← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 163

Sashe 123

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu ta ha'da mata a cup da madara tabata ta ce ta shanye zafin zai daina da iznin Allah.

Teemah da bata san ko menene ba kar6a kawai tayi ta shanye abinta dan so takeyi zafin datake ji ya daina gaba 'daya ko dan tana yin fitsari ba fargaba ma.

Yanzune Anty ta fahimci cewa barrier 'din da Munnira tayiwa Mahmud da Fateemah yayi tasiri akan su, yanzu ne ta sake tabbatar da gaskiya cewa Mahmud be 'dorawa Fateemah iddar komai ba har yakoma ga mahallicin sa.
Ha'kika ta cutar da rayuwar 'danta ta fuskoki da dama, addu'ah tayi masa cikin ranta tare da nema masa gafarar mahalicci.
Lallai da gudummuwar ta rayuwar gidan 'dan ta na cikinta ya ta6ar6are, ha'ki'ka bata kasance uwa tagari ba, bata fatan irin hakan yasake faruwa ga rayuwar wanin ta har abada.

'Ko'kari tayi ta maida hawayen ta tace yah Allahu kayafemin, ka kai haske cikin 'kabarin Mahmud.

*2:20pm*
Hannah ta dawo da mugun gajiyar ta inda tasami Ummah da Abbas zaune a parlour suna 'dan ta6a hira, zama tayi a kusa da Ummah tare da fa'din " _wash Allah na, Ummah na gaji sosai yau 'din nan,_ _Allah gudowa ma nayi_ ".

Abbas kallon ta yayi da mamaki yace
" _saboda me kenan_ ?

Hannah juya idanu tayi sai suka ha'da ido da Ummah afakaice, sai tace " _Yayah lecture 'daya ne yarage mana kuma ance lecturer 'din baya gari shiyasa na taho_ "

Abbas shiru yayi ya dai ji tane kawai ba wai dan ya yarda ba, amma be kulata dan shi yanzu damuwar da ta dami ransa dabance, so yake yasan halin da matar sa ke ciki kafin ya wuce.

Hannah gaishe shi tayi sai ta tambaye shi " _Yayah ya Teemah fah_ ?

Kafin yayi magana sai Ummah ta bata amsa da fa'din " _tana ciki tare suka zo, ba mamaki tana wajen Antyn ta_ "

Hannah najin haka ta tashi da sauri jakar ta ma anan tabari ta nufi ciki.

Teemah har yanzu tana wurin Anty inda take 'kara jan hankalin ta akan ri'ke mutuncin aurenta sanin girma da kuma darajan da mijin ta ke dashi tare da ri'ke sirrin dake tsakanin su.

Da sallama Hannah ta shiga 'dakin ta samu Anty na 'daure wa Teemah gashin kanta.

Da gudu taje ta rungume ta tana fa'din " _i so much miss u matar Yayah!tun yaushe kuka zo_ ?

" _Zaki karyani Hannah dan Allah_ !
Inji teemah

Hannah kuwa sai tace
" _Ba laifi ai kona karyakin be wuci ace 'kiyayyar dangin miji ba_ "

Murmushi Anty tayi tace musu maza su koma 'dakin su suje su huta wannan hayaniyar ta isa haka.

Suna shiga 'dakin Hannah ta sake tambayar ta wai tun yaushe suka zo?

Da
" _Bamu da'de ba_ " Teemah ta bata amsa tana yatsina fuska.

Abbas har zai tafi sai yace da Ummah bari yaga Mummy kafin ya wuce.

Yana shiga 6angaren da zai kaishi 'dakin da Mummyn take sai yajiyo hayaniyar Hannah yasan may be suna tare ne tunda yaji hayani ya har haka.

Canja hanya yayi ya isa 'dakin Hannah be tsaya bugawa ba kawai ya tura 'kofar sai ya tsaya batare da ya shigo ba.

