← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 163

Sashe 98

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima yana gama fa'din haka ya juya yafara tafiya, Teemah kam bayansa ta tsaya tana kallo tana kwa6a baki, mutun kullun kamar ghost be ta6a yin dariya.
'Dan 'karamin tsaki taja da ta tuna cewa duk da hakan da yakeyi bata san meyasa lokuta da dama takanji son ganisa ba duk da kuwa bawani abin kirki ke ha'da su ba amma zuciyarta na yawan janta zuwa tunaninsa ko son ganinsa.

Kamar yanda yace 'din kuwa tana kaiwan wayan ta taho domin kawo masa ruwan tasa meshi tsaye yawani zuba hannaye acikin aljihun army green 'din wandon dake jikinsa.

Ita kanta da ta shigo tayi mamakin yanda 'dakin yayi 'kura ko dan an kwana biyu ba ayi amfani dashi bane oho.

Tana shirin fita daga 'dakin ya dakatar da ita da fa'din " _Zo ki kintsa min 'dakin nan_ _please_ "

Waro idanu tayi waje idanunta har ya fara tara hawaye bata san ma lokacin da bakinta ya furta " _Yayah yanzu fah zamu fita mun gama shiryawa_ !

Gira ya 'dage zuwa sama yace
" _So_ ?
_Come on zo ki kintsa min 'daki, kwaje shopping 'din gobe in Allah ya kaimu_ "

_Comment_
_Vote_
_Share_

(Ga duk me son farkon *CAPTAIN* *ABBAS* har zuwa inda aka tsaya should follow me a shafina wattpad @ *Serlmerh-md*

*Salmerh ce*😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~Dedicated 2 my family~

*Bismillahir rahmanir raheem*

_*3 C’s of LIFE* : Choice, Chance & Change – You must make a choice to take a chance or your life will never change._

🅿 *72*

'Bangaren Hannah kuwa harta gama shirinta tafito bata ga Hannah ba sai ta yi gurin Ummah dan ganin ko tana can ne, amma kuma sai ta tarar da Ummah zaune ita ka'dai, tambayar Ummahn tayi tace " _Ummah ina Teemah fa ko de tagaji da jirana ta wuce abinta dan naga_ _yau zumu'di_ _takeji_ _dashi_ "

Murmushi Ummah tayi tace
kafin ma ta rufe bakinta sai Ummah tace mata " _Ta kaiwa Yayanku abin sha ne bari ta dawo_ "

" _Yayah ya zo ne dama Ummah_ ?
Hannah ta tambaya lokacin tana shirin zama agefen Ummah.

Amsa ta bata da fa'din " _ehh be ma da'de da isowa ba yanzun nan ya shiga ciki, kije mana ku gaisa_ ".

'Dan 'karamin tsaki Hannah tayi tace " _barshi Ummah sai mun dawo kawai naje kafin nan ma kinga ai ya 'dan huta_ "

'Dan hira suka 'dan fara ta6awa da Ummahn kafin Teemah tazo, anan ne Ummah ke sanar da Hannah batun zuwan Mummy harma da Anty da Teemah tafa'da mata.

Hannah tayi murna sosai har zuciyarta da jin cewa Mummy zata zo saboda ita kam tana son Mummy ko dan goya mata baya ma datake yi akan komai sa6anin na Anty data kya6e baki tace " _Allah ya kwaota lafiya_ "

Teemah kuwa nacan tana aiki tana share hawaye, haushi gaba 'daya ya bi yacikata shima Abbas yana tsaye har yanzu be motsa ba har ta shiga tagama kintsa bedroom 'din ta wanke bathroom ta fito yana nan tsaye ,tasan cewa zefi fara bu'katan can 'din kafin parlour shiyasa tafara gyara cikin.
Tana aikin takaici fal zuciyanta tarasa meke damunsa shi akullum yafi son yaga ya 'kuntatawa mutun in bahaka mi ye ruwansa da fitan su harda zai ce wani bazasu fita yau ba sai gobe, salon yanuna halinsa afili kawai, bayan gobe Mummy da Anty zasu zo shine kuma zata fita yawo? tama rasa me ya dawo dashi wallahi, mutum sai fitinan tsiya.

