← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 163

Sashe 93

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated 2 my family._

*Bismillahir rahmanir raheem*

_God is the best listener and you don’t need to shout, nor cry out loud. B’coz he hears even the very silent prayer of a sincere heart..........._

🅿 *69*

Yanda yayi maganar atsare dole yasa ta goge hawayen nata ta ringa ajiyan zuciya kawai ahankali.

Hotel 'din da ya kwana anan suka koma yace tajira shira shi yaje ya nema musu flight 'din zuwa Abuja sannan yadawo.

Ummah na zaune a parlour tana kallon wani Hausa Movie kawai taji muryar Abbas nayi mata sallama kamar daga sama.

A mamakance ta amsa sallamar tare da maida dukkan hankalinta gareshi.

Fuskan nan atamke ya 'karaso ciki Ummah da mamaki take dubansa ganinsa ayau 'din bayan be da'de da tafiya ba, baya ga haka ma tasan yana da uzuri acan, mamakinta ne ya 'karu ganin Teemah ta shigo da sallamar ta itama kanta a'kasa ta 'karaso wajen Ummahn.

" _Ah'ah, Teemah kune tafe_ ?
_Keda waye haka_ ?

Ummahn ta tambaya tana me waro idanu ko zata ga abokin tafiyan Teemahn tare da kamota ta zaunar da ita kusa da jikinta.

Abbas kam 'dauke kai yayi tamkar be san da zancen ba dayaga hakan ma be masa ba sai kawai ya mi'ke ya wuce ciki.

" _Keda waye kuka zo ne Teemah naga shiru har yanzu banga kowa ba_ ?
Ummah ta sake tambayar Teemahn akaro na biyu.

" _Ni da Yayah ne muka_ _zo_ ?
Teemah ta bata amsa ahankali.

Da wuri Ummah tace mata
" _wani Yayahn kenan_ ?

Sai tace
" _Yayah Abbas_ "

" _Abbas dai_ ?
Ummah ta sake tambaya da mamaki.

Kai Teemah ta 'daga mata alamar _ehhh_ .

" _Toh garin yayah haka ta faru_ ?
_a ina kuka ha'du_ ?
_Ko ke kika ce masa zaki zo nan 'din, ina_ _ita Antyn_ _naki_ ?

Shiru Teemah tayi dan bata san wanne daga cikin tambayoyin Ummahn zata fara amsawa ba.

Ganin haka yasa Ummah kam ta fassara shirun da abinda hasashen ta ya bata.

Kafin tayi magana sai ga akwati an shigo da shi wanda kallo 'daya tayi masa ta fahimci cewa na Teemah ne.

Jinjina kai tayi tace
" _lallai yaron nan wato sai da yaje ya taho dake ko,_ _ai dama tun ranar da_ _yaji labarin kina can_ _naga sai wani huhhura hanci_ _yakeyi yana kauda kai gefe ashe shirin da yayi aransa_ _daban_ .
_Zai zo ai yasame ni neh sai naji dalilin_ _hakan_ "

Kallonta ta dawo dashi kan Teemah tace " _maza shiga ciki ki watsa ruwa ki huta kinji Fateemah_ "

Duk wannan dramar Teemah bata ga Hannah ba tun zuwanta Ummah ce tayi mata kwatancen inda 'dakin Hannah yake tace mata Hannahn na ciki.

Koda taje 'dakin ma bata ganta a'dakin ba motsin ruwa data jiyo abayi ne yasa ta gane cewa tana bathroom, cigaba da tsayuwa tayi kamar me jiran abata umarni, bakomai take tunawa ba kuwa sai Mahmud tare da tausayin Anty dayayi matu'kar tasiri a zuciyarta.

Tana tsayen har Hannah tafito daga bayin tagama firgita da ganinta dan bata ta6a zaton ganinta awannan lokacin ba, har kuwa tazo ta fahimci cewa itan ce dagaske ita Teemah bata ma san ta fito ba, sai da Hannah ta taho ta dafa kafa'dar ta tare da 'kiran sunanta kafin tayi firgigi ta dawo hankalinta.

