Sashe 54
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Garin yin dariya ne wata acikinsu me suna Naanah ta danne 'kafafun Teemah dayake ta mi'ke 'kafafun nata ne a abakin gadon saboda gajiya datayi da yanda ta tankwasu tun farkon zamanta agun " waashh....... Naanah kin karyan 'kafata".
Ta yi maganar tana wani kwa6e fuska tare da janyo 'kafarta ta zuwa gabanta.
Duk kan su sai hankalinsu ya dawo kan Teemahn suka zuba mata idanu kowa na mata sannu, sorry, da sauransu.
Fauziyya (Fauzee) ce tace
" ke Naanah ki riinga kulawa kar kisa ahana mu fita daga gidannan bari kiji "!
Sai Hannah ta kar6e da fa'din " gaskiya kam, in ba haka ba ina ke ina jiwa amarya ciwo"
"Ai kuwa de " inji Hauwa da ke 'ko'karin ja wa Teemah 'kafar tata".
"Kuma dai wallahi, ku kyaleta dallah inta karye banda murakata da sabon wheel chair 'dinta agefenta, kunga ta kafa tarihi a auranta".
Dariya dukkansu suka sanya har Teeman, tana cikin dariyar tace " wallahi kin iya wula'kanci yarinyar nan.
" ai gaskiya ne, kya tsaya kina wani yi mana raki anan bayan ciwon bawani na kirki bane.......!
Fauzee ce ta amshe maganar da fa'din
" ke bata son jikin ta ya samu matsala ne ke baki ga yanda ta koma bane ta wani yi fresh da ita".
" 'kwafa Teeman tayi kana tace " har ina wani abin fresh 'din anan dan Allah, ahakan ne zaki ce na wani yi fresh dani?, haba Fauzee..... dubeni fa ke baki ganin irin ramar dana yi ne,?Allah mummy da kanta ma cewa take yi wai na rame dayawa sai ta ta sani cin abinci kullum wai ko zan 'dan murmure".
"Duk da haka de ke kam ki yadda kin canja, ai rama daban canjawan skin ma daban"
Cewar Naanah.
Fauzee kuwa tace
" muma dai ya kamata mu fara haramar yin auren nan ko ya kuka gani"?Ta 'karasa maganar tana rarraba wa sauran idanu.
" toh zakwa'di ai de kya bari ki 'kare secondaryn tukunna ko?" Inji Teemah
Baki Fauzee ta rufe "au ashe fah da sauran mu mu 'din bamu gama ba".
Dariya suka kwashe mata dashi dukkansu sai Jiddah tace " 'yar rainin sense....da 'din mantawa kika yi kenan."
" Tamanta cewa ni ka'daice na girma acikinku" Teemah ce tayi maganan tana musu dariya.
" ai ki bari wallahi nima da nasani da nace wa Babana zan rubuta waec alokacin nasan da bazai hana ni zai barni, kunga da ina yin candy nima sai asha biki na irin na Fatima Kb".
sai Teemah tace
" ke kika sani, yanzu kam ai ya wucheki sai ayi ha'kuri ajira next year "
Haka suka ci gaba da hira atsakaninsu, gwanin birgewa Teemah kwata-kwata mantawa tayi ma wani batun aure, ji take kamar suyi ta zama ahaka kar su tafi.
Acikin hirar ne
Naanah tace da Fatima itafa gaskiya bata san waye angon ba anuna mata shi ko a pix ne, saboda taji ance wai yayanta ne 'dan gidansu, kuma yayun nata kusan mutun biyu tasani bata san kuma wanene shi daga cikin su ba so tana so taganshi.
Sai duka sauran ma suka goyi bayanta dan hatta Hannah ba ta gane shi ba, ko lokacin dayaje gidansu ma basu ha'du dashi ba har yatafi shiyasa bata sanshi ba.
Teemah wayarta ta tashi ta 'dauko ta nemo photon shi 'daya daga cikin wanda yake tura mata tun lokacin suna chat sosai dashi ta nuna musu kar6ar wayar sukayi suka ringa zuzuta kyanshi dan ba 'karya Mahmud ba baya bane wajen kyau da cikar kamala.
