← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 163

Sashe 127

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Teemah ta jijjiga wa Hannah alamar " _ah ah_ " sai Hannah tace
" _wannan taurin kan dake kan kin nan shine ya haifar miki da girman kai, zaman aure_ _da hakan kuwa baya ta6a yiwuwa, ki sau'kar da wannan shirmen ki nutsu ki gyara auren ki ki jawo mijin ki ajiki ki kula dashi da hakkin sa, sannan_ _ki dinga ro'ka muku haske wurin mahallici, Allah_ _Teemah banaso ko da wasa inga wata ta ra6i rayuwar ku, ke kanki kinsan hanyoyin kulawa_ _da mijin ki dan nasan Anty da Mummy suna_ ' _ko'kari sosai akan haka ni shaida ce......._

" _..........Harda maman Amal ma Hannah itama tana bani shawara sosai_ "
Teemah ta tare da fadin hakan.

Hannah jinjina kai tayi tace " _toh kin gani ma ashe suna da yawa masu sin ganin rayuwarki cikin farin cikin_ , _amma abinda ke kanki ne yah hana ki fahimtar cewa Abbas 'din nan_ _dai yanzu shine rayuwar ki kuma aljannar ki, dole_ _ne ki sauke naki dan biyu bata ha'duwa kinga kece 'karama akanshi, kafin yazama miji agare ki Yayan ki ne, kinga dole biyayya naki ne kuma ke ka'dai_ _banda shi, sai kin dage dan maza yanzu babu ruwan su tun kafin_ _yaje yayi miki kishiya awaje ba fata ba amma ki dage gaskiya"_

" _Hannah plz ni yanzu ya zanyi toh ki gaya min"_ Teemah ta fa'da tare da kamo hannun Hannah.

Agogo Hannah ta kalla tace " _yanzu dare yayi may be yana bacci, amma ki daure ki 'kira shi gobe, in kinyi sa'a zai sau'ko, sai kisan me zaki ce dashi wanda zai sanyaya_ _masa rai tunda ke ce da laifi sai ki bashi ha'kuri ki kuma kiyaye gaba"_

" _Bakomai insha Allahu gobe zan gwada 'kiran sa naji"_
Hannah tace
" _Toh Allah ya kaimu ya kuma daura ki akansa_ "

Da haka suka rufe maganar zuwa safiya.

Washe gari Hannah na da lectures a makaranta ita ka'dai tayi break fast 'din ta daya ke Teemah babu inda take zuwa so ba da wuri take yi ba ita, tare sukayi aiyukan da zasuyi dukka 'dakin Abbas ne ka'dai Hannah bata taya ta gyarawa ba ita ka'dai take yin abinta, 'karfe bakwai da rabi Hannah ta bar gidan dan 8:00 zata shiga lecture.

Teemah data gama komai tayi wanka tayi shirin ta tsab kamar me zuwa unguwa, sai ta dawo 'dakin sa tayi dialling number 'din sa, sai de har ta gama ringing bai 'daga ba, sake 'kira tayi shima still har yayi miss called be 'daga ba.

Take ta rintse idanun ta da 'karfi sai ga hawaye ya gangaro mata baya tayi ta kwanta, fuskarta na kallon cielling 'din 'dakin afili tace " _plz Yayah na ka yafemin, ka 'dauki wayata"!_

Abbas na bayi lokacin data 'kira 'din shiyasa be 'daga ba ko daya fito yaga miss called 'din kuwa sosai yayi mamaki amma sai ya ajiye wayar batare da ya 'kirata ba.

Shi kansa yana rayuwa ne amma kewar matar shi na damunsa sosai, tunanin ta na matu'kar hana shi sukuni da walwala yayin da soyayyar ta ya tsaye masa azuciya koda yaushe tana cikin ransa.
Abinda kullun yake fama da shi kenan tare da jin haushin rashin ta a kusa dashi, duk kuwa abin nan dayake yi mata yanayi ne dagangan duk da cewa shi kansa hakan na cutar dashi amma ya nuna mata cewa bai ji da'din 'kin biyo shin data yi ba yasa ya daure ransa, dan yana tunanin idan hakan ya ishe ta next idan yace su taho bazata masa gardama ba koda Daddy ya nuna bai so, dan yasan ita bata fiye 6oye 'kudurin ta ba.

Teemah bata tashi a kwancen ba sai ta sake gwada 'kiran sa da niyyan daga wannan bazata sake ba in har be 'daga ba.

Cikin sa'a kuwa sai ya 'daga Teemah har sai data toshe bakin ta dan farin cikin data tsinci kanta aciki.

Abbas shiru yayi yanajin yanda ta sauke ajiyan zuciya, shima sai ya lumshe ido ya kuma bu'dewa atake.

Teemah a hankali tace " _Yayah_ !

" _Na'am_ " shima ya amsa ta da shi kamar wanda akayi masa dole.

Kuka kawai Teemah ta sanya mai me tsuma zuciyan ma'abocin sauraro.

Cikin kukan ta furta " _Yayah shine ka manta dani ka daina 'ki rana ko_ ?

Yace
" _Ni ban manta dake ba abubuwa ne sukayi min yawa ma shiyasa_ "

Da sauri tace " _Amma Yayah ai kana 'kiran Hannah nice ka'dai baka 'kirana_ !"

Dan ya takaita zancen sai yace
" _Shikenan toh zan na kiranki... owk_ ?

Shiru tayi masa tana share hawaye.