Ai kuwa tana ganin Hannah ta sanya kuka tare da rungumarta zuwa jikinta sannan tacigaba da kukanta.

Hannah kam shiru tayi tama kasa magana dan mamakin zuwan Teemahn tare da farin cikin ganinta duk su suka cika mata zuciya ayanzun.

Sai da taga kukan Teemahn bana 'kare bane kafin tafara bata ha'kuri tana bata baki da 'kyar ta sarara da kukan wanda hakanne yabawa Hannah damar tam
bayarta tace " _ke dawa kika zo ne Teemah kinsan kuwa yanda naji haushin zamanki acan ai wallahi dama niyyata in je in zuga daddy ko kuma Yayah a'dauko ki haka kawai sai awani barki agurin muguwar matar nan, ni ai kin min dai-dai da kika taho wallahi_ , _Allah yasa bazaki sake_ _komawa ba_ "

Cikin rawar murya Teemah tace
" _Anty tana bani tausayi sosai_ _Hannah nasan zata shiga damuwa sosai dana barta_ "
Fa'din Teemah tana me cigaba da zizaro hawayenta.

Hannah kam kwafa tayi tana kallon Teemah sai daga baya tace " _ke wallahi wani lokaci rasa inda wayoki_ _yake tafiya nakeyi, ina ruwanki da ita? tausayinta na banza da wofi, ita ta_ _tausaya miki ne lokacin da take neman cin mutuncin ki duk da kina matsayin_ _matar 'danta kuma 'ya agurin mijinta? Sai yanzu ne data ga babu 'dan shine zata wani kalallame_ _ki dan ki zauna tare da ita tasamu hanyar_ _sake cutar da ke_ _cikin sau'ki ko_ ?

Teemah cewa tayi
" _Hannah ba haka bane fah, Allah Anty ta canja yanzun ba kamar da take ba_ "

Hannah tace " _ni ya isheni haka da_ _Allah bari kiga nayi sallah lokaci na 'kurewa kema jeki yi alwala, ni yau_ _farin ciki ma_ _inajin baze_ _barni na samu bacci_ _ba_ "

Agurin cin abinci suka ha'du dukkansu Abbas kam sai wani shan 'kamshi yakeyi kamar besan me ya aikata ba nan kuwa duk yana hakan ne dan kar Ummah ta samu daman yi masa fa'da akan maganar .

Hannah ce " _tace Yayah bakaga Teemah bane_ ' _dazunnan fah tazo itama bata jima ba_ "

Tunanin ta wai ko Teemah tariga shi isowa ne shiyasa ta fa'di haka dayake bata san lokacin daya zo ba.

'Dago kai yayi ya sauke shi akan Teemah yaga yanda ta ke kallon abincin tana wasa da spoon aciki sai ya maida kansa 'kasa asaman la66ansa yace da Hannah
" _na ganta mana!_ "

Ummah ce tace
" _Hannah ai shi tun kafin ki ganta shi yariga yaganta_ "

Hannah kam waro idanu tayi da mamaki tace " _haba dai, Ummah a ina toh suka ha'du tun 'dazu fah muna_ _'daki_ ?

Atakaice Ummah tace mata
" _shine dakansa ya_ _kawota_ "

Hannah kam kallonta ta miyar kan Abbas 'din da fara'arta tace " _wallahi Yayah ka kyauta kamar kasan meke cikin raina, ni dama_ .... "

" _Stop talking and eat your food Hannah later then kyayi surutun, okay_ "

Cin abincin tafara cikin farin ciki tanayi tana murmushi dan ita yanzu komai normal ne a6angarenta bata da damuwar komai tunda kam ga Teemah agefenta zaune.

Cikin hakan ta waiwaya 6angaren Teemah sai taga ba ta cin ma abincin ita kam.

Zungurinta tayi da kafarta, data 'dago ta kalle ta sai ta mata nuni da abincin Teemah ma sai ta fara kaiwa kamar gaske.

