← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 163

Sashe 142

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita tayi da sauri kamar an kunnata da switch shima sai bita da idanu tare da sakin tsaki, haka kawai yau 'din ya tsinci kansa cikin 6acin rai.

Koda ta koma 'dakin ma sai data sha kukan ta na shagwa6a son ranta dan ba kukan ciwo bane kawai shagwa6ar ce yau ta motsa da kuma haushin ya 'dalli bakin ta, kafin daga baya ta tashi ta koma gaban mirror ta duba fuskar ta da kyau, gani tayi ma bakin bai ko tashi ba amma duk da haka sai ta janyo stool ta zauna taci gaba da 'karewa fuskar tata kallo.

Bata san meke damun sa ba yau 'din amma kallo 'daya zaka masa ka hango 6acin rai tattare da shi, ita kanta tasan bahaka ya kamata tayi masa magana ba musamman dayake neman hanyar da zata janyo mijinta ajiki takeyi yanzun take sai kuma taga rashin kyautawarta.
Wani 6arin zuciyarta ne yashigar mata da tunanin "ai shima bai kamata ya 'dalli bakinta ba bata mar komai ba haka kawai dan ranshi ya 6aci kuma ai tasan ba ita bace ta 6ata masa rai 'din meyasa zai zo ya huce akanta?"

Kalaman Anty ne suka bijiro ranta inda tace da ita " auren ha'di na tafe da wasu irin 'kalubale wanda sai kai da kake cikin sa ne zaka san hakan in kayi sa'a kuwa bazaka fuskanci irin wa'dan nan matsalolin ba sai kaga ka dawwama cikin farin ciki, amma dukkan su ba'a cin galaba akan su har sai in an ha'da da ha'kuri"

Teemah ido ta lumshe tana tunanin abinda Yayah zai yi da result 'dinta tasan dai duk ba zai wuci batun makaranta ba ita kuwa sam bata so, wanda tayi abaya ma Allah yasa albarka amma tunda yace yanaso 'din bari ta 'kira Mummyn taji ko ta san inda yake.

'Daukan wayar ta tayi ta 'kira layin Mummy, bata 'daga ba sai da ya yanke kafin tana sake 'kokarin gwadawa sai ga 'kiran Mummyn ya shigo, gaisheta tayi cikin natsuwa tare da tambayar ta Daddy daga nan ta 'kara da tambayar result 'din sai Mummy tace da ita duk suna nan Dubai ta taho dasu tama manta ne dama taso ta taho mata da shi amma sai ta sha'a fah.

Teemah aranta ta ringa godewa Allah sam bata son damuwar makaranta ita aganin ta ai ba dole bane tunda wasu ma bayi suke yi ba gaba 'daya.

Sallama sukayi da Mummyn ta ajiye wayar sannan ta tashi a hankali take tafiya kamar mai jin tsoron 'kasa tafito daga 'dakin nata.

A parlour ta same shi sai ta 'karasa gefen sa ta zauna tace " Yayah!
Tun fitowar ta ya ji motsin ta amma bai nuna alamun ya ji ta ba sai ma ya rintse idanun sa yayi sama da kansa.
Jin ta ambaci sunan shine yasa ya bu'de idanu tare da juyowa ya kalleta inda take ya hango rauni tattare da ita.

Suna ha'da idanu sai ta ce " Mummy tace wai tatafi dashi Dubai"
A nutse tayi maganar wanda shi kanshi sai da yaji natsuwa ta shige shi, sai yayi murmushi ka'dan wanda ya tsaya masa iya gefen baki yace " kin kyauta ai yanzu kam, it seems like kinfi so ki cigaba da zama agida fiya da zuwa makaranta ko?"

Teemah kam kanta ta 'daga sama alamar " ehh"

Da mamaki ya kalleta yace " wai ke dagaske kike yi ne dama? Degree 'din ne baki so ko kuma me?
Baki so ki rin'ka zuwa makaranta irin na Hannah?

