← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 163

Sashe 34

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ta ankara sai taga har ankusa watsewa gaba d'aya domin d'ai d'aiku ne kawai suka rage dan dolenta tafara tafiyah da niyyar cimmah way'anda suke gabanta su had'a hanya amma taku biyar me kyau batayi ba sai kawai taga mutun tsaye agabanta yana murmushi, kallonsa ta tsaya yi da mamaki hankalinta kuma yana ga wad'anda takeso su tafi taren daya fahimci haka sai ya d'an k'ara matsowa kusa da ita hakan da yayi sai ya hanata ganinsu ma gaba d'aya sanasiyyar katangan ta yayi musu.

" kiyi hak'uri ya kad'ai nakaiki gida"

Yafad'a yana kallon fuskarta.

Muryarta na rawa tace" awani dalili".

" masoyi"
yabata amsa atakaice.

Da mqmaki ta d'ago kanta ta kalleshi.

"Koba haka bane?
Yasake tambayar ta.

Bata bashi amsa ba illah hanya da fara k'ok'arin nema dan ta myi wucewarta.

Amma mutumin ya hanata wucewa domin duk wani motsin da zatayi sai shima ya motsa ya kuma tare gabanta.

Dan dole tasake tsayawa ta wurga masa harara tare da fad'in " wai me kake buk'ata ne"?

" ki saurareni"!
Kauda kai tayi gefe cikin fushi ranta inyayi dubu toh yau jitake ya6aci saboda mutumin nan sam ta tsami hakan dayayi mata ko tace yake kanyi mata.

Shikuwa ganin hakan da k'warin gwiwarsa yaci gaba da fad'in.............

Kamar yanda na ta6a fad'a miki sunana Imran dan nasan kin manta tunda ba damuwa akayi dani ba.

Kuma ni ba a unguwar nan nake da zama ba, nazo ne duba wani fili sai Allah yasa naganki kuma kika kwanta min araina duba da yanayin nutsuwarki.

Dafatan zan sami kar6uwa kodan mu k'ara fahimtar juna da kyau dan ni ji nake nasamu matar aure nagama.........

Murmushin takaici Teemah tayi wanda ya tsaya mata a kan le6e kawai....aranta tace su matar aure manya!

Horn sukaji daga gefensu take dukkansu suka kallo gurin, Teemah naganin motar gidansu ne tatafi da sauri tana hamdala wa mahallici.

Bata kula da mummy acikin motar ba sai da ta shiga ta ja marfin motar ta rufe kafin ta lura da mummyn.

Innalillahi wa innah ilaihir raji'un tafad'a azuciyarta dan yau kam tasan me rabata da mummy sai Allah.

Baki ta bud'e da niyyar yin magana sai mummy ta dakatar da ita da fad'in " waye shi "?

" nima fah ban san shi ba mummy"

K'ura mata idanu mummyn tayi tana karantar yanayinta afili zaka fahimci rashin sabo da hakan da batayi ba ga dukkan alamu tilasta ta tsayuwan akayi kodan ganin yanda ta taho da sauri daga jin horn d'in mota duk da bata ma san wake cikin motar ba balle tace danta ganta ne, amma hakan bazaisa takasa yi mata fad'a ba ko dan saboda ta k'ara tsare mutuncinta a matsayinta na 'ya mace. Wannan dalilin ne yasa mummyn ta d'ago hannunta tare da ware yatsa d'aya ta nuna Teemahn dashi kana tafara magana.

" kinsan Allah Teemah ki shiga hankalinki banason rashin hankali da rashin wayo, baki san mutun ba shine harda tsaywa dashi a k'ofar makaranta?
Owk nagane, saboda ki nuna ke kin isa ko me?

Hawaye Teemahn tafara tare da jijjiga kanta Allah mummy bansan shi ba yau ne fah yafara..........

