← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 163

Sashe 46

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakimce yake a seat 'din baya inka ganshi zaka zaci wani basareka ne musamman inkayi duba da yanayin zaman dayayi, yawani hakimce baya fa'din komai sai in lokacin da zai yi magana da driver ne kafin zakaji muryarsa, balle ma ba wata maganar kirki sukayi tsakaninsu ba inya wuci aikin bada umarni.

Da ikon Allah kuwa lafiya lau suka isa, Abbas saka drivern yayi ya yi tu'ki a high speed shiyasa suka isa dawuri, kuma cikin kariyar ubangiji babu wani abin da suka ha'du dashi ahanya wanda yake ba daidai bane.

Da shigarsu cikin garin Maiduguri sai suka wuche gidan ogansa me suna Oga philip, suna yin horn me gadi ya bu'de musu 'kofa.

Ko zama Abbas beyiba ya fara shirin tafiya inda ya fito oga Philip bai so hakan ba amma Abbas yace ana nemansa ne shiyasa, dolen oga Philip ya barshi yagama kintsawa yafito, lokacin 'karfe hu'du kusan da rabi na yamma 4:28pm , sallama yayi musu tare da godiyah sosai saboda Oga philip mutun ne daya cancanci ayi masa godiya, tun farko Allah ya ha'da jininsu da Abbas tun farkon ha'duwarsu awurin wani course dasuka je bada jimawa ba, yana shiyake kula daduk wani abu dayashafi Abbas 'din ko kuma zai taso ta 6angarensa yakan yi 'ko'kari sosai wajen ganin ba'a samu wata matsala ba.

Duk sau'kan da Abbas zaiyi a maiduguri toh Oga philip ne ke bashi masau''ki ko a agidansa ko kuma wani gidan daban, shiyasa ko wannan zuwan ma da yayi sai ya sau'ka agidansa, bashi da matsala komai,inkuwa yaji an'kira sallah baya 6ata lokaci yake isa masallacin dayake akwai akusa dasu, kuma daya sanar dashi cewa yana so yaje damaturu amma yace bazai kwana ba aranar zai dawo sai Oga philip 'din yace " toh ba matsala daganan ya ha'dashi da driver suka kama hanya suka zo damaturun atare, yakuma ce da drivern yakula da tu'ki da kyau dan kawai saboda Abbas 'din.

Yanzun ma sawa yayi aka 'kara kai Abbas 'din airport yakuma binshi da fatan alkhairi.

Bai 'kira kowa ba aranar sai mummy ya mata sallama awaya dayake itan basu ha'du ba lokacin da zai tafi shiyasa ya 'kirata yace mata ya wuche Porthacourt.

Sai dai kuma tun lokacin da yatafi ya bar Teemah a tsaye yakejin be kyauta mata ba harma dashi kansa, sai yake jin dama ya tsaya ya kar6i leave awurin aiki kafin ya taho 'din da yasan komin yaya de zai 'dan yi kwana biyu, da zaiyi irin wannan tafiyar ba.

Amma yazaiyi hakan ma ba laifi tunda yagama abinda yakawo shi dama burinsa yaganta kuma yagantan, wannan ma satan hanya yayi shiyasa and baya son tun ba'aje ko'ina da fara aikin ba ya fara samun problem dasu shiyasa yatafi aranar batare da ya ko tsaya sun yi gaisuwar kirki da su daddyn ba dan ma kar ya shiga cikin lokacinsa.

*DAMATURU, YOBE* *STATE*

Koda fitan Teemah a'dakin direct 6angaren mummyn ta nufa dan cika umarninta, mummy kuwa bata bi bayanta ba sai ma kujera dataja tayi zamanta, su Abbah nagama cin dinner suka sha hirar yaushe gamo da kuma tuna baya da yayan nata wannan karon faran-faran batare da wani damuwa
ba.

Daddy ne yace maza ta tashi ta tafi dan kamar yaji tace Teemah ta jirata a'daki yace tayi sauri taje kar
ta hana masa yarinya bacci.

