Sashe 12
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Janyo Teemah tayi ta rungume ta kiyi shiru,ki daina kuka kinji,kukan farin ciki nakeyi Teemah cikin ikon Allah bayan wasu tsawon shekaru zanga wani daga cikin danginah,Teemah jinin d'an uwana,maganar take tana murmushi amma still hawayenta bai daina zuba ba,kana ganin yanayinta zaka gane tana cikin wani irin yanayi ne marar misaltuwa.
Daddy ma ido ya zuba mata yana k'ara jin tausayinta acikin ransa.
Sallar la'asar ne ya tada su awurin,Daddy da Abbas suka wuce masallaci,Teemah kuma da mummy kowa ta nufi d'akinta.
Kafin isowar Mahmud d'in mummy akullum annurinta k'aruwa yake yi,komai tana yinsa cikin walwala da farin ciki,da ka ganta kasan annurin daya ke kwance asaman fusakrta har cikin zuciyarta yake,musamman yau daya kasance suna saka ran isowarshi agobe.
Musamman taje kasuwa tayi siyayyah sosai wai afad'arta duk na taran d'anta ne.
D'akin da zai zauna kuwa tun jiyah aka gama gyarasa tsaf,aka sa dukkan wani abin buk'ata aciki.
Washe gari asabar mummy dawuri ta tashi ta taso k'eyar Teemah ma,seda suka koma ta sake duba d'akin da zai sauk'a aciki ta tabbatar da babu wata matsala kafin suka fito,Teemah mamakin wannan al'amarin yabi ya cikata.
Kitchen sukaje da mummyn anan suka samu Baabah Lami,dukkansu mummy taraba musu ayyuka,yau da kanta tayi girkinta duk wanda take ganin zai burgeta shi tayi kusan kala uku,juice kuwa sun had'a d'aya already ansa afridge,gasu kuma suna kan had'a wani daban,inka ga yadda mummy ta dage agirkin,ka kuma dubi yawa da kalolin abincin zakayi tsammanin family guda ne zasu zo,abin ya d'aurewa Teemah kai,ita de jitayi ance mutun d'aya ne zaizo amma ga mamakinta sunyi girkin da kusan mutane goma ma zasu ci su kuma rage saura.
Kallon mummyn nata tayi sannan tace "mummy wai bak'i nawane zasu zo?
Mummy cikin murmushi tace "Mahmud ne zaizo Teemah."
"Mahmud d'in shi nawa ne mummy?
"'D'aya mana Teemah,wai miye matsalarki ne ke kam.?
Kauda kai tayi daga kallon mummyn ta cigaba da blending d'in data keyi,amma sai taji zuciyarta ta kasa hak'uri da wannan abin.
"mummy amma de kinfi sanshi akaina ko?
Dariya sosai tabawa mummyn hakama Baabah Lami,dariyarta sukayi san ransu,Teemah kuwa ta wani basar ko kallon inda suke batayi ba dan ita tambayarta har zuciyarta tayisa,so ta ke taji amsarta amma kuma sai suka maida maganar abin dariyah.
Saida suka tsagaita ne Baabah Lami tace "kai Fatu tun yanzu harkin fara kishi ne?
Fushi ta k'ara akan nada d'in datayi,dan maganar baabah Lami duk abin haushi ne awurinta.
Wai fatu........
Kuma wai tana kishi..........ita aganinta ai gaskiyarta ne,dan yanda taga mummyn na zumud'in isowar Mahmud d'in dole ya sosa mata zuciyah amatsayinta na y'a k'walli d'aya tal agun mummyn,aiko zuwan Yah Abbas ma mummy batayi wannnan azar6a6in ba,koda yake shi zuwan bazata yai musu basu san da zuwan nashi ba,kawai sai de suka ganshi.
Turo baki ta k'ara yi gabamummy ce tace mata
"ki rabu da Baabah Lami d'innan kinji yayanki ne fah,ana kishi da yayah ne kuma ai ba'a yi,
kinga ni kuma ai dole nayi farin ciki da zuwansa shekaru nawa rabo na dasu Teemah."
Lalla6anta mummyn ta cigaba dayi da kalaman kwantar da hankali,dan tasan halin Teemahn nata ba dai kishi ba,haka tayi ta binta a hankali har suka gama aikin gaba d'aya.
Sai bayan la'asar kafin Mahmud ya iso gidan, lokacin Abbas da mummy ne kad'ai agida.