Hannu mummyn ta d'aga tare da dakatar da ita daga cigaba da maganan, sai kawai ta sunkuyar da kanta k'asa tana zubda hawaye, bata so kokad'an mummy tayi fushi da ita akan hakan taso ta yi mata bayanin komai amma mummy takasa tsayawa ma ta saurareta ballantana taji abinda ke faruwa.

Takaicin ta d'aya shine akan wanda bata ma ta6ajin zata so shiba mummyn ta na shirin yi mata fushi.

Motar shiru baka jin k'arar komai sai na shashekan kukan Teemah har suka iso gida.

Koda suka iso gidanma mummy ko kulata batayi ba suka fiffita a motan suka barta, kayayyakin data siyo d'inma Habibu ne da ita suka kwashi abinsu kota kan Teemahn batabi ba.

Sai da Habibu yafito ne yazo gurin motar ya d'an bata baki akan tayi hak'uri ta shiga ta bata hak'uri zata sauk'o ai.

Da jajayen idanu ta kalleshi tace Mummy tana fushi sosai dani ko ?

Yace a'a zata hak'ura ki shiga ki bata hak'uri.

Da k'yar ta daure ta fito a motar ta shiga ciki lokacin ma har maghrib ya k'arato, ganin haka kawai sai ta wuce bayi ta d'auro alwala ta zo ta tada sallah.

Ba ita ta tashi agurin ba har sai da tayi sallahr isha'i.

Addu'a sosai tayi kafin ta tashi ta nad'e abin sallahr.

Ko hijabin datayi sallan dashi bata cire ba ta nufi d'akin mummyn ahaka.

Da sallama ta shiga d'akin sai ta sami mummyn na shirin kwanciya.

Zama tayi ak'asa kanta ak'asa tajira har mummyn ta gama shirin baccin kafin taje gareta da muryar kuka take bata hak'uri.

Mumnyn yi tayi kamar batasan da ita a d'akin ba domin kwanciyarta tayi ta juya mata baya, sai da taga kukan da Teemahn keyi kamar zaiyi yawa kar kuma yasata ciwon kai.

Koda tayi tunanin nan d'inma sai da k'ara minti guda akai kafin ta tashi ta zauna ta fuskanci Teemahn tare da fad'in

" inajinki yah akayi?

Vote, comment and share pls🤞🏻

*Salmern ku ce* 😍

[10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

People say, Find good people & leave bad ones but it should be, Find the good in people & ignore the bad in them. Remember No One Is Perfect in This World.

🅿 *31*

Teemah kamar bata ji abinda mummyn ke fad'i ba taci gaba da rera kakanta ahankali kanta akan cinyoyinta.

Da mummy taga kamar Teemahn bazata yi magana ba sai ta sakeyin wata maganar da d'an d'agun murya tace " idan zaki bud'i baki kimin bayani toh inkuma bahaka ba ki tashi kiyi tafiyarki" .

Daga haka mummy bata k'ara yin wata maganar ba illah ido data zubawa 'yar tata tana kallonta.

Ahankali Teemahn ta d'ago kanta suka had'a idanu da mummy, take tausayinta yah kama mummy musamman yanda taga idanun Teemahn sun k'ara girma da jaaa, alamun rashin nutsuwa kaf sun bayyana agareta, sai taji sam bata kyautawa gudan jinin nata ba, bahaka yakamata tayi mata ba tunda bata ta6a samunta da irin laifin ba yakamata tayi mata uzuri, ita kanta sai ta rasa dalilin da yasa ta d'aukewa Teemahn wuta ma, amma yaxatayi, mutunci da darajar y'arta take son karewa bakomai ba.

Kauda kai tayi gefe daga kallon Teemahn, yayinda Teemahn ma tak'urawa hannayenta idanu tarasa me zata ce da mummyn, tanaso tayi mata bayani amma sam tarasa abinda zata fad'a.

Da 'kyar ta daure ranta tafara magana ahankali cikin natsuwa.

