← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 163

Sashe 131

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki ta ta6e sannan tace
" _Ca6! da na ha'da ka da daddy kuwa ya ramamin nima_ "

" _Nima Zahra ta zata rama min ai akanki kuma_ "

Ranta fari 'kal tace " _wacce kenan, Zahra matar ka ko kuma Zahran 'karya_ ?"

'Dan bu'de ido yayi yace " _karya niii_ ?"

Tashi tayi tsaye da sauri dan yanda ya matso fuskar sa sanda zai yi tambayar sai ta 'dan ji tsoro.

Tana tsayen tace " _ai naji ka fa'da 'dazu_ "

Da mamaki yace mata
" _Me nace 'dazun kuma_ ?"

Ido ta 'daga sama kamar wata mai tunani tace
" _Ka....ce.....kace...._
In ina ta tsaya yi ta kasa fa'din abinda ke ranta sai ta tsaya tana murmushi.

" _Fa'da min mana inji_ ?"
Yayi maganar yana kallon ta.

Bazata iya maimaita masa ba saboda kunya takeji dan haka sai ta matsa zuwa bayan sa da sauri ta sa'kalo da hannayen ta a wuyan sa ta sar'ke su tare da kwantar da kanta akan kafa'dan sa tana cigaba da murmushin ta a kunne tara'da masa " _kunya nakeji ni_ "

Murmushin kunyan iyayin nata yayi sai yace " _rufe idon ki to zaki daina jin kunyan sai ki fa'damin naji_ "

Kai ta juya a kafa'dan sa alamar "ah ah"

"Hmm" yace sannan ya tambaye ta
" _Kunyan wa kike ji anan 'din ni ka'dai ne fa bawani ko ni 'din kike jin kunya_ ?

" _Ummm_ "
Tace atakaice

Sai yace " _naji to, ni bari in fa'da miki tunda banjin kunyar ki, nace Allah Allah yayi wa matata_ _Zahra albarka ya haskaka rayuwar ta ya faranta mata kamar yanda ta_ _faranta min ko haka nace ba_ ?"
ya 'karashe da tambaya.

Teemah kuwa tace
" _Hakane amma ai dayawa ka fa'da 'dazun_ "

Dagangan yace mata
" _d'azun dawani lokaci kenan ni na manta wannan ka'dai nasani......._ _oww na tuna 'dazu lokacin da......_ "

Da sauri Teemah ta 'dage gira sannan ta 'daga hannu ta kai bakin sa ta rufe dan kar ya fa'da.
Ahankali bakin ta dai-dai kunnan sa tace " _Yayah kai baka jin kunya ko_ ?

Kai ya jijjiga mata tare da fa'din " _inaji mana amma banda na matata_ "
Hannu yasa ya dawo da ita ta gaban sa idon su cikin na juna yace " _wato ke ana baki sa'ko ma kina tsayawa 'diban gulma ko_ "?

Zara ido tayi tace
" _Ni kuma gulma Yayah ni banyi gulma ba_ "

Sai yace
" _Wanda kikayi yanzun fah, inba jin gulma ba ya akayi kika san abinda na fa'da duka_ ?"

Rintse ido tayi da 'karfi tana dariya tafa'da jikinsa ta rungume shi.

Murmushi yayi shima tare da fa'din " _silly girl_ " sannan shima ya saka hannayen sa ya rungume ta, a kunne ya ra'da mata " *i luv u Zahraty* "

Batayi magana ba sai ta 'kara yin luf ajikinsa ji take tamkar su kasance a haka har abada, wani tsuma take jin zuciyar ta nayi game da shi, sabon yanayi ke shigan ta wanda bata bata ta6a jin irin hakan ba sai yau 'din nan, ita da kanta tasan cewa tana so da 'kaunar mijinta sosai fiye da yanda mafarkin ta yake bata.
Kalmar 'daya fa'da 'din kuwa ji take shine mafi soyuwan kalmar da tafi mararin son ji daga gare shi koda kuwa zasu dawwama ahaka ne bazata damu ba.

