← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 163

Sashe 88

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty kam kasa magana tayi banda hawaye babu abinda take sharewa, Abbas kansa dauriya kawai yayi beyi 'kwalla ba amma inkaga yanda jijiyoyin kansa duk suka mimmi'ke, idanuwansa suka yi jajazur take zaka fahimci halin da ke ciki da inda zuciyarsa ta dosa.

" _Yayah Mahmud ina hannunka..... guda 'dayan yake......waye ya cire maka_ ?
Teemah tasake tambayarsa tana bin jikinsa da kallo har zuwa fuskarsa.

Murmushi yayi tare da waro idanunsa akanta nan ta 'kara ganin yanda cikin idanunsa suka koma tamkar jini gaba 'daya sun riki'de sun canza launi.

Ahankali takai hannunta saman idanunsa tace " _Yayah......idanunka ma sun koma jini....Yayah......_

" _Allah ne ya min haka Fateemah kiyi min addu'ah kinji_ "
Yayi maganar da 'karfin hali domin shi ka'dai yasan abinda yakeji acikin jikinsa, 'kafafuwansa ma gaba 'daya sun sami matsala dama ana shirin shiga dashi 'dakin thearter ne a'karasa cire 'kafafun domin bazasu sake yi masa amfani ba.

Kafin hakan ne ya nemi ganin iyalansa bayan farkawarsa daga 'dan gajeran suman daya yi
shine aka shigo dasu.

Toh yanzun ma likitocin da suka ga kamar hayaniyan zai masa yawa zuwa sukayi suka ce su fita su barshi ya samu hutu.

Da kansa yace a'a abarshi yagana da iyalansa bayi son hutun komai.

Gurin shiru ko motsin kirki babu me yi acikinsu, kowa yayi tsit hatta su Fateema ba ihun kuka sukeyi ba sai de hawaye kawai suke sharewa.

Da 'kyar muryarsa ke fita amma ahakan ya dubi Anty yace " ku daina kuka mana Anty, ku daina min kuka, ba gani nan ba zan warke ai insha Allahu"

" Haba Mahmud ka dube ka fa bakaga yanda ka dawo bane?

" _Karki damu Anty! haka dama Allah yaso gani na, kuyi min addu'ah kawai kinji Anty, idan kina kuka Fateemah ma bazatayi shiru ba!_

Sai ya juya ya kalli Munnira yace
" _Share hawayenki ki daina kuka kinji, na riga na yafe miki tun lokacin dana san gaskiya, kema ki yafe min nasan nayi ta 6ata ranki abaya, dan... Allah_ _kiyafe min kinji Munnira, ban'ki auren ki dan bana sonki ba kawai de bani da burin yin_ _aure da wuri ne alokacin shiyasa, amma kun kowa ya kasa fahimta_ _ta.........._

Kai ta jijjiga masa itama Munniran tare da fa'din
" _kabar ro'kona Mahmud ni ya kamata ince kayafeni, har abada ni me laifi ce_ _agareka nasani ni kaina bazan ta6a yafewa kaina ba, domin nasan na_ _cutar da kai, ayanzu kam bani da kalmar da zan ro'ke'ka gafara_ _sai de fatana Allah ya baka lafiya Mahmud ya in ganta rayuwarka_ _kai da zuri'arka gaba 'daya_ "

Murmushi yayi mata itama 'kasan ma'koshi yace " _nagode Munnira_ "

Hawaye yaji ya sau'ka akan hannunsa, sai ya waigo ahankali ya dawo da kallonsa wurin, ganin Fateemah yayi tana ta na ta 6ul6ulo da hawaye.

Suna ha'da idanu hawayenta yasake 6ul6ulowa fiye da na 'dazu.

" _Ya...yah Mah........_
Tanaso tayi magana amma sai taji gaba 'daya harshenta yamata nauyi.

" _Shiiiiiii_ "
ya dakatar da ita yana murmushi yace
" _Maza share hawayenki kinji, kin manta nace zamu je Katsina tare_ ?

Kai ta 'daga masa alamar ehh idanunta taf da hawaye.

" _Har Abuja ko_ ?
Ta sake 'daga kanta sama.

" _Yauwa toh yi shiru kiji, share hawayenki_ "

Hawayen tayita 'ko'karin sharewa amma baya tsayuwa kamar sake turosu akeyi haka taji.

