← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 163

Sashe 21

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Muhibbat" tagani arubuce, karantawa rasake yi kusan sau uku, jitayi sunan ya tsaya mata aranta, amma daga ganin sunan tagane itace wacce yayi waya da ita d'azu dan tunda sukayi wayar bai kuma yin wata waya ba, kenan wato sunan wannan yarinyar ne Muhibbat d'in tunda da ita kad'ai yayi waya kafin ya fita a motar , ta6e baki tayi sannan tafita daga wurin k'ira ta nemi gallery ta shiga,images tagani sai kawai ta danna kansa ta shiga pictures d'insa ne zallah aciki, sai wanda taga sun d'auka su uku acikin parlour zaune akan kujera da wata yarinya bazama ta wuce sa'arta ba da kuma Ummahn Daddyn Abuja.

Yarinyar ma dashi take kama aranta tace k'ila itace wacce ake gulamata akanta d'in kwananki.

Canja folder tayi ta shiga camera, anan taci karo da zallan hotunansa masu d'aukar hankali, wasun sanye yake da kayan sojoji wani ma harda bindiga rik'e a hannunsa.

Cigaba da dubawa tayi takuwa dinga cin karo da hotunsa wani kuma bashi kad'ai bane,wani suna training ma akayi,cigaba da bi tai tayi harta iso wanda akayi da daddynta da daddyn Abuja da Ummah da kuma wasu daban da bata ma sansu ba,tana k'ara turawa taga wanda yayi shi kad'ai ya d'aga bindiga kamar zaiyi harbi.

Jitayi photon ya birgeta sosai,sai ta tsaya akan wannan d'in tana ta kallon shi,gani tayi yayi kyau sosai har bata son wuce wurin dan inta d'anyi gaba sai ta kuma dawowa baya.

Afili tace " ai dole kayi mugunta, mtun kullum cikin mugun hali, ashe har bindiga ne dashi shima wannan yanda yake da muguntan nan ai inkayi wasa wataran harbeka ma zaiyi"

Tana cikin maganar sai ta d'ago kanta ta kalli inda suke tsayen,ai kuwa sai taga yana k'ok'arin dawowa,da wuri ta mik'a hannu ta ajiye wayar a inda ta d'auka garin sauri ma ko fita a galleryn mantawa dashi tayi, jikinta har rawa yakeyi tsabar tsoro.

Sa'anta d'aya bai kalli inda ma wayar take ba, kamar yanda ita kanta bata samu kyakykywan kallo daga wurinsa ba.

Tada motar yayi ya nufi hanyar gida, tak'asan ido Teemah take kallonsa, sai yanzu take mamakin yaushe ma yazo garin harda zaiyi budurwa lalle wannan kam akwai aiki agabansa indai hakane, ta6e baki tayi tare da maida idanta ga titi,babu wanda yayiwa d'an uwansa magana har suka iso gida.

Cikin sanyi ta shigo d'akin dan sai da suka shigo harabar gidan kafin Mahmud ya fad'o mata arai.

Sai yanzu taji sabon missing d'in Mahmud d'in aranta," Allah sarki yayah"

Tace afili gurin mummy taje ta zube ajikinta ta kwanta shiru batare da magana ba, sai mummyn ce ta tambayeta ya akayi ?

Amsa ta bawa mummyn cikin sanyi " mummy yah Mahmud ya tafi ya barni"

"Abinda yakawo shi garin kenan ai Teemah"Mummyn tabata amsa.

D'ago kanta tayi sama tana kallon mummyn

"Toh kenan bazai sake dawowa ba mummy"
Ta sake tambayar mummyn nata.

"a a zai dawo mana nan da 3weeks insha Allah"

"Allah ya nuna mana" kawai Teemahn tace sannan ta maida kanta kan cinyar mummyn ta kwantar.

Mummy har ranta sai taji tana tausaya wa 'yar ta ta, domin tasan illar shak'uwa ba dad'i musamman in aka had'a da kalmar rabuwa toh sai a hankali.