Koda wayar tashiga hannun Hannah ma " wow " tafara fa'di tace gaskiya ya ha'du, ni sai na gama kamar kuna 'dan kama ka'dan dashi"?
" badole ba ke kuwa abinki da jini 'daya"
Cewar 'daya daga cikin su.
Mahmud kyakykyawa ne shi, yana da tsayinsa daidai gwargwado, shi ba fari tas bane kuma ba ba'ki ba skin colour 'dinshi me kyau ne kuma ya kar6i yanayi da tsarin sa, gashin kansa irin na asalin fulani ne ananna'de yake kuma akwance luf luf dam ma shi yana yawan aske wa be fiya son tara gashin ba sai dai yabar 'dan daidai, kammanin sa na fulani sak yayi wata 'kila yabi jinin kakarsa ne mahaifiyar Babansa ( Innah Hansatu) sai de shi yana da 'dan kauri ka'dan kamar Antyn sa (mahaifiyarsa )
bashi da sirinta ko ka'dan, abinda kenan ya 'dauko daga wurin mahaifiyarsa."
" danma baki ga 'daya yayan nata ba, shi sun ma fi kama da Kb sosai, inji Fauzee tafa'da tana me kallon Hannah
Azaton su ita 'dinma wata 'kawar Fatiman ce daga wani 6angare daban duk da akwai 'dan kama na jini tsakaninsu, saboda duk wanda yaga Teemah yakuma ganin Hannah sai yaga wannan kamar da suke dashi, amma su basu ma lura da hakan ba, shirman su kawai suka sa agaba.
Daga nan suka cigaba da zuzuta kyawu da tsaruwar yayun Teeman dayake sun sansu gaba 'daya ada lokacin tana zuwa school duk cikin su babu wanda be yi mata rakiyar zuwa makaranta ba daga Mahmud 'din har Abbas.
Fitsari ne yadami Hannah sai ta tashi ta shiga bayi to ease her self, ko da tayi fitsarin tagama sai kuma tayanke shawarar yin wanka saboda lokacin da Teemah tayi wanka 'dazu ita daman batayi ba tana kwance tana ta chat abinta har 'kawayen Teeman suka zo.
Shi yasa data shiga batin sai tace kawai bari taha'da da wanka gaba 'daya.
Shiganta ke da wuya kuwa sai akazo akayi kiran Teemah wai suzo inji Ummah ita da Hannah.
Tashi Teemah tayi tace wa 'kawayen nata "bari inje ina zuwa yanzu, idan Hannah tafito ku sanar da ita Ummah tana nemanta dan Allah".
"Toh" sukace mata daga nan tayi waje.
Koda taje d'in sai Ummah ta tambayeta ina Hannahn kuma bayan nace kuzo tare, yayanku ne yazo kuma zai wuche yanzu shine nache ya tsaya ku gaisa inajin yana 'dakinsa, kinsan shi da gaggawa wai yana da abunyi agabansa".
" Ummah bayi Hannahn tashiga bari in dubota toh sai muje tare".Teemah tayi maganar tana 'ko'karin juyawa har muryarta na rawa.
" ah ah kyaleta kar a6ata masa lokaci ke kije ku gaisa kawai in tafito dawuri sai ta samoki".
Ummah ne tafa'di haka dai dai shigowar Mummy da try ahannunta an shishshirya abinci akai "ingo tafi masa da wannan"inji mummyn tayi maganar tana mi'kawa Teemahn try 'din dake hannunta.
Kar6a Teemah tayi tafara tafiya ahankali, tunda Ummah tace _yayanku ne yazo_ take jin zuciyarta na harbawa da 'karfi, bata bu'katar wani dogon 'karin bayani domin tasan Yah Mahmud ne yazo shi tun da tasan shine future husband 'dinta dole shine yazo, dan shi ka'dai ne zai bu'kaci ganinta awannan lokacin dole tasan sai hakan yafaru.