A babban parlourn gidan suka fara sauk'ar dashi, lokacin da mahmud ya iso daddy baya nan,Teemah ma tana islamiya,mummy tayi murna da farin cikin zuwansa sosai,Abbas kuwa sai dai ido,dan mummy murnar tata tanayi ne had'e da hawaye tana tambayarsa labarin iyayensa,shima d'in duk jikinsa yayi sanyi dan anjima ba'a had'u ba amma shi bai wani yi kuka ba,ganin mummy takasa daina hawayen ne yasa Abbas ya fara bata hakuri duk da bai san manufar kukan nata ba.
Koda teemah tadawo ma sannu da zuwa kad'ai tamasa,dan ba saninsa daman tayi ba,gara shima yasan da ita,kawai dai rashin zumunchi ne yasa babu shak'uwa atsakaninsu.
"Fatima zarah "
Ya k'ira sunanta lokacin data mar sannu da zuwa d'in,dayake sunzo sunanta kuma fatima zarah shine sunan da aka ambaceta dashi aranar.
Amsawa tayi daganan tawuce ciki abinta batare da ta zauna a inda ta tarar dasu d'inba.
Sallar maghrib ne ya tadasu a parlourn,Abbas masallaci suka tafi suna idarwa kuwa suka dawo gida sai a sannan suka tarar da daddy yadawo,gaisawa sukayi da daddyn daganan ya wa mahmud d'in Barka da isowa dan shi ya riga da yasanshi ,dayake suna yawan had'uwa idan yaje Lagos.
Ganin sun dawo d'inne sai mummy tafara kwallawa Teemah k'ira,bakinta d'aya ana biyu Teemah ta amsa.
Akan dinning tasame su,nufo wurin tayi tana fad'in mummy dawuri haka yau kuma?
"Uhmm"
Kawai mummyn tace mata.
Daddy ne yace "yau mummyn ki ta sauya mana tsarin mu angel saboda taga sabon d'anta yazo"
Yana murmushi yayi maganar.
Mahmud ne yace "a daddy harda kaima ko ?
"Ahh toh mahmud ai munga ana mana wariya ne,dole inyi k'orafi"
Sai asannan mummy tayi magana tana murmushi tace
"Bafah haka bane,ina gudun hucewar abincin ne kunsan dawuri aka gama shi kuma nasan idan ya huce bandaro zaiyi"
Dukkansu sai suka murmusa,sai asannan ne mummy tad'an sake ta rage damuwar data ke ciki,da kanta tayi serving d'insu abinci,kowa yayi bismillah ya fara cin abincinsa,amma banda Teemah da take ta kora ruwan juice tana binsu da kallo d'aya bayan d'aya.
Cikin haka suka had'a idanu da Abbas yawani sakar mata harara,murgud'a mai baki tayi sannan ta d'auke kanta gefe,Mahmud kuwa har yanzu haushi yake bata,dan ta lura mummyn ta tafi sonshi akanta,shiyasa shikam ko kallon arzik'i ma bai samu ba,gani yayi tana ta wasa da cokalin bata ci ba, baifi spoon biyu taci acikin abincin ba,
"Yah dai" yace mata
Bata san ma da ita yake ba amma sai ta d'ago idanu,had'a ido sukayi dashi,sai tawani d'ago baki sama,
"Me aka miki ne?
Ya sake tambayarta.
"Kyaleta mahmud daina 6ata bakinka indai wannan ce"
Daddy ne yafad'i hakan.murmushi kawai mahmud da mummy sukayi,Abbas kuwa sai ya kalleta.
caraf suka yi 4 eyes dashi sai tayi k'asa da kanta tana gunguni,minti biyu bata k'ara ba agurin sai ta mik'e tsaye,juice d'in tak'ara tsiyayah ta wuce d'akinta dashi kowa bayanta yabi da kallo,amma banda Abbas.
Sai da suka gama cin abincin kafin suka mik'e suka fice ad'akin,Mahmud da Abbas ne suka fita harabar gidan suna d'an taba hira atsakaninsu.
Sosai suka fahimci junansu dan Mahmud gwani ne a surutu shikam,bakamar Abbas d'in ba.
Tun daga lokacin wani shak'uwa ta shiga tsakaninsu sosai dayake kowa yaji d'an uwansa yamasa har aransa.