Abbas kuwa yana shiga d'aki ya d'aga wayarsa da zummar k'iran daddynsa dan yau basu gaisa ba kwata-kwata yana bud'e wayar sai yaga hotonsa afiskar wayar
mamaki ne yacika shi dan shi dai yasan bai san picturensa a wallpaper ba,amma ga mamakinsa daya shiga sai yaga ashe akan gallery ne wayar take

"TEEMAH"
Ya anbata dan ita tafara fad'o masa kuma yasan inba ita ba babu maiyi masa hakan.

Murmushi ne yaji ya kwace masa da ganin hakan sai zuciyarsa ta tabbatar masa da cewa ai photonsa ta tsaya kallo shiyasa har tamanta ta bari akai abinka da marar gaskiya.

Sai hakan yad'an sanyayah masa zuciyah.

*****
Koda da dare da akaje cin abinci ma cakula ta dingayi M har aka k'are cin abincin ita bata ci komai ba.

Duk Abbas na lure da ita, sarai yasan matsalarta, dan shima dauriya kawai yayi yaci abincin, wannan abin nan da Teemah keui jiyake kamar azabtar da zuciyarsa takeyi,ita kuma bata san hakan ba, dan kar aga kamar abu na damunsa ne shiyasa kawai ya daure yaci saboda sanin halin mummy da yayi dan tana ganinsa wani iri zata saka sa agaba da tambaya ne shikuwa bai san amsar da zai bata ba.

Kwanan Mahmud biyar kacal agidan kai agarinma gaba d'aya amma zakayi mamakin shakuwar su da Teemah, acikin kwana biyar d'in kwana d'aya ce da wuni d'aya rak ta waru wanda yakasance Mahmud bashine ya ciyar da ita ba amma sauran kwana kin duk shike bata abincin abaki hakan sai yana tuno masa da rayuwar su tabaya.

Washegari Habibu ne ya kaita makaranta da yake ya dawo tun last 3days, koda akaxo cin abinci ma da daren ranar haka tayita rarraba idanu,dan rana kam ma bata cikin lissafi ita ba'a maganarta danko waiwayo gun abincin batayi.

Har suka gama bata ciba ita, mummy ce tafara mata surutu akan tunjiya ta lura bata wani ci abinci agidanba, amma daddy yace "tabarta ai ita tayi ra'ayi ba wani ne yace karta ci ba, kuma ai intana jin yunwa dakanta zata nema basai ansata ba".

Jin haka yasa ta cewa " nama fah ci amakaranta daddy"

"Toh ai kinji" daddyn yafad'a yana kallon mummy

Tsaki kad'an mummy taja daga nan bata k'ara kallon inda suke ba ma dan takaici.

Tun daga ranar Abbas yarage ganinta ma gaba d'aya, dan yanzu mummy ma ta daina damun kanta tunda ta lura daddynta ke goye mata baya.

Bak'aramin jin haushin abin nan datake yi d'in yake ba, amma bai ta6a kulata ba, sai dai yana ganin kamar ta raina su ne gaba d'aya.

Kuma abin mamaki rainin datake masa na rashin kunyan bata ta6a yiwa Mahmud ba koda sau d'aya a lokacin da yake gidan.

Idan ya tuno yanda take sake jikinta suyi ta hira da Mahmud d'in suna wasa da dariya,in baka sani bama sai kace agida d'aya suka taso sa shi.

Lokuta da dama idan yana ganinsu a hakan bak'aramin jin haushi da takaici yakeji ba, amma bai ta6a nuna musu hakan ba,nuna musu yakeyi sam bai damu da al'amuransu da shirginsu ba ma.

Koda korarta da ya keyi wasu lokuta idan tazo yana yi ne irirn kamar tazo ne zata damesu da surutu bawai dan wani abu ba kuma ko Mahmud d'in ma haka ya d'auka.

Sai shima Abbas d'in ya tafi a hakan dukda manufarsa daban shi kam, dan azahiri takaicin ganinsu taren ne yake sashi koranta.

