← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 163

Sashe 146

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan ya maida idanun sa kan system 'din yana tunanin yau kuma da wannan zata hana shi natsuwa, sarai yasan halin ta idan ta riga ta furta abu to matu'kar ba samu tayi ba bata ta6a natsuwa balle shi ma ta bar shi ya rintsa, sosai abin nata ya fara isan sa, sai a ciki- ciki ya 'karasa da fa'din " ni kam wannan abin idan cuta ce hakan Allah ya yaye miki?"
Sam baya son hayaniya a kansa amma 'karfi da yaji sai da ya saba da nata, balle ma ita da ta ha'da hayaniyar harda tsirfa da fitina.
Kuma yasa a ransa cewa dole ne suje ganin likita domin a san mekecdamun ta har yake sata hakan, bawai dan ya gaji da kashe ku'din sa ko kuma ya gaji da halintan ba ah'ah sai dan kawai yaji musabbabin hakan tunda yasan ba halinta bane wannan tsirfe-tsirfen, sam bai san inda ta aro hakan ya ya6a shi cikin rayuwar ta ba.

Teemah kuwa data ga yayi shiru ya shareta bayan abinda ya gama furtawan sai kawai ta sanya masa kuka tana fa'din "Allah Yayah ni fa yunwa nake ji kuma pepper soup 'din Ummah nake son ci......"
Tana mai cigaba da sheshshe'ka tayi maganar cike da sakalci da shagwa6a.

Kallon "kin isheni" yayi mata tare da ha'de ransa amma hakan bai wani yi tasiri ba dan tana ganin hakan ma sai ta 'kara sautin kukan ta fiye da na baya kuma still kanta na jikinsa.

Abbas system 'din ya rufe da 'karfi dan takaici sannan ya kalle ta, sosai ya tsani kukan nata baya so ko ka'dan amma bai san meyasa rigimar Fateeemah ya kasa barin ta ba har yanzu sam ita bata sanin girman ta.
Wani lokaci idan tayi masa wani abin ji yake as if tafi kowa wayo a duniya amma kar kaso kaga wurin rigimar ta har sai ta hana shi natsuwa da sukuni idan ta fara domin kuwa 'daga masa hankali take yi ta kuma hana kanta samun natsuwa itama.

Ganin bata da niyyan sararawa sai ya kai hannu da niyyan kamo hannun ta dan ya lallashe ta, Teemah kam sai ta fisge hannun nata da 'karfi ta kawar gefe tana jin in dai ba cewa zai yi zai kawo mata ba to ita babu ruwan ta.

Yanda tayin sai ya bawa Abbas haushi take sai yaji wani iri a ransa, gashi har yanzu bata daina kukan ba sai ma 'kara volume ta keyi duk ta cukuikuye shi sai ya rasa yanda zaiyi da itama gaba 'daya he had no choice than ya bu'de mata idanu dan haka da 'dan 'karfi yace " Wai ni kam ni na saki jin yunwan kika dameni haka? ba fa na son iyayi ina gaya miki"

Itama Teemah kamar an fizge ta sai tace "kaine mana kaine kasani jin yunwa.....kuma sai nacgaya ka da Daddy tunda kullum masifa kake min"

Shiru yayai yana kallon ta tana ci gaba da kukan ta wanda maimakon ya ragu "ah ah sai ma 'karuwa da yake yi akan nada.

Wata uwar tsawa ya daka mata wanda har sai da ta firgita in da yace " Shut up da Allah!
Haba ths is too much, abincin da ba yau akayi ba not even yesterday shine zaki wani ce shi kike son ci? A ina zan samo miki bacin kinsan Ummahn ma kanta ba nan take ba?
For God sake Zahra ki barni na huta ki sarara min dan Allah......in ba haka ba zaneki zanyi idan kika isheni.......baga can kitchen ba kije kiyi duk abinda kike so mana ko tsabar kin raina ni ne yasa kike yi min hakan.......?"

Teemah kam cak kukan ta ya tsaya tun lokacin daya fara masifar, sanadiyyan wani motsi da taji a cikin ta na ban mamaki da bata ta6a jin irin sa ba tun da tasan rayuwar ta.

Taso ta share amma da taji wani motsin na biyu tamkar an harbe ta a cikin ai bata san lokacin data tashi ta zauna ba dafe da cikin nata ta furta " Yah ilahi...Yayah cikina motsi yake yi...., na shiga uku mutuwa zanyi inaga ni kam"
Sai ta 'kara sanya wani sabon kukan.

Wannan dalilin ne ya sanya shi yanke masifar da yakeyi shima ya dawo da hankalin sa gareta da mamaki ya 'dage gira 'daya sama take kuwa salon maganar tasa ta canza da tambayar " Motsi kuma kamar yaya?
Yana 'ko'karin dafo cikin ta nata shima yayi maganar.

Cikin kukan tace dashi
"Allah ni...ma bansani ba Yayah.... ji naimyi cikin na harbi na ni kam mutuwa zanyi Yayah pkease ka taimake ni"

Abbas take jikin sa yayi sanyi dajin irin kalaman nata wanda daga ji ma kasan iya gaskiyar ta take fa'di ba'a baki bane kawai, domin yanayin 'karyar ta ma daban ne.

Dan duk wanda yasan Teemah toh yasan cewa bata fiya 'karya ba ita balle wannan da yasan cewa babu mamaki in dai cikin Teemah ne abinda yafi haka ma zai yi ko dan abubuwan data ke yawan 'dirka masa.

