← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 163

Sashe 72

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afili kuwa sai ta saki fuskarta tare da yiwa Antyn barka da zuwa, bata zauna ba sai data kawo mata abinsha Kafin nan ta zauna nesa da Anty Chidehn ta gaidata.

Cikin fara'ah ta amsa mata sannan ta tambayeta ya zaman gida Teemah ta amsa da " _lafiya_ ' _kalau"_

Sake tambayarta tayi wai ina Mahmud sai *Teemah* tace " _ya_ _tafi office"_

Jinjina kai tayi tana murmushi, 'yar hira ka'dan taja Teemah dashi ganin Teemah bata saki jiki sosai da ita ba yasa bata da'de ba ta mi'ke da niyar zata tafi Teemah ma mi'kewa tayi tsaye kamar yanda Anty Chidehn tayi.

Sai alokacin data mi'ke sannan ta lura da irin she'danin kallon da Anty Chideh ke binta dashi musamman ma 'kirjinta daya kasance ana 'dan ganin kusan rabinsa awaje dan wata armless red top ne ajikin ta mai bu'dadden round neck wanda ya 'kara bayyanar da haske fatarta afili, ba karamin kar6an jikinta rigar tayi ba, ta sanya shi da wani jeans trouser daya kama jikinta sosai, gashi kanta ko 'dan kwali babu gashin kawai takama da wani 'karamin jan ribbom ba mayafi balle tacire ta lullu 6a dashi.

Afakaice ta samu taja rigar sama yarufe mata 'kirjin sannan tama ta rakiya iya bakin parlourn tadawo ciki tare da jan wani uban tsaki.

Wayarta ta 'daga ta buga shi akan kujera kamar shine Anty Chiddyn afili tace

" _Duk sharrin wayar nanne, in bahaka da nasan bazan manta 'dauko mayafi ba balle har matar nan ta ganni ahaka ba, kamar mayya sai ta ta kallon mutum tana_ _murmushi_ ."

_Your Comments always encourage me, pls kar ana manta wa........I heart u all_ *CAPTAIN ABBAS* *COMMENTERs* , _Allah yabar 'kauna._

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmern ku ce* 😍
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_NO matter how talented you are, not everybody is going to like you, but that’s life, just_ _stay strong and always be your self_ .

🅿 *58*

Washe gari ma haka Anty Chideh tazo wurin Teemah bayan Mahmud yatafi office.

Yau ma daurewa Teemah tayi ta kar6eta hannu bibbiyu ba yabo ba fallasa ta 'dan saki fuskarta, sai de yau 'din Anty Chiddy cewa tayi da Teemah wai zata na zuwa kullum tana tayata hira tunda ita ka'dai take wuni agida, Teemah murmushi kawai tamata batare da ta bata kykakkyawar amsa ba, dazata tafi yauma Teemah iya 'kofar parlour tayi mata rakiya amma duk da haka Anty Chiddy kasa ha'kuri tayi har se data 'dago hannu ta shafi fuskar Teemah tare da fa'din _" I really love u"_ 'kasa-'kasa tayi maganar, Teemah kuwa rintse idanu tayi cikin takaici, sannan ta 6ata ranta afili hatta Anty Chiddy ta lura da hakan amma itan kuma sai tayi murmushi ta 'kara 'dago hannu da niyyar shafo la66an Teemahn daya ke matu'kar 'dauke mata hankali a kowani lokaci sai Teemah tayi baya da sauri, Anty Chiddy ganin hakan yasa kawai tajuya ta tafi aranta tana kissima ranar da aka ce tasamu wannan yarinyar ahannu, ga dukkan alamu she is hot, tace ha'kurinta yakusan 'karewa akan yarinyar bazata iya jira har se lokacin da sukayi sabo da ita sosai ba sannan tasameta kamar yadda mum Mahmud ta ce da ita, afa'dar ta in har tace hakan zatayi zuciyarta ze kusan bugawa ne abanza, tace gara taje tasamu mum Mahmud su sake shawara dan she is in need of her, she so much love the girl yadda ita kanta batasan yaushe hakan yafaru ba, bata da buri ayanzu daya wuce taga ta samu yarinyar a hannu.

