← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 163

Sashe 67

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin sa ya yanke ne lokacin daya ji numfashin ta awajen kunnansa, ga dukkan alamu tayi nisa acikin yanayin da take 'din, dan ko daya 'dan matsar dakansa ma sake biyo shi tayi da nata kan da azama.

Afirgice ya mi'ke da 'karfinsa sanadiyyar wani sabon salon daya ji take 'ko'karin yi masa.

Dafe kai yayi tare da zuba mata idanu yaga yadda hannunta ke yawo akan gadon a inda ya 'daga jikinsa ga dukkan alamu shi take lalu6awa
" _Fateemah!,_
" _Fateemah_ !!........
_Tashi kiji...._ _tashi_ _ki gaya min_ _meya faru, meke damunki?_ Yayi maganar yana me kusanta kansa da kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi da kyau koda kuwa bancin me take yi dole zata jishi.

Amma ga mamakinsa kota nuna alamun taji anyi magana da ita ma bata yi ba balle yasa ran zata bi umarnin daya bata, ganin haka sai yasa hannayensa ya tada ta zaune, tana tashi ta zauna 'din sai ta yi luuu tadawo kan jikinsa ta kwantar da kanta akan kafa'dar sa tare sar'ko shi izuwa jikinta da hannayenta.

Kai ya dafe duk abin Fateeman yabi ya 'daure masa kai gaba 'daya yama rasa me ze yi mata, jiyake tamkar ba Fateema bace kamar ba Fateemansa ba, tamkar an canja masa ita haka yake gani, asanin da yayiwa Fateemah ma sam bata da gigin bacci balle yace ko mafarki ne ko kuma gigin baccin ne yasata yin hakan.

Shima kawai sai yasa nasa hannun ya rungume ta izuwa jikinsa ya jinginu da jikin fuskar gadon yana shafa bayan ta ahankali, ahaka bacci ya 'dauke su gaba 'daya har zuwa asubah.

Da asubah da ya tashi sai ya gyara mata kwanciya ahankali yanda baze farkar da ita ba, sannan yaje yayo alwala ya tada sallah, bayan ya idar addu'o'i yadinga jerowa yana ro'kon Allah ya sanya zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu, Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikin wannan auren yakuma kawar musu da Sharrin dake 'kunshe dashi, kuma ya shirya masa mahaifiyarsa shiriya na gaskiya.

Sai daya idar da sallahn kafin yaje yatashe ta dan itama tayi nata sallahn, yana tashinta kuwa ta tashi ta zauna tare da rero salati tana kallonsa.

Kanta taji yayi mata nauyi sosai sai tasa hannu ta dafe kan tayi shiru tare da sunkuyar da kanta.
_"Ya dai"_
Ya tambayeta bayan ya zauna daga gefenta.
_" kaina ciwo Yayah_"!

" _Ohh very sorry, ki watsa_ _ruwa kafin kiyi alwalar zakiji sassauci bi'iznillah_ _inyaso ingari yawaye sai mu je_ _clinic abaki magani_ _ko"?_

Kai ta 'daga masa alamar "toh".

Sai yasa hannunsa ya tayata ta mi'ke tsayen ya rakata har bakin toilet sannan yace mata ta shiga.

Nuni tayi masa da towel sai ya 'dauko ya mi'ko mata da sauri dan yanda yaga idanunta yanda take bu'de su ma da 'kyar sosai yaji tausayinta ya kamashi.

8:00am ya kaita wani 'karamin private hospital aka dubata aka rubuta musu magani kawai suka taho gida, amota ya ce ta jira shi yashiga wani babban chemist dake kan hanya ya sissiyo magungunan da aka rubuta musun sannan yazo suka koma gida.

Ranar Mahmud beje ko'ina ba ya zauna ya dinga kula da ita, sosai yake bata kulawa ita har yana bata dariya ma dan ta da'de da sanar dashi cewa ciwon kan ya daina amma sam ya 'ki yadda motsi ka'dan intayi sai ya tambayeta ko menene.

