Sashe 112
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai 'dakin ya tafi da imanin ta haka tayi tsalle ta fa'da kan gadon tana murmushin farin ciki, ta zubawa farin ceiling fan 'din dake saman 'dakin idanu.
Mummy da Daddyn ta ne ka'dai suka san best colour 'dinta akaf fa'din duniya sai ko Yayah Abbas dan ta ta6a fa'da masa da jimawa tun suna damaturu lokacin daya je hutun aikinsa acan, bayaga su ukun nan kuwa babu wanda yasan favourite colour 'din ta har yau, hatta Hannah ma bata sani ba, amma acikin su ukun bata san waye ya yi mata wannan kyautar ba koma waye ita kam yasata farin ciki mara iyaka.
Shab tama manta da cewa ba kaya ajikin ta duk ta cire su, tana kwancen tana ci gaba da 'karewa 'dakin kallo kawai sai ta ji 'karan sau'kan ruwan sama lokaci guda tamkar da bakin 'kwarya.
Afirgice ta tashi ta zauna tana rarraba idanu sam bata san da akwai hadari har haka agarin m bama ita, sai sau'kan ruwan kawai taji.
Tashi tayi tafara duba abinda zata saka ajikin ta amma ta kasa samu sai masu nauyi ita kuma basu take so ba, da 'kyar hannun ta ya jawo wata figigiyar riga ja mai sharara bata ma ko wuce mata gwiwa ba amma ahaka cikin hanzari ta saka shi ajikinta.
Tana gamawa saka wa sai ta fara duba wani 'dan viel da zata rufe kanta dashi sai kawai taji 'karan thunder mai 'karfin gaske irin mai razanar wan nan ha'de da wal'kiya mai haske.
A 360 ta fito a'dakin tana toshe kunne ta nufi 'dakin da taga ya shiga 'dazu, duk taku 'daya da takeyi tsoro ne yake sake kamata da haka har ta isa 'dakin.
Tana zuwa kuwa dai-dai shima ya bu'de 'kofan nasa sai sukaci karo dashi, jikin shi ta shige tana kakkarwan tsoro shima dayaga haka sai yasa hannun sa ya rungume ta ajikinsa sosai.
Tsawon mintina 8 tana faman sau'ke ajiyan zuciya sannan ya 'dago ta ganin kamar ta 'dan nutsu.
" _Me yafaru ne wai? Me yasa meki_ ?
Tambayar daya jefe mata kenan tare da jijjiga ta.
Cikin in in ta bashi amsa da fa'din " _Yayah ni tsoro nake ji sosai_! "
" _Tsoron miye kuma? ke bazaki bar shirme ki girma ba ko_ ? _Ba gani nan agidan ba babu wani abin tsoro agidan nan da ze kamaki, ko kinga_ _wani abu ne_ ?
Kai ta jijjiga masa sai tace " _thunder nake tsoro_ !
" _Toh ai baya kama mutun shi, oyah jeki 'dakinki ki kwanta ki huta ko zaki ci abinci?_
" _Ah ah_ "
Tace dashi
sai yace " _toh jeki ki huta kinga yau akwai sanyi kar ya shiga jikin ki!_ .
Teemah kam kuka ta sanya mishi tana bubbuga 'kafafu a'kasa tace
" _ni wallahi tsoro nake ji ni ka'dai!_
" _Wai ya kike so in miki ne toh, umm_ ?
Ya fa'da yana kallon ta.
Shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka yasa ya juya ya koma ciki dama dubota zeje yi dayaji 'karan yasan sai ta tsorata sai kuma suka ha'du ashe be yi 'karya ba.
Binshi itama tayi abaya tana tafiya tana waiwaye kamar irin wani abu na binta abaya 'din nan.
Duk da tana cikin firgici amma hakan be hana ta ganin kyaun 'dakin sa ba, compared to nata ma ai nata bakomai bane, hakama bed size 'dinsa ba irin nata bane, ya zarce nata da girma, nashi komai fari tas aka sanya mishi, curtain ne ka'dai mint green da zanen fulawowi su kuma dark green ajiki.
Abbas yana zuwa ya wuce bathroom ya 'dauro alwala, koda ya fito ma kallo 'daya yayi mata ya kauda kansa ya wuce ga dadduma, sallah ya gabatar kusan raka'ah shida sannan ya 'daga hannunsa ya dinga jero addu'o'i wa'dan da bata san iyakar su ba.
Teemah tun tana kallon sa har ta gaji ta lalla6a ahankali zuwa bakin gadon ta kwantar da kanta amma 'kafafun ta na a'kasa ahaka bacci yayi awon gaba sa ita.
Abbas ne daya idar da sallahn yazo inda take ya tsaya akanta sai yanzu yaga tsantsan kyau da tayi cikin rigar dake jikinta, ahankali yakai hannu ya shafi gashin kanta har ya fara yawo da hannun nasa akan nata sai kuma wani abu ya 'dar su aransa, da sauri ya cire hannun yana kallon hannunsa kamar wani sabon abu ne.
Tashi yayi ya tsaya akanta ya 'kura mata idanu yana so ya kauda sa'kar haukan da zuciyarsa ke haska mishi amma ya kasa, ahankali ya gyara mata kwanciyan da kyau ya lullu6e ta sannan ya koma 'dayan gefen ya kwanta shima.
Bacci kasa 'daukan sa yayi ya zubawa fuskar ta ido yana ta sa'kar zuci, sam baya son hakan ya dinga zuwa ransa amma bazai iya ba, gashi yakasa kauda tunanin nan aransa.
Kishi ne ko shai'dan koma miye ke sarrafa zuciyarsa yakasa ganewa.
