← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 163

Sashe 42

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lullu6e kwalin yake da wrapping sheet baka gane kami game da kwalin faa ce size 'din kwalin.

Sai da ya kai dubansa inda yaga mummy ta nufah 'dazu sai yaga hankalinta gaba d'aya baya wani guri aikin dake gabanta kawai ne tasa agaba ga da alama a'kage take taga aikin ya kammala ganin hakan dayayi yasa ya taho da sauri ya nufi 'k'ofan babban parlour, amma cikin rashin sa'a daf dazai shiga parlourn idanun mummy ya hango shi akaro na biyu, hannunsa ta duba da wuri ganin cewa yana ri'ke da abu ahannun sai dai bata wani gane abun ba sai tayi zaton ko jakar kayansa ne.

Da yake yasan kan gidan sosai batare da an jagoran ce shi ba sai ya wuce direct 'dakin Teemah ya ajiye kwalin dake hannunsan kafin ya mi'ke tsaye sai da ya tsaya ya 'karewa 'dakin kallo kaf kafin ya fito ya nufi 6angaren daddyn.

Koda yaje 6angaren daddyn kuwa sallama yafarayi sai yaji shiru ba'a amsa masa ba, sai da ya sake yin wata sallamar sau d'aya yaji still ba'a amsa ba sai ya d'an tsaya na 'dan da'ki'ku, 'karan TVn daya jiyo ne yasa shi fahimtar dalilin dayasa daddyn be ji amon muryarsa ba, kuma yana da yak'inin cewa koda zai yi sau ba adadi ne daddyn bazai ji ba matuk'ar TV d'in akunne yake.

Sanin cewa daddyn shi d'aya ne acikin 'dakin yasa ya tura k'ofar tare da sake yin wata sallamar ciki-ciki, ahankali ya maida 'kofar ya rufe bayan ya shigo d'in, sai ya tsaya kamar an bashi umarni, daddyn ya tsaya yana 'karewa kallo yanda yasha manyan kaya yawani fito shar dashi tamkar wani sabon matashi.

Ahankali yafara takawa yayinda salon tafiyar tashi ya matu'kar amsan zubi da tsarinsa ga duk wanda yasan menene had'uwa toh ba sai na gaya masa yana kallon Abbas yasan cewa ya ha'du sosai, be tsaya ko'ina ba sai dayaje gaban TV d'in kafin ya tsaya, sai dai kuma be bari daddyn yaga fuskarsa ba,baya ya juya wa daddyn da sauri ya maida fuskarsa take fuskantar inda bangon da TVn yake bayansa kuma na kallon daddyn.

Daddy da bai san anshigo bama balle yasan waye ya shigo kawai sai yaga mutum tsaye ya tare masa news d'in dayake gani, lumshe idanunsa yayi dayaga hakan tsawon dak'ik'a goma kafin ya bud'e tare da fad'in " _ABBAS_ " .

Dariya Abbas d'in ya kwashe dashi sannan ya juyo yafara tahowa zuwa inda daddyn ke zaune.

" ya akayi ka gane ni da wuri haka daddy bayan baka kalli fuskata ba " ya tambaya yana kallon daddyn bakinsa d'auke da murmushi.

" toh wa nake dashi da zai min haka banda kai"

Daddyn ma yabashi amsa yana murmushin shima.

Dukka sai suka yi d'an takaitaccen dariya.

sai daddyn ne ya kuma cewa " ja'iri daga ina haka kamar an jeho ka?"

" wallahi kuwa, escaped nayi daddy yau d'innan za koma ma kafin anemeni, ba shiri nataho kuma akwai ayyuka agabana".

" haba kuma sai kace dole ai daka bari zuwa wani lokaci in kasamu isasshen time basai ka zo ba."

" ba na so na.....,,.

Daidai nan mummy tashigo da sallamarta abakinta.

Sai Abbas d'inma ya dakata daga maganar da ya yi niyyan fad'i duk sai sukayi shiru suka jira harta iso ta zauna.

