← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 163

Sashe 28

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikuwa d'an dakali yasamu aga hanyar shigowan parlourn ya jingina sannan yasamu damar amsa wayar da kyau saboda wata gajiya yake ji sosai.

Duk magana ce sukayi da Saleem d'in akan komawarsu wurin aiki dake k 'ara k'aratowa, bayan sun kammala da wayar ne ya dawo ya shiga cikin parlourn da sallama abakinsa.

Mummyn ce ta amsa masa sallamar ta sa dan tuni Teemah kam ta ware d'akinta.

Sai da suka gaisa kafin mummy take tambayarsa ko akwai abinda ya had'a au da Teema ne dan ta lura da ita kamar tana d'ari-d'ari da shi.

Shi kuwa bai 6oye mata ba ya sanar da ita abinda Teemahn tayi masa yau d'in kaf bai 6oye mata komai ba.

Salati mummyn tasanya da jin abinda Teemahn tayi fad'a tafara bayan ta kammala da salatin kamar ta ari baki.

Daga k'arshe kuma sai fad'an yadawo kan Abbas d'in shima dan acewarta shi yajawo har hakan ya faru ai tana lura da shi bata ta6a ganin ya hukunta Teemahn ba duk da irin iskancin data ke masa".

Shiru yayi yan jinta sai da ta dasa aya kafin yafara bata hak'uri dak'yar kuwa ta hak'ura bayan ta hak'uran ne yasake rokon ta akan karta yiwa Teemahn komai dan Allah ta bar shi da ita zaiyi maganinta kafin yawuche.

'Kin kulashi tayi kawai ta kauda kanta gefe hakan ne yasa Abbas yagane ba k'aramin 6aci ran mummy yayi ba da jin maganar nan.

Har sai yaji yana dana sanin sanar matan da yayi ma.

Hira yafar kawo mata sama kamar yadda ya saba saboda shi daman kalaman bakinsa kad'an ne.

Mummy kuwa daga " uhmm ko ehh "
Bata k'ara wani abu akai saboda tagama fahimtar shi so yake abin yawuce dan yaga ranta ya 6aci shi adole ya kauda zancen.

Haka yayita d'an surutunsa yagama dayaga ba response mai kyau sai ya yi mata sallama ya wuce d'akinsa.

Washe gari da safe...............

_Vote, comment and_ _share pls_🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._wad'anda nasani da wanda bansani ba. 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *27*

Washe gari da safe da ya tashi sai yayi shirinsa da wuri ya fito, har kuwa lokacin daya fito d'in Teemah bata fito ba, gashi lokaci yad'anja dayake bahaka tasaba ba duk da bai fiya yawan fitowa a irin wannan lokacin ba amma dai yasan Teemahn bata fiya makara zuwa makaranta ba.

Har zai basar kuma sai ya waske kawai ya wuce d'akinnata da niyyar tada ita, sau uku yana yana buga k'ofar amma shiru ba'a kulasa ba ganin hakan yasa kawai ya tura k'ofar yashiga ko sallamar ma bai yi ba.

Kwance ak'asa ya tadda ita tana ciccije baki tare da mammatse cikinta duk ta had'a gumi ga kuma robar ruwa ajiye agefenta.

Da sauri ya k'arasa inda take ya tsugunna " lafiya kuwa" ya fad'a yana tatta6a jikinta daga fuskarta zuwa hannunta da niyyar jin temperaturen ta, azatonshi ma zazza6i ne amma sai yaji jikin normal sai dai d'umi babu wani abu.

" meke damunki ne wai" yasake
tambayarta jin bata amsa masa tambayar farkon ba.

Ita kuwa Teemah dukda tana d'anjin ciwon kad'an-kad'an amma sai hakan bai hanata jin dad'in har cikin zuciyarta da jin muryar Abbas d'in cikin rahama akusa da ita duk da tana tsoron hukuncin da zai mata amma tasan tana cikin wannan halin bazai ta6a yi mata mugunta ba dan duk abinsa yana da tausayi, balle yanda taga yake tambayarta cikin kulawa da k'yar ne ma idan bai manta abinda yafaru d'in ba.