" _kinji abinda Munnira tafa'da 'dazu ko_ ?

kai ta 'daga masa.

Sai yaci gaba da fa'din " _nima ba nagaya miki ba_ _rannan_ "

Da kai kawai take bashi amsan dukkan maganarsa.

" _Toh ki yafe mana kinji, ni nasan dukkanmu masu laifi ne agareki har Anty, amma Fateemah wani abin sam ni bansan da faruwarsa ba, abakin Umar naji kuma koda na_ _tambayeki ma baki fa'damin ba kika 6oye min, bansan ta yadda zan tunkari_ _al'amarin ba saboda banji daga bakinki, kaina gaba 'daya ya kulle narasa mafita, cikin haka sai Allah_ _ya kawo Munnira ta bayyana miki komai agabanki wanda Allah yasa nima sai ya fa'da kunne na, hankalina yatashi_ _sosai Fateemah dajin sunan Anty aciki, bansan wani mataki zan 'dauka akai ba dan Anty mahaifiya tace_ _ita ta haifeni, daga 'karshe kawai sai na yanke shawaran zamu tafi mu bar_ _musu garinsu, zan 'dauke ki muyi tafiyarmu yafi amma kafin inje inda kike sai gashi yanda Allah ya maida ni, duk da haka nagode wa Allah na dayasa_ _nasan komai tunda ran numfashi na_ "

Bu'dan baki Anty tayi zatayi magana Mahmud yayi saurin dakatar da ita da fa'din
" _Karki ce komai Anty, ni komai yawuce agurina, sai de ko in Fateemah kuma itama nasan tahakura tuntuni_ "

Kan Abbas ya maida idanunsa, suna ha'da idanu sai Abbas 'din ya taho wajensa ya zauna abakin gadon yace " _sannu Mahmud Allah yabaka lafiya cikin_ _gaggawa_ "

Ido ya lumshe tare da bu'de su akan Abbas 'din yace
" _Abbas idan na baka amanata zaka_ _kar6a min_ ?

" _Me ze hana Mahmud zan kar6a_ _mana_ "
Abbas ya bashi amsa da kulawa dan gaba 'daya tausayin Mahmud 'din yabi yacika masa ziciya ya maye gurbin haushinsa da yakeji lokuta 'kalilan da suka gabata.

" _Amanar Fateema zan bar maka Abbas ka kula min da rayuwarta kaji, dan Allah....... kabata farin ciki dan tunda nake da ita bata ta6a 6ata min ba..... naso Allah ya bani tsawon rai nima in cikata da farin ciki.... amma ban samu wannan damar_ _ba Abbas, dan Allah kacika min burina kaji......_

" _bar fa'din haka Mahmud nasan da yardar Allah zaka warke, ka rayu da matar..... ka cikin farin ciki da walwala....._ "

" _Hmm_ "
kawai yace da Abbas 'din sannan yakomar da idanunsa kan " _Fateemah yace bazaki bar kuka ba ko?, in kina kuka fah bazanji da'di ba ko ba kyason in_ _warke ne_ ?

" _inaso yayah inaso ka warke acire maka duk wannan farin abin_ "!

" _Ko anciremin wannan Fateemah ai dole za'a sake sakamin wasu masu yawa ma, amma kiyi shiru kinji share hawayen ki bana son gani, in bahaka ba zan yi tafiyata in barki ke ka'dai.....,Anty kice mata tayi shiru banasan kukan nan_ !

Anty ne ta kamo ta ta share mata hawayen tace " _bar kuka kinji Fateema kukan ya isa haka_ _nan_ "

Dayaga tayi shirun ne yace mata " _yauwa Angel 'din Daddy,_ _zakuje da Abbas kinji Umar ma zai rakaku........idan kinje kice da Innah ni yanzu bani da lafiya ne shiyasa banzo_ _ba, kice mata taringa yi min addu'ah, duk ranar da na samu sau'ki zanje in dubo su da kaina."_

Teemah kam wani sabon kukan ne ya 'kwace mata tace
" _Yayah.....da kai zamuje, ni da kai zani idan kasamu sau'ki zamuje kaji, kai da kanka zaka sa mamanka_ _amakaranta kamar yanda kayi al'kawari da izinin_ ........

