← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 163

Sashe 8

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka tayi ta sumbatu ita kadai,har tafara jin bacci,takuwa kwanta tayi baccinta bayan tacire doguwar rigar dake jikinta.

Ba ita ta tashi ba sai kusan la'asar,tashi ta yi ta watsa ruwa tare da d'auro alwala.

Sai da tayi sallar kafin tashirya cikin uniform tafito taahiga kitchen neman abinda zata ci,duk ba wani abin kirki taciba,amma ita tana ganin hakan yafi mata akan ta zauna taci abincin.

Koda tagama kale kalen nata a kitchen d'in d'akin mummy taje,bata samera a parlourn ta ba,hakan yasa ta wuce bedroom d'in mummyn,sallah tasame ta ta nayi,amma azaman tahiya take,ganin haka yasa tawice gaban mirror tana k'ara gyara fuskarta da kyau.

Tacikin mirrorn ta hanago mummy ta yi sallama,ganin hakan sai ta baro wajen datake tsayen ta taho ga mummyn,
"Mummy natafi islamiyah"

Kallonta mummyn tayi batare data yi magana ba dan bat so ta yanke azkar d'in datakeyi,sai d'an yatsanta data d'aga ta nuno Teemahn dashi tana d'an juya shi kad'an.

"Mummy bacci ne fah ya d'auke ni shiyasa na makara'?" Tafad'a da d'an ta6e baki alamr shagwa6a dan tasan ma'anar hakan da mummyn tamata.

Jijjiga kai mummyn tayi kawai tare da d'auke idanta daga kan Teemar.

Ganin hakan yasa Teema ficewa daga d'akin,dan mummy ta gama sallamarta.

Waje tayi tanufi cikin gidan,tana fita kuwa tafara kwalla wa Habibu k'ira,shima yanaji ya taso da d'an saurinsa ya iso inda taken dan wajen da ake parking motocin gidan ta nufah ita.

"Y'ar gidan daddy ganinan ya akayi"

Cewa tayi
"yauwa malam habibu ka kaini makaranta mana, yau na makara wallahi"

baki yakama sannan yace "ta6,
"kinga kuwa babu key awurina,shiga ki kar6o key saiki zo mutafi dawuri"

Kallonsa tayi sannan tace "toh ina na wurin naka"?

"Wannan bak'on ne yafita dashi."Ya bata amsa.

"Wai yah Abbas kake nufi?"Tasake tambayarsa.

"Oho ai bansan sunansa ba."Zaro ido yayi kamar wanda yaga wani abin tsoro
"Kar dai wannan shine Abbas d'in gidan nan"ya yi tambayar yana kallonta.

"Ehh wai shine inji mummy"itama ta bashi amsa.

"Baki habibu ya sake kamawa cikin tsananin mamakin gani wannan murd'ad'd'en ne wai Abbas,ta6d'i"

Habibun ne yasake cigaba da fad'in "Abbas ne yayi irin wannan girman h.............

Kafin yajai ayar magabar tasa sukaji adanno horn daga wajen gidan,da gudu mai gadi yaje ya lek'a sannan yadawo da kansa ciki ya wangale get d'in.

Ahankali motar ta shigo tazo tayi parking gefe dasu kad'an,

Habibu ne yace "yauwa gashinan ma yadawo"

Teemah kam batayi magana ba illah ido data tsurawa motar.

Tsawon mintina biyu da tsayuwar motar sannan taga anbud'e marfin motar,ta 6angaren da suke tsaye,ita da habibun.

"Wow"
Tace azuciyarta tareda kwalalo ido waje tana kallonsa.
Gani tayi yayi kyau da sky blue d'in shaddar dake jikinsa tare da farin glass a idonsa,iyah abinda ta lura dashi kenan ajikinsa amma ba k'aramin kyau yayi mata ba.

Abbas kuwa tun tsayu warsa agurin yake kallon su hannunsa nakan stairy,kallonsu yake musamman ma ita, tare da mamakin tsayuwar uwar me take yi awurin,gashi jikinta sanye da uniform.

Dayake tinted glass ne da motar shiyasa babu wanda ya hangosa,motar daddy ce dayafi amfani da ita,duhun glass d'inne yahana su ganshi ,duk da lura da yayi duk hankalinsu naga motar dayake d'inne da alama duk ak'age suke suka fitowar tasa.

