Sashe 141
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dukkan su sun yaba da 'ko'karin Rabi'u akan a halin Innah dan sun fahimci cewa yaro ne shi mai zuciya da amana, Teemah kam da farko ta sha shima 'din 'dan Innahn ne sai daga baya cikin maganganuns u ta fahimci basu da wata ala'ka sam.
Nan take Abbas ya ce da shi kafin gobe ya samu ya bu'de account kafin su koma.
Kafin su tafi zuwa masau'kin su kuwa sai da suka je gidan mahaifin Rabi'u suka gaida shi tare da yimasa alkhairi na ban mamaki wanda sam bai yi zaton samun sa aranar ba amma sai gashi dalilin 'dansa ya samu hakan, shima dan farin ciki rasa mai ma zai ce dasu yayi illah albarka da ya ringa sa ka musu tare da fatan alkhairi.
Daga nan masau'kin su suka koma bayan sun sau'ke musu tulin tsarabobin da suka taho musu dashi, gasassun kaji da kayan itatuwa masu yawan gaske sun kuwa ji da'din hakan sosai.
Innah bata bar yaranta sun 6ata tsarabar duka ba sai da ta ware na Rabi'u da kuma wanda zai kai gidan mahaifin sa kafin suma yaranta ta basu sauran.
Teemah kam har suka isa masau'kin su bata daina share hawaye ba, Abbas sai ya share ta duk da abin na damunsa amma dan kar ta sashi yin abinda bai dace ba acikin jama'ah yasa ya 'kyaleta taci gaba da kukan, coz yasan fa'da da baki bazai sata tayi shiru ba, yasan ba komai zai sata kukan ba face memories 'din Mahmud wanda shi kansa ma ji yake duk yayi laushi sosai.
Suna shiga room 'din da suka sau'ka kuwa yajawo ta jikinsa ya fara share mata hawayen yace kukan ya isa hakan nan ta daina"
Da 'kyar ya samu kukab nata ya tsaya sannan shima ya 'danji natsuwa ta shige shi.
Wanka suka shiga a tare wanda kafin su fito daga bayin sai da ya tabbatar ta bar kukan nata gaba 'daya ta sanywa fuskar ta murmushi tukunna ya sarara mata.
Tana shafa mai a 'kafarta ta 'kira sunan sa yayin da shi har ya fara saka kaya ma itan ce dai ta tsaya sai yanzu dayake ma bata 'dan jin da'di sosai duk jikinta bata jin da'din sa ga marar ta dake 'dan mata ciwo.
Yana jin ta 'kira sunan shi sai ya waigo ya dube ta batare da ya amsa ba.
Tambayar sa tayi cewa
"Yayah ina wancen ku'din nan da aka ce wai na gado na ne"
Sai yace mata "yana nan kina so kiyi amfani da shi ne?
Teemah tace "ehh"
Inda ta ro'ke shi akan tana so duk abinda za'a yi wa su Innah ayi musu da wannan ku'din"
Abbas kai ya girgiza mata yace "ah ah wannan ai burin Mahmud ne komai za'ayi da sunan shi ne, yace shima 'din da sunan Mahmud yazo kuma duk abinda yakama ayi zai yi shi koma menene amma duk bada sunan shi ba, su 'din kamar 'yan aike ne domin wannan tafiyar ta Mahmud ce, da sunan ne akayi ta, yace in taimako zatayi tabari idan sun koma gida sai suyi planning wani abin daban yace ko makaranta ma zata iya ginawa da ku'din shima ba laifi bane kuma akwai sosai shima.
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa bawai dan bata yadda da abinda yace 'din ba ah ah, sai dan yanda take jin yanayin da take ji ajikinta na 'kara tsananta.
Abbas barin abinda yake yi yayi da sauri ya 'karaso inda take ya zauna, inda yana zama sai ta kwantar da kanta ajikinsa hawayen ta na 'kara sau'ka a hankali, sosai yaji hankalin sa ya tashi sai yafara tambayar ta mai ke faruwa meke damunta.
Kamar bazatayi magana ba sai can
ta 'kira sunan shi a hankali ta ce " _Yayah_ !
" _Na'am_ "
Ya amsa ta dashi yana me bada dukkan hankalin sa izuwa gareta, sai ta kamo hannun sa ta kai kan marar ta tace "Yayah zafi yake min sosai ka danna min a hankali dan Allah"
Kamar yanda ta bu'kata haka yayi mata sai dai instead ya danna matan sai ya rin'ka shafawa a hankali yana sake kallon cikin nata ganin ya 'dan taso ka'dan.
Yana shafawan yake 'kara lallashin ta da kalamai masu sanyi tare da tambayar ta ko zasu je hospital a duba ta, girgiza masa kai tayi tace " ah ah gajiya kawai tayi shiyasa kuma zai daina ma anjima ka'dan"
Shiru yayi mata kawai ya ci gaba da shafa marar har bacci ya 'dauke ta, ganin haka sai ya saki ajiyar zuciya tare da gyara mata kwanciya ya rufe ta da kyau.
Kafin ta tashi har an kawo abinci da yake dama da yunwar ta tashi so bata tsaya 6ata lokaci ba ta lodi abincin ta, Abbas na ta kallon ta dan shi coffee kawai yasha tun zuwan sa sai ko kayan itatuwa, sai da ta gama kafin tayi sallah inda daga nan suka fita yawo cikin gari ganin ta warware sosai, Abbas ba haka yaso ba dan shi clinic yaso kaita amma Teemah ta'ki amincewa da hakan tace dashi ai ta riga ta warware.
Washe gari da yamma Rabi'u ya tabbatar wa Abbas cewa ya gama komai na bu'de account inda ATM ne ka'dai ya rage masa.
