← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 163

Sashe 39

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" tasamu kenan,
" a' a kai bakomai babu wani abinda yasamu" Mahmud ya dakatar dashi da fad'in haka.

Sai Abbas yace
" kuma kaga nad'anyi tafiya yanzu haka ina borno inajin kuma anjima kad'an za mu wuche".

"Shikenan toh nima yanzu nake shirin komawa sai dai da k'yar mu had'u may be kafin na iso kunwuce kasan nazo lagos 2days back"

" Haba mana 2days kuma har zaka koma?"

" ehh kamanta bautar k'asata nakeyi ne?, Kabari insha Allahu idan na sauk'a zamuyi magana."
Mahmud ya k'arashe maganar da d'an gaggawa dalilin hango mahifinsa dayayi
ya fito da shirin zuwa office dan hannunsa rik'e take da briefcase d'insa, bayan Abban kuma Anty ce itama ga dukkan alamu fitan zatayi.

Yana yanke k'iran suka had'u dayake dama ba wani tazarar kirki bace atsakaninsu.

Suna had'uwa sai ya gaishe dasu, Anty yafara gaisarwa dayake sun riga da sun gaisa da Abbah tun a hanyar dawowa daga masallaci sai dai ko gaisuwa ta biyu.

Antyn ma adak'ile ta amsa masa yayinda Abbansa ya cira hannu yah mik'a masa sukayi gaisuwar muslunci yana murmushi yace "harka shirya kenan"

" ehh Abbah inajin daganan ma sai airport"

" Abbane yace bakace tafiyar sai 11:30 ba?

" ehh zanbi wajen Jabir ne kafin na wuche".

" alright ba matsala Allah ya tsare ya bada sa'a"

"Ameen- Ameen Abbah".

Duk maganar nan da sukayi Anty kauda kanta gefe tayi tamkar bata jinsu, Mahmud kuwa yana gamawa da Abbansa ya dawo gareta yace mata zai wuche .

Tunani tafara aranta wai dama dagaske Mahmud ayau d'in zai koma?
Kar dai duk akan maganar Munira ne ya yanke wannan hukuncin? Toh idan yakoma ayau ai tamkar ya dakatar da batun auren ne, while itakuma dawuri takeso ayi.

Koda ta tambayeshi dalilin tafiyar sai ya ce mata akwai aikin dake jiransa ne acan shiyasa.

Sababi tafara ranta a matuk'ar 6ace take fad'in
" aikin banza aikin wofi, harni zaka nuna wa wani aiki, ince dai service kajeyi acan d'in ba neman aiki ba da har zaka min iyayi anan.

Cewa yayi " shi d'in dai service d'in nake fad'i bakomai ba Anty".

Bud'e baki tayi tacigaba da masifanta inda acikin masifar tace ai akwai mutane dayawa da wannan bautar k'asan duk ba yinta suke ba why not shima ya tura musu ko nawane suke buk'ata inyaso yayi zamansa agida basai ya koma ba"

Shikuwa yace a'a yafi buk'atar yayi bautan dai kodan saboda ya jaddada kasancewarsa cikakken d'an k'asa.

Aikuwa sai tacigaba da fad'in wai Mahmud ya raina ta sam baya bin maganarta dan me zai ringa ja inja da maganarta abinda daa ba haka yake mata ba , kenan ya je yakoyo banzan hali zai zo ya rink'a yi mata sai kace ba ita ta haife shi ba"

Kallonta suke yi daga Abbah har Mahmud suna mamakin masifar tata ta dosa da kuma dalilin yinta.

" wallahi indai kace ni zaka raina akan wata banza zaka..........

Da k'arfi cikin tsawa Abbah yace " shut up maryam....,stop it,how dare you zaki ringa fad'in hakan infront of me!"...

Yatsansa ya d'aga sama yayi nuni da gefensa kana yace " waccen d'in fah da kike so ki zaga 'yar uwata ce!, gudan jinina!!, ita kad'ai nake dashi !!!meyasa baki gane abu ne ke,.......yatsan nasa ya dawo dashi saitin Antyn sannan yace " kinsan Allah, idan nak'ara jin kin fad'i ba dai dai
ba akan Kha.....kha....di...........