Abbas ma kansa wannan moment 'din yatafi dashi he wish da ace Rivers zai koma da babu abinda zai hana shi 'dauke matar sa su tafi, shi ka'dai yasan yanda yayi kewar ta a wata 'dayan nan, bai ta6a zaton zaiyi missing komai nata har haka ba sai daya tsinci kansa acikin damuwa sosai da rashin ta, yarinyar ta, rashin jinta, 'kun'kunin ta, 'dan 'karamin bakin ta na rashin kunyan nan, jikinta da komai nata kafin ya ya gama amincewa zuciyar sa cewa itace farin cikinsa, haushin 'kin binsa datayi kuwa har yaso ya ninka haushin daya shiga lokacin da aka bawa marigayi ita suka tafi.

Yanzu kuwa da yake da ita a gidan sa take kuma kwance akan 'kirjin sa sai yake jin kaf duniyan nan bayaga ahalin sa baya jin akwai abinda yakai girman matsayin ta a zuciyar sa.

*4:30pm*
Yabar gidan domin flight 'dinsa na zuwa Ekiti 'karfe 5:00 ne inda suka rabu da matsananciyar kewar junan su afili da kuma zu'katan su.

5:28pm Hannah ta dawo gidan sai taga Teemah cikin annashuwa ko bata bu'di baki ta fa'da ba amma farat 'daya zaka gane cewa yau walwalar ta na daban ne, musamman idan ta tuna kalmar I LUV U daya fizgo daga bakin sa 'dazun hakan ka'dai ke sata sakin murmushi, jin kanta take sosai tana jin tamkar tafi kowa she feel very exiting, wai Yayah na son ta.

Hannah kam dayake bakin ta baya gani ya 'kyale sai tace da ita " _albishir 'din menene ya iso ki haka da kike irin wannan walwalar_ ?"

Da sauri tace da ita " _uwar sa 'ido kawai........to Yayah ne yazo yau_ "
Tayi maganar da cikakkiyar murmushi kwance akan fuskanta.

Hannah 'dan gwalo idanu tayi tace
" _dan Allah?_
_Kice intattara in koma kunkumin uwata_ "
Hannah tayi maganar tare da mi'kewa tsaye dayake dama a parlour suka zauna.

Dariya ka'dan Teemah tayi tace " _sai ki je 'din kuma ai, abinda har ya tafi ma_ "

" _Haba dan Allah dagaske, shi kuma kamar ana koran sa haka?_
Hannah tayi maganar da mamaki.

Teemah kam hankalin ta kwance ta bata amsa da fa'din " _Ekiti state ya nufa dama yana kan hanya ne shine fa yabiyo ta nan 'din"_

Hannah komawa tayi ta zauna da jin abinda Teemah tace, sai data zauna sannan da sigar zolaya tace " _Yayah yazo duba amarya kenan_ "

Teemah cewa tayi
" _To ko laifi ne yin hakan_ ?"

" _Haba! wace ni ince haka? Ai ban isa ince laifi bane dan ban san sirrin dake 6oye bayan wannan gagarumar fara'ar_ _ba, abinda kawai nasani shine rai yasamu abinda yake so that's all_ "
Fa'din Hannah kenan tana watsa hannu sai Teemah ma tace " _toh ya za'ayi ne Hannah abinda yafi haka ma inajin idan_ _nayi ai ba laifi bane, mijina ne fah Hannah tsawon wata guda bangan shi ba..._
" _hmmm bazaki gane yanda nayi kewar sa bane yarinya_ "
Ta 'karashe da murmushin tsokana.

Hannah ma murmushin tayi tace " _ke kika so hakan ai, amma yanzu da kika ganshin fah_ ?

