Sashe 79
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka matar tasaki tare da godiya ta 'dago kudin ta ri'ke ahannunta hawayenta na sau'ka akansu yayinda yaranta duk suka matso sukayi jigum agefenta suna kallonta.
Tun bayan rasuwar maigidanta yauce rana ta biyu da wasu suka dube su da fuskar rahama, inka 'dauke masu basu zakkar abinci na kowacce shekara idan lokacin sallar azumi yayi Rabi'u ne mutun na farko daya taimakesu kuma yake kan taimaka musu aduk lokacin daya samu dama, domin har yau be ta6a fasa taimaka musu ba, aduk lokacin daya samu canji yakan kawo musu ku'di wataran har ledan taliya yakan siyo yakawo musu yace su dafa suci, randa hakan be samu ba kuwa yakan basu har naira 'dari yace su sayi wani abin dashi.
Atarihin rayuwarsu bazasu ta6a mantawa da Rabi'u ba, na biyunsa shine yau da wa'dannan bayin Allah suka zo suka taimaka musu, cikin kukan taketa jero musu addu'ah, " _Allah ubangiji ya saka muku da alkhairi ya haskaka rayuwarku, Allah yasa ku gama_ _da duniya lafiya, kamar yanda kuka ji 'kanmu kuka taimake mu_ _Allah ubangiji ya ji 'kanku kuma ya.........._
Da " _Ameen_ " kawai suke ta amsawa. Sai da suka mi'ke sazu tafi ne sannan Mahmud ya kalli yarinyar dayaji 'dazu mahaifiyarta ta 'kira ta da suna meram yace " _mamana ana zuwa makaranta kuwa?_
Sai data juya ta kalli bayanta dan ganin koda wa yake maganar ganin saitin ta yake kallo sai taga babu kowa agurin illah ita ka'dai, da kai ta amsa masa alamar " _ah'ah_ "
" _islamiya fah_ ?
Yasake tambayarta
Nanma ta'kara jijjiga masa kanta wanda manufar amsar duk ya bada ma'anah daya.
" _meyasa haka toh_ "
Yayi maganar tare da ya hannu.
Kafin meram tayi magana se mahaifiyarta tariga ta yin maganar da fa'din
" _kayyah 'dannan abincin daza'a ci ma daya aka samu, gagararmu yakeyi ballantana har_ _asamu ku'din biyan makaranta, wannan dakake gani......._
Ta nuna Rabi'u sannan tacigaba da fadin " _shi ka'dai yasan damuwarmu yasan halin damuke_ _ciki, shine akullun yake da burin yagama makaranta domin yasamu abinyi_ _nima kuma shi 'din nakewa addu'ah yasamu yagama koda baze taimaka mana agaba bama_ _bazanji haushi ba kokadan, domin wanda yayi abaya ma ka'dai ya isa, hakanma ya isa_ _yasa nayi ta masa fatan alkhairi har 'karshen rayuwarsa, domin Rabi'u mutun_ _ne yaro ne shi amma me zuciyar manya, burina inga Rabi'u yasamu abinda_ _yake so, amma inbashi ba mukan ai tamu rayuwar daban take, ba wai dan bandamu da_ _rashin karatun yaran bane ah' ah kawai dai inaga kamar mu'din haka Allah yaso ganinmu shiyasa ya yomu daban, kaga kuwa ai bazamu yi shishshigi wa lamarin ubangiji ba_ "
" _hakane kam Innah amma ai ba a yanke kauna da rahamar ubangiji domin idan yaso_ _akowani lokaci ya kan iya sauya ma rayuwa, kuma kinga zama hakan ba ilimi ai babu da'di_ , _duk da Allah ne dakansa ya halicci mutane iri daban daban amma kinga ta 6angaren_ _neman ilimi be bambanta mu ba yace ne kowa ya nemi ilimi.......... amma bakomai_ _nafahimci sosai.......yanzun muna kan hanya ne, da iznin Allah zan sake dawowa_ _kwana kusa insaka mamana amakaranta_ "
Ya dubeta yace " _ko_ _bakyaso_ ?
da murnarta ta bu'di baki tace " _inaso_ ".
