← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 163

Sashe 7

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jijjiga kansa kawai yayi jin yanda ta ja k'ofar da k'arfin gaske.

Idonsa ne yakaiga wayar data jefar d'in garin gudun rashin gaskiya.

"Hmm"
afili,sannan ya k'arasa ya d'auki wayar ya kashe hasken.Daganan ya koma ya d'auki mansa ya shafa ya shirya ya fito da wayar a hannunsa.

Ahankali yake takawa danko k'arar takalmansa ma ba'aji.

Abakin k'ofar shiga parlourn yayi sallama,daga ciki daddy ya amsa masa,jin amsawan da akayi ne yasa shi d'aga labilen yashiga fuskarsa cike annuri........

_Share pls_ 👌🏻

*Salmerh* 😍
[10/2, 5:51 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Dedicated*
*2*
_my family_ 😍

🤙🏻
Masoya ina godiya nima da soyayyar ku ga littafinnan Allah ubangiji ya barni daku.Ameen👏🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🤞🏻🤞🏻🤞🏻
Being quiet and gentle doesn’t mean you’re weak. Such people show deep, inner strength that’s under control. It’s knowing when to speak and when to listen; when to take action and when to wait. Don’t underestimate such people. *They walk* *the earth with the* *greatest strength!*

🅿 *7*

Tana fita daga d'akin nasa waje tayi tana haki,taje tasamu k'ark'ashin wata bishiyar mango da ke acan bayan d'akunan gidan tayi zamanta dayake akwai abin zama agurin,aranta take ta tunani wai daman wannan neh yah Abbas d'in,?

Wannan ai babba ne,wata zuciyarta tace ta ce mata amma fah yah had'u,mtssew taja tsaki afili ,toh sai a gidanmu zai zauna neh,ni bana sonshi wlh, nafi son yah Abbas d'ina na dah,don mummy tace har makaranta yake rakani da islamiyah harda yawo muke zuwa,amma wannan dagani mugunta zai yi.

Haka ta zauna ita d'aya agurin tana ta tunani batare da ta je tafad'awa mummy sakamakon aiken ba.

Daddy da mummy neh kad'ai suke zaune a cikin parlourn sanda ya shigo,cikin hikima yad'anyi yawo da idanuwansa acikin ilahirin d'akin ta yanda babu wanda zai lura da abinda ya akaita ko kuma manufar yin hakan,amma bai ganta ba,ya k'araso inda yakamata ya zauna,harya samu wuri ya zauna mummy bata ga Teemah ba, da farko ta zaci abayansa zata shigo tunda basu shigo tare ba,amma sai taga wayam,hakan yasa ta dube shi sannan tace "ina kuma 'yar aiken ta tsaya?"

"Tun d'azu fah ta taho mummy"
Abbas d'in ya bawa mummyn amsar tambayanta,fuskar sa cike da murmushi.

wayar dataje dashi d'in ya miqawa mummyn
"Harta manta wannan ma"

"Hmm" mummyn tace tare da miqk'a hannu ta kar6i wayar,sannan ta k'ara da fad'in kaga kuwa bata biyo tanan d'in ba,ta fad'a tana me daidaita zamanta, "kode yasar min wayar tayi garin haukarta ko? Mummyn ta tambaya tana kallonsa

Jijjiga kansa yayi alamar a'a.

Daddy kam bai kulasu a maganar tasu ba,don gaba d'aya ya tattara hankalinsa ne akan kallon labarai.

"Yah gajiyar hanya toh?
mummyn tasake tambayar Abbas d'in tana kallon labaran itama.

Da Alhamdulillah ya amsa mata.

Daganan mummyn tamiqe ta isa ga dinning,Bismillah ta musu tana me k'ara shishshirya wajen da kyau.

Abbas ne ya fara mik'ewa tsaye,kallon Daddy yayi sai yaga kamar ma bai san dasu awajen ba gaba d'aya,dan bashi da alamar miqewa,gaba d'aya labarun ne suka d'auke masa hankali,murmushi ya saki sannan ya isa gaban TV d'in ya tsaya k'ik'am ya tare komai,Daddy bazata kawai ya gansa tsaye agabansa,waiwaya wa yayi ya kalli gefensa tukunna kafin ya sawo da kallonsa ga Abbas d'in,dan bai san ma sanda ya bar gefensa ba.