Sai yayi shiru yaja tsaki.
Hannun Mahmud ya finciko ya yi gaba dashi har gurin da driver ya ajiye motar da Abban zai fita da ita.

Nan yace Mahmud yashiga motar sai dayaga yashiga sannan Abban shima yaxaga yashiga.

Mota d'aya suka shiga suka tafi suka bar Antyn tsaye agurin tamkar andasa ta.

Mahmud kuwa hamdala yake ta yi azuciyarsa duk dama ba hakan yaso ba, hak'ik'a duk d'ah nagari bazai so ya ringa kallon husuma na tashi acikin gidansu tsakanin mahaifansa kuma yaji dad'in hakan ba.

Amma shi kan sai yaji farin ciki kad'an bawai dan Abbah yayiwa Anty masifah ba " a'a "
Canjin daya gani azahiri tattare da mahaifin nasa shine yasashi farin ciki.

Lalle Allah maji rok'o ne yakan amsa addu'o'in bayinsa aduk lokacin daya so hak'ik'a yau ranar farin ciki ce ga Mahmud domin yau yaga mahaifinsa na acting as Magidanchi cikakke mai fad'a aji acikin gidansa, sa6anin baya da komai in za'a yi baya ta6a tankawa koda kuwa abin ba dai dai bane sai dai yayi shiru yasa ido yana kallo.

Abbah office d'insa ya wuche da Mahmud sukayi zamansu aciki suna d'an ta6a hira kamar bashi bane yayi masifah d'azun, ayyukan dake gabansa ma dakatar dasu yayi yah bada hankalinsa ga d'ansa suka fahimci juna sosai anan ne Abban ya nemi jin asalin ra'ayin Mahmud akan waccen yarinyar Mahmud kuwa bai 6oye masa komai ba ya sanar da shi akan sam baya so saboda yarinyar yaga kamar bata da tarbiya kuma ma shi ba yanzu zaiyi aure ba sai zuwa gaba.

Kwantar masa da hankali Abbah yayi akan batun auren da baya so d'in kuma yace insha Allahu babu mai yi masa dole matuk'ar yana numfashi, amma batun bayanzu zai yi aure ba yama daina fad'i dan aure lokaci ne idan kuma lokacinka yayi babu makawa sai anyishi koda kuwa ba'a so yana faruwa ne tamkar mutuwa.

Godiya sosai Mahmud yata yiwa Abbahn nasa take kuwa sai yaji duk wani damuwarsa ta kau dama dan haka yake so ya had'u da Abbas saboda idan ya yi magana da mutun akan matsalarsa yakanji kwarin gwiwa sosai sa6anin barinta azuciyarsa.

Magabar dayayi da Abbansa sai yaji yama fasa sanar da Abbas maganar tunda Abbansa yah bashi assurance mai kyau akai so yanzu baya buk'atar sake ji, komai daga wani.

'Karfe goma daidai Abbah yak'ira drivern office d'insu yace ya kaishi airport d'in saboda hold-up ma yasan kafin su isa lokaci zaiyi yak'ara da fad'in ya k'ira jabir d'in yabashi hak'urin rashin had'uwarsun yace masa Abban ne ya rik'esa a wurinsa.

Mahmud
Yana dariyah yace " haba Abbah bakomai zanyi masa bayani insha Allahu"

Daganan sukayi sallama Abbah yayita masa addu'a har suka rabu.

Comment vote and share pls🤞🏻

*Salmerhn ku ce**😍
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

HAPPY ANNIVERSARY
sis HUSSAINAH B ABUBAKAR (Mrs Abubakar)
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Ya Allah, turn our sadness to happiness,frowns to smiles,hate to love, weaknesses to strengths, and cleanse us of our shortcomings.

🅿 *34*

Tun lokacin da Abbah ya fara yiwa Anty tsawa akanta taji duniyar ta tsaya mata cak, wani duhu taji ya mamaye ilahirin kanta har cikin k'wak'walwarta gaba d'aya, wasu abubuwan daya fad'a d'inma bata jisu da kyau ba ido kawai ta tsurawa fuskarsa yayinda yake mata masifar inka ganta alokacin zaka zaci hankalinta da nutsuwarta ta mayar akansa don ta fahimci me yake nufi da kyau, amma azahiri ba haka bane.