Shiru sukayi da ganin san dama ita Teemah ba wani dogon magana takeyi ba Hannah ce me surutun.
Shi kanshi be san me yakawo shi ba, zuciyar sa ke bu'katan hakan, dama ganin ta yaso yi kuma daya gantan sai ya rasa abin fa'da kawai sai ya 'karaso cikin 'dakin a hankali, yazo gabanta ya tsaya yana kallon ta a hankali ya furta " _ya jikin naki_ ?

Da sauri tace dashi " _da sau'ki_ "

Yace " _toh zan tafi amma anjima zan dawo mu koma gida kinji_ "

Teemah shiru tayi masa shima sai kawai ya juya ga Hannah yace
" _Hannah plz ki tabbatar taci abinci_ " Yana gama fa'din haka ya fice a 'dakin cikin takunsa na 'kasaita, shi kansa yana mamakin kansa a yau 'din yanda yake ji game da matar tasa, Hannah na wurin ne ma shiyasa be son jan magana sosai.

Yana fita Hannah ta tashi da sauri ta le'ka bayan sa ganin yatafin yasa ta sake dawowa wurin Teemah ta dafa kafa'dar ta da mamaki tace " _matar Yayah nifa bangane ba, me ya sameki naji Yayah yana tamabayar jikinki harma da bani kwangilar saki cin abinci_ ?

" _banda lafiya ne_ "
Teemah ta bata amsa a takaice.

Karkata kai Hannah tayi da zararran ido take kallon Teemah da sigar tsokana tace " _Ciwon amarci ko?_

" _Wata'kila_ "!
Teemah tace tare da gyara zamanta.

" _Kede fa'di gaskiya matar captain ai nima naganki badai ba_ "

Da 'dan 'karfi Teemah tace
" _Bansani ba Hannah plz ki 'kyaleni ke dama ba mutun ya ha'du dake ba duk_ _yadda yakai ga kewar ki sai kin 6ata ran mutun kike jinda'di_ "

Dariya Hannah tayi tace " _Come down mana amarya! 6ata ran me kuma nayi miki amaryar Yayah fisabilillahi? ke de kice bakya so in san cewa Yayah ya fa'da_ _ne, amma ai tun 'dazu ma bangane kanki ba duk kin canja Allah kinyi wata iri_ _ashe ashe yarinya taji da bambanci ne_ !"

Saukar da murya Teemah tayi tace
" _Hannah Allah banaso bambancin me kuma naji?_

Da murmushi Hannah tace

" _Kin fini sani ai yarinya keda kika san komai kuma ni zaki tambaya, jifa yanda yazo shima 'daya ko kunya_ _bai ji wai ya jikin naki.? Bayan yana gani na wurin ko kunyata fa be ji ba"_
Baki ta kama tace " _kai Allah ya shiryi Yayah wallahi_ ".

" _Kema Allah ya shirye ki ai kema ba kunyar ne dake ba da kike waya da Bilal a inda nake kina jin kunyata ne? kuma kamar a kunnan sa hakan da kika ce"_

" _Bazan yi mamaki ba ai nasan yanzu amarya kike kuma ba kya laifi, so ko kin kareshi ma nasan ba laifin ki bane, ballantana_ _yanzu da kika san da'din miji nasan fiye da haka ma zakiyi, sai dai plz kiji 'kaina karki fa'dawa Yayah_ _abinda nace nayi al'kawarin indai da raina zan tayaki zaman jego da rainon baby_ "

Duka Teemah ta kai mata tare da fa'din "' _yar rainin sense_ _kawai_ "
sai ta goce tana dariya tace " _Toh ina laifi da zan miki zaman jego tunda wannan 'din ba a gayya ceni ba wancen kam_ _ai kinga ko babu gayyata sai naje may be ma sanadin haka na samu namesake_ "

" Allah ya kiyaye 'yata tazama takwararki"

Hannah kwafa tayi tace " _Harma_ ....."?

