← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 163

Sashe 5

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Dakin suka koma fanni tamata wanka kafin su gama kuwa tasha surutu kuma duk hirar yayah ake tayi mata.
Itama fannin ta biyeta,suka tayi tare.

'Dakin mummyn suka dawo bayan fanni ta shiryata.

Mummy naganin sun dawo ta mi'ke tace suje suci lunch dan tana so ne ta'dan fita.

Harsun zauna anfara zuba abinci teemah tace ita kam a'a bazataci abinci ba pineapple ta keso.

Jin haka yasa mummyn ta fara mata masifa da 'dagun murya akan rashin son cin abincin data koya.fanni ce ta tuna da fruits 'din da Abbas ya kawo 'dazu kafin ya tafi.
Bata yiwa mummyn magana ba illah zuwa datayi ta duba,cikin sa'a kuwa tasamu pine apple 'din aciki.shikadai tadauka ta feresa mai kyau sannan ta dauko takawo wa Teemahn.

Sai da taka wo sannan mummy ta tuno dashi,Ashe fah Abbas yasiya mata kafin yatafi kamar yasan ma zata musu rigima akai.

Haka ta wuni tana shan abinta taqi cin abinci.

Da lokacin islamiya yayi habibu ne yakaita ya dawo da ita kuma.

Har washe gari bata wani damu da rashin Abbas 'dinba,don ita duk atunaninta alluran yatafi dagaske kamar yanda ya sanar da ita.kuma ai yace mata sai ya warke sannan zai dawo..........

Dataga lokaci yafara jah ne sai tafara takurawa mummyn akan ina yayan yaje?,mai yasa ya'ki dawowa?

Tun mummy na ce mata yatafi alluran itama kamar yanda Teemahn ta 'dauka harta gaji ta tafara ce mata ya tafi makaranta ne bazai dawo yanzu ba.

*Serlmerh-md*
@ *wattpad*

Vote nd share pls 👌🏻
[10/2, 5:49 PM] Ummiyo: [3/14, 10:26 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated to sister Safiyyah😍Allah yabar zumunchi.🤝

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *5*

Tun lokacin da Abbas ya tafi kuwa Teemah bata ta6a mantawa dashi ba,don mafi yawancin lokuta idan ka ta6a ta ko kamata wani abin takance "sai nagaya ka/ki da yayah,koda kuwa amakaranta ne ko gida,harta mummy da Daddy basu tsira ba,suma abu kad'an sai tace sai ta fad'awa yayah dan ita azatonta har yanzu watarana zai dawo.

Mummy bata ta6a kuskuren had'a su awaya ba don acewarta daga ta gwada k'ira mata shi sau d'aya tasan Teemah ta ringa damunta kenan kullum,shiyasa bata ma fara ba,duk da basu fasa waya da ummahn Abbas d'in ba suna wayarsu kusan kullum, haka sometimes mummy kan bata labarin irin rigimar da Teemahn keyi akan rashin ji daga Abbas d'in da batayi ba har yanzu,dariyah kawai kowaccen su keyi daga haka su shashantar da zancen.

Akwai ranar da ta ta6a saka mummy agaba da kuka wai dole suje gurin yayanta,mummy tarasa yazatayi da ita ta ce mata ai alluran nasa bai k'are ba"kuma in yak'are zai dawo da kansa,amma sam ta'ki yadda.ita wai dan dole suje su kawo shi gida,

Haka data dage sai da mummy tayi wayar k'arya ta tambaya awayar ta ce "abbas nake nema?

"Aw baya kusa?

Alluran haryanxu?

Owk toh shikenan inya dawo ace masa Teemahn shi ce ta ke nemansa.

Da mummyn tacire wayar akunnenta sai tace mata
" ai wai bayanan amma alluran ma yakusa ya k'are kuma idan ya k'are zai dawo.

Ai Teemah najin haka tafara dariyah ta fad'a kan cinyar mummyn.

Salati mummy tafara kamar gaske ,
Kai abbas d'in nan bayajin magana ,ashe yawo yatafi abinsa ya kyale angel d'ina agida.

D'ago kai Teemah tayi ta kalli mummyn

"Mummy ke ba yayanki bane?

"A'a Teemah" mummyn tafad'a sannan ta sa hannu ta d'ago Teemah ta tsayar da ita agabanta.

