← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 163

Sashe 27

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da farko lokacindata fara d'ago kai d'in idonta a bud'e yake amma data ga tana gab da d'agowa gaba d'aya sai tayi saurin rintse idanun take kuwa hawayen daya taru a gurbin idanun ya gangaro zirr ya jik'a kumatun ta.....ahakan ta k'ara sa d'agowa takuma k'i bud'e idanun nata.

Tsayawa yai yana kallonta da kyau, a kullum gani yake yarinyar na k'ara yin kyau ne tafiya take da imaninsa da kuma tunaninsa gaba d'aya.

Kusan mintina uku babu wanda yayi magana a tsakaninsu illah jikin Teemah dake ta faman 6ari dan yau tasan tashigo hannu sai yanda Allah yai da ita abanza ma yaya balle ta aikata laifin azahiri.

Ganin yanda jikinta ke karkarwa ne yasashi murmushi aransa yace " halin yarinyar nan sai ita, ga uban tsoro ga kuma fitina da neman magana".

Sai kuma yaji ta bashi tausayi sosai sai ya tsurawa crying face d'in nata idanunsa shima na tsawon sakanni bai d'auke idanun san daga kallon fuskarta ta ba yace " open ur eyes"! Atsare yayi maganar amma bada zafi ba.

Duk da tana son bud'ewan amma sai ta gagara bud'ewa saboda tsoron yanayinsa dazata gani takeyi, shikuwa da ya ga bata da alamun bud'ewa sai ya sake maimaita mata " I said open ur eyes Fateemah"
Wannan karan ma asanyaye yayi maganar.

Ita kuwa jin yana yi mata magana da muryar rahama sa6anin yanda ta zata da farko sai hakan yasa ta jin d'an sanyi-sanyi sai ta bud'e idanun kamar yanda ya buk'ace dayi.

Cak idanun nata suka sauk'a a cikin nasa tana niyyar sauk'e nata idan ne yayi saurin dakatar da ita da d'an k'arfi..." don't try it!"

Dan dolenta itama ta bar idanun tan akan san duk da yanda take jin bugun zuciyah aduk lokacin data had'a ido dashi, amma haka ta daure batare data so ba.

Tambaya taji ya jefa mata amma sam ta kasa bashi amsar tambayar tashi saboda kwata-kwata ita bata ma san me zata ce dashi ba koda ta bud'i bakinta.

Sai tayi shiru kawai tana rarraba idanu, ganin tayi shirun shikuwa sai ya sake maimaita mata tambayar kamar yanda ya fad'i da farko batare daya canja ko kalma d'aya ba " me yasa kika shafa min nace"!

Wannan karon ma a nutse yayi tambayar sai hakan da yayi yasa taji kusan 40% daga cikin tsoron data ke ji d'in ya kau.

In-ina tafara sai yayi saurin dakatar da ita da jijjiga kansa.

Hannu ya sa ya kamo fuskarta ya d'ago saitin fuskarsa suna kallon juna " then tell me now" Ya sake fad'i.

Ita kuwa sai tak'i magana sai ta sake jin jikinta wani iri tsoronsa ya k'ara kamata ga kuma bugun zuciyarta dake k'ara yawaita, zuwa yanzun koda tace zata yi masa magana toh bata san me zata ce masa ba domin bakinta kansa yayi mata nauyi.

Da yaga bazata yi masa magana ba sai ruwan hawayen ta dake matuk'ar ta6a masa zuciya, sai ya sake mata fuskarta ta ya mik'e tsaye singlet d'in dake jikin sa kad'ai ya cire sai ya dawo inda take ya kama hannunta ya fara tafiya da ita.

Bata yi turjiya ba tunda tasan itace da laifi sai kawai tabisa.

Shikuwa bayi ya nufa da ita,koda taga yana niyyar shigar da ita bayin ne sai ta d'an turje, juyo yayi ya bata wani dirty look take kawai ta d'aga kaf'afu tabishi.

