← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 163

Sashe 126

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi tayi ta zauna tare da dafa Teemah tace " _Me yafaru ne naga har yanzu idanun ki biyu, bakya jin da'di ne_ ?

Kai Teemah ta jijjiga mata tare da fa'din " _bakomai Hannah ki kwanta abinki nima yanzu zan kwanta_ ".

Tana gama maganar sai ta juya ta kwanta ita bata so Hannah tasan matsalar data ke ciki.

Hannah kam da kallo ta bita ganin 'karfi da yaji take 'ko'karin 6oye damuwar ta bayan fuska da yanayin ta sun riga sun bayyana komai.

Teemah kam baya ta juya mata da tunanin zata kwanta itama, yayin da Hannah ta bi bayan nata da kallo tsawon da 'ki'ku biyar tausayi Teemahn take bata ita musamman daya kasance auren ta biyu amma har yanzu batayi dace da samun farin cikin daya kama ta ba duk da yanzun tana mata kwa'dayin samun farin ciki da Yayahn amma tana ga hakan bazai yiwu ba dole sai ta yi nata yun'kurin kafinnan, dan duk wacce Allah ya jarabce ta da auren miji irin Yayah Abbas toh dole sai ha'kurin ta yazarce nakowa sai tayi nin kin wanda kowacce mace keyi agidan mijin ta sannan ta'kara da du'a'i saboda neman agajin mahalicci.

Duk mijin da ze nuna maka abu bai damesa ba ya nuna maka bashida matsala da komai bacin ba hakan bane aransa toh kuwa dole mace sai ta tsaya tsayin daka wurin ganin ta sai ta hankalin sa wuri guda, bako wani namiji bane wanda soyayya ke sashi bin duk abinda kike so, wanin shi ba damuwar sa bane koda kuwa yana yi miki irin son da ya zarce nakowa ne a duniyan nan.

A hankali kamar ba zatayi maganar ba tace da Teemah " _matsalar Yayah ne ke damun ki ko_ ?

Zaro idanu Teemah tayi tana daga kwancen sannan ta juya a hankali ta kalli Hannah bata so Hannah tasan abinda ke faruwa tsakanin su dan haka sai ta jijjiga wa Hannah kai tare da fa'din
" _ni fa bance miki haka ba Hannah plz mukwan ta dare yayi fah!_

Kwafah Hannah tayi ganin yanda Teemah keso ta bin ne ta abaibai bayan kowa yagan ta a wannan yanayin yasan tana tarexda damuwa, ita kanta Hannah bataso yin shidshigi wa lamarinsu ba musamman ma daya kasance mijin Teemah 'din wanta uwa 'daya amma wani lokacin idan abu ya so barin hanyar da ta dace inkana da dama taro shi zai yi matu'kar amfani ko dan saboda gaba ma.
A hankali ta kuma fa'din
" _Karki maida ni shashasha mana Teemah, kin 'dauka bansan meke tafiya bane har yanzu_ ?
_na jima da fahimtar kina tare da damuwa a gidan nan kawai 6oye_ _min kike yi shiyasa nima na 'kyale ki, kuma nasan ba zai wuce matsalar Yayah ba hakane_ ?.

"Ah ah"
Teemah tace da sauri.
Hannah kuwa cewa tayi " _Allah idan baki gayamin ba ina fita gobe Ummah zan samu in fa'dawa_ _nasan zata sanar da daddy kamar yanda nasan cewa Daddy ba zai yi shiru hakanan ba dole sai ya tambayi Yayah_ _kinga ai lokacin dole ki bu'di baki kiyi magana ko_ ?

Teemah da hanzari ta kamo hannun Hannah tace " _dan Allah Hannah kiyi ha'kuri karki fa'dawa Ummah, Hannah yaushe_ _ma akayi auren da har irin haka zai fara faruwa ki taimake ni karki fa'da ma kowa plz_ "!

Goshi Hannah ta ha'de irin boss din nan tace " _sanar dani toh if dont want me to tell Ummah about it_ "

Baki Teemah ta tura gaba " _tace ai nagaya miki bakomai tun 'da zu_ "

"Kin tabbatar?
Hannah ta tambaye ta.

Kai ta daga kamar yarinya 'karama.

Hannah kuwa tace " shikenan toh, ni bazan musa ki ba amma kisani babu abinda zai hanani sanar da Ummah gobe sai dai in ban tashi cikin rayayyu ba"!

Tana maganar ta juya ta kwanta.

Teemah ri'ko ta tayi tace " _Haba Hannah nice fah_ !

Da jin haushi Hannah tace " _ai nima nice!!_

Shiru Teemah Teemah tayi na 'dan lokaci sannan bayan har Hannah ta cire rai da cewa zatayi nagana ma sai taji a hankali tace
" _Hannah laifi ne dan ina yawan tunanin Yayah?Inajin kewar sa sosai Hannah kuma gashi kinga baya ko 'kirana nima_ _kuma tsoron 'kiran sa nakeji dan bansan me zance da shi ba_ "

Hannah muguwa duk da haushin dataji 'dazu amma hakan be hana ta darawa ba dataji abinda Teemah tafa'da.

Teemah kam tsayawa tayi kallon ta idanun ta na tare hawaye dan bata san dalilin dariyar ba, HANNAH sosai ta dara son ranta ganin Teemah na zubo da hawaye ne yasa ta 'dan tsagai ta da dariyar tace " _ashe lokacin da sauri zai zo haka_ ? _Kin manta nace miki naki son idan kika fara sai kin fini amma kika 'ki yadda gashi nan tun ba'aje ko'ina ba abu ya bayyana kansa_ , _yanzu kam ai kin yadda cewa banyi 'karya ba ko_ ?