Yunk'uri tayi kamar zata tashi sai yayi saurin tareta ya zaunar da ita da kyau, " ina......kwana yayah" ta fad'a idanunta na k'asa da d'an in ina saboda cikin yad'an sake murd'a mata ga kuma tsoronsa data keji.

Atakaice ya amsa mata da " lafiya " sannan ya k'ara da fad'in " wai me yasame ki ne Fateemah"

" cikina ne yake ciwo, amma nasha magani yafara raguwa ma ciwon yanzu"Teemahn ce tafad'i haka

Shikuwa tsayawa yayi yana kallonta sanda take kan maganar sai da ta dasa aya kafin ya sake cewa " wani magani kika sha"?

" ibuprofen" tabashi amsa.

" tun yaushe yafara miki ciwon"

" bayan an idar da sallah ne".

Yariga yagane meke damunta tunda shi ma atleast yayi zaman class koba komai yasan amfanin shan ibuprofen musamman ma ita da nata period d'in baya mata da wasa amma hakan bai sa ya fasa k'udurinsa akanta ba daya d'aukarwa kansa al'kawari.

Kallonta yasakeyi dakyau sai yaga tayi wata fayau da ita tamkar wacce ke jinyar satikai.

" me kuke yi a makaranta yanzu."
Ya tambayeta.

" test " itama tabashi amsa atakaice da irin sigar da ya mata tambayar dashi.

" toh yaza'ayi kenan, zaki iya zuwane?"

Kai ta d'aga masa alamar " ehh"

sai yace "okay hanzarta ki watsa ruwa sai in sauk'e ki inyaso inkin rubuta Test d'in sai mu dawo gida.

"Toh" tace tare da fara yunk'urin mik'ewa sai ya sa hannu ya da'agota suka mik'e tare
sannan yasaketa.

Bayi ta nufah da niyyar yowan wankan, shikuma sai ya tsaya yabita da kallo sai yanzu ma yake ganin yanayin kayan dake jikinta ashe ma na bacci ne shi duk bai kula ba.

Juyawa yayi ya fita daga d'akin nata yana mai korar shaid'an azuciyarsa.

Yasamu mummy na shirin shiga d'aki itama ganin sa yasa ta dakata suka gaisa anan yake ce mata ai cikin Teemah na ciwo amma wai tasha magani........

Taran bakinsa tayi tunkan ya dasa aya tace " Allah ya sauwak'a mata, makarantar fah ko bazata ba", a yatsine tayi maganar kamar bata so shid'inma yagane tun 6acin ran jiya ne bai barta shiyasa take hakan ga dukkan alamu ranta ya 6aci sosai da Teemahn, sai kawai ya bata amsa yace mata " a'a zataje tana shiryawa ne".

Tana jin hakan ta juya abinta ta wuce ciki.

Dakansa yau ya had'a mata tea tun kafin ta fito daga wankan,sugar d'an dai-dai yasaka mata aciki saboda condition d'in datake ciki.

Itama Teemahn dawuri tayi wankan ganin lokaci yad'an ja sai ta yi shirin nata da gaggawa tafito dayake ma tadaina jin ciwon marar sai dai kad'an-kad'an shiyasa tayi komai da kuzarinta.

Bak'aramin dad'i yaji ba dayaga ta fito normal kamar ba ita ba sai kawai yace " zonan ki yi breakfast mu wuce karkiyi latti "

Ahankali ta taho ga dinning d'in danji tayi banbarak'wai dayake bahaka Yah Abbas d'in yasabar mata ba, tsakaninsu sai dai kallo, kallonma sai ranar daya ga dama sannan take samu, a kullum miskilanci agurinsa shine gaba da komai, Daddy da mummy ne kad'ai bata ganin yana musu hakan.