Hakan ne yasa shi fitowa.
Yana fitowa bayan ya maida k'ofar ya rufe, gurinsu yanufah direct,hannu yad'aga sama, tana ganin haka ta rintse iso da k'arfi,dan atunaninta sauk'ar mari zataji,murshi yayi dayaga yanda ta tsorata d'in,sai ji tayi yakam kunnanta irin yanda daddy yamasa,harya fara tafiya sai kuma yajuyo,yah wullo wa Habibu key d'in motar,sannan yacigaba da tafiyah.

Cafe key d'in Habibu yayi sannan yacigaba da kallon bayansu
tunani yake aransa taya akayi wannan yazama Abbas?
Abbas ai bay kyashin yiwa mutane magana,amma wannan sai zafin kai,d'azu da kar6ar abu zaiyi awurina ai yamin sallama,amma ganshi yanzu ko kallon arzik'i ma bansamu ba,ballantana sallama.
acewarsa fah😏

Teemah kuwa
Zafi taji kamar tayi tsallen wahala,harda guntun kwallarta,shikuwa k'in sakinta yayi har se da ya isa d'akinsa yatura k'ofar bayan sun shigo,sake kunnan nata yayi,sannan ya tsaya agabanta yana k'are mata kallo.

K'asa tayi da idanunta tare da turo baki gaba,hannunya d'aya kuma na sama kan kunnan tana shafawa ahankali,
"Mugu" tace acikin ranta

Uniform d'in jikinta yasakr kallo,dayake yamma ne,yasan sai dai na islamiya,.

Gyara tsayuwa yayi yan kallon nata sannan yace
"Anan ake islamiyar ko?

Kanta ta jijjiga batare data d'ago ta kalleshi ba,dan muryarsa har cikin kanta take jinsa,lion voice ne da shi mai ratsa jiki,musamman yanzu da yake maganar da ita ,sosai yanayin muryar tasa ta ratsa ko ina ajikinta.take tsoronsa ya shigeta.

"Toh tsayuwar me kike yi agun kuma?
Yasake jeho mata wata tambayar.

Kasa magana tayi dan wannan tambayar bayyanan niyar amsa take da buk'ata.ita kuma sam bazata iya furta komai ba.

Yawan hawayenta taji yaqaru akan d'an guntun dayake mak'ale tun d'azun,ta ke suka fara sintiri akan fuskarta.

Kallonta yayi da mamaki aransa yace "lallai yarinyar na bazata canja ba"

Juyawa yayi yafara tafiyah sannan yace "jeki"

Tanajin haka ta juya da sauri ta fice daga d'ajin.
Gurin mummy taje ta sameta a babban parlour, fad'awa jikin mummyn tayi tana kuka mai sauti,hankalin mummyn ba k'ara min tashi yayi ba da jin kukan da Teemahn keyi ba.
Dan a zatonta ma tuni Teemahn ta tafi islamiyar.

Dakyar ta samu tayi shiru sannan ta tambaye ta dalilin kukan,
bud'e baki teemah tayi sannan tace

'"bawan nan yayan bane yakama yayita jan kunnena ba,kuma ni babu abinda namasa".

Tsaki mummyn taja kad'an sannan ta kauda kanta daga kallon temmahn

"Yah kyauta ai,bake rashin ji ba"
Shine harda zuwa kisani agaba da irin wannan kukan Teemah"?
Ke kinmanta d'azu ba dariyarsa kika yi tayi ba dan iskanci"?

Baki teemah ta turo gaba jin mummy bata goyi bayan ta ba.

"Toh islamiyar fah?
Mummyn tsake tambayarta.

Teema ta bud'e baki zatayi magana kenan sai idonta ya hango mata mutum atsaye daga bakin k'ofar shigowa parlourn.

Suna had'a idanun da ita sai ya ce
"Assalamu alaikum"

Mummy ce kawai ta amsa masa sallamar tasa.Teemah kam kyautar harara ta bashi,amma sai yayi kamar bai gani ba,hakan yabata damar cigaba ta hararsa har ya iso gefensu ya zauna.

Gaida mummy uayi bayan ya zauna,daganan suka cigaba da hirarsu da mummy babu wanda yasake bi takanta.

