← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 163

Sashe 31

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan shiru bakowa bakuma motsin komai dayake ba yara k'anana ne agidan ba ballantana aji hayaniyarsu kuma mummy ma bata nan balle ko k'aran TV ne taji, sai kawai tata shi itama ta fito agidan da niytar fita amma harta kai k'ofar fitan kuma sai taji ranta na 6a ci da fitan kuma ma taka mammiyan inda zataje ma bata sani ba, sai kawai tajuyo ta dawo gida.

She feels like tayi kuka amm bata son ta 6ata hawayenta abanza tunda shima yayan bai damu da ita ba so no need ta ta zubda hawayenta akansa duk da tana ganin idan ba kukan tayi ba sam bazata ji ta normal ba, baza ta ji kanta daidai ba.

*****
Hak'ik'a sabo baida dad'I kokad'an kuma Abbas bak'aramin nasara yaci ba akan Teemah dan wannan tafiyarsa tasa ta matuk'ar jijjiga ta, sosai yashiga jikinta har tana jin kamar tunda take bata ta6a missing d'in wani abu kamar haka ba.

Mummy kanta abin har yaso yafara damunta ganin yanda Teemahn nata ta dawo, kwata-kwata ta canja gaba d'aya kamar ba ita ba, zakayi mamakin inda rashin jin Teemah yatafi wata kalar shiru-shiru tadawo, dayake abin ya had'u mata da girma sai suka had'u da kewar yayanta da kuma girman data yi sai ya haifar mata da wata natsuwa taban mamaki.

Duk wanda yasan Teemah ada idan yaganta yanzu tokuwa yasan ta canja gaba d'aya, bata fiya magana ba yanzun takan zauna tayi shiru na fin awa biyu batare da ko kyaky-kyawan motsi tayi ba.

Wani lokaci mummy tayi ta mata magana amma bazama tasan tanayi ba, makaranta kuwa tsakaninsu sai dai ido idan kaga tayi doguwar magana toh kuwa sai dai in abin yazama dolene sannan takeyi, ko ma menene akeyi ko akayi her only answer is "ehh ko a'a" wani lokaci kuma tayi anfani da wani sassa na jikinta domin tabbatar da abinda takeso agane.

Sabon salon miskilancin nata har classmates d'inta suna mamaki da hakan dan Teemah sune irin class disturbance d'innan amma cikin k'ank'anin lokaci duk wancan halayyar ta kau.

Yanzun kam takan zauna taci abinci 3square meal d'innan baya wuceta ,takan ci dai koda babu yawa ma musamman idan ta tuna da alk'awarin data yiwa Yayan nata sai take daurewa tana d'an kiyaye abubuwan daya sa ta alk'awarta masa akan zata nayi, tunda tasan matsayi da kuma girman alk'awari duk da yanzun tanaji kamar ta tsani yayan nata har zuciyanta amma hakan bazai hana ta kasa cika masa alk'awarin data d'aukar masa ba.

Abbas kuwa suna waya da mummy ko ranar daya bar damaturu ma bayan ya isa gombe yak'ira ta haka dazai wuce ma saida ya k'irata kusan ma kullum sai sunyi waya da mummyn nata inda mummy a kullum take binsa da addu'ar sa'a da kuma kariya aduk inda yake tana kuma k'ara masa tuni akan addininsa da kuma rk'o da gaskiya da amana tare da kwatanta adalci aduk inda rayuwa tajefashi.

Babban dalilin daya sa Abbas ke yawan k'iran mummy kenan saboda baya so akullum yayi missing d'in addu'ar data ke yi masa, sosai hakan ke masa dad'i amma abin mamaki bai ta6a tambayar Teemah ba koda wasa, ita kuwa hakan sai yake k'ara bata haushi, daga baya ma inta ga suna wayar sai ta tashi tayi wucewarta indai tana tare da mummy alokacin inkuwa bata wajen ma shikenan.