Shahada tayi ta bishin duk da bata san mai zai biyo baya ba sai kawai ta rink'a addu'a azuciyarata akan cewa Allah ya ubangiji ya d'ora ta akansa Allah ya ku6utar da ita.

Suna shiga bayin yayi zamansa akan wani stool da ke ajiye musamman acikin bayin.Sai yace mata " bismillah k'arasa aikinki".

Bata gane mai yake nufi ba amma dana haka sai taja tayi tasaye tana wasa da yatsun hannunta.

Tsawon mintina sai yakuma fad'in "banaso idan ina ma mutun magana ana shareni ki kula sannan kuma warning naki na k'arshe kenan"

Haryanzu bata fahimci mai yake nufi da bismillan ba amma tsab ta fahimci warning d'in daya mata kawai dai bata san mai zata yi ba ita.

Shi da kansa ya fahimci bata gane manufarshi ba sai yace mata " ni nace miki ina buk'atar aski ne ko shaving?"

Sai ta jijjiga kanta alamar " a'a"

" Ni nace ki shafa min mai jikina?"

Nan ma jijjiga kanta tayi.

" Ni sa'anki ne agidan nan?"

Harta fara jijjiga kai sai taji ya daka mata tsawa inda yace open your mouth and talk to me or are u deaf?"

Da sauri tace " umm-umm"
Dan gani tayi take ya juye mata tamkar mayak'i idanunsa taga sunyi jajir.

" Raini ne kenan yasaki yimin haka ko?"

Da rawar murya ta ce " ah....'ahh..... yayah..... dan.....dan girman Allah kayi hak'uri.

Bai sake yi mata mata magana ba kawai ya sa hannu ya matso da ita kusa dashi ya d'aga mata fuskar sai da da lumshe idanu kafin ya furta " clear it".........

Dan dolenta tasa hannu ta kunna tap sannan tafara wanke masa fuskar tasa duk inda cream d'in ya ta6a sai da tabi ta wanke tas.

_Comment and share_ _pls_ 🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍

[10/2, 5:58 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *26*

Tana k'arasa wankewa sai ta d'age hannunta daga fuskar tasa shima daidai sai ya bud'e idanunsa ya sauk'e su akan madubi, tacikin mirror d'in suka had'a idanu ai kuwa tana ganin yanda yakoma sai taji dariya yakamata.

Hannunta ta d'ago ta rufe bakinta dashi wani shape da goshinsa yacire ne yasa takasa rik'e dariyar tata sai ta juya kawai da gudu tabar bayin.

Bata zame ko'ina ba sai a d'akinta tana shiga kuwa ta tura k'ofar ta danna lock.

Dariya tayi taci abinta harda rik'e ciki.

Abbas kansa shima dariyar taso kamashi amma sai kawai ya maidata murmushi ya k'yale dariyar, haka ya k'urawa mirrorn idanu yana kallon kansa yanda Teemahn ta sauya mar kamanni, ita kawai yake hangowa lokacin da ta ke shafa masa cream d'in gani yake kamar yanzu ta ke yi masa hakan, sai kawai ya lumshe idanunsa bai dad'e ba ya kuma bud'esu.

Tunanin yanda zai je agyara masa kan nasa ne yafad'o masa, take sai yaji ba dad'i jiyayi ransa na so ya 6aci akan hakan, amma sai ya danne 6acin ran nasa, taimako d'aya Allah ya mata dan dama he is about to leave kuma dole kafin ya tafin sai yayi aski, amma badan hakan ba yace " hmm"
kawai sai da yakai hannu ya na shafa kannasa kafin yace " yayarinyar nan ta gama raina ni wallahi dole inkoya miki hankali".

Tashi yayi yafara rage kayan jikinsa dayake daman bai cire su ba d'azun.

Sai da yayi wanka kafin ya fito daga bayin d'aure da towel yana tsane ruwan dake jikinsa.