Haushi kamar ta sa hannu ta buge sa,abinda ya zaunar da ita ma jin da tayi suna hirar su Hannah ne lil sister d'inshi,da badan hakan bama da tuni tabar inda suke d'in,
Ji tayi hirar tafar dawowa kanta,abin sai yafara bata haushi,wai ita ai ta tsaya canje canjen makaranta ne shiyasa har yanzu bata yi nisa ba ga Hannah nan tana SS2 yanzu,mummy ne tafad'i hakan jin datayi cewa wai Hannah na SS2 daga bakin bakin Abbas.
sannan tak'ara da fad'in ai Daddyn naku ne ma dayake biye ta wlh duk laifinsa nake gani"

Ga dukkan alamu dai wannan abin ya sosa ran mummy,
dayake daman tun sanda sukeyin abin tana tsananin jin haushi,ganin cewa duk makarantar da aka kaita sai tace wai bai mata ba,ba taso,daddy kuwa yabiye mata ya canja mata wani da kyar akasamu ta zauna awannan d'in da ke yanzun,kusan makarantu hud'u tacanja.

Teemah najin haka ta mike ta fice daga d'akin afusace.

Dan tasan anta6o mummy kenan indai akan makarantar tace.

Binta suka yi da kallo dukkansu kowa da abinda ke ransa har ta 6acewa ganinsu.sannan suka ci gaba hirarsu.

Ita kuwa tana shiga d'akin ta fincike hijab d'in da ke kanta tare da rigar sanna ta cire wandon ma duk ta watsar dasu,sai kace sune sukayi mata laifin.

*share pls,nd ur* *comment is needed* 👌🏻 *in ba* *haka ba zan d'au* *hutu* .

*Salmerh* 😍
[10/2, 5:53 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
*Safiyyah Aliyu* *Wakili* . &
*Khadija candy*
I heart u guys tnx 4 ur luv nd suppoart_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

A Mistake increases your experience & experience decreases your mistakes. You learn from your *mistakes* and then others learn from your *success* .👌🏻

🅿 *9*

Zama tayi abakin gadonta daga ita sai pant da bra ranta amatuk'ar 6ace,asama take jin ran nata,"wai wannan shine yah Abbas d'ina kuwa anyah?

"Ayanda mummy take fad'a min ai yah Abbas baya min mugunta,amma shi wannan daga zuwansa gidanmu har ya iyah bayyana nashi salon muguntar,kamar fah yasan abinda nafi tsana kenan arayuwa ta wannan jan kunnan,don ko mummy duk ranar da ta min ma wuni nake bana kulata,shiyasa ma ban fiyah yin abinda nasan zai sa ta min irin hakan ba,sosai nake kiyayewa,Ai kuwa da daddy zan had'a shi ya ramamin abuna.

Murmushi ne ya kwace mata dalilin tunowa datayi da sanda daddy ke jan kunnansa,
"Allah shi kara"

Tace afili.harda cije bakinta irin na muguntan nan.

Daga nan ta ta shi ta nemi kaya tasaka sannan ta fito tasamu Mummy da Baabah Lami a kitchen ko kulasu ba tayi ba,ita adole fishi take yi an mata ba daidai ba,mummy ma ko inda take bata kallah ba,Sai Baabah Lami ce ma tayi mata magana,ita ma maganar tata k'ara 6ata ran Teemahn yayi, dan cemata tayi
"Fatun daddy ya akayi ne naga kinata shan k'anshi haka?

Bata kulata ba sai baki data k'ara turowa,dan ta tsani wannan sunan wai

"Fatu,"

Fuuu......ta juya tafice daga kitchen d'in aikin da batayi ba kenan,daman mummy ce tace matuk'ar tana gida lokacin yin girki yayi toh dole ne tashiga kitchen d'in ayi da itah,shiyasa yanzun ma ta zo,toh amma tun kan ma takama aikin Baabah Lami ta kunnata dayake daman a 90 take,kuma dama tun asali ta tsani "fatun" nan, abakin Baabah Lami kad'ai tafara jinsa
kuma suna yawan shan rigima da baabah Lami d'in akan sunan,kwanaki harta da'n daina fad'ar sunan sai gashi kuma shi yau kuma ta tuno dashi,kawai sai ta fake da hakan k'ara gaba abinta,dama ba son yin girkin takeyi ba tsoron mummy yasa tafito.

Murmushi mummyn tayiwa Baabah Lami tana kallon fuskar ta tace "kin k'ara rura mana wutar kuma ai inaga"

"Aikuwa dai,naga alama"cewar Baabah Lami d'in tana d'an dariyah.
Chapter 8 · 0% Book details