← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 163

Sashe 65

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sa'a ma data 'dan watsa ruwa ajikinta sai taji dama-dama aranar kam basuyi da'de ba sukayi bacvi dan duk sun gama gajiya.

Da safe da Teemah tatashi ji tayi kanta yayi mata nauyi sosai sai data nemi panadol tasha bayan sunyi breakfast kafin tajita 'dan dai dai.

12:00pm nayi abincin rana ya iso musu daga gidan Anty lokacin ma duk basu fara jin yunwa ba kasancewar basu ci break fast 'din da wuri ba gashi Anty tasake lodo musu wani abincin.

Sai da suka yi sallar la'asar kafin suka fito dan tafiya gida, Mahmud da kansa yagama musu komai na tafiya inda sukkansu zasu sau'kane a Abuja zasu kwana agidan Ummah inyaso washe gari sauran 'kawayen Teemah sai su bi mota su wuche gida.

Dazasu tafi Teemah kuwa sosai takeyi ji tayi kamar ta bisu amma badama, haka ta 'karaci kukan ta tayi shiru danko mai lallashi bata samu ba,Mahmud daga wajen gate ya tsaya ya turo aka ce su fito dan haka ko ganin sa bata samu daman yi ba balle har tasamu ban baki daga gareshi.

Bai dawo gidan ba sai 'karde tara na dare 9:00pm wanda alokacin idanun Teemah tsuru tsuru duk tsoro yagama cika mata zuciyata na rashin jin motsin kowa acikin gidan sai ta samu guri 'daya ta takure akan kujera tunda suka tafi bata tashi awurin ba ko sallah bata je tayi ba dan tsoro, motsin kirki intayi jitaje tamkar za' a cafkota ne, anan maghrib da isha duk suka sameta batayi su ba, kuka kuwa tayi shi har sai da idanun ta suka daina fitar da ruwa ta komayi azuciyarta.

Tana zaune agurin taji an mata knocking tare da sallama duk alokaci 'daya, sanin muryarsa ne yasa tatashi da sauri taje tabu'de masa 'kofar dan dama a'kage take taji motsi sai kuwa taji yazo ai ba 6ata lokaci.

Mahmud shi ka'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba.

*Keep following me da sauran chakwakiya fa agaba.👌🏻.*

👎🏻
*Kunsan wani abu?.... yau an 6atan raina ka'dan amma bakomai !*

~Tambayace~ ❓🤔

*|-* Shin mu ba musulmai bane kam?
*||_* Ko munfi 'karfin jarabtar Ubangiji ne?
*|||*_Ko kuwa akwai wanda ya isa yace Allah be ta6a jarabtarsa da wani abu bane wanda yakasance abun 'ki agare shi?

_Ni aganina bakomai_ _bane dan hakan ya faru ga bawa tunda daga_ _daga ne,_ _kuma kafin kai million dubunka sunyi experiancing makamancinsa_ _sannan abayanka ma fiye da dubu na jiran jarrabawa daga mahallici_ . _Sai de fatan Allah yasa kyakykyawa ce kuma yabamu_ _ikon amsarta da_ _hannu bibbiyu_ .

👎🏻
_So wanda suke ganin kamar *SALMERH* tayi babban laifi ko kuma ta canja_ _salon labarinta data_ _ha'da auren_ _Teemah da Mahmud harma suke ganin kamar labarin yabar kan hanya ko kuma suke_ _jin daga yanzu labarin yabar kansu ma'ana sun daina bibiyarshi_ *pls* ' _kofa abu'de_ _take ba' ayi muku dole ba, dan labarin CAPTAIN ahaka yazo kuma_ _babu canji ahaka zamu_ _tafi wa'dan da suka fahimta ne ka'dai zasu gane manufar_ _labarin da kuma abinda yake nufi._

_Jinjina ga wa'dan da suka fahimceni suka kuma 'daura 'damarar bin bayana domin jin 'karshen labarin *CAPTAIN ABBAS* ina godiya sosai ina kuma fatan zaku cigaba da bibiyata dan jin 'karshen labarin.........Much luv mutane nah soyayyata daku ta musamman ce Allah yabar 'kauna._

