← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 163

Sashe 160

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
*Bayan shekara 'daya*
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da haihuwar Anty Leesah inda ta haifi baby girl 'din ta mai suna Aisha amma suna 'kiran ta da Nihal, Hannah kuwa yanzu ne ma take da cikin da bai fi 2-3month ba ga uban wahalar laulayi da take sha duk ta fita hayyacin ta gaba d'aya, har mamaki takeyi irin cikin Teemah yanda har cikin ya zama mutun ajikin ta ba tare da sun san da shi ba, ita kuwa tun baa je ko'ina ba ma ya bayyan kansa, cuz tun yana 1month ya fara wujijjiga ta da su amai ga za6an abinci kamar masifa, Teemah kanta tausayin ta takeji yanzun.
Domin taso rana tsokanan ta amma yanda yanayin Hannah ake sai ta ma manta da waccen batun tausayin ta duk ya cika ta.

Munnira kuwa babu labarin ciki agareta dan ta ziyarci asibitoci kusan uku ma amma duk ce mata suke yi mahaifarta ta riga ta lalace ikon Allah ne ka'dai zai sa ta haihu ko da gaba ne.

Munnira tayi kuka sosai da jin sakamakon ta amma daga 'karshe sai ta ha'kura ta fawwalawa Allah komai dan tasan shine ka'dai mai bayarwa da hanawa in da rabon ta samu ko min daran da'de wa wataran zata haihu.

Anty ma kullum mutuwar Mahmud sabo yake dawo mata musamman idan taga yanda Abbah ke nan-nan da twins 'din sa gashi kullum cikin farin ciki zaka ganshi saboda bashi da damuwar komai, koda kuwa ranar da yake gidan ta ne Abbah dole sai yayi waya da yaransa duk da dama ba maganar suka iya sosai ba amma a hakan wai shi muryar yaran sa yake son yaji, cikin dokar kwanan su ma sai da ya ro'ki Anty akan ta yi ha'kuri koda lokutan girkin tane yana so yana zuwa dubo yaran sa dan bazai iya har kwana biyu kuma suna gari 'daya amma bai gansu ba tare da 'daukan mata al'kawarin babu cin amanar ta koka'dan da zaiyi bayaga ganin gudan jininsa.

Dolen Anty ta amince batare da ta nuna masa damuwar komai ba a fili, duk da bata ba'kin ciki da yaran nasa amma ita ka'dai ta san yanda take ji idan taga Abbah na zumu'di akan 'yan biyun yaran sosai ta ke 'kara neman gafarar mahalicci akan banzatar da rayuwar nata 'dan da tayi sanadin haka ma yasa kullum sai Mahmud ya samu kyakkyawar addu'ah daga wurin ta bata ta6a shagala da hakan ba.
Gashi itama Allah sai ya jarabce ta da masifar son twins 'din, ji take kamar ta 'kwato su a wurin ta, amma babu dama lura da hakan da Anty Sadiya tayi yasa ta yanke aranta cewa idan ta yaye su zata bata little Mahmud kyauta ya zama 'dan gidan ta in yaso ita sai ta ri'ke Nanah in Allah yasake bata wani kuma sai ta hada ta ri'ke su, kuma tana da ya'kinin Abbah ma bazai 'ki amincewa ba, inyaso sai suyi yarjejeniya koda a rubuce ne akan bazata ta6a goran ta mata ko kuma kar6an sa ko da kuwa menene zai faru yariga ya zama 'dan ta, ta dan itama Anty Sadiyan tausayin Anty take ji sosai.

Tana yaye su kuwa ta sanar da Abbah ku'durin ta sai dai Abbah ya so ya nuna 'kin amincewar sa sai da ta ta fahimtar dashi kafin nan ya yarda, amma ba wai har ransa ba dan shi yaso yaransa su taso a tare kamar yanda aka haife su kuma a hannun mahaifiyar su saboda ya yaba da hankali tarbiya da nutsuwar ta k'warai da gaske shiyasa bashi da haufi akan tarbiyar da zata bawa yaransa.

Da Anty ta sami labarin hakan kuwa har sai da tayi kuka dan farin ciki, tun da aka yaye su aka kawo mata shi sai ta sa aka nemo mata mai kula dashi tun daga kano tazo tana tayata rainon sa da kukawa dashi Anty kam sosai taji da'din wannan karamcin kawai sai take ta godewa mahalicci bisa ga chance 'din daya sake bata akaro ba biyu matsayin mahaifiya wannan karon kam tana jin rayuwar 'danta zai kasance ne kishiyar rayuwar da ta bawa Marigayi bazata sake yin haukan da tayi a wancan lokacin ba zata ja 'dan ta ajiki ta bashi tarbiyar data dace ta kuma cika rayuwar sa da farin ciki har sai yaji cewa yafi kowa sa'an mahaifiya.

Wannan abin da amaryar Abbah tayi ba 'karamin daraja ya 'kara mata a idanun Anty ba, sai take jinta tamkar 'yar uwarta ta jini domin tayi abinda ba kowa ne zai iya ba a wannan zamanin da kishi ya zame wa mata tamkar ibada a zu'katan su.