Yana nan tsaye, yana tunanin yanda yaga yau duk ta canja tayi wani kyau na musamman da ita, duk da yake dama ita 'din me kyau ce amma na yau 'din na musamman ne, sai de har yanzu tana nan arame bata mai da jikinta nabaya ba.

Hawayen da yaga take ta sharewa ne ya 'dan 'dauki hankalin sa sai ya fara bin duk wani moves 'dinta da idanu, gani yayi da gaske kuka takeyi da hawaye, alokacin ma barta kammala shara ta goge ko'ina saura goge center table 'din dake tsakiyan parlourn ne ka'dai yarage take kan yi, sai ya taka ahankali ya isa inda take.

Hannunta ya kama ya mi'kar da ita tsaye sai kuma ya tsaya yana 'karewa cikin idanun nata kallo, 'kasa tayi da nata idanun jin gaba 'daya sun mata rauni, sam yanzu bata iya juran kallon tsakiyar idanunsa, intayi hakan kuwa jikinta har rawa yake 'dauka gaba 'daya, Yayah Abbas kwarjini yake yi mata sosai.

Ko yanzun ma 'kasa tayi da nata idanun hawayenta na sake gangarowa ahankali.

Da yatsan sa 'daya ya shafo hawayen nata sai ya sake nuna mata a saitin idanun ta wanda dolenta ta 'dago ta kalli yatsan daga nan ta 'dan kalle shi ka'dan, suna ha'da idanu sai shi ya sake bu'de nashi tare da 'dage gira sama da sauri tayi 'kasa da kanta ahankali yace " _dan nasaki aiki kike yin kuka_ ?

Kai ta jijjiga masa alamar " _ah' ah_ "

" _Toh menene_ ?
Ya sake tambayarta.

" _bakomai_ "
Teemah ta bashi amsa ahankali.

" _Ohh dan na hana fita yawo ne ko_ ...?

Kafin ma ya rufe ba kinsa cikin shagwa6a66iyar siririyar muryarta ta tare shi da fa'din
" _Na da'de fah Yayah banje ko'ina ba, kuma kullun ina son siyan abu_ _amma bana fita ko'ina, sai yau Ummah tace zamu ni da_ _Hannah...kuma...kuma_ ...
Sai ta 'karashe da in-inah ta kasa 'karasawa illah sabon hawaye hawaye daya gangaro .

Abbas ne ya 'karasa mata da fa'din
" _Kuma sai na hana_ _ko_ ?

Shiru tayi masa bata tanka ba, sai ta sake kwa6a fuska kawai.

Abu 'daya ke sanyaya ranta idan ta tuna zata ga Mummynta shiyasa ma take 'danjin dama-dama.

Abbas kam tsayawa yayi yana kallonta yarintarta na birge shi, komai nata ma shi birgeshi yake yi sai de kukan da takeyi 'din har zuciyarsa yake jin ciwonsa, tausayinta yaji ya kamashi, hakan yasa shi lowering voice 'dinsa yace mata " _banace gobe zakuje_ _ba_ ?

Kai ta 'daga masa alamar " _ehh_ ".

" _so why d tears_ ?
Yayi maganar tare da 'dage gira 'daya.

Cikin wani shagwa6an tace " _gobe fa Mummy zatazo, kuma banaso tazo bana nan_ "

Murmushi yayi mata da jin wannan shirmen kuma sai yace mata " _kin fiye kwa6a ke kam,_ _angaya miki idan tazo 'din zata koma kafin ki dawo ne_ ?

Jijjiga kai tayi.

" _Toh oyah wipe all those tears ban son shirme_ "

Fara share hawayen tayi da hannunta 'daya, sai ya 'dago 'dayan hannunsa ya fara tayata gogewa ahankali, yana gogewan yake fa'din, " _kar na 'kara ganin_ _hawayen nan kinji, idan bahaka ba naga kin sake yin wani kuka toh goben ma baza'a je_ _ko'ina ba kuma zance da Mummyn ma karta zo_ ......