Shiri yayi dolensa cikin captan mint green yasa hula ya daidaita ta da kyau ta rufe gurbin kannasa sannan ya fice daga gidan ya nufi barbing saloon d'in dayafi kwanta masa arai domin a gyara masa 6arnar da Teemahn tayi masa.

*****
Teemah ce kwance ad'akinta akan gado sai kwasar dariya take harda hawaye, ko tayi niyyan bari amma sai taji sabuwar dariya na k'ara zuwa mata seconds-seconds take sake jin wata dariya na kamata, cikin dariyar take fad'in " kad'anma kagani ai tunda dai ni kace zaka sa agaba kam sai dai mu zuba mu gani".

Juyi tayi ta kifu agadon sai tunanin yanda suka kwashe da Leemah yazo mata a washegarin ranar daya hanata zuwa birthday.

Har kusan fad'a suka so yi da ita dan tagama saka ran Teemahn zata je sai kuma taga shiru ga shi kuma babu waya a hannun Teemah balle tak'irata sai hak'an ya k'ona ran Leemah sosai.

Haushin mitan da Leemah ke wa Teemah ne aranar ya had'u da haushin da yah Abbas ya k'unsa mata sai kawai ta fara yiwa Leemahn masifah toh dayake Leemahn itama ba baya bace wurin magana sai suka dinga yi atsakaninsu da k'yar suka yi shiru sai da Fauzee(class representative d'insu) tace zata had'a su da Uncle d'insu (Uncle Hasheem) kafin sukayi shiru dayake suna jin tsoronsa sosai.

Har kuwa kusan kwana uku sukayi basuyin magana da junansu kafin daga baya suka zo siluka shirya kowa ya huce.

Shiyasa ko yanzun data masa hakan kokad'an batayi dana sani ba acewarta tunda itama yana had'ata fa'da da mutane gara ta rama.

Wunin ranar kuwa kaf d'insa acikin d'akinta tak'arasa shi dan k'in sake fitowa waje tayi dan ma kar su had'u da shi yaci k'aniyarta ko kuma ya had'ata da mummy.

Batama san ya fita agidan ba dan hatta islamiyah ma yau k'in kulawa tayi da al'amarinsa, Mummy cema data ga shirun yayi yawa ga kuma lokacin islamiya har ya wuce bata ga gilmawarta ba shine tazo ta bubbuga mata k'ofar, amma sai tak'i bud'ewa tace da mummyn wai kanta naciwo ne sosai shiyasa bata fito ba tanaso tayi bacci ne.

Mummyn dataji haka sai tace mata "toh Allah ya sauwak'a" sai kawai ta juya ta koma d'akinta.

8:02 pm

Abbas bai dawo gidan ba sai da dare yana shigowa kuwa yawuto parlourn domin ya gaida mummy kasancewar tun gaisuwan safe da yayi wa mummyn basu kuma k'ara had'uwa da ita ba.

Yana gab da shiga parlourn sai wayarsa tafara ringing, dakatawa yayi da tafiyar sannan yaciro wayar ya duba mai k'iran nasa Saleem ne abokinsa wanda sukayi course tare dashi sai ya tsaya awurin yayi receiving k'iran.

Teemah na daga cikin parlourn suna zaune da Mummy sai taji ringing d'in wayarsa daga waje aikuwa ta wani razana hatta mummy sai data tsorata da yanda tayi d'in, da gudu ta tashi tayi d'aki batare da ko mummy tayiwa magana ba.

Abin ya d'aure kan mummy sosai yau Teemahn na yin wani abu kamar marar gaskiya ta kasa gane inda gakan kuma ya dosa, ko d'azaun da k'yar tasamu tafito bayan sallar maghrib sai da mummyn ta kusan 6ata ranta kafin tafito daga d'akin ahkan ma tana wani d'ar-d'ar da kalle-kallen gefe.
Chapter 27 · 0% Book details