← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 163

Sashe 87

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" _ai kariga kasan dalili, nasan baka manta ba, lokacin dana yi ta fama_ _daku kaida mahaifinka akan karka auri yarinyar kun saurareni ne?_ _ko kana zaton dama i ll give up so easily ne haka da har kayi saurin manta abinda_ _yafaru? .....Mahmud wannan da kake gani ita ce_ _za6ina agareka kuma har abada bazan canja ra'ayi ba, ko ka 'kyaleta ko ka illata ta_ _Munnira itace uwar 'ya'yanka bawata ba, dan haka kama kama kanka ka_ _nutsu banason hauka, duk abinda na aikata kuma ina yi ne_ _saboda kai, ai nagaya maka bana 'kaunar ganinka da yarinyar nan,_ _banaso, bazan iya juran ganin jinina na rayuwa da dangin matsiyata_ _ba_ .
_Kuma da kake batun ancutar da ita ka je ka tambayeta mana, ita tace tanason a tallafa_ _mata dan tana da bu'kata shiyasa na ha'da ta da 'kawata saboda akore mata_ _kishirwar dake damunta, bayaga haka me kuma na aikata agareta_ ?

Mahmud hawaye kawai yaji ya zubo masa na ba'kin ciki yanzun kam yasan Anty bazata ta6a canjawa ba yariga yasan tayi nisa tunda har ta iya tsayawa gabansa amatsayin sa na 'dan data haifa ta gaya masa maganganu son ranta gameda aurensa, ha'ki'ka yasan idonta ya rufe da tsanar da take yiwa dangin mahaifinsa wanda kwak'kwaran dalilinta nayin hakan bazata iya fa'da ba.

Har ya juya zai tafi sai yakuma dawowa gaban Antyn idonsa taf da hawaye ya furta " _Anty ki yafemin........_
_ni 'danki ne ke kika haifeni, albarkar ki dole in nema_ _adukkan al'amurana, ke da Abbah kun yi fama dani tun ina 'karami_ _har girmana..... kun bani dukkan gatan daya kamata, ban_ _ta6a yin kuka dan rashin wani abu ba, amma Anty ki_ _gafarceni..... wannan karon bazan iya 'dauka ba, bazan iya zuba_ _ido ina gani aci zarafin yarinyar da bataji ba batagani ba..... zuciyan_ _Fateemah awanke yake tas bata da hakkin kowa dan haka bazan bari_ _acutar da ita ba , kicewa Abbah na ya yafemin idan ya_ _dawo Anty_ "

Be 'kara magana ba ya juya ya tafi yana share hawayen sa daya kasa controlling 'dinsu.

Yariga ya sanyawa ransa cewar zai 'dauke Fateemah su bar Lagos bari na har abada, zai yiwa Anty nisa, nisan da zai sa ta harse ta manta da kalar fuskan Fateemah ma balle rayuwarta, abu 'daya zai iya dawo dashi shine Abbahn sa, yanaso yasake ganin Abbah kafin yatafi sai de hakan baze samu ba dan haka dole watarana ze dawo kawai domin Abbahn sa.

Tafiya yake yana share hawaye, damuwarsa gaba 'daya ya tattaro ya taru masa akan idanunsa zuciyarsa kuwa cike take da hanzari jiyake ko awa 'daya ba ze iya 'karawa acikin garin Lagos ba, zai 'dauke matarsa suyi nisa yanda ze nisanta ta da dukkan ma'kiyanta.

Kwakwata ma Mahmud mantawa yayi da cewan yana driving ne, ya manta duk wani doka da tsarin tu'ki abinda ya dameshi ne ka'dai yake yawo a 'kwa'kwalwar sa.

Be ta shi sanin hakan ba har se da yaji 'karan wani horn ha'de da taka birki me 'karfin gaske take ya rikice yarasa me ma zaiyi dishi dishi idanunsa suke gani hakan ya sa be ma lura sosai da gabansan ba bayan 'karan da ya ji be sake gane komai ba, kafin ya ankara kuwa rabin motarsa tashige 'kar'kashin wata babbar motar da ke gabansa .