Abbas da mahmud kusan sa'anni ne,Mahmud yasamu delay d'in yin makaranta ne dalilin mahaifiyarsa,shiyasa sai yanzu zaiyi service d'insa.
Koda suka dawo daga sallar isha'i ma ad'akin Abbas suka yada zango,kuma sai alokacin mahmud yake d'an bawa Abbas labarin d'an abinda yasani,shima Abbas d'in sai yaji mummyn tabashi tausayi sosai.
Anan suka ci kusan 2hrs ,sai 10:15 Abbas ya koresa yace "kaje kai ka kwanta ka huta mana,kamanta nisan tafiyar dakayi ko"?
Dariyah mahmud yayi kad'an tare da fad'in "kai de nagano ka so kake in baka wuri ka sake"
"Ehh naji ni dai jeka"
Tashi yayi yabar d'akin yana fad'in mu kwana lpy.
"Allah ya bamu alkairi"
Abbas d'in yabashi amsa.
Sannan ya mik'e yarage kayan jikinsa yayi shirin bacci.
********
Dangantakar mummy da Mahmud tasamo asali ne daga iyayen su mummyn.
Iyayensu asalin 'yan kano ne,dan tun tashinsu a kano suka tsinci kansu,Malam mamman sada shine sunan mahaifinsu,kayan miya yake siyarwa a kasuwa mahaifiyarsu kuma ummah fatsin kusan kowa haka yake k'iranta dashi, iyayensu su biyar suka haifah,amma duk sauran Allah ya kar6i abinsa,su biyu ne kawai suka saura agaban iyayensu har suka girma,suna rayuwarsu cikin rufin asiri da wadatar zuci,yayan mummy mai suna yusuf yana gama secondary mahaifinsa ya dage har seda yaga yasamu gurbin karatu a BUK kafin ya samu nutsuwa,cikin ikon Allah ya fara karatun da sa'a dan bai sami wata matsala ba,shigansu 200level ne suka had'u da kabiru shikuma yazo D.E ne,kuma shine yakasance abokinsa har suka k'are makarantar dan kusan halayyah d'aya garesu.......
Tare suke komai a makarantar inka gansu zaka zaci y'an uwan juna ne ma su,dan basu fiyah rabuwa da juna ba.
Lpy lau suka gama makarantar su,
Cikin ikon ubangiji kuma kamar abinda babansu yake jira kenan yace ga garinku nan,dan kwanan yusuf hud'u da gama makaranta ranar da yamma Baban yana dawowa daga kasuwa mota takad'e shi,garin tsallaka titi hannunsa rik'e da ledar y'ar tsarabar daya saba kawo musu idan zai dawo daga kasuwar,abin ya faru ne akan titin unguwarsu ,hakan yasa ba'a sha wani wahalar ganeshi da gidansa ba.
Dawuri labari ya iso musu,duk kansu suka fice bakin titin da gudun gaske su ummah na kukan fitan rai,dasuka ganshi kuwa take mahaifiyarsu ta suma a wurin.
khadija kuwa kuka ta zube tanayi dan rasa kan wa zata fara zuwa tayi.
Da k'yar aka samu aka tattara su aka kai gida,shikanshi wanda ya kad'e mahaifin nasu kuka yakeyi da hawaye, ba'a wani d'au lokaci ba aka masa sutura, kanshi ne yafashe dan bazama kaso kaga yanda kan yayi ba hatta likkafanin ma sai da yayi ja,dukda an d'an ninka a wajen kai d'in amma sai da ya ratso,Yusuf ne kad'ai mai dauriyah addu'a kawai yakeyi azuciyarsa har suka sada baba da makwancinsa na gaskiyah.
Dayake wanda ya kad'e baban ma zuciyarsa mai kyau ne,dashi akayi komai har zuwa sadakan bakwai,kuma aranar ne ya bayyana abinda ke ransa game da batun diyyah.
Yusuf ne yace su basu son wani diyyah akan mutuwar baban,koda akaso fahimtar dashi akan musulunci ne yazo da hakan ma cewa yayi ya sani,kawai bazai iya kar6ar komai akan dan babansa yarasu ba,mutuwa ai ta Allah ce.
_Drop ur comment_ as u do always🤞🏻 _pls_ ,
_and i don't need that_ *heart* ❤
or
*tnx* / *Thanks*, _even the_ *sticker* 👎🏻 _I don't like it,all i_ _need is ur_ _comments_ .🤙🏻
*Salmern ku ce* 😍
[10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*