Sashe 14
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matar Hassan kuwa ta haifi d'a namiji Hassan sai ya maida sunan mahaifinsu wa yaron wato _Muhammad_ ,sunyi matuk'ar farin ciki adangin gaba d'aya dan mahaifinsu mutumin kowane bade taimako ba,tun daga lokacin suka fara k'iransa da suna _Abbas_.
Zahra kuwa lokacin dazata haihu tarasu daga ita har y'ar data haifa babu wanda yayi rai acikinsu.
Hak'ik'a wad'an nan mutane sunga ikon Allah sai dai fatan Allah yajikan magabata .
"Ameen"
Yusuf shikada'ai wannan karon ma yaje ta'aziyar Zahra a Gombe,dan matarsa cikinta ya tsufah sosai.
_Share and comment_ _pls_ 🤞🏻
*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_In dedication_
_2 sister Safiyyah Aliyu Wakili. 😍
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
No need for revenge. Just sit back & wait. Those who hurt you will eventually screw up themselves & if you are lucky, God will let you watch.
🅿 *14*
Bayan rasuwar Zahra baifi da 3 weeks ba matar Yusuf ta haihu,ta haifi d'a namiji mai kama da ubansa sak,yaro kyakykyawa dashi,tun da Khadija ta ga yaron nan ya shiga ranta sosai dan dama ita kad'ai ke rayuwarta bata abokin hira inde tana gida,
dan matar yayanta ba wani sake mata fuska take yi ba asalima shiyasa tun da aka haifi yaron nan farin ciki yacika ta,
Atunaninta zata samu abokin yin hira da wasa.
Ranar suna yaro yaci suna Mahmud,akayi shagalin suna aka watse,
Bayan anyi suna ne kabiru yazo ganin jariri,alokacin kuma yaron yana tare da Khadija ne so da yusuf yashigo da zummar kai wa abokinsa yaron sai ya gansa a hannun khadijan,
mahaifiyar yaron kuma tana bacci,kawai sai yace ta kaiwa Kabiru mahmud d'in yana can d'akin bak'i bari zai watsa ruwa yanzu,toh ta ce tare da d'aukan mayafinta tafita daga parlourn.
Da sallamarta ta shiga d'akin ba'kin,daga ciki ya amsa mata
shiga tayi kanta a'kasa ta isa har inda yake zaune ta mi'ka masa yaron.
Kar6ansa yayi amma idonsa nakan fuskarta ganin ta'ki ko ha'da ido dashi.
Juyawa tayi da niyyan barin 'dakin sai ya dakatar da ita yace tazo ta wuce da Mahmud d'in shi sauri yake y yanzu zai wuce,dawowa tayi kusa dashi ta tsaya,tsayuwar minti 3 zuwa hu'du tayi sai ya mik'a mata yaron bayan ya masa addu'a a kunnensa.
Leda ya sake mik'a mata a nan ne ta d'aga kanta ta kalle shi suka had'a idanu,da k'arfi ta gyara zaman yaron da ke ri'ke a hannunta,dan ji tayi kamar ze su6uce mata.
Dawuri tayi 'kasa da idanunta ta maida kallonta ga mahmud da ke 'dan motsawa saboda yanda ta matse shi a jikinta.
Sake mik'a mata ledar yayi tare da fad'in "kayan yaro na ne aciki naga kina wani tsorn kar6a"
Hannun ta d'aya ta mik'a ta kar6i ledar sannab tajuya,sai data fara tafiya kafin tace "angode"
Dan alokacin data kar6an idan akace dole sai tayi magana ma toh kuwa da sai de tasa kuka,dan ji tayi zuciyarta ta tsinke sosai da suka had'a idanun dashi,da zai lura ma da ya fahimci irin yanda jikinta ke rawa sosai.
koda ta koma d'aki kuwa rasa mai yake mata da'di tayi,shiru ta zauna tana tunani
tunanin da ita kanta bata san na menene ba.