Mafiya yawan mutanen dake gurin Hannu kawai suka 'dora akawunansu wasunsu na fa'din " _jesus crist_ " yayin da tsirarun su ke maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ ..............

_Comment vote and_ _share pls_ 🤞🏻

*Salmerh ce*😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_People change, love hurts, friends leave, things go wrong but just remember that life goes_ _on........Love_ is _so strange.......Sometimes it becomes reason to live life and sometimes to leave life._

🅿 *66*

Umar na tsaye jingine da jikin mota, Fateemah kuwa na gefe har yanzu 'kirjinta rungume da kayan Munnira idanunta banda ruwan hawaye babu abinda yakeyi, ita kanta bazata ce ga abinda ke sata kukan ba amma yanayin datake jin zuciyarta ayanzun shi yafi komai 'daga mata hankali, tare da karya mata zuciya.

Abbas ma tsaye ya juya musu baya, sam baya son ganin hawayen Fateema koka'dan hakan na matu'kar soya masa zuciya, baya jin cewa ha'duwar su da Mahmud ze yi kyau koka'dan, jiyake kamar babu wanda ya ta6a 6ata masa rai kamar Mahmud 'din aduk fa'din rayuwarsa ,hannunsa 'daya cikin aljihunsa yayinda 'dayan yake ri'ke da wayarsa bayan ya gama 'kiran Mahmud yaga baya 'dagawa, ransa duk a6ace shi tunaninsa yabashi akan Mahmud ya'ki 'daga wayar ne dagangan dan kawai ya wula'kanta Fateemah .

*****
Cikin 'kan'kanin lokaci mutane suka zagaye wurin kowa na fa'din albarkacin bakinsa, da 'kyar akasamu aka ciro motar Mahmud 'din daga 'kar'kashin 'dayan motar se da ma suka 'daure motar Mahmud daga baya 'dauri sosai yanda ba ze motsa ba, tare da jan babban motar zuwa baya ka'dan sannan akasamu aka raba tsakaninsu.

Da fitowar Motar Mahmud 'din kuwa sai da kowa jikinsa yayi sanyi wasu ma kauda kansu sukayi dan baza su iya kallansa ahaka ba.

Sai da ambulance yazo kafin aka ciro shi tare da duk wani abu nashi na amfani dake cikin motar aka me dashi cikin ambulance 'din zuwa asbiti.

Tun a cikin ambulance aka fara bashi taimakon gaggawa har zuwa asbitin suna zuwa kuwa aka wuce dashi A&E (Accident & Emergency) likitoci kusan uku ne suka ha'du akansa domin ceto rayuwarsa cikin gaggawa.

Da 'kyar suka samu suka daidaita numfashinsa tare da yi masa dressing 'din raunikan daya samu.

Bayan hakan ne wani daga cikin wa'danda suka taimaka masa har zuwa asbitin da kuma drivern babban motar da wani likita sune suka fara neman wanda zasu 'kira cikin 'yan uwansa.

Misscalled 'din _Oga_ _Abbas_
Suka fara gani da be wani da'de da 'kiran wayar ba dan haka shi suka fara dannawa 'kira.

Abbas na tsaye a inda yake tsayen tun 'dazu be motsa ba, ya dai 'kira layin mahaifinsa yasanar dashi cewa yashigo Lagos sannan ya'kira wani abokinsa ma sukayi magana, daganan yaci gaba da tsayuwa jira kawai yake yi yaga zuwan Mahmud gidan tunda kam baya office dole ai idan yagama abinda yakeyi 'din gida ze dawo.

Wayarsa ce tafara 'kara alamar shigowan 'kira, yana 'dagota kuwa yaga sunan Mahmud na yawo a fuskar wayar.

Da sauri Abbas ya amsa 'kiran tare da yin shiru danjin wace 'karya Mahmud ze shirga masa.

Ga mamakinsa kuwa sai yaji ba muryar Mahmud bace ke tashi acikin wayar yake fa'din " _hello_ !
_helloo_ !!