Koda Daddyn ta yadawo shikansa yayi mamakin canjawarta dayake bai samu yadawo a washegarin ranar da Abbas d'in yaje Gomben ba saboda wani issue daya rik'esa kusan 3days yak'ara bayan sunyi sallama da Abbas d'in.

Shi da kansa ya jawo Teemahn jikinsa ahankali da lallami yake tambayarta ko wani abu ke damunta dan yanda yaganta d'in bak'ara min mamaki yayi ba, amma tace masa ba komai yayi tambayar har ya gaji amma bai samu gamsashiyar amsa daga gareta.

Daga baya ne bayan sun ke6e da mummy yake sake tambayarta me yasamu Angel d'insa yaganta bakamar yanda yasaba ganinta ba, sai mummy bata 6oye masa ba ta sanar dashi cewa Teemahn tadawo hakane tun bayan komawar Abbas wajen aikinsa.

Dariya daddyn yayi sannan yace " ta gaji mamanta kenan"

Cike da mamaki mummyn ta d'aga kai ta kalle sa, sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.

Yakuma k'ara da fad'in kin manta da k'yar nasamu kika dawo hayyacinki lokacin rabuwarku da Alh.Yusuf?"

"Murmushi kawai mummyn tayi masa dan kokad'an bata so ta tuna baya shiyasa bata k'ara furta wata kalmah ba ta basar da maganar kawai.

Babu wanda yakuma kulata akan maganar kowa sai ya k'yaleta dan sun san na lokaci k'ank'ani ne zata warware dakanta.

Ita kuwa hakan yafi mata tagi so kowa yabarta yanda yaganta bataso ake yawan tambayarta akan hakan dan bata sanin amsar bayarwa sai dai ma taji haushinka kai mai tambayar abinda yasame tan.

Kwanan Abbas shida da tafiyah sai ga Mahmud ma ya dawo, aranar dasuka fita daga camp, Teemah kam bazata ce batayi murna da dawowar tashi ba saboda shima tayi kewarsa amma tagagara bayyana murnarta afili.

Shikansa yayi mamikn inda rawar kan Teemah yatafi amma sai yabar hakan amatsayin girman data san yasameta ayanzun,duk da yake yasan sun fara shiri da Abbas kafin yatafi amma bai ta6a zaton shak'uwar dake tsakaninsu har takai matsayin da rabuwarsu zai ta6ata har haka ba shiyasa ma sam wannan dalilin bai zo kansa ba.

Sai kawai yayi ta tsokananta wai ad'an tafiyan daya yin neh harta yi wayo haka?, ko kuma idan tayi wani abin yace " iyeh irin angirman andaina yarinta" murmushi kawai takeyi masa shikuwa daman dayake akwai wasa atsakaninsu sai baya ta6a gajiya da tsokanan nata koda bazata kulashin ba sai yayi.

Mahmud yaso yayi zamansa a damaturun kafin yafara aikin bautar k'asan amma Anty ta rink'a damunsa da k'ira akan wai yadawo gida tana son magana dashi.

Dafarko yaso ya share ta yak'i zuwa saboda babu wani anfani zuwan nashin, gani yake gufin yayi nisa sosai kuma idan yaje d'in ko 1week mai kyau bazaiyi ba zai dawo toh ina amfanin zuwan nashi.

Data matsa masa sai kawai yace mata shi bashida kud'in transport d'in dazai kaishi lagos manufarsa intaji ta hak'ura da tafiyar amma abin mamaki sai yaji Bank alert tamasa transfer d'in kud'i isassu daza su kaishi su kuma dawo dashi, ko k'ira bai yi yamata godiya ba, sai kuwa k'iranta yabiyo baya inda take cewa yabi flight maza yataho.

"Toh" kawai yace mata tare da yanke wayar aransa yake mamakin fitina da kafiya irin na mahaifiyar tasa.

Dabara ce ta fad'o masa na k'iran Abbansa yagaya masa amma shima abin mamaki sai yace masa wai yatahi d'in kawai wai ai suma sunyi missing d'insa musamman Antyn nasa acewar Abban wai sosai take damuwa da rashin Mahmud d'in akusa dasu.

