← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 163

Sashe 89

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama fa'din hakan ya juya ya fita sauran biyun dake taimaka mishi suma suka bi bayansa.

Yayin da Abbas ya 'daga 'kafafun sa da 'kyar ya koma gaban gadon ya 'daga lullu6in da aka yimasa.

Gani yayi fuskarsa shar har yanzu da murmushi, sai ma wani 'kara yin fari dayayi kamar yace tashi Mahmud amma wai babu shi.

Acikin zuciyarsa yace " _Allah ya ji'kanka Mahmud yayi maka rahama, Allah ya haskaka 'kabarin ka yasa aljanna itace makomarka, Allah yasa mutuwa hutunka ce Mahmud_ "

*Masoyan Mahmud ayimin afuwa, tun asali ahaka labarin yazo, ina fatan zaku cigada bina dankin 'karshen labarin.*

~Team Abbas ku kuma muna jiran jin yadda zaku ri'ke mana amanar Teeman mu~ .

_Comment_
_Vote and share_

*Salmerh ce* 😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Every moment of life is a step towards death......._

🅿 *67*

Ahankali suka fito daga cikin 'dakin tamkar wa'danda basu so suyi tafiyar, kawunan su duk na kallon 'kasa.

Anty ne tafara tambayar su " ya jikin nasa ? yasamu yayi bacci ne?
Ta jero tambayoyin nata ajere.

Abbas ne yayi dauriyar yin magana dan shi kam Umar yana daga bayan Abbas 'din yana faman share hawaye.

" _Muje akaiku gida_ "
Abbas yafa'da idanuwan sa na kallan gefe, sosai mutuwar Mahmud 'din ya bige shi, acikin idanuwansa ka'dai zaka gane hakan.

Anty ne ta hango Umar daga baya ka'dan da Abbas yana faman share hawaye take ta maida hankalinta gurinsa tace.

" _Umar me ya samu Mahmud kake kuka?,nunfashinsa ya tsaya ko_ ?.

Ganin Umar be tankata ba kuma be 'dago ya kalleta ba yasa ta furta " _Nashiga uku na Mahmud ya rasu Munnira_ "
Tayi maganar tare da 'dora hannu akanta, sai luuu ta zube a'kasa sumammiya.

Tsawon mintina ashirin kafin ta farfa'do inda ta tsinci kanta kwance agadon asibiti, farko idanuwan ta akan Teemah ya fara sau'ka dake gefenta azaune tayi tagumi ta 'kurawa gadon idanu, yayinda Munnira ke zaune agefen gadon da Antyn take kwance itama tayi shiru.

Ita da Munnira ne kawai a'dakin su Abbas kuwa na can suna preparation na tafiya da gawa.

Anty na farkawa ta gansu zaune jigum-jigum ai sai kawai tasa kuka wanda kukan nata ya sa suka farga da cewa ta dawo hayyacinta.
Cikin kukan take fa'din
" _Dagaske ne Mahmud 'dina yarasu ko Munnira_ ?
_Dagaske ne yarona_ _ya tafi ya_ _barni_ ?

" _Yi ha'kuri Anty dan Allah ki daina kukan nan haka nan, addu'ah zakiyi masa kinji_ "

Cewar Munnira dake 'ko'karin tallafota .

Teemah kam binsu kawai take da idanu bata san me zata furta ba sam.

Sai da aka wuce da Mahmud gida kafin Umar yaturo driver yazo ya koma dasu Anty gida, kafin nan kuwa gidan harya fara cika da mutane.

Abbah ne yace a 'dan jinkirta masa ka'dan yazo yaga gawar 'dansa da idanuwansa hakan yasa aka 'daga jana'izar Mahmud 'din sai zuwa bayan sallar juma'ah.

Kafin hakan kuwa jama'ah da yawa sun iso daga 6angarori da dama, ciki harda su Daddyn Abuja, Ummah, da su Daddyn Teemah mutanen Dubai, Abbah ma ya iso tuntuni inda ganin gawar 'dansan kwance yasa yakasa ri'ke zuciyarsa sai da ya share hawaye kusan sau uku amma be tsawaita ba dan yasan kukan bashida wani amfani koka'dan ga dukkan mamaci.
Amma shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa , 'dansa 'kwaya 'daya tak daya keso kamar ranshi amma yau gashi kwance agabansa da gawa, wanda yafishi ya amshi abinsa, Allah ka jikan Mahmud ka haskaka masa 'kabarinsa, nasan beyi gaggawa ba muma kuma ba jin kiri mukayi ba.

Dayake Ummah tariga su Mummy isowa yasa Teemah tunda taga Ummahn ta tafi ta lafe ajikinta tayi shiru gaba 'daya koman ta ya tsaya mata cak hatta tunani bata iyawa sai de idanuwa da take faman rarrabawa ko rintse idanu bata son yi saboda tana rintse idanun sai taga Yayah Mahmud nayi mata murmushi lokacin dayake kwance a hospital, hakan yasa ta 'kin rintse idanu koka'dan.

Sai da Mummy tazo sannan tatafi wajen Mummyn ta rungume ta tare da sanya kuka abin tausayi tace
" _Mummy ance wai Yayah Mahmud ya rasu_ "!

" _Yi shiru toh ki daina yi masa kuka, addu'ah zakiyi masa ba kuka ba kinji_ "

tace
" _ai kema kukan kikeyi Mummy_ !

Janta Mummy tayi ta ha'da ta da jikinta sosai ta rungumeta dukkansu na kuka da rashin Mahmud 'din, ga kuma tausayin Teemahn datake ji sosai ahalin yanzun.

