← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 163

Sashe 91

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Daddyn Abuja yayi ya kauda kai gefe, hakan yasa Daddyn Teemah 'karasowa ya zauna shima.
Dan ya fahimci ran 'kanin nasa a matu'kar 6ace yake tunda har ya nuna halin ko in kula da zuwansa.

Da 'kyar yasamu yashawo kansa ya sassauto.

Amma be wani saki jiki sosai ba, duk lokacin dayaga Abbas 'din sai kawai ya tuna da abubuwan da yayi taji a labarai sai yaji ransa ya 6acida hakan.

Kusan kwana uku da dawowar Abbas amma maganar bata wuce ba, su daddy suka koma Dubai da Mummy sai daga baya da ya samu Daddyn nasa yayi wata tafiya kafin yasamu ya 'dan sake a Abujan.

Sai da su Mummy sukayi kwana biyar da tafiya kafin yasamu suka zauna da su Ummah har suka 'dan tattauna akan rasuwar Mahmud wanda dukkansu abin ya ta6a rayukansu ciki harda Hannah ma da ita bataje ba kuma ma bawani sabo tayi dashi ba, amma yanda Ummah ta ke basu labarin yasa duk takejin tamkar tana gurin akayi komai, dataji batun saka Teemah ta aikata lesbian da Anty taso yi da wata mata wacce bama musulma ba ce yasa tunanin Hannah yayi saurin kawo mata cewa waccen matar ne data ganta ranar da suka kai Teemah gidan uwar mijinta dan taga yanda matar take kallon Teemah alokacin tamkar zata cinyeta 'danye bata ta6a raba 'dayan biyu itace.

Hannah ce ta tambaye Ummahn tace da ita " _toh meyasa kuma aka baro Teemah acan bayan duk faruwar wa'dannan_ _abubuwan, basa jin tsoron abinda ze biyo baya ne_ ?

sai Ummah tace
" _Antyn yanzu tana bata tausayi ne sosai kuma ita ta ro'ki abar mata Teemahn saboda_ _ka'daici_ "
Ummah tace itama bata amince ba da farko 'ki tayi dan taga yanda yanayin Teemahn yake har yanzu bata saki ranta ta sosai ba, taso a 'dan nesantata da garin ko zata samu ta warware da wuri, amma se Mummy tayi saurin amincewa da batun Antyn.

Ummah tace
" _koda muka ke6e ma naso in tuhumi Khadija akan_ _meyasa tayi haka amma sai ta nuna min bakomai ai yanzu Anty tayi_ _nadama ta gane kuskurenta, mutuwar Mahmud ya kasance aya ne agareta me girma, dan haka abar mata Teemahn kawai wai_ _Antyn tausayi take bata sosai itama yanzun_ "

Ta6e baki Hannah tayi ta 'dauki wayarta taci gaba da latsawa tamkar bata damu ba amma Allah ne ka'dai yasan yanda taji haushin hakan azuciyarta, abar yarinya ma da abinda ya dameta za'a wani 'kara barinta agurin muguwar matar nan, itama Teemah ai abin tausayi ce ba wata Anty ka'dai ba, ji take da 'ace tana da iko da sai ta je ta 'dauko 'yar uwarta zuwa gida , yayinda Abbas ya kauda kansa gefe sam yaji nutsuwarsa ta kau, shi ai be ta6a tunanin an baro yarinyar acan ba, taya ma za'ayi ace tana can gurin matar da ta fi tsananta aduniya se kace tarasa 'yan uwa ko kuma tarasa inda zata zauna , wannan ai rashin gata ne akayi mata, sam ya tsani matar nan har zuciyarsa, halinta sam be masa ba, yanzu kuwa dayaji komai kaf sai yakejin ma gaba 'daya itace abu mafi girma dayafi tsana arayuwarsa, tausayin banza tausayin wofi
shi be abin tausayi awurinta ba sam.

Be ce da Ummah komai ba kawai ya tashi yana wani ha'da goshi yakoma 'dakinsa.

Ummah da idanu kawai ta rakashi dan ta fahimci ba'a saiti yake ba.