Hannu ya ware ya dan k'wali 🖐🏻Abbas d'in dashi,tare da fad'in "kaci gidanku"

Dariyah Abbas ya k'yalk'yale dashi,yana kallo, daddyn.

"Abinci zaiyi sanyi kuma naga alamar baka da niyyan tashi"Abbas d'in ya fad'I bayan ya tsagaita dariyar tasa.

Mik'ewa daddy yayi ya isa ga Abbas d'in,hannu yasa ya kamo kunnan Abbas d'in d'aya yana murmushin shima,fara jan sa yayi ahakan ya nufi gurin cin abincin dashi.

Yana kama kunnan
Abbas d'in take yayi k'asa ya rage tsayi kad'an, dan ba bak'aramin zafi yajiba.Daddy da k'arfi ya kama kunnan nasa.

"Awchhh daddy zafi"Abbas d'in yafad'I tare da dafe kan hannun daddyn da duka hannayansa biyu.

Ahaka har suka isa gurin dinning d'in bakin Abbas baiyi shiru ba sai cewa yake "afuwan,afuwan daddy wlh bazan k'ara ba".

Daddyn sakinsa yayi har se da suka isa daf da wajen cin abincin.

Dariyah suka ji an k'yalk'yale dashi daga bayansu.

Daddy dayasan wace mai dariyar ko juyawa baiyi ba yasake kunnan Abbas d'in,dan yasan wannan aikin sai Teemah,dama yamasa hakan nema dan ganin bata nan,datanan da ko farawa bazaiyiamba dan sanin halinta dayayi.

Waigawa Abbas yayi inda yaji sautin dariyar,four eyes sukayi da ita,take ta zaro ido waje tare da d'ago hannunta ta rufe bakinta dashi,da gudu tajuya tayi hanyar d'akinta,daman shigowarta kenan,sai taga daddy yana jan kunnansa shine ta tsaya dariyar mugunta.

Mummy da tunda taji dariyar itama ta waiga tana kallonta da mamaki."Allah ya shirya"mummyn tace bayan Teemahn ta wuce ciki.

Cigaba tayi da zuzzuba musu abincin,tana aikin zubawan ne tace wannan yarinyar akwai shakiyanci wallahi,Zo ka zauna Abbas manta da ita zanyi maganinta ai.......

Tahowa yayi yaja kujera ya zauna d'in kamar yadda mummyn tafad'a,
yana zama mummy ta tura masa nasa abincin danshi daddy kam ma har ya fara aikawa da su.

Bismillah yayi shima yafar ci,kamar yanda kowa dake gurin yayi,amma ga mamakinsa har suka kusan gamawa babu Teemah babu alamarta kuma babu wanda ya damu da rashinta awurin.

Baisan cewa su sun riga da sun saba da rashin cin abincinsu batare da ita ba.

Gyaran murya yayi kad'an sai yaga duk sun kallo sa.
Ganin hakan sai ya d'aga hannunsa ya nuna inda tabi d'azun tare da fad'in wancen yarinyar bata cin abincin ne ita?
yayi maganar ne batare da kallon kowa ba daga cikinsu.kuma hakan kenan yana alamta cewa daga bakin kowa ma amsa kawai yake da bukata inda hali.

Daddy ne ya d'an murmusa sannan yace "kamanta kaika koya mata?,
"Wannan yarinyar ai rainonka ce Abbas"sai da yad'an bud'o idansa kadan sannan yasake fad'in "ta kware yanzu kuwa a wannan tafiyar"

Abbas kallon daddy yayi da fuskar mamaki.

"Ehh"
Daddyn yasake tabbatar masa da abinda ya fad'i.

"Tun barinka gidannan Teemah bata bar al'adarta ba na k'in cin abinci da rana ba sai ranar data ga dama take ci.

K'asa yayi da kansa yaci gaba da cin abicinsa batare da yayi magana ba.

Mummy ce taci gaba da fad'in
"Aini bakina har kusan tsayi yayi akan cin abincin nan,sai da naga da gaske takeyi sannan na kyaleta nima na hutawa raina."

Murmushi kad'an Abbas yayi acikin ransa yace "zakuwa musa k'afar wando d'aya da ita".