Tun kafin ta 'karasa maganar tari ya sar'keshi ganin haka yasa likitan cewa su 'dan fita su barshi ya huta please surutun yayi masa yawa ne"

Anty ce tafara fita sannan Munnira followed by Teemah,
Abbas kam be ko yin yun'kurin tashi ba hakama Umar da sai yanzu ma shikam yasamu damar matsowa kusa da shi.

Godiya Mahmud yake 'ko'karin yi masa saboda sosai umar yabada babbar gudum mawa arayuwarsa amma karan nan maganan yakasa fita gaba 'daya, da sauri Umar ya dakatar dashi yace karya damu basai ya gode masa ba,yace komai dayayi yayi ne saboda Allah and for d sake of there friendship bakomai ba, yace Allah ya baka lafiya Mahmud"

Lumshe idanu kawai yayi tsawon mintina uku kafin ahankali bakinsa ya furta sunan _Abbas_
kasancewar yana kusa dashi ne yasa ma yajishi da wuri sai ya amsa masa da fa'din " _gani nan Mahmud me kake_ _so_ ?

" _Abbas..........'kaina.....kir....jina_ _bayana....._

Sai ya kuma yin shiru.

" _ciwo ko_ ?

Sosai Abbas ke jin tausayin Mahmud, gaba 'daya zuciyarsa ta karye da al'amarin dan yasan Mahmud ba 'karamin dauriya yake yi ba har yake bu'dan baki yayi magana, kana ganinsa zakasan yana jin jiki sosai bayaga haka ma ga wasu munanan raunikan dayaji wanda su ka'dai ma masifa ne amma ahakan yake daurewa yayi magana.

Likitocin Abbas ya bawa guri yace su kula dashi suyi masa abinda ya dace.

Har sun juya zasu fita a'dakin sai suka ji shi yana wani wahalallan tari,
Da sauri suka koma kanshi suna yi masa sannu, idanunsa alumshe gefe da gefen idanun kuwa wasu sirarun hawaye ne yake bi ahankali.

Bakinsa duk ya bushe yayi fari fat kamar wanda yayi sati be sha ruwa ba,

" _Ab...bass_ !

" _Na'am Mahmud gani nan agefenka_ "

" _Abbas_ _inajin....tamkar.....laifina_ _ya girmama.....ka tayani ro'kon Fateemah tayafemin dan Allah"_

" _Haba Mahmud ba anwuce wannan gurin ba, ka daina fa'din haka ka_ _kwantar da hankalinka kaji, batace ta yafemaka_ _ba_ ?

Kansa ya 'daga har sau uku alamar ya tuna.

Daga nan yayi shiru, still idanunsa alumshe.

Matsawa Abbas yayi inda likitoci suka ci gaba da aikinsu, shi da Umar 'dinne suka juya zasu fita, Abbas har ya ze juya sai kuma yaga kamar bakin Mahmud 'din na motsi, sai ya dawo da sauri kusa dashi yayi 'kasa da kansa zuwa wajen bakin Mahmud 'din.

" _Rasulullah_ " kawai yaji
Sai ya 'karasa da fa'din " _sallallahu alaihi wa sallam_ " amma beji farkon abinda yace ba, sai de yana kyautata zaton kalmar shahada ya jero, daganan kuwa be sake ganin ya motsa ba, duk da yake dama ba yawaita motsin yayi ba amma yanzun daya 'kura masa idanu sai yaga kamar yanayinsa yacanja damma yanayin fuskar cike take da murmushi shiyasa ma yake 'dan jin dama dama.

Umar ne yayi saurin ankarar da likitocin abinda ke faruwa, take kuwa ya iso ya dudduba shi, ganin dayayi cewa nunfashin sa baya tare da shi ahalin yanzun yasa shi jan farin mayafin dake jikinsa ya lullu6e shi zuwa sama har kansa.

Sannan ya jiyo garesu, yanda yaga Abbas ya 'kuresa da kallo baya ko 'kiftawa yasa shi tsaida idanunsa akansa yace " _i'm_ _sorry_ ......."!

Tsam Abbas ya kasa 'dauke idanunsa daga kallon likitan hakan yasa likitan ganin cewa ko be fahimce shi bane sai ya sake cewa " _i mean Allah yayiwa 'dan uwanku rasuwa_ ".
Chapter 88 · 0% Book details