" _Yauwa Mamana sai dawo ko_ "
Yafa'da tare da juyawa suka nufi hanyar fita matar nasake zuba musu ruwan albarka da godiya har suka 6acewa ganinta.
Rabi'u ne ya rakasu har gurin motarsu, wanda anan Mahmud ya ciro card 'dinsa yabashi yace ze iya nemansa idan ana da bu'katar wani abu kafin yadawo 'din ko kuma idan ku'din daya bashin suka gaza yin aikin yace ya'kirashi.
Sannan ya 'kara ciro 10 thousand yabawa Rabi'un yace wannan nashine ya ri'ke agurinsa.
Rabi'un ma godiya yayi yana 'daga musu hannu har motar tayi nisa ya daina hangosu.
Katin ya tsaya yana kallo aransa yake tunanin dama ashe har yanzu akwai irin mutanen nan ne aduniya, lallai kuwa Allah yayi gaskiya ha'kuri nada riba watarana, gashi yau ha'kurin innah yayi mata rana.
Allah ubangiji yasaka musu da gidan Aljannah ya biya musu bu'katunsu na alkhairi ya 'karashe da fa'din haka.
Mahmud tasha suka zarce suka nemi motan zuwa kano shi Umar, gidan kakansa Alhaji muhammad ya nema.
Alhaji muhammad ba 'karamin farinciki yayi da zuwan jikan nasa ba hakama matarsa, sosai suka rin'ka nan nan dashi, kamar su goyashi, Mahmud kansa yaji da'din hakan harma yakeji aransa dama tun farko agurin kakan nasa yatashi dayafi masa yanzun ma jiyake kamar karya tafi badan yabaro aikinsa da kuma matarsa ba da babu abinda zai sa shi komawa lagos.
Gidan 'yan uwan Anty kaf sai da ya zaga ya gaidasu kowa na farin ciki da ganinsa, musamman ma dashi 'din suka ga sam beyi halin 'yar uwar tasu ba hakan yasa suka 'kara sonshi fiye ma da mahaifiyar tasa.
Kwanansu biyu suka wuce 'kauye gurin danginsu na can, wato 'yan uwan mahaifinsa, nan ma haka suka ta hidima dashi kowa na tambayarsa iyalinshi da iyayensa, kafin yatafi sai da yabi yaraba musu ku'di 100k ma dukkansu mazan dayake lokacin damina ne sai yace suyi aikin gona dashi.
Hakan dayayin ba 'karamin farin ciki ya sanya azu'katansu ba, nan kam be kwana ba aranar suka wuche kuma ko tsaraba 'kin kar6a yayi yace bagida suka yi ba tukunna kuma kayan zai zama musu damuwa ne tunda motar haya suke hawa.
'Karfe hu'du na yamma suka baro 'kauyen suka dawo kano.
Da 'kyar suka sami flight 'din da zai sau'ka a Lagos da daren ranar, dan haka suka je suka gabatar da salllolinsu kafin nan.
'Karfe 11pm suka sau'ka acikin garin Lagos ganin dare yariga yayi yasa suka wuche gidan Mahmud suka kwana acan sai washe gari da safe suka shirya suka fita atare inda Mahmud ke jan motar Umar na gefensa.
Dayake ma already Teemah tasan da dawowar shin so tun dawuri tagama ha'da kayanta suna zuwa bawani 6ata lokaci tabi mijinta suka wuche gidansu amma zuciyarta cike da kewan matar Umar da 'yaranta musamman ma little Amal.
Aranar Mahmud beje shi ko'ina ba acikin gidansa ya wuni dayake ma ranar takama ranar asabar ce shiyasa ma be fitan ba, sai da akayi sallar azahar kafin yafita yaje masallaci yayi sallah daga nan yawuche gidan mahaifinsa.