Tsaki ne yaji na shirin kubce masa yayinda yake shirin yanke k'iran amma sai ya danne yayita acikin ransa.

Haka ransa baiso ba ya shirya yayi sallama dasu mummyn yatafi maiduguri daganan yabi jirgi yawuce Lagos d'in.

Abin takaici ma ba komai zai mata ba kawai a fahimtarsa fitina ce ke damunta bataso yad'an zauna tare da mummyn in an barta nan wai ita mai dabara.

Washegarin zuwansa wata tazo gidan mai suna Munira, mahaifiyarta ce ta aiko wajen Antyn, lokacin data zo kuma Antyn bata nan sai Mahmud tasamu kwance akan kujera.

Wani fi'ili da salo tafara yi masa ita adole tana yanga, shikuwa haushi yabi ya cikashi da k'yar ya bata amsar tabayar data yi masa na cewa ina mum d'in sa take?

Zata sake magana ya tare ta cikin k'osawa da kasancewarta akusa da shi d'in ga kuma haushin uzura masa da Anty tayi inda azafafe yace mata " contact her mana karki dameni ni dallah"

Jan bakinta tai tayi shiru tana k'are masa kallo, shikuwa yana da kwancen yaga ta kasa d'auke idonta akansa da farko yabata chance saboda yanayin kallon na d'an lokaci ne zata 'auke idanun ta amma sai yaga ina bata da niyyar dainawa, sai yatashi ya zauna da sauri yana kallonta idonta acikin nashi yace mata "naci miki bashi ne?

Jijjiga masa kai tayi alamar "a'a"

" so why the eyes?"
Yasake fad'i sai sannan ta kauda idonta gefe cikin jin d'an nauyi.

Tsaki yaja kana yakoma ya sake kwanciya amma ko 2mins bai k'araba ya tashi ya bar parlourn yayinda munira ma ta raka shi da idanu.

🔏🔏🔏🔏🔏🔏
our pencil is up!!!!

*Anan zamu dakata*

_inai mana fatan Alkhairi yah y'an uwa al ummar musulmi ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,haskensa rahamarsa,da falalarsa acikin wannan wata mai alfarma.Allah ka datar damu kabamu ikon yin ibadunmu cikin natsuwa.Allah ubangiji yasa ibadunmi kar6a66u ne Allah yasa yanda muka ga farkonsa lafiya Ubangiji Allah yasa k'arshensa ma yazo mana da falala masu d'aurewa, Allah ubangiji kasadamu da daren lailatul qadr Allah kasa muna cikin bayinka dazaka y'antar acikin wannan wata mai alfarma ( *AMEEN SUMMAH* *AMEEN* ).

Sai idan Allah ya nuna bayan sallah lafiya zamu d'ora daga inda muka tsaya, idan kuma Allah bai sa zamu sake ganawa ba zan iya cewa ayi min afuwa akuma gafarce ni hak'ik'a ranmu ba'a bakin komai yake ba zamu iya tsintan kanmu akowani irin halin idan ya Allah ya.gadama karmu manta da wannan.

Ban rik'e kowa azuciyata ba kuma dan Allah nima inaso ayafeni kunsan d'an Adam ajizi saida yafiya da kuma uzuri.

Labarinmu kusan zan iya cewa ba'ayi komai aciki ba inajin yanzu ma aka fara sauran kuma sai wanda suka bibiye ni abayan sallah in da rai kenan.

Fatan alkahiri ga dukkan masoyana nagode sosai da irin addu'o'i da kuma uzururrukan da kuke min Allah ubangiji ya baku dukkan abinda kuke so, Allah ya amsa muku dukkan addu'o'inku ( *Ameen)*

*Salmerhn ku ce*😍
[10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!

Hak'ik'a munga k'arshensa kamar yadda muka ga farkonsa, Allah ubangiji yasa mun dace acikin wannan wata mai alfarma daya gabata.

Allah yasa muna daga cikin 'yantattun bayi.

' *'YAN UWA BARKA DA SALLAH* .
Chapter 31 · 0% Book details