" su yarinya manya"
Inji mummyn
Tana dariya tabar 'dakin tare da yi musu sai da safe.

Koda ta isa 'dakin nata kuwa barci tasamu Teemahn nayi abakin gadonta kamar ma zata zame ta fa'do, aranta tace " Allah sarki harta gaji da jira tayi bacci.

Taso ta tasheta amma ganin yanda tasake take bacvcn sai ta 'kyaleta kawai anan 'din sai dai ta 'dan bigeta ahankali tace " ta gyara kwanciyar tata da kyau.

Daddy har yayi shirin bacci sai kuma yaji kamar akwai kukan sauro ka'dan a'dakin kuma gashi yanada ba'ko sai yace bari ya 'dauko magani dayake shi dama ba so yakeyi ba be fiya anfami dashi ba dama mummy ce dayake ita ko kukan sauro na hanata bacci shiyasa sam bata rabuwa da insecticide a'dakinta.

Mummy nagama shiri kenan saura ta kwanciya, sai kuma tajiyo kamar motsi a parlour da farko harta 'dan tsorata sai ta tsaya cak a inda take tsayen, tana cigaba sauraron motsin yayinda yake 'kara tunkaro ta sai kuma tajiyo muryar daddy yana sallama ahankali
saboda dare.

Sai da ta amsa kafin tace " ai har kaban tsoro ma"

" very sorry, maganin sauro za'a bamu naji kamar akwai 'dan kukan sauro a'dakin".

" ah ah kaida kece bakaso?".

" ehh albarkacin ba'ko za'a bani "

"Hmm kai de fa'di gaskiya "

Tayi maganar tare da juyawa dan zuwa inda maganin yake ajiye, sai kuma asannan daddy ya lura da Teemah dake kwance, "sai da kika samin yarinya bacci anan ko?"

Sai tayi saurin fa'din " kafin nazo ma harta yi baccinta".

" badole ba ina zata iya jiranki kinje kin samu Yayanki kina ta'di kin manata da ita, badole tayi baccinta ba itama, aini banga laifinta ba".

Batayi magana ba bayaga " hmm" kawai sai mi'ka masa Insecticide 'din shi kuma maimakon ya kar6a a'a, sai ya mi'ka hannunsa ya cafko nata hannun yajata zuwa parlour binsa tayi kamat ra'kuma itama.

Zama yaje yayi akan kujera ita kuwa sai takalleshi da mamaki tana daga tsayen tace " yalla6ai ya haka naga ka zauna?".

" magana zamuyi Khadija "

Ido ta zaro waje tare da fa'din yanzun kuma?, da daren nan."

" ahakan tazo Khadeeja, kuma ahakan za'ayi"
Ya fa'da in a serious tune ,ganin hakan yasa mummy taje ta zaunan itama ta fuskance shi.

" yauwa ki saurareni da kyau kiji, kinsan Yusuf 'din nan abokina ne shi tunma kafin na ha'du da ke right?

Sai tace " ehh".

" toh amatsayinsa na abokina misali idan akace ya nemi alafarma agurina kina ganin ya kamata na'ki saurarensa"?

tace
" a'a "

" saboda me"?

" saboda zumunchi ,kuma ya kamata ka karramashi amatsayinsa na aboki agareka."

" idan kuma ya 'kara da zamowa sirki ( in-law) agareni fah "?

"Fiye da hakan ma zakayi masa inda hali".

"good".
Yace da jin da'di sannan yaci gaba da fa'din
" Yataso ne musamman all d way from Lagos ya zonan dan kawai yasada zumunci dake tsakani, wanda nake tunanin cewa ada sam babu shi, nasan kinsan da haka ko"?

" ehh"
Tace asanyaye dan tafara jin tsinkewan zuciya akan wannan irin maganganun daddyn.

" Lokacin da zaizo be zo da niyyar neman aure ba face abin da nafa'da miki abaya, saboda ya sanar dani da jimawa akan zezo mana nan amma bai sa rana ba saboda kar ya saka rana yazo tafiyar bata yiwu ba, shiyasa yabari ahaka nima kuma dalilin dayasa na'ki fa'da miki kenan, amma Alhamdulillah sai gashi yazo mana batare da munsan ma yataso ba, sai kawai muka ganshi.