Sarai yasan rashin sakin fuskan da baya yi matane ya sa ta ke k'insa da kuma hana tayi sabo da shi, dan shi da Mahmud they are 2 different people halayyarsu ta d'an banbanta kad'an amma tsabar zafin kai sai ya take wannan ya d'au laifin gaba d'aya ya d'ora mata.

Kawai sai yasa aransa cewa ai raini ne yake damunta..........

Koda awurin cin abinci lokacin da Mahmud yake nan sosai suke bashi haushi, dan tunda Mahmud ya fahimci bata kula abinci sai an gayyato ta ko kuma an tilasatata, tundaga lokacin sai Mahmud ya d'auki d'amarar sata taci dan dolenta koda bata da ra'ayi.

Ko kunyar su mummy baya ji haka zai ta lalla6ata akan ta ci abincin ita kuwa tayi ta yanga da shagwa6a, haushi kamar yakashe Abbas amma adole yake mazgewa.

******
Gani yayi abin nata sai k'ara gaba yakeyi gashi indai aka zauna sai ta sako hirar Mahmud,abinci kuwa sai abinda yayi gaba.

Abbas ma daga baya daina zuwa kan dinning d'in yayi gaba d'aya, da farko mummy ta tura Teemah akan tak'ira sa sai yace mata he is full,the following day ma haka sai dai wannan karon da taje ki'ran nasa cemata yayi taje ta kawo masa abincin ad'aki zaici.

Zuwa tayi ta had'o takawo masa,tana shirin fita ya tsaida ta kamar wanda zaice ta mik'a masa wani abu amma sai jitayi ya tambayeta wai " taci abincin ne ita"
kai ta jijjiga masa alamar a a, ai kuwa ya tsareta yace wai dole sai taci abincin data kawo masa d'in inbata ciba kuwa shida ita ne dan harbeta zaiyi da bindigan sa wai kanta zai fasa babu abinda ya damesa.

Vote, share nd comment🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 5:57 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_This page is specially dedicated to my dear fans

Mar-yerm
Ummu Haidar
Meerameen
Ummul Abdul
maman Husna
Ummi
Tamama
Bintu kabir
Nanah
Wash........ idan nace zan k'irgo ku yawa ne daku

Hak'ik'a ku na daban ne, kamar yadda soyayyar ga littafin nan yake na daban.
Allah ya bar k'auna.❤😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

There’s a story behind every person. A reason why they are the way they are. Think about that before you judge someone.

🅿 *21*

Aikuwa tazauna ta hau cin abincin adole duk da ranta bayaso amma haka ta ta turawa, shikuwa yana kwance abinsa da wayarsa a hannu yana ta aikin dad-dannawa, data ga ta k'oshi sai kawai tafara hawaye.

Allah ya taimake ta adaidai lokacin sai ya d'ago kai ya kalleta da niyar ganin ko tana ci d'in ne ko kuma a a, sai yaga taci ma kusan rabi amma tana kuka, suna had'a idanu kuwa ta sake kukan nata mai sautin sa ya bayyana.

Dariya tabashi shikam amma sai ya tsare bai dara ba.

Tashi yayi ya zauna kafin ya zubo da k'afafun sa k'asa sannan ya sake kallonta.

"Miye kuma na kukan?
Ya tambayeta.

Batayi magana ba kawai sai ta cigaba da kukan ta abinta.

Kyaleta yayi kawai yatsaya kallonta tana kukan kusan mintina biyu sannan yasake magana "idan bazaki fad'a min ba kimin shiru inba haka ba Allah makeki zanyi"

Cikin shash-shek'a tabashi amsa da
"nah.........nah......k'oshine..........daga k'arshe taja dogon ajiyar zuciya.

Sosai maganar ta d'in ya k'aramar dariya amma sai ya jijjiga kansa kawai"yarinyan na bazaki ta6a girma ba"
ya fad'a acikin ransa sai yayi murmushi agefen bakinsa.

"Tashi kije"

Yafad'a yana komawa kwanciyar daya tashin.
Chapter 21 · 0% Book details