Hannah ce ta iso da sallamarta da niyyar duba Teemah ganin lokaci na tafiya kuma tajita shiru.

Cak ta tsaya tana mamaki ganin su tsaye daf da daf Kamar ze mai da ta cikinsa yana share mata hawaye.

Abbas kam ko ajikinsa sallamar Hannah kawai ya amsa tare da 'dauke hannunsa daga kan fuskar ya yi kamar babu abinda yayi.

" _Ina yini Yayah_ "
Hannah ta fa'di tare da kawar da kanta gefe.

Da
" _lafiya_ " kawai ya amsata daga nan ya juya ya shige cikiabinsa, itama Hannah bata damu ba dama tasan iya amsar dazata samu kenan dan haka sai ta nufi gurin da Teemah ke tsaye da sauri ganin ta wata iri.

Hannunta takama taja ta suka nufi hanyar fita, sai da suka 'danyi nisa da 'dakin nasa kafin Hannah ta tsaya ta tambaye ta cewa
" _me Yayah yake miki afuskarki yau kuma_ ?

Bata bata amsar tambayar taba sai tace
" _Yayah yace wai ba zamu fita yau ba, sai de gobe_ "

Duk da taji haushi sosai da jin abinda ya fa'da 'din amma ita bashi take son ji ba dan haka sai tace " _that a side Teemah bani amsar tambayata_ "

Shiru Teemah tayi mata dan bata san me zata ce mata ba,tace da hawayen ta ya goge mata ko kuma tace me?

Juyawa Teemah tayi ta nufi hanyar 'dakinsu.
Shan gabanta Hannah tayi tace " _to shikenan tsaya,_ _wai dagaske cewa yayi bazamu_ _ba_ ?

Cikin sanyin murya tace " _Dagaske ne mana Hannah zan miki karyane_ "!

Hannah cewa tayi
" _Toh shi dama baya zo ba sai ya damu mutun, sarkin kwafsi ai nasan ze aikata tunda naga kin da'de baki dawo ba sai dana ayyanah, Allah Yayah ya cika bada mutun wallahi, sai dana gama 'daga wa kaina hankali nagama shiri ina murnar zan kaiki kiga gari shine ya hana kuma_ "

'Dakinsu suka koma ko wajen Ummah basu kuma zuwa ba. sai can da Ummah taga shirun yayi yawane shine tafito dubasu.

Direct 'dakin Abbas ta nufa dan tayi zaton ko shi yari'kesu.
Koda ta isa 'dakin nasa zaune tasame shi akan cujera ya na duba system 'dinsa ganinta yasa shi 'dago kansa zuwa kallonta.

Ummah kam ganin ko'ina fes sai tayi mamakin yaushe kuma aka gyara shi, atake ta tuna ashe fa ba'a gyara 'dakin ba shaf ta manta wallahi, wata'kila akan aikin yari'ke min yarinya.

Kauda zancen tayi ta jefa masa tamabayar " _ina yaran nawa suke_ ?

" _Ummah ai sun da'de da barin nan_ "

Mamaki tayi tace masa " kamu su wani abin 'kila dan nasa haka banza bazan ji shiru har haka ba"

Murmushi yayi yace mata " _toh ni me zan musu Ummah_ ?

Tace
" _Ni da kai ne ai idan_ _naji wani abu_ "

Be yi magana ba kawai ya sunkuyar da kansa yana murmushi da jin maganar Ummahn.

Ahankali Ummah tace
" _ya bangansu ba toh, bari dai_ _induba ko suna 'daki_ "
Tayi maganar tare da juyawa ta koma zuwa dakinsu.
Tana tafiyar take tunanin kardai tafiya sukayi batare da sun mata sallama ba, in kuwa haka ne tasan duk tsirin Hannah ne.
Chapter 98 · 0% Book details