Sashe 97
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuntuni Anty take zubda hawaye tana 'karawa tasan koma me ya faru duk laifinta ne, laifinta ne da ta saka.son.zuciya ya rinjayi duk kan al'amuranta, yau gashi mahaifinta da kansa yake bada shawarar kar azauna da ita.
Godiya Abbah yayi masa sannan ya sanar dashi cewa shi bashi da burin 'kuntata mata koka'dan kuma.duk abinda zaiyi zaiyi shi ne dan gyara duk wata 6araka da ke tsakaninsu, yace ha'kika Maryanlm.ta 6ata raina ta shammace ni alokacin da banyi zaton faruwar hakan ba, Maryam ta ninke ni a baibai da sunan ta kar6i maganar auren Mahmud bansani ba ashe mugun sa'ka tayi a6oye wanda warwareshi ke da matu'kar wahala, ban ta6a zaton Maryam zata aikata haka ga 'dan cikinta ba, wanda ya kamata ace ta so shi fiye da komai arayuwarta, amma kash!
Mahmud be yi dacen samun hakan ba sa6anin haka sai ma ya rasa rayuwarsa.
Bayan jin hakan na tsani Maryam irin.tsanar da banta 6a zaton zan mata shi ba, naso in hukunta ta ta yadda bazata ta6a ma tunanin sake aikata wani abu makamanciyar wannan ba, sai de banyi hakan ba saboda ganin girma da kake dashi Alhaji a idanu na, bayaga haka ma Fateemah sai ta nutsar dani muhimmancin yafiya da falalar ta, kuma na gamsu sosai sanadin hakan na yafi Maryam azuciyata sai de bakina nawi yamin in furta mata haka nabari har se naga nadama ya ratsata tukunna.
Cikin hakan Allah ya nufe ni da neman aure kuma nasamu Alhaji zancen ana danake maka ayanzu kwanaki goma ne suka rage a 'daura aure "
Fuskar Alhaji tuni ya cika da murmushi ya ringa sanya masa albarka tare da fatan alkhairi yace yayi matu'kar farin ciki da faruwar hakan kuma yana bayansa 'dari bisa 'dari.
Anty kam hawaye masu zafi ne suka zubo mata wanda tun rasuwar Mahmud basu fasa zuba ba, sai de na yau yasha bambam dana kullum, akowani 'digon hawayen ta nadama ke lullu6e ta tare da wanke duk munanan halayenta dake zuciyarta, yanzu kuwa kukanta na godiya ga mahalicci ne da Abbah ya furta mata yafiya, ta tsani kishiya abaya amma yanzu kam ji take matu'kar ze yadda ya amince ya sake zama da ita toh a shirye take ta zauna da kishiyoyi uku ma ba 'daya ba.
Komai faru laifin tane, Abbah be ta6a yi mata maganar kishiya ba tunda suke dashi sai yau 'din, yanzu kuwa da duk abubuwa suka yimata yawa ina ita ina 'daga hankali dan zeyi aure, tace Allah ubangiji ya ha'de kawunan mu ya sa hakan shine mafi alkhairi.
*****
Abbas tunda ya tafi kusan 3weeks kenan har yanzu be dawo ba, kullum sai dai su gaisa dashi awaya sai ya ta cewa ayyuaka ne suka yi masa shiyasa be le'ko gidan ba, Ummah bata damuwa dan tasan yanayin aikinsa dama fiye da hakan ma zai iya faruwa shiyasa kullum da addu'ar nasara da kariya kawai take binsa.
Daddynsa kam ko ajikinsa, sarai yasan matsalar Abbas 'din gudun ha'duwarsu yakeyi saboda batun aure shiyasa ya'kizuwa Abuja shikuwa babu fashi lokacin daya 'dibe masa na cika zaiga abin mamaki dan kuwa ba ze fasa ba.
