← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 163

Sashe 145

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin yasata itama dan jin dadin wai duk ita zata haifi wannan harma bata san lokacin da bakin ta ya furta "Yayah to yaushe zan haihu?
Abbas cewa yayi
"Tashi in gaya miki"
yana maganar yana 'dago ta daga jikin sa.
Dariya tafara a hankali tare da k'ank'ame shi sosai.

Shima Abbas dariyar yayi sannan shiru ya dan ratsa wajen.

Abbas ne ya yanke shirun da fa'din " "tashi ki mi'ka min phone 'dina"

Tashi tayi ta 'dauko wayar ta bashi sannan ta koma gefensa ta zauna tayi shiri tana kallon sa ganin ya maida hankalin sa ga wayar.

Numbern wani friend dinsa ya 'kira wanda shima yake nan cikin barikin, sun rabu dazu da yamma akan zaije night party 'din wata babe 'dinsa dake birthday yau a hotel.
Christian ne shi kuma bashi da aure sunan sa Samuel amma da Sam ake 'kiran sa.

Koda Abbas ya 'kira shin kuwa tambayar shi yayi ko ya dawo sai ace "ah ah but he is about to"
Abbas bayani yayi masa na abinda yake so 'din da sunan shi tare da sanar dashi inda zai mu nan kan hanyar da zai 'dauko zuwa gida ba sai yayi yawo ba.
Take Sam ya yi masa al'kawarin siyowa sannan sukayi sallama.

Abbas nada tabbacin matu'kar samuel ya samu dama zai cika al'kawarin sa musamman da yake cewa ya san baya shan hiya so cikin hankalin sa zai dawo.

Bai wuci 40mins da yin wayar ba kuwa sai wayar sa ta 'dauki 'kara, ganin Sam ne sai ya tashi tare da 'daukan wayar ya fita harabar block 'din nasu wanda anan ya hadu da Sam, hannu suka sha sannan ya bashi sa'kon.

Abbas sosai yaji da'di, koda ya ciro kudi ya bashi kuwa Sam 'kin kar6a yayi kawai yayi gaba abinsa.

Abbas ma sai ya koma ciki yana 'kara maimaita tunanin abin a ransa, murmushi yayi 'dan ta k'aitacce yace " _Zahra rigima_ "!

Teemah kuwa duk da haka sai taso ta kawo masa rigimar ita ba na company take so ba ai ta gaya mishi, sai yace "yanzu kam sai kizo ki tsotse ni Zahra k'ila hankalin ki zaifi kwanciya tunda ke ba'a miki gwanin ta, banyi kokari bane ko da da daren nan a ina zan samo miki wancen?"

Ita kanta tasan hakan amma daya ke tasa ba rigimar ne shiyasa.

Ciki-ciki take mita akan maganar daya gama yi yanzun wanda ita ka'dai tasan abinda take cewa Abbas kam share ta yayi yaci gaba da al'amuran sa.

Dan haka sai ta sa hannu ta 'dauki wanda ta ciro da farko 'din ta bu'de a hankali ta 'danyi tasting.

Sosai taji ya ratsa mata zuciyar ta, baran ma sassanyan k'amshin da yake yi gashi da kauri sosai ai sai taji yama fi na asalin da'di.

"Nagode Yayah" tace masa tana murmushi sai ya kauda kai yace "yi ki gama ni dai kiji dani"

Bata tanka ba sai ta cigaba da shan abinta kamar wasa sai gashi ta tada roba guda ta kuma ciro wani wanda ko rabin sa ma bata shaba sai bacci yayi gaba da ita.

Abbas duk na lura da ita, harta yi baccin, kai ya jijjiga kawai daya kalle ta aransa yace "sarkin rigima, bayan tace tafasa kuma da taga an kawo kuma harda mita"

Sai da ya gama kallon abinda yake yi sannan ya juyo gareta, tana daga zaune ta kishingi'da a hakan kuma tayi baccin.

Kiss ya bata a bakin ta yana 'dan murmushi.
Teemah sai ta 'dan motsa ka'dan.
Shima sai ya 'dan ja baya dan kar ya takura ta, sauran fresh milk 'din ya 'dauka ya je ya sassaka mata su cikin fridge sannan ya 'dauke ta ya maida ta bedroom ya kwantar da ita sai kuma ya sake dawowa parlourn ya kakkashe komai sannan ya koma shima ya hau shirin bacci.

*****
Har kwana biyu bayan haka Teemah bata 'kara neman wani abu ba, sai dai ta kanyi da kanta idan taji tana so.

Duk ranar da tayi wani abin kwa'dayin to dole shima yake ci dan bata sake yin wani abincin kuma, wasa-wasa har Abbas ya saba da irin cimar tata dan in dai tayi sai ta ajiye masa, tun yana 'kinci har dai ya saba shima dan ma da rana ne tafiya yi masa hakan da dare kam zagewa takeyi tai tayi masa girki mai rai da lafiya wanda tasan ba zai ci da takaici ba.
Girki salo-salo.kuwa duka ta iya su, kuma ko a TV tgaa anyi kalan girki bata wasa sai ta gwada shi tagani in tgaa yayi kyau sai ta ta jin da'di shikenan daga lokacin kuwa ko a wani akace ta koya toh zata iya.