_Masu tausayin Abbas kuma kuyi ha'kuri ni kaina yabani tausayi sai dai kuma kunsan_ _wani abu.......... yace kwananan zai mana new catch muyi ha'kuri inajin_ _sunanta...........ohh so sorry namanta ashe yace kar na fa'da yanzu shida kansa zai zo ya sanar damu.........._

Wattpadians,
Facebook followers
and most af all Masoyan CAPTAIN na whattsapp jinjinar bangirma sosai nake yabawa da kokarinku......kuma ina yinku iriin trillions 'dinnan.❤

*ACIGABA DA GASHI* ..........🤞🏻

_Comment_
_Vote_
_Share_👌🏻

*Salmerhn ku ce*😍
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

⚠ ~NOT EDITED~

_In dedication_
_2 my Famliy_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_Nobody wants to hear this but it's true that sometimes the person you want_ _most is the person you are best_ _without._

🅿 *54*

Mahmud shika'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba, fuskarsa ba yabo ba fallasa lokacin daya ganta ,be yi mata magana ba kawai yasa kansa zuwa ciki itama sai ta bishi abaya ahankali bayan ta tura 'kofar.

Babbar rigarsa yacire ya ajiye sannan yakoma ya kukkule 'kofofin gidam gaba 'daya ya daqo yasameta zaune akan kujera.

Umartan ta yayi da tayi alwala taje tayi ta dawo sai ya mata nuni da dadduma ma'ana ita yake jira.

Ahankali tace masa " _banyi maghrib ba_" dan ita zaton ta sallar isha'i zasuyi.

Kallon ta yayi da mamaki ya ce " _meyasa bakiyi ba tun 'dazun"_?

" _Ni tsoro nakeji Yayah tun 'dazu fah nika'dai ce agidan kuma su Hannah tafiyar su sukayi suka barni"._! Cikin shagwa6a tayi maganar tamkar zatayi kuka.

Shi kuwa sai ya samu ya zauna yace mata ta hanzarta tayi toh dan lokaci na tafiya yace kuma kiyi harda isha'i ma.

Sai data jero sallolinta duka biyu sannan ya tshi ya jasu suka yi wata raka'ah biyu ,sosai yajero musu addu'o'i kusan na mintina ashirin sannan suka shafah zuwa lokacin kuwa Teemah tayi hamma yafi sau a 'kirga idanunta duk sunyi luhu-luhu.

Cemata yayi taje kitchen ta 'dauko plate da cups takawo.

Batayi musu ba kuwa ta tashi taje har wani jiri jiri takeji tsabar baccin daya ci idanunta, babu ma inda tasani acikin gidan ita dan tunda tashigo gidan bata je ko ina ba su Hannah keta shige da ficen su tana kallonsu batare data nemi sanin ko'ina agidan ba.

Ko yanzun ma da ta tashin bata da'de ba ta dawo ta e masa ita bataga kitchen 'din ba. Sai kawai ya 'mi'ke yakama hanyar zuwa itama sai ta bishi abaya, dakamsa yashiga ya 'dauko plate 'din suka dawo parlourn.

Yayi-yayi da ita taci abinci ta'ki ci sai kawai tayi kwanciyarta akan kujerar dake gefensa tare da yin pillow da 'dan 'karamin throw pillows 'din dake kan kujerun, take sai bacci ya 'dauke ta awurin bada jimawa ba, shima be wani ci abincin ba dan shi'din ma ba ra'ayin cin abincin yake ba dama dan ita ne kuma ta'ki ci dan haka sai ya ture daga gabansa.

'Debe tarkacen yayi gaba 'daya ya mai da su kitchen sannan ya dawo ya tsaya akanta kamar ya tasheta dan ta koma 'daki amma sai ya barta ganin yanda ta saki ranta take baccin cikin kwanciyar hankali ga dukkan alamu akwana kin bata samu wani baccin kirki ba. Sai de duk da haka yana ganin kamar kayan dake jikintan zasu mata nauyi, anyways bari na barta in sun dameta ai dakanta ma zata tashi ta nemi rabuwa dasu.