Ranar da Teemah ta gama watannin takabarta ranar har se da tayi mamaki dan yanda Ummah ta fitar da ita tsab, sai dama ta ha'da ta driver suka je saloon suka dawo sannan tabata wasu ha'da'd'dun gown 'yan italy matsu kyau da tsada sai alokacin ne Teemah take jin labari ashe wai Mummy ce ta aiko musu dashi tun zuwan Abbas kwanaki shine Ummah ta 6oye su sai yau ta fitar ta bata nata na Hannah kuma tace sai ta dawo zata ksr6i nata.
Data shirya tafito kuwa ita kanta tasan tayi kyau har jin kanta takeyi, ji take yi kamar wata dabance ba Fateemah ba, for about 4months da wasu kwanaki tana ta fama da atampopi yau kam wani iska takeji yana shiganta me da'din gaske, tun ba ma da Ummah ta bata wasu turaruka masu kyau tace nata bane, take ta rungume Ummahn tana dariya tare da godiya.
Haka taringa fesawa ajikinta tana 'karawa har se da 'kamshin ya 'dan fara yimata yawa kafin ta sarara.
Jin kanta yau 'din takeyi tamkar wata sarauniya gaba 'daya ta dawo daban.
'Daki ta koma ta ringa kashe selfie kala-kala wasu abin dariya wasu kuma abin birgewa ita adole tana farin ciki yau tasamu freedom afa'darta.
Ummah da kanta tace idan Hannah ta dawo da wuri ko da da yamma ne sai sunje shopping musamman kawai saboda Teemah.
Ai kuwa Teemah taringa 'kiran layin Hannah amma baya shiga kusan 5 missed calls ta mata, data ga bata 'daga ba sai ta tura mata text " _Hii bae, pls ki dawo da wuri today is my day, Ummah tace zamu_ _fita_ "
Hannah na can tana rubuta test dan haka bata ma bi takan wayarta ba sai da tagama rubuta test 'din tafito sannan ta ga missed calls 'din Teemah tare da text 'din da tayi mata, ai kuwa tana gani ta hau murnan yau zasu fita da 'yar uwarta , bata 'kara bi takan sauran lectures 'din da zata yi ba batare da jiran komai ba ta kamo hanya ta dawo gida.
Tana zuwa suka rungume juna suna murna, Hannah da kanta itama sai da taga canjawar Teemah har ta kasa daurewa sai da ta tambaye ta aka wai yaushe kuma har tayi saloon batare da tasani ba?
Murmushi Teemah takeyi ta bata amsa da fa'din " _yau da safe naje nayi lokacin already kina school ai shiyasa_ .
'Bata rai Hannah tay tace
" _shine kuma kika 'ki jirana muje tare ba, duk laifin Ummah ne_ _ai da ta gaya min da wuri_ _da sai in fasa makarantar mutafi amma shine aka 'kyaleni harna tafi_ "
Teemah tana kan haska selfie tace
" _yanzu kam ai ya wuce ki, yi sauri ki shirya muje yawo yarinya yau zanga gari yarinya, kayanki ma na gurin Ummah, ke ko irin kice nayi kyau 'din nan ma baki fa'da ba kintsaya surutu_ "
Tashi Hannah tayi taje wurin Ummah ta amsa kayanta tare da shigar da complain 'din bata je saloon ba ita.
Ummah lalla6ata tayi har zancen ya wuce sannan ta wuce 'daki domin watsa ruwa.
Abbas kam be dawo Abuja ba har sai da ya cika sati hu'du cif-cif kafinnan, ranar daya dawo 'din kuma sai yayi dai-dai da ranar da Teemah ta gama takabanta.
Bayan shigan Hannah wanka ne Teemah ta 'kira Anty tana 'dauka tace " _Anty albishirin ki_ ?
" _Goro fari 'kal-'kal_ "
Anty tabata amsa tana murmushi.
" _Anty yau zan fita_ _yawo nida___ _Hannah...._
" _Kai dan allah kice_ _yau sabuwar_ _rayuwa_ ' _yata zata fara_ "
Labari Teemah ta bata na irin kayan da ta saka da sauransu.