Ranar da kansa ya tafasa musu indomie da rana suka ci da dare kuwa yace ta shirya suje eatry suci acan dan ba ze iya girkin komai ba yanzu duk ma be fi exercise ba, Teemah tace yaje yaci ya dawo ita kam bata jin cin komai yanzu, Mahmud kuwa yace dole sai taje, tayi-tayi dashi ya'ki barin ta har tace toh yaje in yaso yazo mata da nata still ya'ki amincewa saima ya 'kara da fa'din wai idan ya fita bazai dawo gidan ba sai 11:pm yace in dai zata iya zama agidan ita 'daya toh shikenan sai yatafi karkuma ta kuskura tayi masa complain idan yadawo, dagangan Mahmud yafa'di haka dan yasanta gwanar tsoro ce ita, aikuwa yaci nasara dan yana fa'din haka tami'ke taje ta 'dauko zunbulelen hijab tasa akan kayan dake jikinta suka fita tare.

Mahmud nata cin abincinsa yayinda Teemah tari'ke spoon 'ahannunta tana ta juyawa tare da kallon abincin, murmushine ya kubce mata sai ta 'dago kai ta kalli Mahmud sai kuwa suka ha'da idanu " ' _yanmatan Daddy ya_ _dai_ yace mata.

Sai itama tace bakomai.

" Yah Abbas na tuna wallahi, shifa sam be son cin abincin waje ko yunwa zata masa illlah ne baya ta6a ci har se yadawo gida"

Murmushin shima yayi tare da fa'din " _Abbas zakin fama ba, haka halinsa shikam ai kominsa yana da nasa tsarin."_

Hirar Abbas suka tayi har suka 'kare cin abincin inda Mahmud ne kawai yaci Teemah 'dan cakula tai tayi kawai daga nan kuma sai suka wuce shopping store suka 'dan siyi wasu abubuwan anfani.

Mahmud gidan mahaifinsa yawuce dasu basu sami Abbah agida bama sai dai Anty na nan sun same ta tana waya ne sai suka yi zaman jiran ta, jisuka yi tana fa'din "ehh lafiyan ta gasu nanma yamzu suka zo, ok ta'kqre maganar dashi tare da mi'kawa Teemah wayar kar6a tayi tare da fa'din "Hello" atakaice duk da bata san waye akan layin ba amma sai ta tsinci zuciyarta da rashin son yin magana alokacin.

Daga cikin wayar taji wata murya da bata san ta tana fa'din _"Baby how are_ u?.

Da 'yar muryarta da haushi yafara cikawa ta furta
_" Fateemah ce !"_ atakaice

_" i know naa, don't_ _worry u ll_ _soon........._

Bata bari ta 'karasa jin mai matar zata fa'da ba tacire wayar akunnanta tare da mi'kawa Anty wayar, afakaice Anty ta doka mata harara batare data bari sub lura ba sannan ta kar6i wayar dan ayanayin response 'din Fateeman Anty ta fahimci ba gaisuwar kirki suka yi ba hakan kuwa sai yasata 'kara jin haushi amma bata bari yanuna akan fuskarta da yanayinta ba sai ta tsare ta daidai ta nutsuwarta atake.

Tana kar6ar wayar ta yanke 'kiran tare da 'ka'kalo murmushi tace " ga dukkan alamu dai amarya tayi uwar 'daki, kinga kuwa yanda ta damu kullum sai ta tambayeki idan ta'kira awaya ,ai dan tayi tafiya ne ma inbahaka ba nasan da yanzu har kun saba ma da ita tun ranar da kuka sau'ka agidannan taji kin manta.................