Da kanta ta sake bashi amsa tana wasa da yatsun hannun ta.

"Wonders shall never end" Yace aransa yayin da mamakinsa ya 'karu fiye dana da.

Bai 'kara kulata ba kawai ya shareta aransa yake tunanin may be bata da lafiya ne coz bai fiya ganin wanda ya nuna zallar 'kiyayyar sa da karatu har haka ba, shi ada datake cewa bata so 'din nan duk ya zaci wasa ne sai yanzu ta suprising 'dinsa amma duk da haka bai fasa ba yasan idan ta tsinci kanta cikin makarantar dole ne zata waraware ai tayi abinda ke gabanta.

Abbas be 'kara kulata da maganar ba har akayi kwana uku, kafin hakan kuwa zama mai kyau ma basu yi da ita ba dan saboda abubuwan da ke gabansa.

Ran kwana na ukun ne shine yace da ita nextweek zata fara registration dan already an yi nisa da bada admission shima da 'kyar yasamo mata admission 'din tunda batayi jamb ba zata fara ne tun daga remedial kawai sai ta fara preparation na zamowa student.

Tana jin haka sai ta yatsine fuska tace " Allah nifa banson wata makaranta Yayah"

Abbas be kulata ba kawai ya 'kyale ta coz ya riga ya yanke decision cewa matu'kar bazai tafi da ita Rivers ba kuwa makaranta dole ne agareta.

Kafin lokacin registration ne 'din ma shi ya koma ports bakin aikin sa, aranar ne kuma ya 'kira ta da sassafe cewa su tafi tare da Hannah ta rakata NILE, inda yace ta duba drawern 'dakin sa zata ga komai da zata bukata aciki.

Ko 'kala Teemah bata ce da shi ba har ya yanke 'kiran shima bai damu ba tunda yana da tabbacin tajishi.

Tana cire wayar a kunnan ta sai ta dannawa Ummah 'kira cikin siririyar muryarta da shagwa6a tace " Ummah kinga Yayah ko?
Wai sai na je Nile ni kuma banaso!

Cike da kulawa Ummah ta tambayeta "to wanne take so?"

Teemah kuwa tace " ni fah Ummah banason ko 'daya kuma ai na gaya mishi tun ranan ma"
Ta 'karashe tamkar zatayi kuka.

Ummah kam lalla6a ta ta hauyi tana bata baki da ha'kuri wai ko zata amince.

Amma Teemah ta kafe akan ra'ayin ta, Ummah ganin haka sai ta ha'kura ta 'kyaleta kawai tare da sanar mata cewan zata yi masa magana daga nan ta sallame ta.

Take Ummah ta sake 'kiran Abbas ta sanar dashi yanda sukayi da Teemah tare da bashi ha'kurin ya 'daga mata 'kafa zuwa wani lokacin 'kila da kanta ma ra'ayin karatun zai shige ta Ummah tace yabita a hankali aga iya gudun ruwanta.

Abbas kam zuwa yanzun haushi tafara bashi yarasa sam ita wace iriyar yarinya ce da komai ra'ayin ta sai ya bambamta da mutane ga shegen taurin kai, in haka ne kuwa tsab zaiyi maganin ta shima akan zuwa University 'din nan sai ya bata mamaki.

'Kin amincewa yayi da batun Ummah duk kuwa da da'da'dan kalaman da ta ringa yimasa saboda sanin halin sa amma duk da haka maganar bata wani shiga kansa ba sai ma yake ganin kamar iskancin Teeemah ne kawai yayi yawa ba komai ba, kuma ai karatun dan kanta ne zata yishi bawai shi zata yiwa ba toh ma miye abin gudu a makaranta in banda shirmen ta.

Ummah data ga bazai saurare ta ba sai ta sanar da Daddyn Abuja abinda ke faruwa.