*****
Yanzu komai ya dawowa Anty sabo fil, ibada kawai tasa agaba tana neman gafarar mahallici tare da yiwa marigayi Mahmud addu'an neman dacewa, kusan kullum sai ta zubda hawaye musamman idan ta dubi Teemah sai taji dama ta bari sun yi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali sun haifa mata jikoki masu kyau kamar su, da ma bata shigo da su Munnira cikin rayuwarta ba, tasan da yanzu komai be faru ba,
lallai gaskiya ne da'ake cewa tsalle 'daya tak zakayi kafa'da rami amma fita daga ciki kuwa sai kayi dagaske, yanzu gashi nan ita gari ya waya dan kowa na zaune da 'ya'yansa cikin so da 'kauna ita kuwa babu nata, tsanan data yiwa Khadija na ba gaira ba dalili gashi ita abin ya cutar, awannan lamarin bata tashi da komai ba face hasara me girma, ko Anty Chiddy da take aminiyar tama gashi tun rasuwar Mahmud 'din har yau sau 'daya tak taganta agidan, bata 'kara zuwa ba, ha'ki'ka masoya nada wahalar samu wani lokacin ma'kiya kuwa ko'ina suna nan birjik akewaye dakai, gashi ita masoyanta ma na kusa da ita amma ta rintse idanu ta ringa hango ma'kiyanta dake nesa da ita 'karfi da yaji ta matso dasu kusa da ita, bata sani ba ashe kanta zata cutar, gashi nan Khadija data nunawa tsana muraran itace ta bar mata 'yar cikinta amatsayin sanyin idaniya dan ta rin'ka 'debe mata kewa batare da ta yi musu ko da ka'dan ba, yau da ace burin Anty Chiddy ya cika akan Fateemah tayi lalata da ita da bata san ya zatayi da abin kunya ba, tasan ita kanta da se ta tsani kanta da rayuwarta, Alhamdulillah ma da abubuwa suka 'dan yi sau'ki Allah ya tsare Fateema ya bata kariya.

Abbah kansa yanzu baya kula ta ko da ya shigo sede su gaisa da Fateemah ya 'dan jata da hira da tambayarta damuwarta sannLnan ya yi mata nasiha daga nan ya tafi abinsa ko kallon inda Anty takeyi ma bayayi.

Da farko tana damuwa da hakan amma ganin dagaske yakeyi yasa itama ta ha'kura ta daina damuwa tasawa ranta cewa girban sharrinta kawai takeyi adun'kule, tariga kuma ta kar6i duk wani 'kalubale da zai zo mata ko da kuwa Abbah zai ce ne yasake ta bazata damu ba in kuwa yankan naman jikinta zai rin'kayi kullum shima bazata yi musu ba, dan tasan ka'dan kenan daga cikin abinda Allah ze mata dan ba 'karamin amanar amintattun bayinsa taci ba.

Abbah kullum idan ze dawo sai ya kawo mata wani abu naci sha kona sawa sannan yayi ta mata hira har se yaga ta 'dan saki jiki kafin ya barta, shi kanshi ma bawai mutuwar bata dameshi bane a'a sosai yake jin kewar 'dansa amma baya nuna damuwarsa afili, sai ko in yana 'dakinsa shi ka'dai kafin nan yake tunani tare da yi masa addu'ah sosai, amma kana ganinsa kasan mutuwar ta bigeshi, musamman idan kayi duba da irin ramar da yayi, tausayin Teemahn yake ji ayanzun ganin cewa wannan lamarin ya sameta ne tun a 'kananun shekarunta, tana yarinya 'karama da ita shiyasa ma kullum yake 'ko'kari wajen ganin ya faranta mata.

Anty kuwa kawai dubanta yakeyi baze iya koda maimaita abinda yafaru abaya da ita, be ta6a sanin haukarta takai hakaba, shi dai baze rabu da ita ba saboda darajar mahaifinta amma bayajin ze 'kara yadda da ita har 'karshen rayuwarsa, tsana me girma yake yi mata wanda baya jin akwai ranar da hakan ze bar ransa.