Teemah shiru tayi mata sai ma tafara 'ko'karin kwanciya dan taga alama abin dariya tazama harta regretting fa'da matan da tayi ji take badan ance magana zarar bunu bace da babu abinda sai hanata mai da maganar ta cikin ta ta rike damuwar ta ita ka'dai.

Hannah naganin ta kwanta sai ta ha'diye dariyar tata tace " _yi ha'kuri matar Yayah tashi muyi magana plz na daina dariyar_ "

Teemah 'kin kulata tayi sai Hannah ta dawo ta gabanta ta fuskanceta tare da fa'din " _I'm serious Allah tashi kiji, nayi al'kawarin bazan sake yimiki dariya ba yanzu"_

A hankali Teemah ta yun 'kura ta tashi ta zauna.
Hannah ma zamanta ta gyara da kyau sannan tace "Kin san Allah ko tun ranar da naga Yayah yayi 'kirana awaya nayi tunanin ko dai be same ki bane shiyasa amma daga baya sai naga ya zage da 'kirana ba gaira ba 'dan dalili sai na fahimci akwai dalilin hakan dan ba haka muka saba da shi ba, Yayah be fiya 'kiran layin na ba sai dai in akwai wani dalili, na fahimci bakwa waya ne kuma saboda ban ta6a ganin kunyi ba, nasan halin Yayah da zuciya akan abu koda kuwa yana son abin zai iya basarwa idan ransa ya 6aci wannan kadan ne cikin halayyar sa.
Ni kaina banso kika 'ki binsa ba tunda yanason hakan bazai ta6a cutar dake ba, wallahi Teemah Yayah na matu'kar son ki tun ba yau ba na fahimci hakan, ya na 'kaunar ki da dukkan zuciyar sa irin son da be ta6a yiwa wata 'ya mace irin sa ba a dunitan nan bama na tunanin ko agaba akwai wacce zata taro ki a zuciyar sa bansani ba ko in wani ikon Allahn ya sanya, Yayah na miki son da kowacce mace take burin mijin ta yayi mata irin wannan son, Teemah ki lura mana yanda kike yiwa Yayah abu son ranki wanda na tabbata ba ze 'dau hakan daga wurin kowa ba koda kuwa nice danake autar 'kanwar sa Yayah ba ze sarara min ba shiyasa ma kika ga bana farawa, sau tari ina mamakin yanda kuke rayuwar ku dashi kamar abokan gaba wani lokaci kuma na kanji kuna birge ni sosai, a hankali sai na fahimci 6oyayyan soyayyar dake tsakanin ku wanda bakowa ne yasan da shi ba, daga zuciyoyin ku sai de ko Mummy"!

Da sauri Teemah ta 'dan bu'de idon ta akan Hannah da Mamaki, sai Hannah ta jinjina kanta tace
" _Yes... Mummy ce ka'dai tasani, lokacin auren ku ta sanar dani yanda tayi farin ciki da ha'din auren_ _naku take ce min ta jima da fahimtar son Yayah Abbas dake 6oye a zuciyar_ _ki, wanda tana ganin kamar ke kanki ma baki san dashi ba, tace damuwar ta Abbas_ _ne bata sani ba ko zai kar6i auren ko ah h, nice nan take_ _na bata tabbacin Yayah baze 'ki ba danshi ma yana tsananin sonki_ _fiye da zaton mutun_ .
_Bazan 6oye miki ba Teemah duk da nasan kin fini sanin menene aure tunda kinyi shi har sau_ _biyu, amma har ga Allah kina sakaci da kulawa da mijin ki, lokuta da dama_ _nakan ji wani iri idan naga kina nuna halin ko in kula da shi, mijinki ne fah, naki ne_ _Teemah me yasa zaki 'ki binsa bayan kinsan yana da bu'katar hakan zaman me zakiyi_ _anan 'din tunda wanda kike zama domin sa baya nan, ba 'da ba ba komai_ _ba me yasa kika za6i raba muhalli dashi?_
_idan baki kila dashi yanzu ba yaushe kike son rayuwar auren ki tayi saiti_ ? _kin fi son sai ranar da wata ta shigo tsakanin ku ko kuma yaushe_ _Teemah_ ?
_Ki duba fah duk da ransa a 6ace amma bai fasa 'kirana dan yaji lafiyarki ba_ _ke da kanki ki duba wannan lamarin dan Allah_ "

A hankali Teemah tace
" _Ni kaina Hannah naga kuskure na kuma Allah yayah fushi yake yi dani ban san yanda zanyi ba banson fushin san_ _koka'dan_ "

Hannah cewa tayi
" _Nima banaso Teemah, dukkan ku 'yan uwa nane kuma mafi soyuwa abin 'kaunata, lokacin danaji auren ku bazan iya misalta miki_ _irin farin cikin dana shiga ba, inson ku sosai bazan ta6a son 'daya na bar 'daya ba har abada kamar yanda bazan so ganin ba'kin_ _cikin 'dayan ku ba ballan tana na dukkan ku biyu_ "
_Wannan laifin kinsan naki ne ko_ ?

Kai Teemah ta 'daga mata, sai ta cigaba da fa'din " _so kinga ke ya kamata ki gyara laifin, nasan Yayah ma be kyauta ba daya share ki amma kema da naki laifin me yasa da kika ga baya ko 'kiran_ ki _baki 'kira shi ba......._
_kinsan wani abu ne matar Yayah_ ?
Chapter 126 · 0% Book details