Ita duk atunaninta Mahmud ne yazo ,kuma bata san me yasa taji tsoro yashige ta ba, duk da wani tsoron Yah Mahmud 'din take ba amma sai takejin wani iri tamkar karta taje gurin shin haka taji, wai yau zata ga Yah Mahmud 'dinta, her beloved brother, amma ba'a wannan matsayin da ta sanshi akai ba, yau Yah Mahmud amatsayin wanda zai kasance miji ne agareta zata gani.
Bata so tasake ganin Yah Mahmud ba, inda son ranta ne har se bayan anyi auren wata 'kila alokacin zataji son ganin shi amma yanzu kam da za'a tambayi ra'ayin ta kafin yazo da ta ce yayi zamansa basai yazo ba, bata san me zata ce da shi ba ko da ta ganshin ma yanzu.
Tafiya takeyi ahankali tana tunani har ta isa 'kofar 'dakin da tasan na Mahmud 'dinne wanda iya zaman sa agidan anan yayi rayuwa, hannun ta da abu so babu daman ta tsaya yin nocking a'kofar, thank God ma 'kofar ba'a rufe gam take ba sai kawai tasa 'kafa ta tura sai 'kofar ta bu'du, ciki ciki tayi sallama bata wani jira jin amsa ba ta tura kanta ta shiga ciki.
Bugun da zuciyar ta keyi ne ya 'karu fiye da na baya, sai ta kasa 'daga kanta ta kalleshi har taje ta ajiye tire 'din a kan centre table 'din dake cikin 'dakin sannan ta 'dago ta kallo bayan wanda ke tsaye agurin window tamkar andasa shi.
Maganar mummy ta tuno da kusan kullum sai ta mata tuni akai inda take cewa " ayanzu baki _da wani makami Fatima face addu'arki da kuma ha'kuri, dan nasan su ka'dai ne zasu jagorance ki ga dukkan al'amuranki, dole ne kiyi ha'kuri da duk wani abu da zai faru ko zaki gani, kawai kisawa ranki daga Allah yake kuma 'kaddararki kenan, kuma shi yaso ganinki awannan matsayin, domin yawan nuna damuwa akan abu bashine zai kawo miki sau'ki ga al'amarin ba face addu'ar ki, damuwar taki bata da amfani koka'dan sai ma yasake 'daga miki hankali, tunda ke kanki kinga alamun Daddyn ki ba barin zancen auren nan zaiyi ba inajin mutuwa ce ka'dai zata sa yafasa 'daura auren nan ayana yin da naga yake ciki, ki daure ki ya'ki zuciyarki kisawa ranki san auren tun yanzu, idan ma kina jin rashin son Mahmud 'din ne to ki dole ne ki daure ki kauda wannan tunani tun yanzu, Mahmud 'din nan dai da kika sani shine zaki aura ki kuma zauna dashi, dan haka kiyi ha'kuri na tabbata Allah yana tare da dukkan bawansa me dogaro dashi, Fatima ni mahaifiyarki ce kuma mai tsananin sonki fiye da zaton ki, wallahi da'ace inada wata dama ko hanyar da zan iya hana faruwar wannan auren da zan hanashi ko dan ganin farin cikinki ka'dai ma, amma na tabbata dai dai da 'kwayar zarra ban kai ubangiji mahalicci sonki ba kuma shine yaga dama ya za6a miki shi Mahmud 'din dan haka kinga mu bamu isa mu ja da lamarin ubangiji ba, sannan mahaifinki ma basai na sanar dake son da yake miki ba Fatima ke kanki kinsani, kuma shi kanshi bazai ta6a yi miki abinda yasan cutarwa ne agareki ba har abada nasan kinsan wannan, ki daure kiyi masa biyayya kinji.... ina da ya'kinin duk daran da'dewa watarana zaki ga haske arayuwarki insha Allahu_ "
Hawayen daya zubo mata tasa hannu ta goge shi tas tana yi tana sake bawa kanta 'karfin gwiwa