Da " _ehh_ "

" _aw ashe ma zaki haihun kinga kuwa zuwana tabbas_ "

Teemah ta amsa mata tayi da fa'din " _bismillah sai ki je ai mugani_ "

" _Dai na gagagwa kamar yau ne insha Allahu matar Yayah ai anyi me wuyan.... kai amma fa nasan kin ji jiki da ganin_ _yanda kika koma har kina bani tausayi wallahi_ "

Juya wa Teemah tayi ta kwanta kawai tana mita wai Hannah ta tattare surutun duk 'yan gidan nan akanta, she is so talkative ita bazata iya da surutun Hannah ba.

Hannah ma tashi tayi tana rage kayan jikin ta take sake fa'din " _dan Allah matar Yayah in zaki haihu ki haifo min baby girl me kama dani_ _kinji_ ?

Teemah 'kin kulata tayi da Hannah taga haka sai tace bari ta je ta kawo musu abinci......tana fitan tasake fa'din " _ko baki kulani bama de sai kin haifa_ "

Abbas daga wurin Mummy ya wuce bai sake dawowa ba.

Ko gurin cin abincin Hannah bata bar Teemah da tsokana ba har suka 'kare.
Sai daga baya suka koma wajen su Mummy anan ta sake suka ta hira abinsu kamar ba ita ba.

Sai bayan sallar isha'i Abbas ya dawo gidan dan su tafi, lokacin kuwa hajiya Fateemah an saki jiki a gida kawai sai taji labarin wai yazo.

Ummah ce tace ko za'a barta agida kawai zuwa gobe sai ta koma saboda ganin kamar Teemah batason tafiyar.

Teemah kam da murnar ta ta amsa da " _ehh Ummah...._ "
Da sauri Mummy da Anty suka ce " _ah ah tafiya zatayi, zaman me zatayi musu kuma anan, gara ta koma gidan_ _mijinta yafi_ "

Dole Ummah tayi shiru dan bakin su yafi nata.
Da fushi kuwa ta tafi suka bar su Hannah da kewa.

Bayan tafiyar su ne Anty tayi wa su Ummah bayanin cewa dama ba iddar Mahmud akan Fateemah, Mahmud be 'dora mata iddah ba, tabasu labarin duk abinda ya faru game da hakan da yake a baya lokacin rasuwar Mahmud bata bayyana wannan 'din ga kowa ba saboda aganin ta sirri ne.

Dukkan su sunyi mamaki sosai sai abin yaso ya dawo musu sabo aransu kowa na tunanin ashe har haka Teemah tayi zaman 'kunci tare da Mahmud lalle duniya abin tsorone, tunda gashi wanda akayi domin san ma babu shi yatafi ya bar kowa da tarin nadama.
*Allah Ubangiji ya sa mufi 'karfin zu'katan mu ya kyautata mana 'karshen mu.*
( ~Ameen~ )

Mummy ce ke wannan addu'ar acikin ranta, Anty kam hawaye take sharewa a hankali dan ta tuna da 'danta marigayi, Ummah kuwa har taje bacci tana tunanin wannan abin aranta.

Suna komawa gida direct 'dakin Abbas suka wuce amma bai bari ta kwanta ba sai da ya bata magani tasha sannan ya bari ta kwanta yaraka 'dakin ta canjo kaya ma 'ki yayi dole sai da ta saka wata t-shirt 'dinsa mai 'dan girma sai kuwa rigar ta rufe mata jiki ka'dan domin ya'dan sau'ko mata, shi kanshi Abbas rigar tana bashi balance bai fiya sakata ba sai in yanada bu'katar shan iska., wanka ya shiga koda ya fito ya shirya ma sai da yayi sallah sannan ya hawo gadon, jikinta yazo ya matso ya rungumo ta Teemah take ta fara 'ko'karin barin jikinsa da sauri dama 'dari-'dari takeyi dashi shiyasa tun 'dazu bacci yakasa 'daukan ta, Abbas sai ya ra'da mata " _come on... ki nutsu ban son rigima i thought rage miki wahala zanyi, naga anjima dakan ki ma zaki shige min jiki_ _ko da banaso_ "
Chapter 123 · 0% Book details