Tare dashi suka je store amma Abbas bai bari Teemah ta bisu ba yace babu inda zata, siyayya suka yo na kayan abinci masu yawan gaske inda duk suka sau'ke shi gidan Innah.
Sannan Abbas yayi transfern ku'di cikin sabon account 'din Rabi'u yace ya tabbatar da cewa yaran Innah basu nemi wani abu sun rasa ba kuma duk suna zuwa makaranta, shi kansa Rabi'un ma Abbasa ya bashi daman ya rin'ka yin bu'katun makarantar sa da ku'din kar yaji tsoron ta6awa tare da yimasa al'kawarin 'daukan nawin makarantar tasa in har yana raye har inda ya ga daman tsayawa da karatun.
Abbas yayi al'kawarin cewa da izinin Allah zai yi 'ko'karin ganin ya kula da hakan.
Kuka da godiya ranar kam yasha su sosai kamar su goyashi, Umar kansa sai da ya ga karamcin Abbas sosai inda shima ba'a barshi abaya ba ya ciri ku'di kimanin 20k ya dam'ka a hannun Innah.
Shi kuwa Abbas duk abinda yayi 'din ko 'daya bai yishi da sunan kansa ba yayishi ne da niyyar cikar burin marigayi Mahmud coz niyyar sa ce hakan shine yafaro abin tun farko dan haka duk da cewa da dukiyarsa yayi amfani amma niyyarsa daban ce.
The following day suka koma Abuja inda suka bar Umar acan saboda mahaifar sa ce zai tsaya ya duba 'yan uwa da dangi kafin ya wuce Lagos.
Da komawar su kuwa Abbas yaji zaman Abujan kwata-kwata ya isheshi gaba 'daya, da isarsu ko hutawa bai yi ba ya wuce ya dubo gininsa da yake yi acikin unguwar tasu, washegari kuwa gidan Ummah suka dira, suna can ma sai kuma wani abokin sa ya 'kira shi cewar suna hanya zasu kawo musu ziyara.
Wannan dalilin ne yasa suka dawo gidan nasu suka tari ba'kin da suka zo,
Teemah naganin Nasreen ai sai ta washe baki tana murna ta rungume ta tare da fa'din " oyoyo my baby girl", Nasreeen kam harta manta ma da ita, amma dayake asali bata 'kin mutane sai suka sake yin wani sabon kuma, yanda Teemah takeyi da yarinyar tamkar wata yarinya 'karama itama ta koma, Maman Nasreeen kam sai de tayi ta musu dariya.
Da zasu har wajen mota suka yi musu Rakiya inda Teeemah tacikawa Nasreen haka da kayan ciye-ciye irin nata.
Abbas yaso ya koma da matar sa Rivers su 'karasa hutun acan amma ganin Daddy nagari
sai ya sashi ha'kura dan jin tsoron abinda daddyn zai ce coz sam shi bai son haniya akansa ballantana har ransa yasake 6aci karo na biyu akan zancen tafiyar.
Sai ya cire batun tafiya da ita aransa ma gaba 'daya kawai ya yanke cewa gara tafara zuwa makaranta tunda babu abinda takeyi yanzun illa zaman gida wanda yake ganin kamar hakan ma zai 'kara sata ta warware in tana shiga cikin 'dalibai 'yan uwanta 'kila ko lokacin yin tunani ma bazata samu ba.
S.S.C.E result 'dinta ya nemi gani dan ya san ta ina zai fara nema mata admission kafin ya wuce.
Nan kuwa yasha mamaki dan Teemah kam da taji yace " Result 'dinta " Sai ta zaro idanu kamar da mamaki tace " Ni.... ni kuma nawa Yayah?
Abbas yace " da 'din wa kike ganin zan tambaya anan?"
Teemah da iskanci, juyawa tayi kamar dagaske ta 'dan kakkalli cikin 'dakin wai ko zata ga wani daban a ba ita ba sai kuma ta tura baki tace " Nima fa Yayah bansan inda yake ba"
Waro idanu yayi akanta da mamaki yace "kamar yayah bangane ba?"
Sai tace "
Ni....nifa agida na barshi can damaturu kuma bansan inda yake ba yanzu sai dai a tambayi Mummy"
Abbas tsaki yaja ka'dan yace " Yanzu fisabilillahi result 'din makarantar ki ne kike cemin baki san inda yake ba, to ke da kanki baki adana ba waye kike tunanin zai adana miki?"
Allah zanga ranar da zakiyi wayo kekam, a hakan ne kuma kike wani son baby, salon ki ta koya musu shirmen ki ko?"
Kauda kai tayi gefe ta 'kasa-'kasa tace " Ni kam inada wayo na"
Muryarshi data jiyo yace mata" _meaning_ " neya sata gane cewa yajita.
A'dan firgice tajiyo sai ta cikaro da shi tsaye kusa da ita da gira 'daya a'dage sama ya kama kunkumi da dukkan hannyensa kamar mai shirin fa'da da sa'an sa.
'Kasa tayi da kanta tana muzurai.
Sai taji ya sake fa'din "tambayarki nakeyi ko?"
Teemah 'dan matsawa baya tayi ka'dan ta kauda kai tana 'kun'kuni sai taji ya 'dalli bakinta da yatsun sa biyu.
Kuka ta fara tana ri'ke bakin tana kallon shi sai ya daka mata tsawa inda yace " Shut up da Allah, dama ni sa'anki ne da zaki rin'ka yimin hakan?
Kuma karki min shiru kiga abinda zan miki right now, cry-cry kawai"
Hanyar barin 'dakin takama sai ya sake fa'din " kuma ki 'kira Mummyn ki tambaye ta yanzun nan ina jiranki kizo ki sanar dani feedback"