Barka da isowa tayi masa tare da fad'in " dazu ina sauri bamu wani gaisa da kyau ba ".

Murmushi yayi mata kawai sai ta sake fad'in " gaskiya ka shammace mu Abbas gashi bansan da zuwanka ba ko muhalli ba'a gyara maka ba" .

" Ai ba komai mummy ina ma kan hanya ne yanzu zan wuce"

" dawuri haka?, ka de bari ka 'dan huta ka'dan de ko,ai nayi zaton ma graduation d'in kazo halatta dana ganka"!

Abbas cewa yayi wai " a'a shi yama manta da wancen batun ai tuntuni tun bayan data sanar da shi abin be kuma zuwa kansa ba.".

Su kuwa duk sai suka yadda akan ehh dagaske yamanta d'inne ba mamaki ko dan saboda irin aikinsan,wani lokaci abubuwa kansha kan mutun sosai.

Abinci aka shishshigo dashi da abin sha aka jejjera sai da aka gama sannan mummy tace toh bismillah ya d'an samu ya ta6a ko kad'anne ma kafin ya wuce d'in.

Dukka atare suka mik'e har daddyn suka nufi wajen da aka jera abincin, mummy na zuzzubawa tace

" kamar kuwa kasan kullun sai anmin mita agidan nan, harda su kaiwa 'kara na wai bana bata waya kuma kaima baka tambayarta ko ka 'kira wayan ".

" daddy ne ya kar6e da fad'in toh dah d'in 'karyane?, ai da gaskiyarta" , daganan sai ya dawo da dubansa wurin Abbas yace " me yasa baka tambayarta awaya idan ka'kira kuma ko sa'kon agaishe ta ma baka ta6a fad'a ba."

Dukkansu sai maganar daddyn da yanda yayita kamar titsiye sai ya basu dariya, shima daddyn sai ya taya su dariyar, sai da suka tsagaita kafin yace

" toh haka nayi al'kawarin zanyi ku kuma naga kuna min dariya".

Abbas baiyi magana ba sai mummy ce tace "ai idan kabiye Teemah kam abinda yafi haka ma zakayi shi".

Murmushi sukayi daganan suka fara cin abincin da mummy tagama zuzzuba musu, mummyn kuma tafita abinta ta basu waje tatafi domin ta shirya.

Abbas na gamawa yacewa daddyn shi zai wuce dama ya shigo ne brief ya gaishe su, cikin sa'a ma kuma saiya samu daddyn nagida.

Albarka da addu'o'i sosai daddy yata yimasa sannan ya rakoshi har wajen parking inda drivernsa yake, tambayar drivern daddy yayi wai anya kuwa yaci abinci yace" ai be san cewa tare suke ba da an masa iso shima", sai ya 'daga hannu ya d'an mari 'keyar Abbas yace " ai duk laifin kane dabaka fa'da cewa dawani kuke ba "

Abbas 'kasa ya d'anyi kad'an tare da shafa gurin kamar irin yaji zafin nan, sai yace " Afuwan daddy Allah na manta ne shiyasa".

Murmushi sukeyi gaba d'aya har drivern ganin yanda Abbas yake yi agaban daddy kamar bashi ba amma idan awurin aiki ne ko ha'koransa da wuya kake gani.

Sai drivern ma yace " yalla6ai aina ci abinci Hajiya ta aiko an kawo min anan"

" Ahh toh shikenan sai ya juya ya kalli Abbas d'in ya sake cewa "Allah ya taimakeka da sai ka jira yaci abinci duk da saurin naka".

Abbas da daddy kawai yayi sallama ko mummyn be jira sun sake had'uwa ba yayi tafiyarsa.

_Comment,vote and_ _share pls_ 🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

⚠ *NOT EDITED*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

SMILE ….. It irritates those who wish to destroy you.