Teemah kan takaicinta na yau na musamman ne dan ita ka'dai tasan yadda takeji azuciyarta , dama akwai damuwar rashin samun iyayenta da bata yi awaya daya matu'kar tsaya mata azuci, ko da ta yiwa Mahmud maganar kuma shima sai ya nuna mata rashin damuwarsa akan hakan, sai ma ya tabbatar mata da matsalar network ne kawai bakomai ba, tana cikin wannan takaicin kuma Anty Chiddy tazo tasake jagula mata lissafi, ita ka'dai sai zuba tsaki takeyi, haushin Anty Chideh da haushin abinda tamata duk yabi yacika mata zuciyarta, wani mugun 'daci takeji aranta, taci alwashin sanar da Mahmud damunta da matar nan takeyi dan ita baso takeyi ba gara ayi mata magana ta daina zuwa gidannan tunda ita bata san girma da arzi'ki ba.

Sai akayi rashin sa'a kuma ranar Mahmud be samu yadawo gida da wuri ba, sanadiyar aiki da ya musu yawa a office, hakan yasa be shigo gidan nasa ba sai kusan 9:01pm ya dawo, alokacin ma Teemah harta fara yin bacci.

Koda yadawo a parlour yasameta kwance tana bacci, da shigowarsa kuwa ta ta shi ta zauna ta na mar barka da isowa.

Zama yayi agefenta tare da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu amatu'kar gakiye yake, Teemah ma bata bu'katan wani 'karin bayani saboda tun da yamma ya 'kirata yayi mata bayanin abinda ya ri'ke shi a office 'din, awa biyu da suka wuce ma ya 'kara 'kiranta yaji lafiyarta hakan yasa bata wani damu ba yin daren nasa, duk dama tana 'dan jin tsoro amma zuwa yanzu dolenta ta'dan fara sabawa da zama ita ka'dai agida.

Ruwa Mahmud yaje ya watso ya dawo parlourn da niyyar yi mata magana akan ta tashi ta koma bedroom ta kwanta, sai yasameta ma harta koma bacci abinta, kyaleta yayi dan shi be fiya son tada mutun ba idan yana bacci dan haka sai yaje shima yakwanta aparlourn akan doguwar kujera bayan yagyara mata nata kwanciyar tare da gabatar da duk wani al'adunsa daya saba yi kafin yayi bacci.

Kamar kullun yauma yana kwanciya bacci me shegen nauyi ya 'dauke shi da be san inda yasamota ba, badan ma ya kasance yana da iyali ba, da bazai ta6a sanin cewa yana irin wannan baccin ba saboda ada idan yariga yayi bacci toh yatafi kenan domin shi bashi da irin al'dun tashi cikin daren nan, ko nafila zaiyi yakanyi ne kafin ya kwanta bacci sai de hakan.baya hana shi sanin duk lokacin da ze juya cikin baccin ko kuma yaji motsi ya farka, amma yanzu sam baya 'kara sanin ina kansa yake da zarar ya 'dora jikinsa a makwanci, kasancewar yana da Teemah akusa dashi ne tasa yagane mummunar lalurar daya ke tare da ita da be san tsawon yaushe yafara ta ba, abakinta yake fahimtar wannan sabuwar lalurar data sameshi, mamaki yake yi idan gari ya waye yaga ta canja wurin kwanciya ko kuma yaga ta bar 'dakin ma gaba 'daya.

Sau tari yakan ji kunyar kansa da kansa idan tafara yi masa mitan ya'ki yi mata abu kaza da dare ko ya'ki yi mata kaza sai yasaki baki kawai yana kallonta, akullum so yake ya nemo mafitar wannan abu amma ya rasa, bayan yasan sarai shi bahaka yake ba.