"Mummy yah abbas fah sunansa ke kuma kina ce mishi "Abbas"

Kumatunta mummyn takama duka 6angare biyun tana mata murmushi.

Teemah "Abbas d'ana ne ba yaya na ba.ke kuma kinga ai ke k'arama ce.K'anwarshi ko?

Kai TEEMAH tad'aga wa mummyn tana d'an smiling itama.

"Yauwa my angel
"maza jekiyi home work d'inki ko"
mummy is sleepy"

Da haka mummy tasamu ta kora ta daga wurinta dan tasan inba hakan tayi ba to hirar bazai ta6a k'arewa ba.

Teemah da fara'arta ta fita daga d'akin mummyn ta nufi nata.Yau farin ciki ta keji har aranta don yayah yace zai dawo in allurarsa suka k'are.

Ai kuwa daga ranar tafara lissafin ranar da abbas d'in zai dawo.ita kadai tayi ta ware rana amma kullum shiru ba labarinsa.

"Mummy gobe yayah zai dawo ko"?

Kullun sai tambayi mummyn,amsar mummyn kuwa baya wuce "bansani ba nima Teemah"dan bata so tafiye yi mata k'arya.

Inkuwa daddyn ta ne zai fita ce mas take yi idan yaje yadawo mata da yayah!

Shima cemata yake toh,inya dawo ta kuma tambayarsa kuma sai yace ai basu had'u bama da Abbas d'in.

Itama Teemah tun tana damuwa harta zo tadaina damun kanta akansa,takance "ai ba ruwana da yayah yanzu tunda ya manta dani yah daina sona" haka ahankali harta ha'kura ta manta dashi ma gaba 'daya,abinku da yarinta.
Hakan da yafaru kuwa ya matu'kar samawa mummy lafiya,dan acewarta itama ta huta da fitina.

Har ta gama primary tashiga Js class amma Abbas bai 'kara dawowa gidan su ba itama kuma ba'a ta'ba zuwa abuja da ita ba.Kuma zuwa wannan lokacin kwata kwata ta manta da tarihin rayuwarta tare Abbas d'in,tadai san tana da 'dan uwa amma ko da a photo taganshi bagane shi zatayi ba.

Tana Ss1 wata ranar jumma'ah tadawo gida dayake dawuri ake tashinsu. In ranar Friday neh,motar su na shigowa ta hango wata sabuwar mota a wajen parking bata san me motar ba,dan haka ta shiga parlourn da sallamarta,Daddyn Abuja tagani azaune shi kad'ai a parlourn yana waya.da fara'arta ta k'arasa inda yake zaunen ta zauna kusa da shi,daga inda ta ke zaunan tana iyah jiyo muryar wanda suke magana da daddyn,tana jin irin yanda yake yiwa daddyn nata.
Kauda kai tayi tare da ta6e baki.

Daya gama da wayar ne ya kalleta ya ce "uwata kin dawo ne"

Dariyah tayi kad'an tace "nadawo daddy ya hanya yah 'yan Abuja?

"'Y'an abuja gaba d'aya "dadyn ya tambayeta.sannan yacigaba da fad'in mamana fah ashe an girma"

Kunya taji da sai tad'an rufe fuskarta da hannunta.
Daidai nan kuma daddynta ya fito cikin shirin sa na fararan kaya.

Sai da ya iso ya zauna akujerar da take fuskantarsu kafin yace mata "ya akayi ne baga kin dawo da wuri?"

"Daddy yau fa friday kamanta ne,"

Ohh sorry haka ne fah,ashe dawuei kuke tashi,"

Na zaci ai ganin daddynki kika dawo kiyi dan kinji yazo" ya fad'a mata da sigar zolaya.

Toh aini bansan ma yadawo ba daddy waye zai fad'amin nida nake makaranta.

Nasani ne angel "
Ko daddyn naki ne yasanar da ke.

Dariya sukayi gaba d'aya daga nan ta tashi ta d'auki jakarta "daddy ina zuwa "
Tafad'a tare da barin d'akin.

Parlourn mummy tafara zuwa tana yin sallama taga ummah azaune au da mummy,yada jakar tayi ta tafi da gudu tafad'a kan cinyar ummahn tana dariyah,
"ummah na ashe harda ke akazo shine daddy bai gayamin ba?