Daga 'karshe Anty tace mata itama insha Allahu gobe tana hanya zata zo Abujan, Teemah murna kamar tafasa wayar da ihu, sai da Anty ta kauda wayar akunnanta tana murmushi da gode wa Allah ga dukkan baiwarsa.
Tana gama wa da Anty ta 'kira layin Mummyn ta.
Mummyn ma tace ai tana ta 'kiran layinsu be tafiya tun jiya har na Ummah ma, tace Teemah ta ha'da ta da Ummahn pls.
Fita tayi dan kaiwa Ummah wayar inda ahanyan ne take bawa Mummy labari akan yau zata fita yawo ita da Hannah tace Mummy kinga kayan da kika aiko manan nan kuwa yanda yamin kyau dan Allah Mummy ki 'kara siya min wani, idan nazo kawai in samu, zan ro'ki daddy ai yabar ni inzo.
Mummy cewa tayi
" _Nima zanzo ai insha Allahu gobe ko jibi_ "
Wani tsalle da ihun da Teemah ta buga da jin furucin Mummy tare da gwalo idanun ta yasa Abbas dakatawa daga tafiyar dayakeyi ya tsaya kallonta.
" _Dan Allah Mummy_ _dagaske_ _zaki zo_ ?
Ta tambaya da murna kamar zata fasa wayar ta ganta agaban Mummy.
Mummyn ma cewa tayi " _zanzo mana Teemah ina miki 'karyane_ !
Tsalle ta buga tace Anty ma zata zo tace min Mummy, dan Allah karku fasa kinji.......
Maganar tata yankewa yayi jin an fizgo wayan daga kunnanta daga bayanta, juyi tayi da 'karfi zaton ta ma Hannah ce harta gama shiri ta fito hakan yasa ta fara furta " _banason iskanci_ _Hannah da_ _mum...._
ganinshi tsaye tayi yana kallonta, baki ta rufe da hannunta tare da zaro idanu waje.
Wani kyau da kwarjini taga yayi mata, muryarta na rawa tace " _sannu_ _da zuwa Yayah_ "
Kallonta yayi kawai batare da ya amsa mata ba, sai ma yace mata " _welcome back Nana_ _parrots_ !
_Ke ihun naki be_ _damunki ne_ , _ke 'daya amma kinbi kin cika gida da hayaniya kamar kasuwa_ ?
Anutse yayi mata maganar bada masifa ba ita kanta tayi mamakinsa yau 'din.
Amma duk da haka sai tayi shiru tai 'kasa da kanta batare da ta furta komai ba.
Dayaga bata da niyyan yin magana sai ya huya kansa tare da fa'din
" _Any ways, i heard u said zaki yawo ko?, har zuwa ina kenan haka_ ?
" _Shopping zamu_" Ta bashi amsa atakaice.
Sake tambayarta yayi
" _ke da waye_ ?
Tace da " _Hannah_ "
" _inji wa_ ?
'Dago idanu tayi ta kalleshi jin yanata jero mata tamabayoyi kamar wani 'dan jarida, da suka ha'da idanu sai ya 'dage nashi idanun zuwa sama.
Ta fahimci manufarsa dan haka sai tace
" _inji Ummah_ !
Tana fa'din haka tafara ro'kon Allah azuciyarta akan Allah yasa kar ya hanasu fita tasan ka'dan ga aikin sa ne yace bazasu ko'ina ba, ita kuwa tana jin da ya hanata fitan nan gara yayi mata komai ma amma banda shi.
Cikin haka wayan ta dake hannunsa yafara ringing 'dagowa yayi sai yaga Mummy ce ta'kira, yana ganin haka sai ya mi'ka mata wayar yana kallon cikin idanunta.
Ahankali tasa hannu ta kar6a tare da sada ta da kunnenta tace
" _hello, Mummy_ !
" _Ah ah ban kai ba tukunna bari nayi sauri inkai mata_ "
Iyah abinda yaji ta fa'da kenan.
Tana fa'din haka ta yanke 'kiran tare da juyawa da niyyar tafiya.
Muryarshi tajiyo yana fa'din
" _In kin kai mata wayan ki kawo min ruwan sha_ "