Anty ta kusan minti goma agurin tsaye tana tunani abin ne takeji wani banbara k'wai it seems different, kamar almara............wai yau ita Abbah ke yiwa tsawa akan abinda be taka kara ya karya ba.

Jijjiga kai tayi da k'arfi take sai tunaninta ya dawo daidai, gani tayi ba kowa agabanta ita kad'ai ce tsaye awurin, koda ta kalli gefe da gefenta ma duk haka tagani bakowa,da sauri ta juya takalli inda motar Abban ke ajiyeh sai taga wayam bakomai, alamar sun ma bar mata gidan gaba d'aya batare data sani ba tsabar yanda ta shiga zurfin tunani.

Ranta taji ya matuk'ar 6aci,wani 'kullutun daya kullera azuci ji tayi tamkar ta kurma ihu ko zai waraware, ahankali tafara d'aga k'afafunta tajuya da niyyar shiga cikin gida saboda fitar ma jitayi tafice mata arai.

Kan kujera taje ta zube sharab tamkar wata majinyaciya, sam takasa yadda cewa wannan ABBAn mahmud ne, ji take kamar an exchanging mata shi ne gaba d'aya, inkuwa wannan mutumin da kuma wannan al'amarin daya farun ya kasance gaskiya to kuwa hakika zama bai ganta ba.

Bazata ta6a bari aci nasara akanta ba matuk'ar tana numfashi,kuma nan take tayiwa kanta alk'awarin tarwatsa rayuwar duk wani mai shirin yiwa aikinta _zagon k'asa_ (khadija candy).

Tayi alwashin koda waye ke yi mata hakan sai taga bayanshi sannan wannan auren data fara magana akansan bata ga uban daya isa ya hanasa faruwa ba matuk'ar tana numfashi, ada bata d'auki al'amarin da wani girma sosai bama, saboda kawai tana tunanin zata lalla6e shine ahankali ya amince ya auri Muniran tunda ita ta nuna tana sonshi, amma yanzu ji takeyi aranta kodan abinda Abban Mahmud yayi mata ayau d'in sai ta bawa duk wani mai shirin shiga tsakaninsu kunya, sannan kuma daga baya ta kuma tarwatsa shi kamar yadda yafara had'a mata hargitsi acikin gida.

(Kunsan shi me yin abu akullum shi tunaninsa kowa ma yanayi ne, gani suke kamar duk abinda yasame su toh yi musu akayi, gaba d'aya mantawa sukeyi da k'addara)
Allah ubangiji kasa mufi k'arfin zuk'atanmu _AMEEN_ .

Koda Mahmud ya koma damaturun babu wani abinda yakeyi saboda already ya gama abinda zaiyi tun kafin yaje lagos kwanaki.

Abinda ANTY tace yayi d'in batasan yayi hakan tun kafin ta furta ba,so yanzu bawani zuwa wurin bautan k'asa daya keyi zamansa yake kurum agida, sai dai suje yawo, ko suyi karatu suje ziyara inda suka sani idan ta kama,wani lokaci kuma daddyn Teemah yajashi suyi tafiyah tare.

Yakan d'an ziyarci wajen dayake service d'in amma sai lokacin daya ga dama, kuma zuwan ma yana zuwa ne bawai dan yayi wani abu ba kawai yana zuwa ne dan ya san meke faruwa awurin kar shirun yayi yawa.

Wani lokaci acikin ransa sai yaji cewa bai kyautawa Anty ba daya k'i zama awurinta, yasan amatsayinta na mahaifiya dole tana buk'atar sa akusa da ita musamman ma daya kasance shi kad'ai ALLAH YA BATA dole tarink'a jin kewar d'anta.

Amma sam bazai iyah zama a Lagos ba yanzu, sosai yagaji da fitinar Anty, bata k'aunar azauna lafiya ita sai k'ak'ale-k'ak'ale.

Wannan dalilin ne yasa yaji zamansa a damaturun yafiye masa can tunda mahaifinsa bai hanasa ba.
Chapter 39 · 0% Book details