*****
Ranar ya kasance saturday ne tun bayan da sukayi sallar asubah suka yi karatun al-kur'ani sai ta koma gado da niyyan koma wa bacci, Abbas ne ya hana ta baccin dan shima dawo wa yayi kusa da ita ya fara aika mata sa'konni, tun qcikin idanun sa ta fahimci sauyi tatare da shi, daya ke kusan kwana uku kenan yau bai samu kanta ba, ita kanta tana jin kewar sa amma kawai take basarwa.

Sosai Abbas yau 'din ya rikitata da salo da tsarin sa na zallar 'kauna da soyayya wanda ke tafiyar gangan jiki da zuciyan duk ma'abota soyayya, ita kanta sai da tasan cewa mijin ta cikakke ne, gwani ta kowani 6angare domin sosai ya tafiyar da 'kananun matsaloli da damuwar dake cikin zuciyar ta, Abbas bai barta ba har sai da ya tabbatar da cewa ta 'dauki darasin sa kuma irin 'daukan nan ma mai wuyan mantawa.

Sai bayan da komai ya lafa kafin suka koma bacci baya sun tsarkake jikin su.
Shine ya riga ta tashi in da ya tashin a hankali dan kar ya tashe ta, A gadon ya zauna daga gefen ta 'kafar sa 'daya na 'kasa yayin da 'dayar ke lan'kwashe daga saman gadon ya zubawa system idanun sa.

Around 10:04am itama ta farka daga baccin ganin shi zaune a gefen ta yasa tayi luf daga kwancen tana kallon sa.
Jikinta da wata riga ce pink mai dogon igiya daga gaba wanda aka saka igiyoyin ya zama tamkar bottle, sai ya kasance shine ya tare gaban rigar ya hana aga jikin ta, daga rigar kuwa babu komai ciki dan ko bra bata sanya ba, wandon skinny ne daga 'kasan ta shima pink mai zanen flowers a jiki sosai kayan suka yi mata masifar kyau ta koma tamkar 'yar yarinya.
Abbas ne da kansa ya za6a mata kayan yace shi zata sanya ajikin ta kuma shine ya siya mata dan ganin kamar zai mata kyau wani ranar da suka je shopping tare da shi.

Gashin kanta har yanzu babu kitso sai ta kama shi ta 'daure da ribbom kanta babu 'dan kwali.

Kallon sa take yi tana sakin 'kayataccen murmushi, daga zuciya har ga6o6in ta take jin masifaffan son mijin ta na ratsa mata, tana jin kamar duk duniya ita tafi kowa son shi, bata kuma 'kaunar ganin ranar da za'a ce yau ya kasance da wata matar wacce ba ita ba bata ko 'kaunar wannan irin hasashen.

A hankali ta bu'di baki tace "Yayah ina kwana?"

Sai da 'dago ya kalle ta sai ya sau'ke ajiyan zuciya kafin ya amsa mata da " lafiya Fatan komai normal?"
Ya 'karasa da murmushi, itan ma murmushin tayi tare da 'daga masa kai.

Sai da ya gyara zaman 'kafafun sa da kyau inda duk biyu ya hawo da su gadon ya mi'ke straight tare da 'dora system 'din akai sannan ya cigaba da dubawa.

A hakan suke 'dan ta6a hira sama-sama idanun sa na kan system 'dinsa.

Cikin hirar ne yake mata mitan rashin kitson nata har ma yace zai nemo inda za'a samu musulmai masu kitso suyi mata.

Shiru ne ya biyo bayan maganar tasa, saboda ita abinda yake ranta daban ne a dai-dai wannan lokacin, tunanin pepper soup 'din da Ummah take kawo mata sa'ilin da baya nan ne yazo ranta take kuwa taji matsanan cin kwa'dayin cinsa ya bijiro mata.

A hankali sai ta d'aga kanta ta dawo dashi kan 'kafar sa ta lafe luf, ta 'kira sunan shi a hankali har sa jan sunan tamkar bata so tayi maganar.

Abbas yaji ta amma sai yayi shiru bai amsa ta ba dan so yake ta 'kara saboda yanda yanayin maganar tata ya ratsa masa kwanya sosai tsigar jikinsa ta ta shi.

"........Yayah!
Ta sake fa'di a hankali cike da shagwa6a.
Sai ya amsa ta da " Uhumm ya akayi ne?"
Yayi maganar batare da ya kalleta ba.

Teemah kam bata damu ba sai ta cigaba da fa'din "Lokacin da baka nan katafi course ko kullum Ummah na aiko min pepper soup mai da'di na hanta"
Abbas sai cewa yayi " Ummah ta kyauta sosai, Allah ya biyata"

Itama Teemah da "Ameen" ta amsa sannan taci gaba da fa'din
" kasan wani abu?"
Yace " ah ah, sai kin fa'da min"
Teemah sai tace
"Shi fa nake son in ci yanzu"
Tayi maganar cikin marairaita.

Abbas kwafa yayi yana duban bayan kanta da mamaki, zaton sa ko tsaban ta tsokane shi ko kuma taji bakin sa ya sa ta 'kirkiro wannan maganar, in ba haka ba miye ala'kar wancan lokacin da wannan ko de ta manta garin da suke ne a yanzun......
Wannan tunanin ne yasa shi fa'din
"Sai ki ci mana to Zahra tunda shi kike so ko na hana kine?"
Da gangan ya fa'di hakan ba dan komai ba sai dan cewa da akayi "silly magana or tambaya need silly answer"
Chapter 145 · 0% Book details