← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 163

Sashe 157

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duba gadon Annur tayi bata ganshi ba haka ma nasu gadon ma baya kai wannan dalilin ne yasa ta juya ta kalli Teemah tace da ita " ina yaro na yake in mai gudnyt rabo na da shi tun da maghrib gashi bacci nake ji yanzun"

Teemah bata juyo ba ta bata amsa da fa'din " ki je ki kar6o shi a wurin Yayah"
Hannah sai cewa tayi
"Ta6'di ke de shirya ki kar6o shi ina jiranki kun fi kusa ai".

Shiru Teemah tayi ta cigaba da goge jikinta, bata shafa mai ba sai kawai ta 'dauki turaren humrar ta tabi jikinta da shi sannan ta nemi kayan bacci riga da dogon wando ta sanya dan ita tafi son irin su dama.

Tana gama shirin ta 'dauki hijab 'din ta babba ta sanya da silifas ta bar 'dakin ba tare da ko kallon inda Hannah take ta sake yi ba.

Zuwa lokacin kuwa tuni hankalin Hannah ya riga ya 'dauku ga wayar data keyi bama tasan lokacin da Teemah ta bar 'dakin ba.

A hankali ta tura 'kofar tare da yin sallama 'kasa-'kasa sai amsa mata shima ba tare da ya 'dago ya kalle ta ba fuskar sa na kan ta Annur yana yi mai wasa.

Shigowa tayi tare da tura 'kofan sai ta ja ta tsaya ta na kallon su, ita haushin ta 'daya warning 'din da Anty tayi mata akan sa, sam bata son ya wargaza mata gyaran da aka soma yi mata tun ba aje ko'ina ba dan ko itama tana so ta tsumu ba yanzu ta so ha'duwar su ba, amma ga dukkan alamu ba fahimtar ta zaiyi ba har da cewa wani amarya zaiyi.
Tsaki taja a ranta ta dan ta tsani wannan kalmar sam..

A hankali ta 'karasa inda yake ta tsaye nesa ka'dan dashi sannan tace " Yayah kawo shi mu tafi kaga dare na 'kara yi kuma Hannah ma na so ta ganshi "
Sai yace
"Ni kuma so nake mu kwana da shi ya za'ayi?"

Shiru tayi ta tura baki gaba tare da 'kura masa idanu, bata san yaushe Yayah ya koyi irin hakan ba bata san me ya canza shi ba dan Yayan ta data sani ada ha'kurarre ne akan komai, kallon kallo suka tsaya yi kiwa abinda ke ransa daban, shikam ransa fes babu komai illah so da 'kaunar ta bayaga haka babu komai, shine ya yanke shirun nasu da fa'din " Zo ki zauna ki bashi abincin sa naga yana shan yatsu"

Zaman tayi kamar yanda ya fa'da 'din ta mi'ka masa hannu akan ya bata babyn sai bai bata ba sai yayi mata nuni da hijab 'din dake kanta.

Ja tayi ta cire shi ta ajiye a gefe.
Abbas sai ya mi'ka mata Annur 'din sannan ya taya ta 6alla botiran saman rigar guda uku yace to ta bashi.

Shi kam zuba musu ido yayi yana kallon yanda babyn ke sha cikin nutsuwa, babban abinda yafi tafiya da imanin sa ajikin ta bai wuce boobs 'din ta ba, yanzun kuwa ganin yanda suka sake cika suka tsaya sai yake jinsa cikin wani yanayi, dan basuyi komai ba illah da 'da cika da sukayi sosai yake kewar su yake kuma jin son sarrafa su.

Har Annur yayi bacci Abbas na gefe yana kallon su, Teemah sai ta cire shi tana rufe bottles 'din ta Abbas ya 'dauke babyn cak ya kwantar da shi sannan ya rungumo ta ta baya tare da ri'ke hannun ta a hankali yace " saura ni ko".

Shiru tayi sai ya juyo da ita ta fuskance shi ya sake fa'din " aji dani nima"

Tana 'ko'karin yin magana ya 'dora yatsan shi saman la66an ta alamun tayi shiru dan yasan bai wuci complain zata yi ba, matso da fuskar sa yayi kusa da nata ya ha'de musu hanci suna jin 'dumin numfashin juna tare da sau'ke hannun san dake saman bakin nata ya jone bakin nasu wuri guda ya fara shan harshen ta, tsawon da'ki'ku kuma sai ya tsaya tamkar ya manta me yakeyi yayi jim, Teemah kuwa da ta ga haka sai ta cigaba da kissing 'din nashi kamar dama can ita ta fara.
Ita kanta tasan tayi kewar shi kawai dai bata son ta watsar da maganar Anty ne shiyasa take 'dan denying 'dinsa, kuma gashi tana jin nauyin Ummah bazata iya sakewa da shi a gidan ba.
Tana cikin tunanin sai taji hannun sa a cikin rigar ta yana mata tafiyar tsutsa har zuwa saman 'kirjin ta. Ajiyan zuciya kawai ta sau'ke duk dama bai fito fili ba amma yanda yaga yake samun response 'din ta ma sai bai yi tunanin kusantar ta ba ya tsaya a iya romance ne kawai ba komai da ya mata.
Inda ya 'dau tsawon lokaci yana juya ta son ran shi haka kuma itama dan sai da ta tabbatar tayi easing abinda ke damun sa kafin sukayi bacci manne da juna tuni ta manta da fushin amarya.