🅿 *36*

Suna fita ya fad'awa drivern sa inda yake so ya kai shi, koda suka je kuma basu tarar da kowa ba face mai gadi.

Zuwa yayi ya mi'kawa mai gadin hannu suka gaisa sannan ya tambaye shi inda 'daliban suke take mai gadin ya sanar dashi.

Abbas godiya yayi masa tare da juyawa ya koma cikin mota driver yaja suka nufi wajen.

Da kwatance drivern ya gane wurin koda ya isa yayi parking a wurin Abbas kamar bazai fito ba kusan 10:mins kafin ya 'daga hannu ya duba agogon dake hannunsa sai yayi maza ya fito daga motar.

Tsaye yake jingine ajikin motar yana ta 'karewa 'dai'dai kun mutanen dake wulgawa kamar me karantar wani abu tattare dasu.

Tafiya ya fara cikin 'kasaita in ka ganshi zaka zaci daga wani gidan sarauta yafito, ahankali yake tafiya ya nufi hall 'din daya fi tunanin nan ne ake programme d'in dan anan ya ga anfi taruwa.

Daf da zai shiga hall 'din daga gefe ka'dan ya idonsa ya hango masa ita cikin gungun 'dalibai sunata surutu ga dukkan alamu shirin yin pix suke yi ko kuma har sun 'dauka domin dukkansu zagaye suke da photo grapher ne.

Tsayuwa yayi kamar andasa shi awurin shi bai shiga ba shi kuma be matsa daga inda yake tsayen ba.

Be san mai suke tattaunawa atsakaninsu ba shi dai kawai sai yaga ta fara dariya, yayinda da dariyar tata ta matu'kar birgesa, sosai ya tafi da yanayin tsari da kwalliyar da ta tsantsara ayau d'in.

Aransa sai yaji kamar tunda yake da ita be ta6a ganin kwalliyar sata amsheta irin wannan ba.

Yanda ya 'kura mata idanu sai ajikinta taji tamkar ana kallonta, tana cikin dariyar sai ta 'dan fara dube-duben gefen ta.

Garin dube-duben nata sai idanunta ya hango shi take kuwa idanunsu ya sar'ke cikin na juna, Abbas lumshe idaunsa yayi ita kuwa bata gane shi ba koka'dan saboda akwai 'dan rata atsakanin su kuma bata ta6a zaton ganinsa awannan lokacin ba, hakan yasa kawai tayi masa kallon kamar tasanshi sai ta kauda kanta gefe da sauri.

Sai de kuma sam taji zuciyarta takasa nutsuwa da hakan sai ta 'kara juyawa ta kallo wurin, wayam tagani babu kowa abin ya matu'kar bata mamaki hakan kuwa yasa tafara tafiya ahankali ta baro cikin mutanen.

Tsoro ta fara ji kardai ace ba mutun tagani ba yanzun, amma ace daga ganin mutun sai kuma tarashi.
Allah yasa dai mutun ne inbahaka ba ai nashiga uku!
Haka taketa nanatawa azuciyarta,yayinda tsoro yake 'kara cika mata zuciya aduk wani step 'dinta.

Caraf taji ancafko hannunta tabaya,wani firgita da tayi shi kanshi sai da yaji wani iri, tana shirin k'walla ihu sai yasake hannun nata dawuri ya rufe mata baki da hannun.

Bakinsa ya matsar daidai kunnanta ahankali yace mata " bana son hauka ki juyo ki ganni I'm your b...........

Sai kuma yayi shiru ya 'kirasawa, ido ta zazzaro waje dan tana jin amon muryarsa tagane shi, muyrasa ko acikin dubun mutame zata iya ware shi.

Bakintan daya rufe yasake mata, yana sakewa kuwa ta juyo da sauri ta fuskance shi, da 'karfi tace " Yah Abbas kaine dagaske"?!

Tsaye yake agabanta ya maida hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya 'kurawa fuskarta idanu tamkar yau ne farkon ganinsa da ita.
Chapter 42 · 0% Book details