Ummah ma ta lura da hakan amma bata nuna ba dan zatonta ko idanun mutane ne yayi mata yawa shiyasa takasa ci, sai ta bari akan idan sun gama zatace da Hannah ta 'diba mata zuwa 'daki wata'kila can zatafi sakewa.

Abbas kam da hanzari yake cin nashi abincin 'ko 'karinsa yayi ya tashi ya bar gurin dan yasan Ummah dole ne sai ta tuhume shi shikuwa be san ma me zece da ita ba.

Ummah ma duk tana lura dashi sai ta 'kyaleshi kawai tana jiran su Hannah su tashi dan bata son yimasa surutu agaban 'kanwarshi sam shima kuma yasan hakan shiyasa yake hanzari yayi ya rigasu barin table 'din.

Yagama kenan yana niyyan tashi sai yaga Hannah ta rigashi mi'kewa tana shirin yin magana sai Ummah tari bakinta da fa'din " _'Dauka wa Fateemah abincinta naga bata ci ba sam may be a'dakin zata fi sakin jiki taci_ "

" _ah' ah nifa nama koshi Ummah basai_ _ta 'diba min_ _ba_ !
Cewar Teemah tana 'ko'karin mi'kewa itama.

Wani kallo da Abbas ya watsa mata yasa take tayi kasa da 'kanta 'kirjinta na harbawa.

Ummah cewa tayi " _ah'ah Fateemah ni banga wani abin kirki da kika ci_ _anan ba_ ,
" _Hannah maza 'diba mata ko ka'dan ma tasamu taci zama_ _da yunwa ai bashida da'di koka'dan_ ,
_dubi fah yanda duk kika 'kare abanza_ "

Hannu Hannah tasa ta harha'da mata komai sannan tace da ita
" _tashi muje_ "

Shima mi'kewa yayi daniyar barin gurin sai kuma Ummah tace masa
" _zauna Abbas_ "
Dayake yana kusa da ita shiyasa shi ka'dai yaji maganar da Ummahn tayi.

A'darare ya koma ya zauna yana me shafo kansa da hannunsa 'daya.

Sai da su Hannah suka shige ciki kafin nan Ummah tace masa
" _sannu ko_ "

Kallon " _me nayi_ " ya yiwa Ummahn yana murmushi

" _Haba Muhammad yazakayi haka dan Allah bayan da kai rannan mukayi_ _magana akan yarinyar nan, shine kuma ka san'di jiki ka koma ka taho da_ _ita_ ?
" _Kai ko kunya ma bakaji ba, ka duba halin da matar nan take ciki amma sai_ _ka yi wannan rashin mutuncin, itace fah da kanta ta nemi_ _abar mata yarinyar nan_ _agurinta harta gama watannin takabarta kuma aka amince mata_ _sai daga baya kuma_ _haka yafaru kai kana ganin zata_ _ji da'di_ _ne_ ?

Ta 'karashe maganar tana kallonsa.

" _'kyale ta kawai Ummah yariga ya_ _wuce ai yanzu tunda gashi mun_ _taho_ "

Ya bata amsa yana me duba agogon hannunsa.
Shi koka'dan bega rashin kyautawar sa ba a wannan lamari dama me yasa za'a barta acan 'din in ba ahanata mantawa da mutuwar ba.

Ummah kam kwafa tayi tana dubansa jin irin amsar daya bata sai tace masa
" _Toh na barta tunda haka kace, amma shikuwa kawun nata fah, miye laifinsa acikin_ _lamarin ko kuma shi 'din kana ganin zaiji da'dine ace rana tsaka_ _kawai ka dira masa ka wani ce zaka tafi da ita bayan sun saki ransu cewa_ _zata zauna tare dasu, kuma ai baka ji ra'ayin yarinyar ba akan haka baka_ _sani ba ma ko can 'din yafi mata fiye_ _da nan_ ..."
Chapter 93 · 0% Book details