← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 163

Sashe 50

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Abbas da Mahmud tare suka fita daga gida bayan Ummah ta ha'da su tayi musu nasiha sosai daganan ta sallame su suka tafi kowa ya nufi inda zashi, bayan Abbas ya sake 'karfafa wa Mahmud gwiwa akan maganar daya zo da itan tare da jaddada masa muhimmancin bin maganar iyaye kamar yadda Ummah tayi musu.

Haka suka rabu Mahmud na yiwa Abbas 'din godiya da kuma fatan alkhairi domin zuwa yanzun Alhamdulillah ya ji dama-dama a zuciyar sa, he is now ready to face his reality.

*DAMATURU*

Daddyn Teemah be bari mummy ta sanar da ita ba shine dakansa ya zaunar da ita yayi mata bayani yanda yasan zata fi fahimta, itanma da farko ta 'dan ji tashin hankali amma aranta, dayake bawani zama takeyi ta fahimci me zuciyarta take ciki ba shiyasa takasa gane inda nutsuwarta ta dosa akan maganar daddyn.

Ji takeyi tamkar tayi na'am da maganar amma deep down tana jin kamar kuma bata aikata daidai ba.

Daddy kuwa kafin su rabu sai da ya tabbatar da cewa ta amince da maganar 100% kafin hankalinsa ya kwanta, daman damuwarsa kenan shine kar Fatiman ta'ki amincewa duk da yana ganin kamar wayo be gama isanta ba kuma hakan bazai barta ta kasa amincewa da maganarsa ba, amma 'dan adam sai Allah, kowa nada nashi kalan burin arayuwarsa.

Har Daddy suka gama maganar su da Teemah mummy bata saka musu baki ba, ita abubuwa ne suka taru suka yi mata yawa azuci, tunda ranar da akayi maganar auren nan mummy bata sake yin baccin kirki ba, tausayin 'yarta ta yawa yake yi mata ta fuskoki da dama.

Babban damuwarta shine yanda Anty zata kar6i batun nan, tasan da wahala ta yadda da auren, idan ma ta yadda 'din toh wani irin zama zatayi da Fatiman.

Sannan secondly alamu da yawa sunnuna cewa tun ba yau ba Teemah ta fara son Abbas, she can proof that Zuciyar Fatima Abbas takeso, amma rashin wayo irin nata yasa takasa bambance abinda takeso harma gashi ta amsawa mahaifinta cewa ta amince da auren Mahmud.
Yanzu kam mummy ta saduda ta barwa Allah komai " bani da abin cewa nikam ayanzu sai de nayi ta miki addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi aryuwarki".

Teemah sai da ta koma 'daki sannan ta fara fahimtar yanayinta, jin ta tayi wata iri, kaf sai ta nemi nutsuwa azuciyarta ta rasa sai asannan taji tamkar bata yiwa kanta adalci ba.

Fa'dawa tayi rigingine akan gadonta abun duniya duk sun taru sun mata yawa, Abbas ne ya fa'do ranta karo guda sai taji zuciyarta ta tsinke da 'karfin gaske, har sai da ta rintse idanunta ta kuma dafe 'kirjinta da hannunta.

Daga nan abubuwan da suka faru atsakanin su suka rin'ka dawo mata 'daya bayan 'daya......
Yah Abbas.....Rashin fara'arsa......Muguntarsa....Masifarsa....
Komai ma nashi yaringa dawo mata azuciya, juyi tayi zuwa 'dayan 6angaren yayin da ta tuno lokacin da Mahmud ya zo gidan su, basu wani 'dau lokaci ba suka saba da juna sa6anin Abbas da alokacin ma kullum sai sunyi fa'da dashi.

Tashi tayi ta zauna abakin gadon ta cigaba da tunani haka kawai batare da tasan dalili ba taji zuciyarta tana mata comparing halayyar Abbas da Mahmud amma kwata-kwata ta kasa samun laifin Mahmud aranta ko 'daya sai de duk da haka zuciyarta takasa nutsuwa da maganar da suka gama da mahaifinta lokuta 'kalilan da suka gabata, sai take jin ma dama ba Yah Mahmud daddy ya za6a mata da sunan ta aura ba.

Tashi tayi da gaggawa kamar wacce aka bawa umarni ta nufi wurin ajiyan kayanta sanadiyyar tuno wani abu da tayi, bincike tafarayi acikin kayan inda ta ringa ciro kayan da 'da'dd'aya tana zubo dasu 'kasa sai da ta ciro kusan rabi daga cikin kayan nata kafin ta samu abinda take nema 'din.

Da sauri ta tattara ta dawo 'kasa akan tiles ta zubasu itama ta zauna dirshan agabansu.

'Ko'karin ha'da papers 'din takeyi amma har yanzu ta kasa ha'dasu, haushi hakan ya bata dan ayanzu damuwarta be wuce tasan miye acikin takardan ba da tun ranar daya batan takardan ta lalace da gumi, tun ranar taji ba'kin cikin rashin ganin abinda ta kardan ta 'kunsa ga dai alamun rubutun da akayi da biro tana gani amma gane ko menene sam ya gagare ta.

Ko ta 'dan harha'da sai taga beyi yadda take so 'din ba ga dukkan alamu guri me muhimmancin ne ya fi ji'kuwa tun awancen ranar.

Haushin bazata ta6a ganewan ba yasata ta dun'kula su tayi jifa dashi kamar zatayi kuka.

Tana watsarwan kuwa sai tajiyo muryar mummy ta 'kira sunanta tare da 'karasowa cikin 'dakin nata ahankali.

Tana ganin mummyn sai taji hawaye ya gangaro mata da bata san dalilinsa ba, tahowa tayi da sauri ta rungumo mummyn suka zauna abakin gado.

