Sashe 96
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sau tari Anty na addu'ar Allah yasa Fateemah nada cikin Mahmud saboda zata so ace tasamu jika daga ita, amma lokaci guda take kauda wannan tunanin idan ta tuno kato6arar da Munnira ta aikata, musu sai dai akullun bata cire rai idan son jikan yacika mata zuciya sai kuma taji kamar batun Munniran 'karyane babu wani barrier da ta yi atsakaninsu ,alokacinn ne take 'karyata Munnira da kuma aikin bokayen sai taji kamar tunanin ta gaskiya ne, Fateemah nada cikin Mahmud ajikinta.
Har kwatanta ranar da za'a ce maganar ta tabbata takeyi tana misalta irin farin cikin da zataji, takance da kuwa anga zallar so dazata nunawa jikan nata, bata jin akwai abinda zata so fiye dashi aduk fa'din rayuwarta kuwa.
Lokacin da sukayi sallama da Anty Fateemah ma shiru tayi tana tunani, abin na damun ta sosai, yanda akabi aka tsare ta agida kamar munafuka, turare wannan Ummah hanata amfani tayi da shi, duk kuwa da yanda Teemah ke da jarabar turare amma hanata akayi amfani da masu 'karfi, sai da taga Teemah na shirin yi mata kuka kafin da 'kyar ta barta take amfani da wani me sanyin 'kamshi sam bashida 'karfi, wani lokaci idan tasaka shi ajikinta mintina biyar bayayi ajikinta sai taji babu 'kamshin duk ya gushe, sannan bata kwalliya kullum tana nan sai fama da waya a'daki.
Islamiya wannan idan suka ce zasuje tare da Hannah Ummah hanata takeyi, akwai ranar dama ta san'di jiki suka fita ta 'kofar kitchen har suna murna amma cikin rashin sa'a sai ga Yayah agabansu take kuwa ya maida ta gida yace maza ta koma babu inda zata je.
Ranar kam tasha kuka, wani lokaci gani take kamar ita ka'dai aka tsana agidan shiyasa akeyi mata haka, yayinda kuma taga ake riritata tare da girmama bu'katunta fiye da Hannah sai kuma ta 'karyata zancenta na farko, sam tarasa dalilin hakan gaba 'daya ta gaji.
Dai-dai lokacin da tacika sati uku cif da zuwa gidan adai-dai lokacin Yayah Abbas ya koma bakin aikinsa wanda yayi dai-dai da wata biyu da kwana uku da rasuwar Mahmud.
Zuwa lokacin kam Teemah ta saduda ta daina damuwa, ri'ke 'kuncinta kawai tayi azuciya.
Abbas 'din ma dayake bazama sosai yayi agidan ba, ita dai tasan yaje Gombe inda daganan taji labari abakin Ummah cewa ya wuche Dubai daga can.
So rashin zaman nasa yasa bata fiya ganinsa ba, amma duk da haka 'ko'kari sosai ko da bayanan amma yana kula dasu yana yawan turawa Hannah ku'di yace suyi amfani dashi, wai shi duk a'ko'karinsa naganain ya kula da amanar marigayi da ya kar6a, Hannah kam murna ta ke yi aduk lokacin da taga alert awayan ta takance " _albarkacin ki fah nake ci Teemah, da Yayah baya son bani ku'di ko na tambaya baya bani sai yaji 'kwa'kwkwaran dalili kafin nan yabani, kuma Daddy ma baya bani idan na tambaya sai ya wani ce in tambayi_ _Yayah na yabani kuma fah yasan dramar da muke sha dashi, amma duk da haka gurinsa yake turani, shi wai adole_ _be so_ _insaba da kashemanyan ku'da'de sai kuma_ _yanzu naga ba'a tambaya bama bayarwa yake yi_ "
Ta6e baki Teemah kwaia tayi dan ita bata da matsala da wannan.