Da yar ka'dan 'din muryar tace " _Yayah fushi kake yi dani ko?_

Sosai yanayin data yi maganar ya ratsa shi har 'kwa'kwalwar shi amma ya basar.
Sai ma yace " _i ll hang d call now office zan je.....see u later ummm_ "

Bata yi magana ba har ya yanke 'kiran sai kawai tabi wayar da kallo da mamaki, lalle ta 6ata ran Yayah sosai acikin muryar sa ta fahimci hakan dan duk wasu abubuwan shi dayake yi abaya bata ta6a jin muryar sa a irin wannan yanayin ba, sai dai abinda takasa ganewa shine haka 'din da yake yi soyayyar da Hannah tace yana yi mata ne yasa ko kuma haushin kawai ta'ki binsa?

Share hawayen ta tayi tare da tabbatar wa kanta cewa zata bishi aduk yanda yake so 'din harta gano asalin matsayin ta awurin sa.

Abbas ma daya yanke 'kiran sai daya jinginu da jikin kujera ya lumshe idanu baya son irin wannan na faruwa tsakanin su koka'dan amma tunda hakan take so, so be it!, shi zai daure rashin ta na tsawon lokaci ko dan ya koya mata yanda ake kewar masoyi da yanda tasirin soyayya yake a zu'kata.

Tun daga ranar Abbas yafara 'kiran ta safe da kuma dare, amma kullum daga gaisuwa baya sake fa'da mata komai, duk da hakan Teemah najin da'di domin yafi ace baya 'kiran gaba 'daya, sau tari har 'kaguwa takeyi ya 'kirata dan kawai taji muryar sa ita hakan ma ya isheta.

Baya yi mata magana mai tsayi sai in har bu'katan hakan ya taso, farkon dogon maganar su shine ranar da ya ta6a tambayar ta cewa bai ga debit alert ko sau 'daya har yanzu ko bata da bu'katan komai ne?

Sai tace masa Hannah na zuwa musu shopping every week.

Ya sake tambayar ta cewa ku'din fa sai ta bashi amsa da fa'din " _Ummah ce ke bada ku'din idan Hannah zata_ "

Shine ranar da maganar tsakanin su tayi tsayi, na biyun sa kuma ranar da Hannah zata je saloon kuma itama Teemah tanaso tayi dan kanta cunkus take jinsa.

'Kiran safiya da yayi mata sai ta tambaye shi zuwa saloon 'din, ai kuwa hana ta Abbas yayi sai ma yace in har yazama dolene sai tayi 'din toh Hannah taje ta siyo komai zai turo ayi mata agida, Teemah sosai taji haushi dan kuwa ba 'karamin gajiya tayi da zaman gidan ba.

Sosai take so ta'dan fita amma Yayah fir ya hana ta.

Hakan kuwa akayi dan da yamman ranar wata mata tazo gidan Teemah bata san ta ba, Hannah ce dai ta gane ta dan ta ta6a zuwa gyaran gashi wurinta sau 'daya, sunan ta madam Mansoora, agida tayi musu komai harda Hannah ma, hatta da gyaran farce sai da tayi musu mai kyau ta kuwa yi 'ko'kari dan su kansu sai da suka yaba da aikin nata.

Sai daga bayane ma da Hannah taje gida n Ummah sai suka ji labarin ashe Ummah yasa ta turo ta.

Duk abin nan dake faruwa bai sa Teemah taji haushin sa ba sai ma 'kara ganin shi data ke sonyi ga begen sa dake yawan damun ta.

Ita kanta wani lokaci mamakin kanta takeyi, yanda ta damu sosai da rashin sa kusa da ita yanzun bata san dalilin wannan canjin ba, sosai take kewar mijin ta a yanzun sai dai bata bari ko Hannah tasan hakan ba saboda Anty tace mata komai dake tsakanin ta da mijin ta sirrine mai girma, kar ta yarda ta ringa bari wani na sani, shiyasa ta ri'ke sirrin ta aranta.

Kullum take shiga 'dakin sa ta share koda babu dattin komai amma bata gajiya da share shi, ta tsaftace bayi kullum ta kunna burner, anan take wuni da rana har in bacci yakama tayi abinta da dare kuwa tare da Hannah suke kwana a'dakin ta, idan gari ya waye suka kammala ayyukan su gaba 'daya sai Hannah ta shirya ta wuce makaranta.

Teemah kuwa nan 'dakin san take komawa tayi baccin ta kwanta tana kallon photon sa tare da rungumar pillow a 'kirjin ta.

Tana fitowa sai ta kulle 'dakin ta kai key 'din cikin drawer 'dakin ta ta ajiye shi.

Duk weekend Hannah ke zuwa shopping idan ta dawo kuma sai ta gudu gidan Ummah ta 'karasa yinin both saturday & sunday acan haka takeyi, amma bata kwana sai ta dawo, hakan ma Ummah bata barin taringa mitan ta baro Fateemah agida ita ka'dai.

In kuwa zata dawo Ummah sai ta ha 'data da wani abin ta6awa na zamani ko na gargajiya tace ta kawo wa Teemah.

Su hajiya Teemah kam najin da'din hakan har sai ya zamana ma duk ranar da Hannah taje gida bata cin komai jiran ta kawai takeyi ta dawo sannan taci abinda Ummah ta ha'do ta dashi, tasan Ummah na 'ko'kari sosai dan kamar tasan abinda ranta ke 'dan iya bi takan rin'ka yiwa Hannah santi musamman ranar da aka kawo mata pepper soup 'din hanta ko dambu mai ha'din isassun kayan lambu, ranar kam har rowa take yiwa Hannah ma.
Chapter 127 · 0% Book details