dan dashi.
" _What is ths kuma?, bayan kin gama min rashin kunyar ki 'dazu shine zaki zo kimin wani fi'ili anan ko? Zo matso nan ki gaya min_ _wama ya koya miki......_
Tun kafin ya rufe bakinsa tace
" _ni babu kowa_ "
Gira ya 'dage sama yana kallon ta yace
" _Really_ ?
Shiru tayi ta kauda kanta gefe.
Sai yace " _to naji shikenan, zo in koya miki wani da bakiyi 'dazun ba ko baki so ki koya?_
Kai ta 'daga masa alamar " _ehhh_ "
Bata ankara ba taji ta ajikinsa inda yazo ya rungume ta bayan ta hannun sa daga cikinta ya sa'kalo su yayin da ya kwantar da kansa kan kafa'dar ta a hankali kamar ra'da yace " _guduna kike yi ko_ ?
Kamar zatayi kuka tace " _umm-ummm_ "
tambaya ya sake jefa mata da fa'din
" _To meyasa baki son zuwa kusa dani?_
" _Ni....ni... bani da lafiya ne fa shiyasa....._ "
" _Shiyasa kike gudun mijinki_ ?
Sai tayi shiru.
" _what's wrong with u then, meke damunki_ ?
Sai yanzu ne tabashi amsa da fa'din
" _Nima bansani ba 'dazu ne naji kamar banda lafiya amma yanzu yayi sau'ki_ "
Sai yace
" _muje wurin Anty nurse ta dubaki ko?_
Kafa'da ta 'daga da sauri ta kwa6e fuska sannan tace " _ai na warke yanzu_ "
Hannun ta dake cikin nashi ya kamo ya 'dago shi sama ya 'kara kalla da kyau sannan yace
" _Kuna sayan lightning cream kuna amfani dashi da bana nan ko_ ?
" _Ah'ah_ "
Tace dashi dashi.
Da mamaki yace " _ya akayi haka to ke baki ga kin canza sosai ba, miye dalilin_ ?"
Cewa tayi
" _Nima fa bansani ba Allah Yayah_ "?
Shiru yayi yana feeling 'dumin jikinta kawai sannan ya cusa kanshi 'kar'kashin wuyan ta ya sumbace ta
sai ya 'dago kansa a hankali yace " _Zaki fara zuwa makaranta kema, gaya min wanne kike so kiyi_ ?
Tace " _bana son ko wanne_ "
" _Kamar Yayah_ ?
Ya tambaya da mamaki.
Sai tayi shiru bata bashi amsa ba.
Cigaba yayi da fa'din " _kin fi son kiyi ta zaman ki a gida haka kawai kenan_ "
kai ta 'daga masa up&down.
Sai yace " _saboda me to, baki ga Hannah na zuwa tana karatun ta ba......_
Taran sa tayi da fa'din
" _Ni fa banaso ne kawai Yayah_ "
Juyo da ita yayi ta fuskance shi sai yaci gaba da lalla6an ta dan ta yarda yace " _baki son ki zama doctor ne irin na Anty nurse?.......ba wahala fah idan kika gama kinga_ _sai ki haifi babyn ki dayawa ko ba haka ba?_
Teemah najin zancen baby tasaki fuska tana murmushi amma duk da haka sai tace dashi " _to ni Yayah shikenan bani da daman in zauna agida batare da yin wani makaranta ba_ ?
Idanun sa cikin nata yace " _Yes kinada shi mana, Fatima nada wannan daman a ko'ina sai dai akasin da aka samu shine ita wannan 'din Zahra_ _ce!, Zahran Abbas kuma,_
_Zahran Abbas kuwa batada wannan damar ita_ "
Baki ta turo gaba tayi fushi sai ya kamo chicks 'din ta duka biyu da hannun sa yace
" _Angel 'din Yayah a daure a cikawa Yayah wannan burin plz kinji_ "
Batayi magana ba illah bugan 'kirjin sa da tayi a hankali da hannun ta 'daya tana 'kif-'kif da idanu.
Shikuwa kamar gaske sai yayi baya akan gadon ya 'dora kansa cikin hannayen sa ya wani lumshe idanu.
Da sauri tabishi tanaq 'kiran sunan shi " _Yayah_ !
_Yayah_ !! Tare da jijjiga shi.
Abbas 'kin tashi yayi ya kuma 'kin motsawa ko ka'dan, sai daya ga ta rikice sosai sai ya 'dan bu'de idonsa 'daya ya kalleta caraf sai akan idanun ta.
Da sauri ya maida idon ya kuma rufe shi.
Ita kuwa dan mugunta harda cije baki ta kai kanta a hankali zuwa saitin fuskar sa kamar zatayi abin kirki sai kawai ta cije mai hancin sa.
Zafin dayaji ne yasa shi bu'de idanun da sauri tare da fa'din " _awwshh_ " yana shafa hancin.
Tana 'ko'karin guduwa ya cafkota take ya maida ta 'kasan sa, suka fara kokuwa tana dariya take fa'din " _Allah Yayah bazan sake ba please kayi ha'kuri_ "
Shima yace " _Babu ruwana ramawa zanyi, in ada kin min mugunta na barki yanzu kam ba'a cutata na 'kyale mutun_ "