Haka tasa Mahmud d'in da kayan agaba ta tsura musu idanu,kukan Mahmud ne ya fargar da ita,dawuri ta tashi ta 'dauke sa tare da ledan da niyyan ta kaiwa Mahaifiyarsa shi.
Ha'duwa sukayi a kofar shiga parlournta,tana ganin su sai ta juya ta koma ta zauna,khadijan ma sai ta biyo bayanta
Saida ta zauna sannan tafara fad'in
"Daman zaman me kike min da yaro bayan kinajin irin kukan da yake yi tun 'dazu dan salon rashin imani bazaki kawon shi ba"
Tana kar6ar shi ta 'karasa maganar.
Karkata kanta tayi gefe sannan tace
"Ayyah Anty yanzu fah ya fara kukan shine na kawo shi"
"Dallah ni rufe min baki,wawuya kawai"
Antyn ne tayi wannan maganar tana 'ko'karin sawa yaron mama abaki.
Ajiye ledar tayi tana shirin juyawa ta fice tajiyo muryar Antyn tana fad'in
"wannan fah malama zaki ajiye min abu batare kinmin wani bayani ba."
Tsayawa tayi amma bata juyo ba tace "na Mahmud ne yah Kabiru ne ya kawo masa"
Tsaki Antyn taja batare data sake magana ba,domin ita asali jininta bai wani ha'du dana kabirun ba,kuma haka shima,shiyasa ko yau d'in ma dayazo bai nemeta dan su gaisa ba.
Yusuf dake shirinsa acikin 'daki yanajin duk abinda suke fa'di amma bai kulasu ba.
Ita 'dinma bata san yafito daga wankan bane da bazata yi wa khadijan fa'da ba.
Sai da ya gama shiryawa sannan ya fito,kallon da ya mata ka'dai yasa tagane yaji abinda ta yiwa Khadijan.
Saboda a idonsa bata ta6a nuna wa khadijan tsana sai dai in abayan idonsa,saboda yanda yake nuna mata muhimmancin Khadijan a wurinsa.
Sosai tasha jinin jikinta,amma dayake ta riga ta yi nisa kuma tasan halin sa sai ta watsar da batun kawai.
Rakiya yayiwa abokinsa wani wuri kuma daga can ma yayi wucewarsa Gombe.
Yusuf sai da yamma lis yadawo gidan,dayake bashi da ri'ko sai bai dawo da wani 6acin rai ba,amma still abun yana ransa hakan yasa yamata maganar anutse,daman shi in abu yafaru adaidai lokacin yafi nuna 6acin ransa,amma in aka d'an 'dauki lokaci toh shi kenan 6acin ran nasa ya kau.
Kamar de yanda ya kasance yau d'inma,atake kuwa ta nuna masa ai yau 'dinma bada niyyah tayi ba kawai haushin kukan da taji yaron yanayi ne shiyasa tayi mata fad'an.
"Ni dai banaso pls ki kiyaye kinji"
Sai ta 'daga masa kai alamar taji.
Kad'an daga cikin irin
rayuwar da Khadija takeyi kenan agidan yayanta tun bayan rasuwar mahaifiyarta,bata da sukuni ko ka'dan agidan dan ma tanada ha'kuri da kau da kai ga abubuwa.
Aikin gidan kaf ita ke yinsa,ga rainon Mahmud data riga ta saba da shi,ga masifah da hantara idan abayan idon yayanta ne.
Islamiyah kuwa tun haihuwar Mahmud bata 'kara zuwa ba dan babu lokaci,bokon ma da 'kyar take samu taje ahakn ma kusan kullum sai tayi latti.
Kuma a kullum sai ta dawo daga makarantar take d'aura abincin rana,dan babu mai yi Antyn bata yi,toshuwar da suke zama tare kuwa ba lafiyar idone da ita ba balle ta ringa yi musu girki,ga wankin kayan yaro duk tara mata akeyi idan ta dawo take wankewa,ga 'daura ruwan zafi,ita zata 'daura idan yayi ita zata ha'da ta kai ban'daki sannan ta dawo ta ha'da na jariri ma ta kai wa tsohuwa.