Haka yasata agaba yace tasha Tea d'in sosai, tana kur6a taji salam sai ta d'aga kai ta kalle shi had'a idanu skuayi dashike shima d'in ita yasa agaba da kallo.

"Ba sugar aciki"
tafad'a tana kallon gefen fuskarsa.

" ahakan zaki sha ai, ke baki san illar sugar agareki ba ko?

Tsoron masifarsa yasa tadinga kur6a tana kuma danna bread a bakinta kamar wasa sai gashi tasha mai yawa dan cup d'in daya had'a mata gaba d'aya ta shanye shi.

Dire cup d'in tayi bayan tashanye d'in sai ya kalleta yana murmushi yace " iyehhh, irin yau anyi abin kirkin nan".

Maganar tasa sai ya sata dariyah shima dayaga tana dariyar sai ya tayata suka yi tare gaba d'aya yau ya canja mata kamar ba yah Abbas d'in data sani ba, zata iya cewa yau ce rana ta farko data ta6a ganin dariyarsa tun zuwansa gidan nan, take sai tata dariyar ta tsaya sanadiyyar tunanin data shiga.

Ita data ke tsammanin mummunan hukunci daga wurinsa sai kuma akasin hakan ya faru, bata ta6a zaton yah Abbas zai yafe mata laifin sata masa da wuri haka ba amma ga mamakinta sai ya sauya hakan da wani sabon salon annashuwa da farin cikin da bazata ta6a mantawa dashi ba.

Idonta k'ur akansa amma sam hankalinta ba'a kansa yake ba, sau d'aya ya mata magana da yaga bata amsa ba sai kawai shima ya yi shiru ya k'ura mata nasa idanun yasan bai wuci mamakin sauyin data gani tattare dashi take yi ba wanda yasan dole ne daman tayi wannan tunanin,bama ita kad'ai ba duk wanda yasanshi idan yaganshi yanzun sai yayi mamakin sauyawarsa.

Sai dai shikuma kokad'an baya so ta samu chance d'in da zata yi tunani akan hakan har sai ya bar garin tukunna dan haka sai ya d'ago hannunsa yaja kumatun ta tare da jijjigawa, ai kuwa sai ta dawo daga tunanin tare d'an firgicin tsoro bayyane a cikin k'wayar idanunta dayake daman bata gama sake jiki dashi ba har yanzu, amma ganinsa da smiling face yana kallonta sai ta saki ajiyan zuciya slowly, " kin manta zakiyi Test a school ko?, tashi kije ki gaida mummy sharp-sharp kizo muwuce".

Asanyaye ta tashi tsaye tana duban fuskansa afakaice shikuma alokacin agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa yake dubawa amma duk da haka sai yace " kiyi sauri kije nace kuma kin wani tsaya anan kina kallona!

Fuskarsa sake take aduk lokacin da zai kalle ta ko zai furta mata wata magana shikansa jin kansa yake wani iri daya ke bahaka ya saba ba amma wannan d'in aganinsa dolensa ne yayi mata hakan kodan ya yi maganinta saboda rashin jinta.

Bata fi 3mins agun mummyn ba ta fito da d'aurarren fuska, tana fitowa kuwa shima ya mik'e tsaye ya iso gareta dan ganin dayayi bata da walwala
" ya akayi ne "
ya tambayeta bayan ya tsare gabanta wanda dan dolenta hakan ya dakatar da ita daga cigaba a tafiyan datakeyi.

" ba mummy bace ta min masifa.......

" me kika mata "
Ya jeho mata tambaya tunkafin tak'arasa fad'in abinda tayi niyyar fad'a.

" Nima bansani ba"
Tabashi amsa ashagwa6e sai baiyi magana ba kawai ya juya yafara tafiya sannan yace "oyah hurry up muje kiyi test d'in idan mun dawo sai ki bata hak'uri.

Bin bayansa tayi itama batare da ta yi wata magana ba.
Chapter 28 · 0% Book details