"Hakane"?

Mummy kai kawai ta 'daga masa domin jikinta yafara yin sanyi da wa'dannan irin maganganun, kardai Yah yusuf ku'di yake bu'kata awurin Daddy, haba no waonder taga ya rame ba kamar da dayake da 'dan 'kibarsa ba, ashe ya'dan shiga damuwa ne shiyasa...............

Firgigi tayi tana kallon daddyn domin tana cikin tunanin tajishi yace " kina jina" da 'dan 'karfi, bata sani ba ashe bakinsa na biyu kenan domin na farkon kamma batasan yayi ba.

Ran'kwafowa yayi yana dubanta da kyau sannan yace
" tunanin me kuma kike yi Khadeeja"?

Bakinta har karo yakeyi wajen fa'din " ba komai".

Owk
Yace sannan yaci gaba
" Allah cikin ikonsa tun da yaga Fateemah sai ya yaba da hankalinta harma yace yanason aurenta ma 'danshi Mahmud"

Ido mummy tazaro waje tare da mi'kewa tsaye akan daddyn.

" Mahmud de"
Tafa'di tare da nuni da wani 6angare tamkar Mahmud 'din yana wajen.

" shi de bawani ba, be yi bane ko me"

Shiru tayi still tana tsayen.

Hannu ya mi'ka yakamo nata hannun

"Zauna mana sai ki yimin bayani da kyau wala Allah zanfi fahimtarki".

Zaman tayi kamar yadda ya bu'kata amma bata iya yin wata magana ba.

Daddy kuwa sai yaci gaba da fa'din

" Khadija mun kusan kammalawa da maganar ahalin da ake ciki yanzu 'karshen furuci na kawai yake jira yaji".

"Toh kace masa baka amince ba kawai"

" awani dalili"
yaddyn ya tambayeta.

" Habah, haba dan Allah Mahmud fah naji kace?

" ehh mana, ko kina da wani wanda kike ganin yafi Mahmud 'din"

Karka'da kai tayi cikin takaici
"Amma inajin ka manta wacece mahaifiy..........

" hold it pls, lets go straight to d point, ok!".
Yatari maganan da tayi niyyan fa'din cikin gaggawa harma da 'daga hannunsa 'daya sama , wanda hakan 'karara yake nuni da cewa baya bu'katan jin komai daga gareta.

Shiru mummy tayi tare da binsa da idanu, mamaki ma yake bata daman ta da'de da fahimtarsa aganin ta shi sam baya so yaji anfa'di karkatacciyar magana akan Yah yusuf 'din sai yayi 'ko'karin gyarata, shiyasa da datake yawan complain akan sharetan da yakeyi shi daddyn shine me tausarta akullum sai ya nuna kamar wai abubuwa ne suka masa yawa, sai da abin yayi yawane kafin shima ya saduda ya goyi bayanta amma duk da be ta6a nuna mata cewa Yah yusuf 'din badai dai yakeba, sai de yace suci gaba da addua kawai, kuma duk wannan abubuwan dasuke faruwa ita aganinta bakomai kesa daddy yin hakan ba face akan goya masa baya da Yah yusuf 'din yayi lokacin da daddyn ya nemi auranta.

Jinsa yayinda shi kuma yaci gaba da fa'din
" munyi magana dashi kuma na fahimce shi, ayanzu kuma gab nake da nuna amincewa ta 100% saboda girma dayake dashi a idanuna, bazan iya 'kin nuna amincewata ba kuma ina fatan kema zaki goya min baya with all your support".

Ya 'karashe maganan yana kallonta.

Itama kallon nasa ta tsayayi daga baya baya kuma ta kauda kanta gefe.

" taya za'ayi na goyi bayanka alhali ina da tabbacin Anty bazata ta6a son zuri'armu ba, balle ma har ace 'yar da ni na haifa, 'danta ya aura!"
Gashi kai kuma ka kasa fahimta ta"
Chapter 46 · 0% Book details