Da mamaki da kuma izzah Abbas ya amsa da fa'din " _Yes, who is on the_ _line_ ?

Bayani aka yi masa akan abinda yafaru ata'kaice.

Sosai Abbas yaji zuciyarsa ta karye da jin al'amarin amma be nuna afili ba yanda zasu gane koda ya juyo ma cewa kawai yayi da Umar su shiga mota suje wani guri.

Har se da suka hau titi kafin Abbas ya sanar da shi asbitin da zai kaisu.

Teemah kam bata magana sai aikin hawaye bugun zuciyarta ne yasake 'karuwa fiye ma dana baya koda suka isa asbitin ma ita da 'kyar take ciran 'kafa take binsu abaya domin gaba 'daya 'kafafun nata nawi suka yi mata, hakan ma bata ji abinda yafaru gaba 'daya ba dan har suka isan Abbas beyi musu bayani cikakke ba, zuciyarta ce ke gaya mata cewan Mahmud ne ya illata Munnira shine har aka kawota nan shiyasa suka zo.

Daga Abbas sai suka 'kira layin Abbah shima sukayi masa bayani.
Hankalin Abbah ba 'karamin tashi yayi ba dan shi baya ma 'kasar dan haka ya 'kira Anty ya sanar da ita sunan asbitin yace taje ta duba halin da Mahmud ke ciki kafin ya dawo, yace mata zuwa anjima shima ze dawo insha Allahu.

Isan su Abbas keda wuya sai ga Anty ma ta taho itada da Munnira dayake har alokacin basu rabu ba suna tare lokacin da Abbah ya 'kira Anty.

A reception suka zauna gaba 'daya suna jiran ji daga likitocin, domin sun ce sai zuwa nan da 30mins zasu ganshi kafin nan an 'dan kintsa shi kuma watakila ze farfa'do ya dawo hankalinsa.

Duka abin nan dake faruwa
Abbas da Umar ne ka'dai suka sani shima Umar 'din be da'de da samun labarin ba,bayan isowansu ne suka je tare wurin likitan inda shi yayi musu bayanin komai, Teemah kam har yanzu bata san abinda yafaru ba.

Shigowarsu Anty ne ma ya 'dan fara bata mamaki ganin ta tare da Munniran ga kuma Antyn hankalinta duk atashe.

Da farkawar Mahmud kuwa doctor ya basu damar shiga su ganshi, nan suka shiga gaba 'dayansu zuwa ciki.

Anty ne ta wuce gaba da sauri ta isa gaban gadon tana 'kiran sunan shi.

Wanda Teemah ma sai alokacin ta farga da wanda ke kwance agadon, ai bata san lokacin da ta zubar da kayan dake hannunta ba ta taho da gudu itama tana fa'din " _Yah Mahmud kaine anan?_ me _yasameka haka,Yayah Mahmud dan Allah ka tashi, ka tashi kaga Yayah Abbas yazo_ ?"

Anty na kuka tana 'karawa tare da kamo hannunsa wanda be samu raunin sosai ba, Teemah ce tashiga tsakaninsu dan ita ta na zuwa sai ta shige gaban Antyn tana kukan fitan rai.

Abbas da Umar kam tsayuwa sukayi suna 'kara jinjina al'amari na ubangiji, Umar tunani yakeyi awanni 'kalilan da suka wuce rabuwarsu da Mahmud yana cikin 'koshin lafiyarsa, sai gashi yanzu kwance agado cikin yanayin da bama ze iya fasaltashi ba.

Ahankali ya bu'de idanunsa ya sau'ke su akan Teemah gefe da ita kuma Anty ce yaga dukkan su suna kuka.
Ga Munnira ma daga 'dayan 6angaren itama tana share hawaye, can tsaye kuma Umar ne shida Abbas da rabuwarsu yanzu kusan wata uku kenan.

Murmushi yayi tare da motsa hannun nasa da 'kyar ya ri'ke hannun Fateema dake risgar kuka iya son ranta.
" _Yah.....Mahmud me yasame ka haka?....._
Teemah tasake fa'da cikin kuka.
Chapter 87 · 0% Book details