Alhaji muhammad hanata zuwa wankan gida yayi yace tayi zamanta a gidanta yafi,sai ya 'dauko wata babarsa daga kauye yace su yi arba'in d'in tare.
Wankan jariri kawai tsohuwar keyi,dan ko wankan mai jegon ma Anty da kanta takeyi.
Alhaji muhammad ko mahaifiyar Antyn ma hanata zuwa gidan yayi,acewarsa baya son fitina.
Koda tace zata zo bayan da akayi suna ma sai ya ce sai dai zuzo tare da ita,haka ya sako ta agaban mota suka zo,basu wani jima bama ya ce su koma gida.
Haushin hakan yasa bata 'kara maramarin cewa zatazo d'in ba.
Sosai zaka tausaya wa Khadijan agidan,idan ka ganta.
Amma ita hakan bai wani dameta ba dan tasan komai lokaci ne komai yanada 'karshe.
Babu irin ha'kurin da batayi ba da matar yayan nata har suka gama kwana arba'in d'in,
Akwai ranar da zazza6i ya damu Khadijan harta je makaranta ma sai akace ta dawo ganin yanda jikin nata yayi zafi sai kakkarwa takeyi,Antyn ne da kanta ta 'kira yayan khadijan tasanar dashi cewa Khadijan ta dawo gida da zazza6i,yanajin haka kuwa ya garzayo ya nufoh gida,asibiti ya kaita da gaggawa mafi kusa dasu aka duba ta aka rubuto musu magunguna da allurai,kafin suka dawo gida.
Fita yayi bayan ya dawo da ita gidan,yakoma ya siyo mata magani tare da kayan marmari,da kansa yazauna ya bata maganin tasha daganan yace maza ta kwanta tayi huta,tana kwanciyah sai bacci ya 'auke ta,tun a baccin tafara gumi
cikin ikon Allah kuwa tana tashi a baccin tajita garau kamar ba ita ba,ganin hakan yasa Anty tace to ta goyi Mahmud tunda ta warke ita sai tayi girkin saboda yau 'din rigima shima yakeji dashi.
Aikuwa tana goyashi yafara ihu yana zille-zille dan daman shi basan goyo yake ba.
Kamar an jeho yah Yusuf gidan sai gashi ya yi sallama,cikin mamaki ya sake ledar da ke ri'ke a hannunsa ta fad'I ak'asa
"Me nake gani haka ?
Yafad'a da fuskar mamaki tare da nufowa inda take tsayen.
"Sannu da zuwa yayah" tana murmushi tayi maganar.
Hannunsa ya 'daga mata "ba wannan na tambayeki ba ni"
"Khadija yaushe jikin naki ya sau'ka dahar zakiyi goyo"
Baki da hankali ne?
Fusata ya sake yi ganin yanda yaron yake zizzille wa abayanta har yana 'ko'karin kada ita.
"ina mamar tashin take ?
"Tana kitchen ne yayah tana girki shiyasa na goyeshi"
Ta fa'da tana me 'kara jijjiga yaron,abinku da me zazza6i,kuma daman zazza6i ya iya yin lamo kamar ya sau'ka nan kuwa yana nan daram, take khadija tafara jin 'karfin ta duk yayi low sai ta fara jin jirijiri,aikuwa caraf yah yusuf yah ri'keta dan ganin ta fara yin alamun fad'uwa,kunce goyon yayi daga bayanta ya zaunar da ita da kyau,tacigaba da maida numfashi.
Kitchen d'in ya nufa da yaron ahannu,ranshi duk ya gama 6aci,a ganinsa wannan ai rashin imani ne dazata ha'da yarinya da goyo bayan tasan ba lafiya ne da ita ba ga shi Mahmud 'din ba laifi akwai auki dayake baruwa ake basa ba _baby_ _friendly_ suke masa shiyasa yazama wani 6ukeke dashi.
Ranshi a6ace ya isa kitchen d'in,suna ha'da idanu ya sake mata wata muguwar harara
take jikinta yayi sanyi