Sai ganin Anty sukayi tsaye akusa dasu tace " _Khadija kema kuka kike yiwa Mahmud ko_ ?
'Dagowa Mummy tayi ta kalleta idanun ta duk hawaye.

Murmushi Antyn tayi me ciwo tare zama daga gefen Mummyn sannan tace
" ba ke ya kamata kiyi kuka ba Khadija nice,
kuka dani ya dace, inajin kamar da hannayena na kashe shi, ha'ki'ka na cuci rayuwata na cuci rayuwar mutanen da basu ta6a min koda kallon tsana ba balle su cutar dani, bansani ba Khadija ashe sakayyata me girma ce, ban ta6a tunanin mugun halina ze iya sanadin 'dana na cikina ba, banta6a tunanin haka ba, sai gashi Allah ya nuna min iyakata ta yanda ban isa inja da yinsa ba koka'dan koda da wasa"

Idanuwa ta lumshe sai ga hawaye sun ziraro mata da gudunsu bata damu ba taci gaba da fa'din " yaune rana ta farko dana ta6a yin dana sanin aikata mummunan laifi arayuwata, Mahmud 'dina yarasu Khadija, Mahmud ya tafi ya barni da tarin laifukana bansani ba ko Allah ze ji'kaina ya yafeni"

Wata mata dake zaune daga gefenta ce ta fara bata baki akan tayi shiru ta daina kukan mana tace fa'de-fa'den ma bashi da amfani.

Ko kallonta Anty batayi ba kawai ta jijjiga kanta tace
" baki san yawan abubuwan dana aikata ba ne, na tabbata da kinsani nasan da kema tsanata zakiyi kamar yanda yarona yatafi da mugun tsanata azuciyarsa, juyawa tayi ta kalli matar tace kinsan abinda yakashe min Mahmud ne ? Kinsan sanadin mutuwarsa?
ko kinsan mugun ciwon da ya dasu acikin zuciyarsa kafin ya rasu?
Ni naga wannan 'kuncin acikin idanuwansa naga hawayensa dayake fitarwa me ciwo kafin yabar gidan nan, duk naga hakan rintse idanu nayi ban ko ji tausayinsa ba, ni de 'kudurina kawai ke gabana"
Mahmud yaro ne me matu'kar biyayya yana kula da dukkan hakkin iyayensa daya rataya akansa be ta6a yin abu dan ya 6ata min rai ko mahaifinsa ba duk kuwa da surutun da Allah ya bashi hakan be sa ya kasance mara kunya ba, nice nafara 'kuntatawa rayuwarsa ta hanyar dasa masa 'kaunar yin makaranta a'kasar waje wanda tun bashi da ra'ayin haka har yazo ya amince saboda yanda yaga na kafe akan hakan , nariga nasan mahaifinsa baso yakeyi ba amma na dage nace sai anyi, sanadiyyar haka har ya 'debi shekaru kusan biyu batare da yayi makarantar ba, daga 'karshe me yazo yafaru ?
"anan garin lagos yayi makarantar kuma yagama lafiya, tun anan ya kamata nasan abinda kalmar 'kaddara yake nufi amma sam ban yadda ba sai ma na 'kara jahilta kaina da tunanin sakacina ne yakawo hakan, lokacin da Mahmud yace min zai je service ajahar yobe wallahi hankalina ba 'karamin tashi yayi ba, naso na hana hakan badan komai ba sai dan muguwar 'kiyayyar da na kewa Khadeeja wanda alokacin ajahar yoben take da zama, anan kam Mahmud yace shi fa sai yaje dole na nayi ha'kuri na barshi yatafi duk da raina be so ba amma haka na ha'kura na barshi se de har yayi yagama hankalina be kwanta, nakan yawaita takura masa akan yazo gida duk da bani da wani takamman dalilin yin hakan amma zuciyata tariga da tayimin muguwar sa'kar 'kiyayya da be anfane ni da komai ba sai da nasani da bashi da amfani.

Mahaifinsa da kansa ya nema sa auren Fateema musamman dan yabawa da yayi da natsuwarta da tarbiyyarta wanda kafin hakan ni kuma nayi masa maganar auren Munnira duk da ya nuna min baya ra'ayi amma na nace akan sai ya aureta haka abaya so 'din ya amince min sai de mahaifinsa dayake yafini iko dashi, shine ya nemasa auren Fateema alokacin bazan iya misalta yanda naji ba dan haushi da takaici, nayi-nayi iya 'ko'karin dan ganin na hana auren amma hakan ya gagareni, hatta bokaye da malamai duk nabi amma ban iya dakatarwa ba, tsana kuwa 'karara nake nunawa duk wani abu daya danganci auren, sanadin haka mahaifin Mahmud yakai 'karata wajen mahaifina a kano, sosai mahaifina yaja kunnena, yayi min garga'di, yamin wa'azi amma duk abanza koka'dan ban 'dauka ba, ganin haka mahaifina har la'antata yaso yi amma mahaifin Mahmud ya hana shi sai yace matu'kar na aikata wani abu da be kamata ba toh be yafemin ba.

Wannan kalmar batasa na yi wa kaina fa'da ba, mahaifiyata matayi 'ko'karin jan hankalina amma na nuna mata bata isa ba dole itama tazuba min idanu ta 'kyale ni.

Ko bayan auren nayi ta neman hanyan dazan rabasu amma narasa yadda zanyi, ni kaina bansan me yasa na tsani auren ba, bansani ba ashe shai'dan ke ingizani, dan Fateema bata ta6a 6ata raina ko sau 'daya ba amma duk da haka banji amincewar barinta ta zauna amatsayin matar 'dana ba.
Chapter 89 · 0% Book details