Tsaban yanda ta tsorata da abin kallo 'daya zaka yi mata ka fahimci a firgice take motsin kirki ma 'kinyi tayi hannun ta dafe da cikin ta har yanzun tana kuma sau'kar da hawaye.

Tashi yayi ya tsaya yana kallon ta ita kuwa kanta a 'kasa.

Yana gwada kaiwan hannu jikin ta sai tayi saurin fa'dawa jikin sa ya rungume ta, itama ma kuma haka.

Chance ya bata ta sha kukan ta shi kuma ya sa hannu acikin yana shafawa a hankali take wani tunani yazo ransa jin taurin dake marar ta ya 'karu fiye sa wanda ya taba ji kwanaki.

Yin tunanin keda wuya sai ya cire ta a jikinsa ya ri'ke gefe da gefen kafa'dun ta yace "let's go to d hospital Zahra we need to see........"

"Yayah....
Zatayi magana ya tare ta fa'din " shiiii....
Sai tayi shiru dan dole
"Oyah hurry up canza dressing ina jiran ki now"

*~_UR COMMENT IS GETTING LOW KO HUTU KUKE SO_~* ❓

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce* 😍
[10/13, 8:01 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Allah ya raya mana Princess Fatima, Allah ubangiji ya haskaka rayuwar ta da hasken sa yasa cikon addini ce.(Ameeen)👏🏻 @ Dr. khausar*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_A *true friend* sees d 1st tear, catches d 2nd one nd stops d 3rd.....they ar not d ones who ar there when it’s convenient only...... *True friends* ar also there when it’s not...Hold a true friend nd don't ever let them go coz *True friend* comes just once in a lifetime._ 🤞🏻

🅿 *92*

Abbas ma bai fiya barin ta tana shan za'ki ba saboda an gaya masa cewa hakan nada illah musamman ga mai ciki irin ta.

Koda ya koma office kuwa baya yin cikakken 1hr ba tare da ya 'kira yaji lafiyar ta ba.

Matan blocks 'din su ma na nan-nan da ita musamman saboda karamcin Abbas a wurin su.
Bata aikin komai sai yi masa girki, duk kuwa da cewa tana son yi 'din amma Abbas hana ta yin komai yake yi sai dai wani lokacin ta saci jiki tayi idan taga baya nan.
Amma da kansa yake yin komai a gidan.

Matan block 'din su ma da yake yawancin su manyan mata ne so sai suke tausayin ta da ganin 'kan'kantar ta, su kansu duk ranar da sukayi katari da ita ta 'dauki tsintsiya hana ta suke yi.

Cikin ta na da wata bakwai sannan ta sanar da Hannah a chat dan sosai zuciyar ta ta kasa daure rashin sanar da Hannah labarin cikin, duk iya 'ko'karin da ya kamata tayi amma ranta yakasa sakewa, inda suna cikin chat tace da ita " Hajiya ki fara shirin raino fa dan Matar Yayah nada ciki har na tsawon wata bakwai"

Hannah kam wasa ta 'dauki abin dan haka sai itama tace " wacce matar Yayahn kenan kike magana? Kinsan ai ni bansan ya 'kara yin aure ba".

Teemah bata ba ta amsa ba sai kawai ta 'kirata video call tana murmushi ta nuna mata cikin.

Hannah mamaki, murna da farin ciki gaba 'daya sai suka hanata magana ta bu'de baki kawai tana kallon ta. Teemah ma kallon t take yi sai dai ita murmushi ne akan fuskar ta mai sanyi.

Hannah nuna ta tayi tace wai dagaske ciki ne a jikin ki?"

Teemah cikin ta k'ara nuna mata tace " ga zahiri kuwa kina gani Hajiya"

Hannah ihun murna ta sanya tare da tashi ta nufi wurin Ummah tana 'kwala mata 'kira.

Da sauri Teemah ta yanke 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya tana dariya.

Taso ta 'kyale Hannah kawai sai dai taga suprise 'din baby kamar yanda take ganin take-taken Yayah, amma sai ta kasa jurewa saboda sam bata ga dacewan ace har tana da cikin daya kai ciki amma Hannah bata da labari ba.

B'angaren Hannah kuwa tana isa wurin Ummah ta dago wayar tana fa'din " Ummah kalla kiga abin mamaki, Fateemah na da babban ciki tace min har ya kai 7months....."
Gani tayi Teemah bata kan layi sai ta sake gwadawa amma baya tafiya, ta kira voice call shima akace mata switch up.

Ummah kuwa gaba 'daya hankalin ta ta tattara ta mayar kan Hannah jin ta kusan samun jika, ganin Hannah na jan tsaki ne yasa ta tambayar ta " meya faru?"
Sai Hannah tace " Wallahi Ummah kinga tayi disconnecting call 'din kuma na 'kira baya tafiya"
Ranta duk a jagule tayi maganar ga dukkan alamu bataji da'din hakan ba.
Ummah cewa tayi " amma kin tabbatar cewa cikin na ajikin ta?"
Sai tace " Allah dagaske ciki ne Ummah ai ta nuna min kuma tace har 7month......"

Taranta Ummah tayi da fa'din shikenan naji 'kira min mijin nata, tunda isheshshe ne shi wato har yayi wayon 6oye min abu irin wannan ko?
'Kira min shi da sauri zai zo yasame ni ne"
Chapter 146 · 0% Book details