" Mum......my kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin , kar kiyi fushi dani, ni bansan wayeshi ba, last week na fara ganinsa nima, kuma duk ranar da.......dana fita saina ganshi, shine dakansa yafara zuwa k'ofar makarantarmu amma wallahi mummy ki yadda dani banta6a sauraransa ba yau d'inma bada son raina bane bayadda zanyi ne shiyasa natsaya.............daganan mummy dakatar da ita daga magana inda tace " saurara yah isa".

Tsawon mintina biyu kafin mummyn ta mik'a hannunta ta kamo na Teemahn yayinda hakan ya matuk'ar haskaka zuciyar Teemah tare da sanyayawa tasan ko ba komai hakan kad'ai da mummy tayi yana nuni mata ne dacewar mummyn nata ta d'an sauk'o daga fushin data keyi da ita........

Mummy ne taci gaba da fad'in " kina jina ko?

Da wuri Teemah ta d'aga kanta alamar " ehhh tanajinta" wa mummyn.

" Waye mahaifiyarki?
Mummyn ta tambayeta tana kallon fuskarta.

" kece".
Teemah ta bada amsa a sanyaye

" waye ya kamata yasan damuwarki da kuma walwalarki?

" kece mummy"

" kina ganin zan iya ganin kin hau hanyar da bata dace ba in kuma barki akanta kici gaba dabinta?

Kai Teemah ta girgiza tare da fad'in " a 'a ".

Toh kin gani ko, ki fahimceni, ba ina nufin k'untata miki ko kuma takuraki bane sam, bani da burin da ya wuce inga kina farin ciki Teemah sannan duk duniya babu wanda zaiso ganin walwalarki sama dani.........amma banda ta wannan hanyar, har yanzu ke yarinya ce, da sauranki, banason tun yanzu ki fara wannan kule-kulen samarin saboda bashi da amfani.

kuma ma baki san wani abu ba ayanda kike d'innan duk wani wanda yake ganin sonki yake da gaskiya toh iyayenki zai fara nema ba ya dinga bibiyarki yana tsaidaki a ko ina ba, me sonki bazai ta6a yi miki haka ba ki kiyaye kinji.

Kai Teemah ta sake d'agawa alamar toh

Sai mummyn tacigaba da fad'in
" daga yau karki k'ara kula kowa ki bari ko secondary school d'inma ki k'arasa ta tukunna kinji kafin nan ki,ga awancen lokacin ko auren kikace kina so babu Me hanaki."

'Kasa Teemahn tayi da kanta dan k'arshen maganar mummyn kunya ya bata sosai.

Daganan mummyn tasake mata hannu tare da fad'in tashi kije ki kwanta toh.

Bata mik'e ba kamar yadda mummyn ta umarceta sai ta jefawa mummyn tambaya kanta ak'asan batare da ta kalli mummyn ba tace
" shikenan kin huche mummy" tana murmushi tayi maganar.

Mummyn ma murmushin tayi sannan tace mata " zan huce dai idan naga kin kiyaye maganata"!

" da sauri ta tashi tana murna har hak'oranta na bayyana afili tace " insha Allahu zan kiyaye mummy"

"Allah yasa " kawai mummyn ta'kara fad'i tare da yun'kurin mik'ewa da niyyar shiga bayi.

Teemahn ma hanyan fita tayi tana jin ranta fari k'al " Mummy sai da safe " tace wa mummyn tana tafiya ahankali.

Mummyn ma na gab da shiga bayin ta amsata da " Allah ya bamu Alkhairi".

Koda mummy tagama uzurinta tafitoh ma zama tasakeyi abakin gado tana tunanin hali irin na zamanin yanzu, daga k'arshe addu'a tayiwa 'yarta akan Allah ya kareta ya rabata da sharrin masu sharri yarabata da soyayyar wahala da duk wani al'ummar musulmi.
Chapter 34 · 0% Book details