Shima yayi mamakin hakan inda da kansa yasa suka zo da Hannah yaringa lalla6ata da bata baki akan ta amince da makarantar, saboda shima Abbas ya sanar da shi komai ya sanar dashi babban dalilin sa na son tashiga makarantar musamman ko dan ta rage zaman gida ita 'dayan ma da takeyi shiru kullum tunda Hannah ma ba yini take ba kwana ne kawai, Daddyn ma da kansa yayi supporting Abbas 'din 100% ya goyi bayan hakan dayake yasan shine ya hana Abbas 'din tafiya da ita. Dalilin kenan daya sanya ya ringa nuna mata muhimmanci da amfanin ilimi musamman ga 'ya'ya mata, harda manyan misalai ya ringa kawo mata amma yarinya ta 'ki canja ra'ayi duk kuwa da cewa ta fahimce shi.

Amma hakan bai yi mata tasiri ba sam dan ita aganin ta tunda ba ilimin addini bane toh babu ruwanta.

Daddy kam dayaga ita da Abbas 'din duk sun kafe akan ra'ayin su sai ya sanar da Daddy babbah ( mahaifin Teeemah).

Daddy murmushi yayi daya ji labarin abinda ya farun sam bai yi mamaki ba coz sarai yasan halinta da kafiyar ta kuma indai akan karatu ne haka Allah yayita tun tana yarinya 'karama sam bata so har garama na islamiya ta kan bashi muhimman ci.

Daddy ma awaya ya 'kirata cike da farin ciki ta gaida shi tare da tambayar sa Mummyn ta, Daddy yace tana nan lafiya sai ya 'kara da fa'din " Angel 'din Daddy sarkin rigima, ba nace ban son taurin kai ba shine kuma kike yiwa yayanki ko?"

Shagwa6e murya tayi tace " banayi masa fa Daddy "

"Toh ya akayi naji wai ance baki son karatu har kina 'karan Yayanki akan hakan?"

Hawaye tafara inda cikin hawayen tace dashi " Allah ni Daddy ban son wani makaranta shi kuma Yayah yace sai nayi ni kam banaso Allah"
Sai yace
" gaya min to ni inji meyasa baki so Angel?"
Tace "ni haka kawai ne Daddy"

"Bakya tunanin gaba zai miki amfani ko? karfa watarana kizo kiyi regretting akan hakan?"

"Insha Allahu bazanyi ba Daddy karka min fatan hakan, kuma ko nazo nayi ma bazan yi blaming kowa ba tunda nasan babu wanda ya hanani"

Daddy cewa yayi "shikenan to Angel 'din Daddy amma fa banda rashin ji kinji "

Da murnar ta tace "toh Daddy ai na ma daina"

"Yauwa uwata Allah yayi miki albarka yasa haske cikin rayuwarki"

Da "Ameen" ta amsa masa sannan sukayi sallama.

Daddy yasan kowani irin mutun nada kalan nashi burin da Allah ya halicce sa da shi hakama ra'ayoyin mu suke mabambanta ne.

Yasan halin Fateemah da taurin kai akan abu musamman idan batayi ra'ayi akai ba toh da wuya ka iya tan'kwarata, ha kama karatun yasan koda ansata bayi zatayi ba tunda bata yi niyya ba ba abin kirki zatayi ba kuwa ko da ta fara, shiyasa ma ya rin'ka biyeta lokacin da takeyin secondary school, makarantu sun kai hu'du ya ringa canza mata duk dan ta nutsu, duk wanda tace tana so baya gardama yake canza mata da 'kyar ta tsaya tagama aguda 'daya.

Shi karatu ra'ayine kuma ba'a ta6a yiwa mutun dole, domin kuwa ko ka tilasta wa mutun ya fara to in bashi da ra'ayi bazai ta6a yin karatun ba ballantana har asamu abinda akeso.
Chapter 142 · 0% Book details