Babu wanda yasakeyin magana acikinsu har suka k'are cin abincin.
Daddy ne yafar tashi awurin ,yabar mummy da Abbas wanda shima tun d'azu ya ajiye spoon d'insa dan already yaji shi full,amma bai bar kan dinning di'nba illah baya da yayi ya jingina da jikin kujeran dayake zaune akai.

Har sai da yaga tashin Daddy tukunna kafin ya dawo da jikinsa kan kujerar da kyau,sannan ya fusaknci mummy.

K'asa yayi da muryarsa yanda ba kowa zaiji sa ba.

"Mummy "
Ya ambata ahankali

Kallonsa tayi batare da ta amsa ba,ko dan ganin suna kusa ne oho,

"Kardai waccan Teemah ceh"yafad'a tare da nuna hanyar databi d'azun kamar yanda yayi da farko da zai tambaye su ita.

'Daga masa kai mummy tayi alamar "ehh"tana d'an murmushi,daganan tacigaba da duban cikin wayarta data keyi tun da farko.

Abbas kuwa baya yayi yakoma ya jinginu tare da lumshe idansa yakuma bud'esu atake.
Arannasa yake jinjina al'amari irinna ubangiji da ba'a ta6a yimasa gyara.

Tsinkayo muryar mummy yayi tana cigaba da bashi labarin irin rigimar da suka sha bayan wancen tafiyar tasa.

Mamaki yaringa ji aransa danshi bai ta6a zaton ma zata jima batare data manta dashi ba,saboda bawani jimawa yayi tare da ita ba alokacin, its just 3month l,bud'an baki yayi yace "lallai mummy kinsah rigima.

Murmushi mummyn tayi sannan taci gaba da fad'in aikasan halin yaro sai ahankali, yaro yana da saurin saboda kamar yadda yake da saurin mantuwa,dan idan yaro ya riqe abu akansa zaka samu ba fiya mantawa ba,sai dai idan akayi rashin sa'a ya manta d'in toh kuwa da wuyah yasake tunawa.

Jinjina kansa yayi alamar gamsauwa da maganar mummyn,dan kuwa shima yasan da hakan dan baya raba d'ayan biyu yanzu Teemah tamanta da ko shi d'in waye ne agurinta.

Koda ya koma d'akinsa ma kwanciyah yayi bayan ya cire rigar da ke sanye ajikinsa,rigingine ya kwanta yana tina yarintar Teemahn,
Murmushi yasaki daya tino inda mummy tace wai Teemah tace mummy tak'irashi da yah Abbas ba Abbas ba,So ths stubborn girl bata manta dani da wuri ba kenan,take yaji yana ma son yaganta dakyau, dan duk haduwar da suka yi ba haduwar arzik'i bace tunda yazo gidan.so yake ya ganta da kyau yanzu.

Juyi yayi zuwa d'ayan b'angaren hannunsa,ya cigaba da tuno rayuwar da suka yi abaya,muguntar yarinyan nan har yanzu bai barta ba.

"Hmm" yace afili sanda ya tuno irin dariyar data k'yalk'yale dashi dan kawai taga daddy yana jamasa kunne.

Tashi yayi ya zauna ya d'au wayarsa yak'ira wani abokinsa.sukayita surutusu.Daganan ya tashi ya canza kaya sannan yabi jikinsa ya feshe da turarukansa masu dad'in k'anshi,wayoyinsan yasa hannu ya d'auka,ya fice daga cikin d'akin cikin tafiyarsa mai k'ayatarwa.

Gurin habibu ya nufah yaje ya anshi key d'in mota,da kansa yayi driving ya fice daga gidan zuwa inda zashi.

*ur comment is* *needed* 👌🏻

_Share pls_ ☝🏻

*Serlmerh* 😍
[10/2, 5:53 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
_my family_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Never let the experiences of your past bring harm to your future. Remember, your past can’t be altered and your future just doesn’t deserve the punishment.

🅿 *8*

Teemah kuwa tun fitar ta d'azun bat k'ara fitowa ba,bacci ne yad'auketa bayan tagama dariyar muguntar ta,ita adole in anbarta wai taga babba yanan kuka,"kai daddy ya iyah purnishment tafad'a cikin dariyar,nima fah haka mummy take min inna yi mata laifi,gashi nima yau daddy yarama min,Horhh daddy kabiya ni wallahi"
Chapter 7 · 0% Book details