Da gari yawaye yau kam da sauri-sauri yayi kominsa yagama, ya fita daga gidan tun 7:o clock dan baya son Teemah ta samu chance 'din yi masa complain akan wani abu daya faru cikin dare domin hakan na matu'kar sanyaya masa jiki da zuciya, be san wani irin ha'kuri ze jero mata ba, shiyasa yafice da wur wuri batare da ya bata wani 6ari daga cikin lokacinsa dazata yi anfani dashi wurin kawo 'kararsa wa kansa ba, toh wani irin hukunci yakamata inyiwa kaina tunda kullum nine me yin laifin kuma ni ake kawo wa 'kara, Mahmud tun yanzu su fara 'yar hakan ba, tun ba'a je ko'ina ba su fara wasan 'yar 6uya da ita ba amma gani yake yi inbahakan yayi mata toh akullum kunyarsa gareta 'kara 'karfi zai rin'ka yi, saboda bashida wata mafita, sai de akullun yana ro'kon Allah ya ye masa wannan matsalolin da suka kunnowa rayuwarsa wuta suke son su hanashi sakewa da walwala shida iyalinsa, dan zuwa yanzu abubuwan sun fara zarce tunaninsa dole ne ya nemi mafita, mafitar dazata 6ille musu gaba 'daya batare da an shiga hakkin juna ba, aransa ya ayyanacewa idan yadawo gida ayau duk zai zauna su fahimci juna da ita, ze yi mata bayanin matsalolin daya fuskanci yana tare dasu in yaso ita tasani, saboda ta daina zarginsa da yawan shareta dayakeyi cikin dare wata'kilha ma inta fara saka shi acikin addu'arta sai yaga yasamu sassauci.

Da burin hakan ya'kara office 'din su, yana zuwa kuwa yaga aiyuka sun taru masa dayawa saboda rashin kula dasu sosai da baya yi acikin 'yan kwanakin.

Rarrabasu yayi wa'danda ze sa hannu da wa'dan da ze tura su ne zuwa wani guri da kuma wa'dan da zai 'dora a Internet.

Signing 'din yafara sai de be yi nisa da yi ba wauarsa tafara 'kara , ajiye biron dake hannunsa yayi sannan ya 'dauki 'kiran, Abbas ne ya 'kira shi suka gaisa atakaice dashi ya tambayi lafiyar kowa, sannan ya 'kara da fa'din suk lokacin da yasamu lokaci da iznin Allah ze ziyarce su.

Sosai Mahmud yaji da'din furucin Abbas 'din har ma yakasa 6oye murnarsa sai da bayyana ta har Abbas yagane.

Mahmud yaso yayiwa Abbas maganar abinda ke damunsa amma daya tuna cewa sirrinsa ne, sirrin auren sa kuma Abbas tamkar wa yake agurin Fateemah so da kunya ace yasana sirrin zaman aurenat irin wanann dan haka sai yayi shiru kawai yayi tagumin yana tunanai bayana sun gama waya da Abbas.

Fitar Mahmud daga gida agag gaucen ne ya dakatar da Teemah ga fa'da masa abinda tayi niyyan sanar da shi, amma duk da haka bata ha'kura ba dan har ga Allah ita bata son damuwa, matar nan kuwa tafara shiga rayuwarta ta inda bata so, so take ayi musu tsakani kowa yayi rayuwarsa yadda yakeso.

Wani abokin Mahmud a office 'dinsu ne wanda yakasance mataimaki ne ga Mahmud 'din mai suna Umar yashigo yasame shi da tarin files agabanshi amma yayi zugum yana aikin tunani.

Umar ' dan asalin garin katsina ne aiki yakawo shi nan garin Lagos har suka ha'du da Mahmud kuma sukayi sabo da juna dai-dai gwargwado, domin har damaturu akaje dashi wurin 'daurin auren Mahmud.
Chapter 72 · 0% Book details