*****
Washegari kuwa tunda sassafe suka tattaro inner wears 'dinsu gaba 'daya wa'danda basu sawa a loundry machine suka wanke atare, Teemah natayi masa dariya wai be iya wanki ba, itanma bawani iyawa tayi ba amma yanda taga Mahmud 'din keyi sai yana bata dariya shiyasa take ganin kamar tafishi iyawa.
Kasuwa suka shirya suka tafi bayan sungama wankin, sukayo siyayya ni'ki-ni'ki tarkacen kayan abinci.
Dangin su stock fish, ice fish, naman kaza dana 'karamar dabba, cry fish, ganyen su oghou, tarkacen fruits da sauransu kaya de dayawa suka siyo.
Atare suka shiga kitchen suka adana komai a inda yadace nasawa a fridge suka saka na , ajiyewa haka duk suka adana abinsu.
Fruits salad Teemah ta ha'da musu mai da'di suka sha aranar wanda shi ka'dai dasuka sha basu 'kara neman abinci ba har sukayi bacci.
Washe gari tunkan yagama shirinsa Teemah ta shirya ta yi zaman jiransa yagama nasa shirin, suna gama yin breakfast yatashi da niyyar tafiya anan Teemah ma ta ce itafa bazata iya zama agidan ba gaskiya tsoro takeji sai de sutafi tare, bayason ta 6ata masa lokaci dan haka yace toh sutafi .
Gidan Umar yakaita daga nan yawuche wurin aikinsa.
Matar Umar ta'danyi mamakin zuwan Teemahn amma bata tambayeta dalili ba haka suka wuni abinsu dan yanzu kam Teemah tariga da tasaba dasu sosai.
Da yamma Mahmud yabiya ya 'dauko ta suka dawo gida.
Mahmud kansa yanzu yana mamaki yanda yake samun damar yin baccinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali tun bayan da ya fara amfani da magungunan da aka ha'da mai, yanzu kam Alhamdulillah, dan ko jiya da Teemah ta tashi cikin dare ma dakansa ya farka dayaji motsinta, gashi yauma har ya kwanta suna hira da Fateemahn sa6anin da da yana 'dora jikinsa akan gadon zaiji wani bacci me shegen nauyi harma baya sanin lokacin da baccin yake 'daukansa.
Labarin duk abinda yafaru wajen tafiyar sa yake bata, na yanda yaga wannan matar da 'yarta dama duk abinda yafaru agidan yace tausayin matar da yaranta yakasa barin zuciyarsa, duk lokacin dayasamu chance zai koma yasake duba su, Teemah najin haka tace itama zata bishi tana so tagansu itama.
Be musa taba ya amince, dan yasan ko yace baza bishi bama ba yadda zatayi ta zauna agidan ita ka'dai ba dan haka gara yatafi da abinsa yafi masa.
haka suka ci rabin satin yana fama da ita, sam ta'ki zama agida kuma ya kaita gurin Anty ta'ki, sai de ko su tafi office 'din tare ko kuma ya kaita gidan Umar.
Sosai abin yafara isansa yarasa takamamman dalilin dayake sata wannan abin while ada da bata saba bama bata yi masa haka, ya tambayeta kuma sai de tace bakomai kawai tana tsoro ne.
Toh tsoron na menene sam yarasa.
Anty Chiddy kuwa zuwa yanzun hankalinta sam ya daina kwanciya da rashin samun Fateemah, domin tagama saka rai da samun yarinyar sai gashi kuma bata samunta agida, kullum bata nan tarasa ina take zuwa, gaba 'daya ta 'dora ranta akan yarinyar har hakan yasa ta sallami yaran datake hul'da dasu ganin tasamu sabuwa.
Tayiwa Anty maganar ma kuma duk abanza dan da kunnanta taji ranar da Mahmud yake fa'din wai ai islamiya take zuwa shiyasa bata zama agida.
Da yamma kuma ai Mahmud nagida babu damar taje.
Daga baya sai tayi wani tunani wanda take ganin shine dai-dai, ta yanke shawarar kawai gara tasa ayi mata kidnapping yarinyar taje ta 6oyeta sai ta gama abinda zatayi da ita sannan tadawo musu da ita gida.