*****
Teemah ma tuni ta yaye Annur 'din ta tun yana da 15months da haihuwa ganin yanda yake girma, tsayi da wayo duk lokaci guda, yana da 7 month yafara takawa, da kansa ma sai bai damu da yasha maman ba, dan wataran a yini bai fi sau biyu yake sha ba kuma ko bata bashi ba baya rikici, ganin hakan yasa Abbas yace da ita kawai ta daina bashi ma gaba 'daya ita kama ai dama gaba ta kaita dama bata son ta jima da shi abakin mama har ranta take jin tsoron kar su lalace ganin cewa Abbas nan yafi so a ilahirin jikinta shiyasa take nan nan da shi itama.

Ginin makarantar ta da Abbas yace za'a yi mata ma an kammala shi tuntuni amma a Abuja aka yi, wanda makarntar ta tsaru iya tsaruwa, sosai Abbas ya kashe maku'dan ku'da'de dan ganin makarantar ta ginu bisa tsari da daraja har an luncher shi, inda ake bayar da karatu arabi da boko daga 8am to 5pm ha'de da babban masallaci aciki 6angaren mata da maza, inda suke ajiye fannin boko 'karfe 'daya bayan sun yi sallah sun 'dan huta kuma 2:30 sai su siha fannin islamiya sosai ake horara da yara kan dukkan 6angarorin biyu.
Abbas ne ya sanyawa makarantar suna A-Z international School, kuma ba laifi makarantar ta samu kar6uwa sosai musamman da yake suna da fannoni da dama tun daga 6angaren Nursery, primary har secondary duk aciki.

Haka kuma Abbas bai manta da su Innah ba, bai sake komawa ba kam amma a duk 'karshen wata yake transfer 'din ku'di wa Rabi'u wanda yasan zai ishe su hidimar makaranta da kuma gida, kuma Rabi'u na 'ko'karin 'kiran sa akai-akai yana ha'da su da Innah ma su gaisa da ita.
Yanayin yanda yake jin ta ka'dai ma ya ishe sa sanin cewa Rabi'u bai ci amanar su ba daga abinda yake tura masa.

*****
Wata ranar Alhamis da 'karfe biyu na rana 2:09pm,
Abbas ne ya shigo gidan jikin sa uniform kaki ne da hular sa da wayar sa duk ri'ke a hannu.

A gajiye yake gaba 'daya dan haka sai ya zube a parlour kan kujera yana 'kwala 'kiran sunan ta.

Teemah iska ta hura a bakin ta ta furzar da jin muryar tashi bata so ta amsa da 'karfi har baccin da Annur ya fara yanzun ya yanke gashi daga jin tashin muryar Abbas 'din har ya bu'de idanu dayake baccin ya 'dan fara cin idanunsa sai take ya kuma mai da wa ya rufe su tasan badan baccin ba da ko ita bata isa ta riga shi isa wurin Abbas 'din ba, dan wata muguwar sha'kuwa ce a tsakanin su, itan ma shiru tayi bata amsa ba dan kar ta tashe sa tun safe be yi bacci ba sai rigimar tsiya yau 'din yake ji dashi, hatta bathroom bai barta ta shiga ba sai da ya bita sukayi wankan tare, inda da dabara ta samu da tayi masa nasa sai ta ha'da shi da abin wasa cikin bathtub daya 'dauki hankalin sa sannan ta samu ta faki idanun sa tayi wankan 'kar'kashin shower tana yi ma tana kallon sa dan kar ya lura da ita bata wanke fuska ba ma sai bayan ta d'aura towel jikin ta sannan ta wanke fuskar tata daga nan sai ta 'dauko shi suka fito.

Tsawon mintina biyar tana lalla6a shi tare da mai wasa cikin kunnan sa da hannun ta sannan ta samu baccin ya 'danyi nauyi, sai ta sau'ko daga gadon a hankali ta baro mishi 'dakun bayan ta daidaita masa 'karfin fan yanda iskan baze yi masa yawa ba....jikinta bomshot ne na blue jeans da wata 'yar 6ingilar riga mai bu'da'd'den gaba sky blue sosai tayi kyau cikin kayan kamar 'yar turawa.

A parlour ta hango shi zaune idanunsa a lumshe ya kishingi'da ga dukkan alamu agajiye ya dawo domin yanayin sa ne ya fallasa asirin zuciyar sa, 'kafafunsa kawai ya iya sa6ewa daga cikin boot 'din dake 'kafar sa baya ga haka babu abinda ya sauya daga yanayin shigar sa.

Isa tayi ta zauna daga gefen sa taja hancin sa a hankali tana murmushi, shima 'din murmushin yayi batare da ya bu'de idanu ba.
Sai da ta zauna da kyau kafin tace " Saura 'kiris ka hana min yaro na bacci da wannan ihun naka fa, da bai yi ba kuwa yau 'din zaka koyi goyo babu ruwana"

Bu'de idanun yayi ya sau'ke su a kan fuskar ta a hankali ya kuma sau'kar da idanun yabi jikinta yana murmushi yace " really?"

Itama murmushin tayi tare da jinjina mai kai sannan ta mi'ke ta 'dauko mai ruwa mai sanyi da cup dayake tasan halinsa matu'kar ya dawo gidan ruwa yake fara nema kafin sauran hidimomin su biyo baya.

Shi kam a fakaice yabita da idanu har taje ta dawo in baka sani ba zakaui zaton ko idanun a rufe suke saboda yanda ya 'kan'kansu.

Da isowanta sai ta cika mai glass cup 'din da ruwan ta mi'ka mai sai yasa hannu ya kar6a.
Chapter 160 · 0% Book details