Hannah kam har ta gama waya tayi zaman jiran Teemah amma shiru har kusan 11pm kawai sai itama ta kwanta tayi baccin ta ganin basu da niyyan dawowa.

Da asussuba Teemah ko ta gudo daga 'dakin sa wai dan kar Ummah tazo ta ga basa nan.
Sallah ta samu Hannah nayi dan haka sai ta kwantar da Annur ta tafi bayi itama sai da tayi wanka kafin ta 'dauro alwala ta fito.

Da ta idar da sallar ne Hannah ta jefa mata tambayar
" Yayah ne ya ri'ke ku ko"

Da'din tambayar Teemah taji dama bata so Hannah taga kamar itace ta 'ki dawowa dan haka da wuri ta bata amsa da fa'din " ai wallahi kamar kinsani...Yayah cewa yayi wai shi sai da 'dan sa zai kwana, ni kuma wallahi kunyan Ummah nake ji kar ta gane a wurin sa muka kwana shiayasa ma kika ganni sassafen nan"
Hannah kuwa sai tace
" Hmm, kin makara ai Ummah da dare tazo duba Annur wai ko yau ma ya'ki yin bacci irin na jiya? sai nace mata ai kun tafi wurin Yayah"

Zaro idanu Teemah tayi tace " dan Allah Hannah dagaske?, na shiga uku ni kam yanzu ya zanyi duk fa laifin Yayah ne Allah"

Hannah murmushi tayi tace " Firgici haka sai kace dagaske bayan kinje kin 'din kuma miye abin damuwa?"
Teemah sai tace
"Ba zaki gane bane Hannah ke kam, ai da kunya irin wannan abin, ni dan Allah ki gaya min ya zanyi?"

Murmushi Hannah tayi yanzun ganin yanda duk Teemah tabi ta rikice sai tace da ita
"Wasa ni nake miki dan Allah ki nutsu, bata zo ba kuma yanzu kam ai bazata sani ba tunda kun dawo, amma shine kuma kuka barni na raba dare ina zaman jiran ku bayan kin san bazaku dawo ba...Allah naji haushi?"
Ajiyan zuciya Teemah ta sau'ke tare da fa'din
"Very sorry lil sis baza'a sake ba"
Ai ma baki san wani abu ba? Yaron nan in gaya miki yau ko damuna baiyi ba yayi ta baccin sa...."
Hannah sai tace
"Ah to yaga innar sa taje neman lada ba dole ya risina ba"
Fa'din Hannah tana murmushi.

Teemah sai tayi murmushi kawai batare da tayi magana ba.

Aranar kuwa Abbas ya koma kamar yanda ya fa'da mata, ita kam da fatan alkhairi ta bisa dan bazata iya ce ga takamamman yanayin data ke ji game da shi ba, fama take da zuciyar ta tana ta 'ko'karin 'karya ta kewar shin data ke ji 'karfi da yaji ta sanyawa ranta 'karfin hali da nuna halin ko in kula game da tafiyar sa tasa.

Teemah tun bayan sati da haihuwar ta tafara yin sallah, gyaran da ake yi matan kuwa ba 'karamin fitar da ita yayi ba, idan ka ganta tashin farko bazaka ta6a cewa itace ta haifi Annur ba, dan yanda tayi 'das abinta abin ba'a cewa komai.

Kullum matar take zuwa daga 10:00am zuwa 12:00pm tayi mata duk abinda zata yi ta tafi so gyaran bai wani takura ta ko shiga lokutan wasu al'amuran ta ba.

Shi da Abbas a nufin sa wai suna gama 40days 'din nasu zasu koma amma Ummah ta tayi babakere tace sam bata ji zancen ta haka ba sai sun 'kara hutawa.

Abbas har ransa ya 'dan 6aci da hakan amma sai ya 6oye bai nunawa Ummah ba, sai dai Teemah da suka ke6e da ita ya bayyana mata halin daya ke ciki inda ta matu'kar tausaya masa tana jin ba dan Ummah mahaifiya ba ce da babu abinda zai hana ta bin mijinta, domin ita kanta tasan yayi ha'kuri sosai sai dai bazata iya ja da batun Ummah ba dan haka kawai sai tai ta bashi baki har ya ha'kura ya koma Ports.

Wasa-wasa har sai da suka haura 2months da 'yan kwanaki kafin Ummah ta bashi matar sa, hakan ma sai data ga ya shiga wani yanayi kafin nan ta sallame su domin a wani zuwa da yayi ya ri'kewa Teemah wuta Annur nata faman ihu amma bai ko kula da hakan ba, Teemah ce ma hankalin ta ya kasu biyu amma shikam yayi nisa cikin son kasancewa da ita, k'aran bugun 'kofa ne yasa shi 'kyaleta ba wai dan yaso ba yayi saurin kintsawa tare da zuwa ya bu'de 'kofan, ganin Ummah yasa shi jin kunya take yayi 'kasa da kansa yabi ta gefen ta ya fice daga 'dakin batare da ya ha'da ido da ita ba, Ummah kam da kallo ta bishi cikin ranta tace " kaji kunya ai fitinanne kawai".

Duban ta ta mayar kan Teemah dake faman jijjiga Annur tana sussunne kai itama Ummah sai tace " ki bashi ko ruwa ma yasha zaiyi shiru"
Da kai Teemah ta amsa mata batare da ta 'dago kai ta kalli Ummahn ba.
Chapter 157 · 0% Book details