Abinda ke damunta ma ya isheta, dan haushi ranar kam har kuka tayi musamman da ta tuno da Mummy, da ance aure toh yanzu kuma fah tunda babu auren memiye kuma dalilin tsareta,
bata ja tsawon lokaci ba ta bawa kanta ha'kuri, wani lokaci harda laifin mummy take gani, tasan ai itace ta shareta da bata manta da ita ba da duk haka be faru ba.
Daddy kam ba'a ma maganarsa dan shi samun layinsa bata fiye yi ba dayake yana yawan tafiye tafiye shiyasa bashi da takamammiyar number da zata sameshi akai
.
Ko bayan tafiyar Abbas ma bata damu ba dan zuwa yanzun babu ba'konta cikin duk rayuwarta komai tasaba dashi, zaman gida da sauransu, ita kanta ma yanzu tana jin da'din rayuwarta mafi yawan damuwarta ya kau, Anty ma har yanzu tana kano bata koma Lagos ba kuma cikin sabo da sha 'kuwarsu babu abinda ya ragu sai ma 'karuwa.
Ahaka da da'di ba da'di har Mahmud yacika wata hu'du da rasuwa, inda duk mutanen zuwa yanzu alhinin rashin sa ya ragu azu'katansu addu'a kawai suke binsa dashi.
Alhaji Muhammad kuma sosai yagaji da zaman Anty agida koda yayi mata magana kuwa sai tace Abbah ne yace tazo gida, tafa'di hakane kuma dan bata so mahaifin nata yaringa damunta da batun komawa.
Shikuwa da be san manufarta ba suna rabuwa da ita sai ya tuntu6i Abbah awaya yace masa " _Yusuf wai meke faruwane, naga tsawon wata biyu kenan harda_ _kwanaki Maryam nagida, bamu ta6a tattauna dalilin zaman ba, naga_ _kuma ko ka 'kirani baka kawo maganar ince dai lafiya ko?_
Abbah cewa
" _Lafiya 'kalau Alhaji ina nan ma zuwa kwanan nan insha Allahu nima_ "
" _Toh Allah ya kawoka lafiya, gara de ayi abinda ya dace ina ganin zai fi_ _ko_ "
Cewar Alhaji Muhammad yana me shafa gemunsa.
Abbah sai ya tabbatar masa da cewa
" _insha Allah komai zai tafi dai dai bisa dacewa_ "
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* 😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Crushes are more beautiful than affairs because there is no_ _responsibility, no worry_ , _no commitment. Just look at your crush and smile like an_ _idiot_.
🅿 *71*
Abbas kam yanzu girma ya 'karu, ta'kama da izzah sai abinda yayi gaba, Daddynsa ne ka'dai yake 'dan kashe masa gwiwa aduk lokacin da yayi masa zancen aure walau awaya ne ko kuma azahiri, sam bayason maganar auren nan amma yarasa yanda ze 6ullo masa, babban damuwarsa kenan ayanzu shiyasa ya tsani maganar ma kwata-kwata.
*****
Kamar yanda Abbah ya yiwa Alhaji Muhammad al'kawari hakan ne ya faru domin acikin satin ranar wata laraba ya sau'ka garin Kano, Alhaji Muhammad yaji da'din zuwansa dan kuwa ko ba komai yana ganin yanzu ne ze san matsayin da 'yarsa ta take awurin Abbah, dan haka bayan gaishe-gaishe har Abbahn ya huta ma sannan Alhaji Muhammad ya nemi jin salin abinda ke faruwa daga bakin sa, Abbah kam be sanar da shi komai ba yace masa kawai tace ne zata zo ta duba iyayenta shi kuma yace ta bashi lokaci in yayi settling sai suzo tare, ganin kamar lokacin tmya'ki samuwa ne shi yasa ta taho, batun kuma cewa shine yace ta zo 'din bahaka bane, yace wata'kila bata ahirya komawa yanzu bane shiyasa ta fa'di.