Ranar Abbas har makara yayi na zuwa masallaci, lokacin da ya tashin kuwa Teemah na jikinsa kamar de jiya haka yau ma tayi, sai ya 'dan bata glance ka'dan dai-dai kuma itama ta bu'de idanun ta caraf sai sukayi 4eyes dashi, wanda motsin da yayi ne ya farkar da ita daga baccin da take yi.
Take ta diririce ta fara kalle-kalle ganin yanayin kusancin dake tsakanin su dashi yasa da sauri ta tashi zaune tana sussunkuyar da idanun ta 'kasa dan ta fahimci itace, laifinta ne.
" _Mage ce ke ko_ ?
Taji ya ce da ita
Yayi maganar bayan ya tsareta da kallo.
Kai ta jijjiga masa tana 'kif-'kif da idanu, maganar tasa it's clear that ita mai son jiki ce, haka yake nufi kuma ta fahimta amma sai ta'ki bawa kanta laifin ita ka'dai, asace take duba 6angaren daya kwanta itama ko zata ga space 'din daya bari abaya ya matso amma sai bata ga komai ba.
Abbas be sake kulata ba dayake ma be fahimci me take yi ba gudun kar ya makara yasa ya mi'ke ya nufi bayi yana tunanin irin shegen son jikin datake da shi ga uban birgima kamar wata yarinya 'karama.
Har ya shiga bayin ya gamo abinda zai yi ya fito tana nan zaune awurin kamar yanda ya barta 'dazu.
I'kama ya tayar ya gabatar da Sallar sa cikin nutsuwa tare da yin addu'o'in azkar 'din sa cikakke.
Al-qur'ani ya mi'ka hannu ya 'dauko saman drwaer ya bu'de suratul A'araf ya fara karatun sa cikin sauti mai da'din sauraro tamkar bashi ne Abbas ba mai jin kai da rashin son maganan nan ba, qur'ani kenan, zancen Allah mai abin mamaki, duk wani girman kan ka ,miskilanci da 'kafafan ka duk rashin iya hausan ka da 'karfin da harshen ka keda shi akan yaren ka but when it's comes to it (QUR'ANIL KAREEM) dole harshen mu ya dawo iri 'daya.
Karatun nasa ba 'karamin shigan ta yake yi ba, hakan yasa ta koma ta maida kanta akan pillow tana sauaraon sa tare da zuba masa idanu, wani 'ka'k'karfan ala'ka take jin zuciyarta na 'kulla mata game da Abbas 'din sai take jin tamkar he is the only man in d entire universe take wani sabon babin 'kaunar Yayan nata ya shige ta take jin shi 'din na daban ne, kamar kar ya 'kare karatun haka take ji.
Ko da ya 'kare karatun kuwa sai ya sake bu'de wani page daga cikin 'karshen Al'qur'anin yafara karanto addu'ar da ke rubuce a ciki wanda akeyi bayan an gama karanta Al'qur'ani mai girma ( Du'ah 'u Khatmil Qur'an).
Yana shirin ajiye wa bayan ya kammala karatun sai suka ha'da idanu dashi kauda kanta tayi da sauri yayin da shi kuma ya kasa 'dauke nasa idanun daga kanta, fuskar ta yake 'karewa kallo har zuwa la66an ta, wani sabon salon 'kaunar ta ke 'kara nin kuwa masa a zuci, wanda har be san lokacin da ya mi'ke ya isa gaban gadon ahankali ba, ita kuwa tuni ta rintse idanun ta ganin ya nufo ta dan bata san me yake shirin aikata wa ba.
Abbas kam shai'dan mai masa muguwar sa'kan nan be zo masa ayanzun wata'kila sanadin karatun da yayi ne shiyasa, wannan karan shai'dan 'din be yi masa mummunan sa'kar daya saba yi masa akanta ba, jiyayi kamar ana fizgansa zuwa gareta idanun sa na 'kara haska masa asalin kyaun surar datake dashi......da 'kyar ya dawo da tunanin sa dai-dai tare da jijjiga kansa ahankali.
Wani 6ari na zuciyarsa ne ya wurga masa tambayar " _me kake shirin yi ne Abbas_?
Lumshe ido yayi yakuma bu'de su atake sai ya sau'ke su akan fuskarta dake 'dauke da rintsetsten idanu har yanzun bata bu'de ba, 'karfin gaske yake jin zuciyarsa na fizgarsa zuwa gare ta.
Dakewa yayi a tsayen sai dage ya harha'do wasu 'kabilun kalaman da sam basu ne acikin ransa a wannan lokacin ba " _yau ma bazaki... yi sallar ba...ne?_ "
Yayi maganar yana wani gyara tsayuwa.
Jin yanda yayi tambayar yasa Teema ta bu'de idanunta ta 'dan waigo a karkace ta kalleshi dayake dama ta bayan ta yazo ya tsaya, goshi ta ha'da dan ji tayi tarasa me ma zata ce dashi, aranta tace " _ina ruwansa toh da sallan ta_ ?
Jitayi yasake jefa mata wata tambayar inda yace
" _Ko har kinyine bansani ba_ ?
Kai ta jijjiga masa amamar ah ah tare da sau'ke idanun ta zuwa 'kasa.
Abbas taran ta yayi da fa'din " _amsani da baki i thought mun gama da wannan 6angaren tun ba yau ba_ ?
Ahankali ta bu'di baki tace
" _a'a banyi ba_ "
" _Sai yaushe kenan_ ?Ya sake tambayarta.
Cewa tayi
" _May be gobe_ "!
Tayi maganar kaman an matsi bakin ta ne an sata dole.
" _Okay_ "
Kawai yace da ita tare da
juyawa ya koma parlour dan kallon news 'din safiya.