Teemah har karatu take 'karawa Anty ka'dan dan gaba 'daya ta mantasu duk da ta yi karatun abaya amma rashin kulawa yasa yanzu ko izu biyu bazata iya kawowa da kanta ba, hakan yasa tace Teemahn tana yi mata ko zatana tunawa dasu.

Tanajin da'din hakan kuwa dan kuwa sosai take 'karajin kusancin ta ga mahallici, sai de lokuta da dama sukan bar karatun ne saboda kukan da Anty takeyi musamman idan ta tuna baya ta tuna da 'ko'karin da mahaifinsu yayi tayi akansu amma duk ta watsar, shima yau gashi da fushinta ya yabar Lagos beko tsaya ya saurareta ba, tasan yanzu kusan kowa ya tsaneta tunda gashi iyayenta ma basu saurareta ba, saboda mummunan halayenta.

Anan ne Teemah sai tayi ta bata ha'kuri tana mata nasiha hartayi shiru, gaba 'daya damuwar Anty sai ta nunka na Teemah harma wani lokaci manta nata takeyi sai de Anty.

Itama yanzu sosai Antyn take bata tausayi ganin yanda gaba 'daya take damun kanta alokuta da dama.

Gashi Abbah ma sai ya daina shigowa sai de ya 'kira Teemahn zuwa 'dakinsa suyi hirarsu ya bata duk abinda zai bata sannan ya sallameta, sau tari sai bayan ta fita damuwarsa ke 'kara yawaita addu'arsa kullum agareta shine Allah ubangiji ya bata miji nagari wanda zai so ta ya kuma kula da rayuwarta.

Haka rayuwar Abbah ayanzu sam Anty kwatakwata ta daina ganinsa ma.

Ganin kamar abin ze mata yawa ne yasa Teemah ta 'dan fara yiwa Abbah magana akan ya yafewa Anty kar damuwan yayi mata yawa tunda yanzu ta tuba tace ya yafe mata shima, Allah ma yafe mana yakeyi idan mukayi masa laifi meyasa mu bazamu yafi junanmu ba.

Da 'kyar da su'din goshi Teemah tasamu kyakkyawar kalmah daga gurin Abbahn dan kusan kwana uku sukayi akan maganar kafin yace zai yafe mata amma sai in ya ga cewa tuban gaskiya tayi sannan yace hakan ma darajar Fateemahn zataci in ba dan haka ba da beyi niyyan sake waiwayanta ba.

Sosai Teemah taji da'di harma takasa ri'kewa sai da ta gayawa Antyn abinda Abbah ya fa'da, Anty tana jin haka kuwa ta rarumo Teemah ta rungumeta tana mata godiya tare da sanya mata albarka .

Duk wani kulawa da ya kamata uwa tayiwa 'yarta Anty nayiwa Teemah shi inka gani sai kayi zaton tun tasowarta tare suke da ita, gata babu irin wanda Anty bata mata shi komai takeyi hankalinta nakan Teemahn motsi ka'dan tayi kuwa sai ta ji dalili ita kanta Fateemah wani lokaci murmushi kawai takeyi da canjuwar Anty.

Anty tariga ta yanke shawarar Teemah agidanta zata yi duk watannin takabanta dan haka tasaki jiki sosai ta rungumi rayuwarta dana Teemahn tare da kiyaye duk wani abu da ze sa Abbah ya zargeta daga wani abu.

Kwanan Abbas shida agida amma sam zuciyarsa ta gagara saduda da barin Teemah da akayi a Lagos, gani yake kamar 'kara salwantar da rayuwarta ne akeso ayi abanza.

Gashi shi ba ze iya 'kara tunkarar Ummah da batun ba kawai abin nacinsa ne azuci, wani lokaci ko dadare kasa bacci yakeyi, sai ya ringa tuno da mafarkin da yayi kwanaki, idan ya fasa mafarkin nasa sai yaga kamar azahiri abin ke faruwa, tunda kam gashi Mahmud yatafi yabarsu, toh in hakane kuwa meyasa za'a bar Teemah wajen Anty data so ta lalata mata rayuwa abanza.
Chapter 91 · 0% Book details