Alhaji Muhammad kam shiru yayi masa amma bawai dan ya gamsu ba, duba da yayi da cewar tun tsawon shekarun auren su da ita hakan be ta6a faruwa ba, toh me yasa sai yanzun kuma, yana kyautata zaton matsala suka samu amma Abbah yake 6oye masa, Alhaji be tsawaita tunani ba shima ya basar da zancen dan yasan basu ta6a samun matsala har abin yazo gabansa ba sai de lokacin auren marigayi Mahmud da ya kawo 'karar ta, wannan ma Abbah ya kawo 'karan ne dan kawo gyara wa lamarin, kafin da bayan hakan kuwa be ta6a sanin ya yanayin zamansu ba, yanzu kuwa da babu ran Mahmud be san takamam man menene matsalar su ba kuma ya san de baza'a rasa ba dole akwai wani abu, kawai de Yusuf na 6oye masa ne shikuwa ba haka yaso ba, yaso yaji abinda ke faruwa domin ya 'dan gyara al'amarin idan Allah ya bashi dama, dan shi da kanshi wani lokacin Maryam na bashi tsoro duk kuwa dayake 'yar cikin sa ne amma tun lokacin dayaji asalin 6oyayyen halinta gaba 'daya ya tsinke da lamarinta.
Alhaji aikawa yayi akayi masa 'kiran Anty (Maryam), koda tazo kuwa mamaki tayi da ganin Abbah ita kam, domin bata ta6a zaton zuwansa adai-dai wannan lokacin ba.
Sai ma taga ya 'dan murmure yanzun ba kamar da ba, fuskarsa se wani 6oyayyan annuri ke haskawa.
Alhaji Muhammad ne ya nemi jin abinda ya faru daga bakinta karo.na biyu, sanin da Anty tayi cewa yariga yasan komai yasa bata bata 6oye masa ba ta kwashe duk abinda ta aikata da dalilin da Abban Mahmud ke fushi da ita duk ta sanar dashi.
Alhaji Muhammad beyi mamaki ba dan yariga yaji duk abubuwan da yafaru 'din tun a Lagos sai de be san cewa hakan.ne ya kawo sa6ani tsakanin su ba, duk da kuwa cewa yasan ba kowa ne ne zai juri faruwar hakan ba, ko shi kanshi idan hakan yafaru cikin iyalinsa yasan da 'kyar ya iya sake zama da me shi shiyasa sam be ga laifin Abbah ba ko ka'dan sai ma ya jinjina masa da be aikata fiye da wannan ba, sake tambayar Abbah yayi inda ya tambayan ne kawai dan tabbatar wa.
Nasiha dukkan su ya ha'da su yayi musu game da zamanta kewar su, sosai yaja hankalinsu game da tsoron Allah cikin al'amuransu, sai da ya gama nasihar kafin ya baiwa Abbah dama yace yana da ikon za6an duk abinda yaga yayi masa wanda ya dace dashi, yace " _karka damu dani Yusuf, ni tamkar mahaifinka nake bazan takuraka akan komai ba, sannan ina so_ _kayiwa kanka adalci karka dube ni kowani abu daya shafeni, Maryam matar kace,_ _kuma_ _kai ke da ikon za6an sake zama da ita ko kuma akasin haka, duk ra'ayinka_ _ne_ _Yusuf_ ,
_bazan ta6a tilas ta ka dan ka zauna da ita ba dan tana matsayin 'yah agareni, wallahi_ _Yusuf da ace ni ni ke da iko da kai da bazan ta6a barinka kasake zama da Maryam a matsayin_ _mata ba, kuma ko yanzun ma kana da damar za6a ni nawa_ _shawara ne koma me ka aikata ni.kam.ina maraba dashi Yusuf domin kuwa nasan kai 'din'dan halak ne me matu'kar ha'kuri sosai wanda ina zaton da iznin Allah rayuwarka bazata ta6a birkicewa ba Insha Allahu_ ".