Da sauri Teemah ta tare ta fa'din " _sai naji tamkar kar yatafi wallahi_ "

Baki Hannah ta ta6e tace " _ehh lallai yarinya kin hau layi Yayah ya koya miki halin sa ni dai ba ruwana_ "

Dariya ma tabawa Teemah wanda cikin dariyar ta furta " _dai-dai kenan, ai baki san wani abu ba Hannah? har fa da kyautar I LUV U na samu yau daga wurin sa_ "

Ido Hannah ta zaro tana dariya tace " _kice dara taci gida kenan_ ?"

Dariyan sukayi dukkan su, suka sha hannu cikin so da 'kaunar junansu.
(TeemHan)

*****
Yanzu kam sau 'daya yake 'kiran ta a duk lokacin da ya samu dama wata rana kuma ma ko 'kiran nata baya yi.

Haka kuma salon 'kiran nashi bai canja ba sai ma abinda ya ragu dan yanzun baya fin 2-3mins kullun idan ya 'kirata saboda abin da yake gabansa, daga gaisuwa baya jan magana ahakan ma yafi yin 'kiran da dare wani lokaci ma har sai tayi bacci kafin ya 'kira da safe ne kawai take ganin missed call.

Tana kuwa jin haushi sosai idan hakan yafaru kuma ko ta 'kira shi baya 'dagawa har sai lokacin da ya ga dama sannan sai yayi calling nata back, daga baya ma sai ta ha'kura ta daina 'kiran nasa gaba 'daya.

Shikuwa Abbas rashin sakewa da ita a wayan ya samo asali ne da kasancewar Hannah na tare da ita, sam baya iya tambayar ta komai daga yaji lafiyar ta da damuwar ta shikenan dan baya so yayi wani abinda zai sa Hannah ta ringa yi masa kallon wani abu daban.

Satin sa shida (6weeks) A Ekiti yanzun amma sau 'daya tak yabata daman zuwa gaida Ummah tun farkon tafiyar sa daga nan bai 'kara barin taba, takan yawai ta mamakin hakan aran ta sau da dama Hannah ce ke 'dan wayar mata da kai akan wasu abubuwan da suka shige mata duhu.

Damuwar ta 'daya yanzun shine yanda 'karfi da yaji ta zama chop-chop daga wayewar safiya zuwa dare tana cin abinci a'kallah kusan sau shida ko ma fi, wani lokaci har cikin dare ma yunwa na damun ta wani lokaci dole sai ta tashi ta nemi abinda zata saka abakin ta koma wani iri ne kafin take jin dai-dai.

Abin na damun ta sosai musamman ma da taga sai 'kara huruwa takeyi tasan bakomai ne yake sata yin 'kiban ba sai lodin data ke yawan yi acikin kwanakin nan, bata so amma dole zuciyar ta ke tilastata yawan cin abincin.

Gashi wani sa'in sai ta kasa bacci da dare sai dai tayi ta gadin Hannah har sai ta kusan raba dare kafin bacci ke 'daukan ta.

Takan yawaita blaming sabon salon cin abincin datake yi yanzun game da komai dan aganin ta duk shine yake sata yawan baccin dama shiyasa ta tsani cin abu mai nauyi ita tun asali, Hannah na tafiya school itama take yin bacci dayake sai sun kammala dukkan ayyukan su kafin Hannah take wucewa shiyasa take iya yin baccin ganin babu wani aiki a gabanta, dan ma baccin nata baya tsayi dududu in tayi dayawa shine takai 30mins tana baccin.

Lokacin data lura da yanda ta 'kara haske boobs 'din ta ma ya 'kara huruwa shima yawani cicciko bakin yayi ja sai abin yafara bata tsoro ma data yiwa Hannah mitan hakan sai Hannah tace " _ki bari idan Yayah ya dawo sai ki sanar dashi in ciwo ne zai nema miki magani ai, in kuma kiwona ke da kyau kinga sai in samu kyauta da lambar yabo daga wurin sa_ "

Hannah na maida abin wasa kullum while Teemah kam abin har ranta yake damun ta.
Chapter 131 · 0% Book details