Fatima bata sani ba ashe tun fara binciko kayan da Teeman tayi mummy ke tsaye tana kallon ta dama so take taji asalin ra'ayin ta akan maganar, koda tazo tasameta awancan halin kuwa sai ta tsaya karantar yanayinta tayi zaton ko wani abin ne daban yake faruwa , and now she's crying.

Sai da ta yi kukanta kusan na mintina biyu kafin nan mummy ta 'dagota daga jikinta, atsare tasa ta tayi shiru kana tace tasanar da ita meke damunta, menene yasata kuka.

Ido mummy ta zuba mata tana karantar yanayinta da kyau, yayin da Teemah ta maida kanta 'kasa kamar me jin kunyar ha'da idanu da mummyn sai kawai taci gaba da tsiyayar da hawaye, hawayen ma da sauri suke 6ul6ulowa dan koda mummy tayi 'ko'karin goge mata ma kasa tsayuwa suka yi dolenta ta barta .

Sai da tasake maimaita tambayar tata kafin ahankali Teemah ta 'dago tace da ita " kirjina zafi yake min mummy"
"Miye dalili" mummyn ta tambayeta.

Hannu ta 'dago ta 'dora akan kirjin nata sannan taci gaba da fa'din " mummy dagaske daddy yakeyi wai aure zai min?"

" miye saki zafin 'kirjin "
mummyn tasake tambayarta maimakon ta bata amsar tambayar da Teemahn tayi mata.

Sai tace itama bata sani ba, kawai de tana jin kamar bata son auren ne.

" bakya son auren ko kuma Mahmud 'din ne bakyaso"?
Mummyn tasake tambayarta idanunta kafe akan Teemah.

" Nima fah bansani ba mummy nide kawai zafin nakeji a 'kirjina".

Shiru sukayi dukkansu na 'dan wasu da'kiku sai mummyn tace mata ta share hawayenta kukan ya isa haka.

Tambayarta mummy tasakeyi wai "meyasa ta amince wa mahaifinnata bayan tasan bataso.

Goge hawayen tayi kamar yadda mummy ta bu'kata, amma kuma game da tambayar sai ta rasa amsar dazata bawa mummyn dan haka kawai sai tayi shiru.

Ganin hakan da Teemah tayi tasan zaiyi wahala tasamu jin amsarta dan haka sai ta juya ta kallo cikin 'dakin inda Teemah ta zauna 'dazu.
" wa'dancan 'kananun papers 'din fah na menene su kuma"?

Juyawa Teema tayi ta kallo inda suke itama batare data yi niyyan fa'din komai game dasu ba.

Fahimtar da mummy tayi cewa Teemahn bata da niyyan sanar da ita sai kawai ta mi'ke tsaye tace " inkin gama kisame ni apalour ina jiranki."

Da kai Teemah ta amsa mata daga nan takama hanyar waje.

Binta da idanu Teemah tayi harta 6acewa ganinta, daganan ta tashi sai ta nufi gurin data watsar da pieces 'din takaddun, ta tattare su gaba 'daya ta maida su can 'kar'kashin jerin kayan da suka rage bata wargaza ba.

Tana 'kokarin fara gyara kayan sai ga Baabah Lami ta shigo da sallamarta tace "Hajiyarki tace kayanki sun zubo "

Kai ta 'daga alamar "ehh" sannan ta matsa daga gurin kayan ta nufi hanyar bayi domin ta watsa ruwa dayake daman bata yi wanka ba lokacin da daddy yakirata.

Daga ita sai towel tafito abayin, yayin da tabaro kayan data cire abayin domin wanki suke bu'kata.

Fitowarta kuwa keda wuya Baabah Lami ta jefa mata tambayar wai yau kuwa lafiyarta ?

"Uum lafiya ta 'kalau me kika gani"?
tayi maganar tana 'ko'karin goge fuskarta da wani 'dan 'karamin wiper dake ri'ke ahannunta na dama .

Baabah Lami shiru tayi taci gaba da gyaran kayan da takeyi, Teemah kuma sai ta wuce gaban madubi ta sake duba yananyin fuskarta daganan ta dawo inda kayan tan suke zube aciki tasamu wanda zata sanya sai ta koma 'daya 6angaren da tuntuni arufe yake ta bu'de shi ,bakomai aciki illah tarkacen inners 'dinta dasuke kala kala.

Zura doguwar rigarta tayi bayan tasaka ta saka bra da pant ko kunyar Baabah Lami ma bata ji ba tayi shirinta abinta, tana gamawa kuwa ta zari mayafi ta fice a'dakin tare da cewa Baabah Lami " ina zuwa"
ta nufi gurin mummy.

Tana isa gurin mummyn ko gama daidai ta zamanta bata yi ba mummyn tace " yanzun muka gama waya da Abbas yace wai agaisheki"

Murmushi ne ya kubce mata har sanda ha'kwaranta suka 'dan bayyana afili.

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh*😍
[10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all _cApTaIn_ _AbbAs Fans_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

To know that you do not know is the best. To pretend to know when you do not know is a disease.

🅿 *43*

Har bata san lokacin da tace
"Kuma mummy dakansa yace agai sheni?
kai mummy ta 'daga mata, sai ta sake cewa " lallai Yah Abbas sai yau yaga dama ya tuna dani kenan"

"Da in cemiki akayi ya manta dake ne?

" ya manta dani mana mummy "!
Teemah ta bawa mummy amsar tambayarta.

Mummy bata 'kara kulata ba sai de afakaice take 'kara kula da yanayin ta saboda murmushin da tayi tun 'dazun yakasa barin kan fuskarta harma sai ya 6oye damuwar da take ciki 'dan lokuta ka'dan da suka gabata.
Chapter 50 · 0% Book details