Komawa bedroom yayi yawo shirin baccinsa sannan ya 'dauko pillow yazo ya jefa akan carpet for d first time arayuwarsa ya kwanta bacci ba akan gado ba.

Duk da sanyin da tiles 'din ke badawa amma haka ya daure ya kwanta awurin dan kawai ya kasance kusa da ita, domin cika amanar aya kar6a baya so hakkinta yafara hawa kanshi tun daga ranar farkon auren su.

Da zai iya kwantawa akan kujerar shima amma kuma 2seater yayi masa ka'dan bazaiji da'din kwanciya akai ba, Teemah kuwa baccin ta ya riga yayi nisa akan 3seatern shiyasa kawai ya yanke shawarar kwanciya a'kasan.

'Karfe biyu da mintina sha takwas 2:18am tafarka garin yin juyi sai idanunta ya sau'ka akansa taga yanda yatakuru ga dukkan alamu sanyi sosai yakeji, sai data ta tashi ta zauna ta fahimci manufar kwanciyarsu aparlourn tunowa datayi cewa tariga shi yin bacci dan ta barshi ne yana 'ko'karin cin abinci.

Sake kallonsa tayi sai taji tausayinsa ya kamata "Allah sarki Yah Mahmud" tafa'di aranta.

'Dakin da duhu amma ta daure ranta ta tashi dayake ma akwai hasken farin wata kuma ya 'dan ratso ka'dan ta jikin windown glass 'din dake parlourn dan haka batayi wahalar gane mashigar bedroom ba, sai data shiga kafin ta kunna bulb 'din bedroom 'din sannan haske ya gauraye ko'ina a'dakin, abin rufa ta 'dauko ta dawo ta lullu6a masa ahankali sannan ta koma ta sake yin kwanciyarta ko kayan jikinta ma bata tuna cirewa ba haka ta dawo ta kwanta.

Kusan 22mins ta 'dauka idanunta biyu kafin wani baccin yakuma 'daukanta.

Washe gari Mahmud ya rigata tashi, koda ya tashin kuwa mamaki yayi daya ga jikinsa lullu6e da abin rufa domin a iya saninsa shi be 'dauko wani abin rufa ba jiyan amma sai gashi ya tashi yagansa dashi, kallon inda take yayi sai yaga tana ta baccin ta kamar dae jiyan be ga wani canji atattare da ita ba.

Ture abin ruafar yayi ya tashi yaje yayo alwala dan gabatar da sallar asuba sai da ya idar da nashi salkahn yayi azkar kafin yatashe ta dan itama tayi tata sallar.

Koda ta idar sai ta hau gado tasake bu'de wani sabon babin bacci.

'Karfe shida da kwata 6:15am Mahmud ya shiga bedrrom 'din da kayan da yayi amfani dasu wurin bacci sai yaganta na'de agado, dama yayi tunanin haka tun daya ga shiru bata fito ba kuma tun 'dazu baiji motsin ta ba.

Ajiye su yayi sannan yashiga yayo wanka ya dawo ya shirya cikin 'kananun kaya ya fita parlour ya zauana tare da bu'de system 'din sa.

Teemah kuwa bata tashi ba sai takwas saura 7:46am ta tashi wanda ba 'karamin baccin safen datayin taji ba dan in har batayi baccin ba da wannan farkawan daren datayin ba'karamin ciwon kai zai sata ba kuma bacci zai dameta darana sosai amma yanzun kam tasan kozai dameta da sau'ki.

Sai da tayi wanka ta shirya cikin atamparta suoer holland mai kyaun gaske 'dinkin dai dai jikinta, powder kawai ta shafa afuskarta sai kwalli data saka acikin idanunta ta, simple'dauri tayiwa kanta amma duk da haka sai gata tayi fess da ita, fitowa tayi parloun tasame shi zaune yana aikin duba system 'dinsa.

Sai data zauna agefensa kafin tace _" ina kwana Yayah"_!
Chapter 65 · 0% Book details