Teemah baki ta ta 6e lokacin da idanun Anty yabar kanta, aranta tace " _su uwar 'daki manya, shine har da wani cemin baby, ce_ _mata akayi ni inason uwar 'daki ne?, mummy na_ _ma ta isheni nikam_ "

Mahmud kuwa shiru yayi kawai yana nazari dan kuwa yasan wannan uwar dakin bana gaskiya bane, bazai so ya tankawa mahaifiyarsa magana a gaban Teemah bane dan gudun watarana kar kuma yazamana shine da kansa yabada kofar raini ga mahaifiyarsa, inba dan haka ba daya ce baya son wannan ala'kar saboda yasan duk wani abu dazai tunkaro su ta 6angaren Anty toh ba alkhairi bane shiyasa yake tsoro, amma azuciyarsa sai yayi alwashin cewa ze tsaya tsayin daka dan ganin ya ruguza wannan ala'kar tun kafin tayi 'karfi.

'Bangaren Anty
kuwa kar6an su tayi ba yabo ba fallasa suka gaisa, tare da gabatar musu da abinsha agabansu sai dai suna gama gaisuwan ta tashi ta shige ciki tace dasu tana zuwa, zaman kusan 1hr sukayi ba Anty ba labarinta, Mahmud daya gaji sai yace mata ta tashi su wuche be ko sake neman Antyn ba sukayi tafiyarsu dan yasani sarai Anty dagangan tayi musu hakan.

*****
Tun ranar da Abbas yabar garin damaturu bayan 'dauri auren Mahmud be 'kara samun lokacin kansa na kirki ba, harma hakan sai ya zamana kamar taimako ne agareshi da zuciyrsa harma da rayuwarsa dan sam be samu lokacin da zai zauna har yayi tunani akan rayuwarsa da rabuwarsa da Fateema ba sai dai duk da haka 'yar walwalar dayake da ita yanzu babu shi koka'dan, yanayin komai ne ayanda sabuwar rayuwarsa ta zo masa da shi.

Saleema kansa tunda Abbas 'din ya sau'ka a wurin shi be gane kansa ba, kuma sam ya'ki ya bu'di baki yayi masa bayanin meke faruwa dashi, ya dai ce masa daga damaturu yake yaje 'daurin auren sister 'din shi, tun daga nan be 'kara yi masa wani bayani akai ba, dayake Saleem yasan halin kayanshi sai ya 'kyale shi dan yasan matu'kar Abbas be yi niyyan yin magana ba toh babu wanda ya isa yasashi dole, dan haka sai shima yabarsa kawai yaci gaba da abinda ke gabansa, toh dama ma yaya lafiyar kura......

Washe garin ranar daya bar Barrack 44 Kaduna, aranar ko zama beyi ba ogansa ya wakiltashi zuwa wani taro acikin garin porthacourt 'din.

Ranar lahadi ne ka'dai ya 'dan samu ya huta washegari kuwa rakiya yayiwa ogansa zuwa Biu Borno state domin halartar wani taron bu'de wata makaranta acan cikin garin Biu Nigerian Army Institute of Technology & Environmental Studies (NAITES).

Sosai hakan ya'kara taimakon Abbas dan kuwa taron sosai ya me dashi busy man harma sai ya 'dan manta da damuwarsa ya ajiyeta agefe guda ganin cewa saka damuwa aransa ayanzu tamkar yana kashe kansa tabaya ne dan kuwa cutar kansa kawai zaiyi batare da yasami dan taimako ba idan har yace sai ya zauna yayi tunaninta, yarinyar datariga ta tafi ta barshi, bari na har abada toh miye abin 6atawa kansa lokaci shi kuma akanta.

*LAGOS*
Mahmud duk wani 'ko'kari dayasan ze wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin sa da matar shi yayi 'ko'karin ganin ya aikata shi duk dama har yanzu beji cewan shima magidanci me iyali bane shi gani yake kamar wata 'kaddara ce tasasu kasancewa atare, amma hakan bai hana yabata dukkan kulawan daya dace ba, ko dan kasancewarta matsayin matar sa da jama'ah da dama suka shaida, sannan kuma 'kanwa ce mafi soyuwa azuciyarsa, abu 'daya ke 'daure masa kai yanda akowani dare sai yanayin Fateema ya canja yakasa fahimtar inda matsalar take tasowa yama rasa gane meke yawo akanta da har yake sata lalu6ansa akowani dare bayanshi hakan kokadan baya gabansa.
Chapter 67 · 0% Book details