Ai gani kinganni"

Ummahn tafad'a tana maijin dad'I har cikin ranta yanda Teemahr take sonta.

Gaida ummahn tayi tare da yimata ya hanya amma still bata bar jikinta ba.

Mummy ce tace mata
"Ai se ki d'aga ko tunda hankalinki ua kwanta,da wanne zataji da gajiyar hanya ko kuma da nauyinki"

"Katuwa da ke sai son jikin tsiyah"

Ai tana jin haka ta turo baki gaba
[3/14, 10:28 AM] 🌸Salmerh🌸: "Ummah wai ni k'atuwa ce inji mummy"!

"Kyaleta mamana bawani k'atuwar da kike"Kawai dai tana fad'a ne.

"Hakama fah d'azu
naji wani ma babba dashi yana yiwa daddyn Abuja shagwa6a awaya"amma ni sai mummy tahana ni tace min wai ni k'atuwa?
Tak'arashe da turo baki gaba.Dariya ne yaso kama ummah dan tasan wannan sai aikin Abbas.

Amma afili bata cewa Teemahn komai ba illah
cigaba datayi da lalla6ata harta hak'ura.

mummy kuwa kauda kai tayi sannan tace "rashin aiki dai"

"Ai in kika biye ta wannan zaki sha fama"
mummyn tafad'a tana mai nuna Teemahr da baki.

Murmushi sukayi ummah da Teemah dajin abinda mummy tace, mummyn kuwa ta ta6e baki.

Tashi tayi daga kan cinyar ummahn ta zauna sannan tasa hannu ta d'auki d'aya daga cikin abin ta6awan da aka ajiye wa ummahn.

"Ummah bari na watsa ruwa in dawo"
Da toh ummahn ta amsa mata,ita kuwa tuni ma takusa barin parlourn.

Sai da ta cire kaf d'in kayan uniform d'in dake jikinta sannan tafara k'ok'arin neman abinda zata d'aura ajikin nata amma bata samu ba,
tana daga tsayen tafara kwalla k'iran Baabah lami mai aikin gidansu na yanzu,bakinta biyu kafin tayi na ukun baabah lami ta amsa mata tare da tahowa d'akin,bata tuna ba kaya ajikin ta ba harse da taji motsin tafiyar Baabah Lami d'in kusa da d'akinta kafin ta tuna,hijab d'in makarantarta ta d'auka tasaka akanta ko gwiwa ma bai rufe mata ba,amma dai yafi babu.
Da sallama Baabah Lami ta shigo d'akin
Tun kan ma ta gama shigowa Teemah ta jefa mata tambayar

"Baabah Lami banga Towel d'ina ko d'aya ba."?

"Aw suna baya bakince a wanke miki su ba".

"Owk toh anwanke d'in ne ?

"Ehh anwanke"

Baabah Lami d'in ta amsa mata dashi. Sannan ta k'ara da fad'in barin je inkawo miki.Daga nan tajuya tafita daga d'akin.

Dayake fanni tajima dayin aure hakan yasa tabar aiki agidan nasu sai aka samo musu wannan Baabah Lami d'in.

Baahbah Lami bawata babba bace don bazata wuce 27/28yrs ba amma dayake bazawara ce,yaranta hud'u kuma sune suke k'iranta da wannan sunan wato Baabah Lami hakan yasa sunan yabita kowa ma haka yake k'iranta da shi yanzu.

Koda Baahbah Lami ta kawo towel d'in azaune tasame ta abakin gado tana kallon fuskarta acikin d'an madaidaicin mirrorn dake rik'e a hannunta.Daganin Baaba Lami d'in kuwa ta tashi ta kar6i kayan ta,tsayuwa tayi har sai da taga baabah Lami tafita taja mata k'ofar kafin ta cire hijab d'in kanta ta d'auki towel d'aya ta d'aura ajikinta, sauran kuma ta ajiye su a inda tasaba ajiyewa sannan ta d'auki wani fari k'arami daga ciki ta rik'e ahannunta kafin nan tashiga bayin.

Ta 6ata ak'alla kusan 40mins a wanka da yin shirinta kad'ai.
Chapter 5 · 0% Book details