← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 163

Sashe 147

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannah ba tayi magana ba sai ta hau 'kiran nashi wayar amma cikin rashin sa'a sai na shin ma bai tafi ba.
'Dago wa tayita kalli Ummahn sannan tace " ba fa na samun sa Ummah shima 'din"

"K'yale shi zuwa anjima may be za'a same shi"

Hannah kam kasa hak'ura tayi ta ringa gwadawa nashi da na Teemah amma gaba d'aya ya 'ki shiga, abin ya 'kona ran Hannah sosai jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta taho Ports a lokacin kawai dan taga Teemah.

Teemah kuwa bata sani ba ashe da gangan Abbas ya'ki sanar mawa Ummah gudun kar ta uzzura masa akan ya maida ita gida dan yasan Ummah najin wannan labarin ba barin sa zata yi ya runtsa cikin kwanciyar hankali ba.

Shikuwa yanzun sam baya so yaga yayi nisa da iyalin sa ba ma ya 'kaunar abinda zai kawo rabuwar koda kuwa menene shi.

Sosai yake so ya cika rayuwar ta da zallan 'kauna da soyayya.
Hatta hakkin sa da ke kanta daya zama dole ma daina kar6a yayi dan gani yake tamkar abin zai yi mata yawa ne, musamman ma da yake ya san kansa yanda yake galabaitar da ita a duk lokacin daya kusanceta shiyasa ma ya sau'ke mata wannan nauyin, sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya danne nashi bu'katan, in dai ba ita ta nema ba da kansa kam baya ta6a kusantar ta kuma itama Teemah yanzu da sau'ki ba sosai abin ke motsa mata ba sai tayi sati biyu zuwa uku ma bataji wani abu ya dame ta ba game da hakan, itama kuma bata sanyawa ranta damuwa ba musammn data ga cewa shima baya ra'ayin hakan sai itama take 'ko'karin binsa akan yadda yake so 'din duk da bai fito fili ya gaya mata dalilin daya sashi yin hakan ba amma tasan dai ba zai ta6a yin abu dan ya cutar da ita ba.

Har kusan 2hrs Hannah bata gaji da 'kiran layin sa ba dan yanda ta 'kagu ta tabbatar da labarin, ga Ummah ma da nata masifan a gefe, da 'kyar suka same shi a nashi wayan har sai data sau'ke ajiyan zuciya data ji ya shiga, da murnar ta ta mi'kawa Ummah wayan tare da fa'din "yesss ya shiga Ummah".

Ummah kar6a tayi da sauri ta sada wayar da kunnan ta da fatan Allah yasa abinda taji daga bakin Hannah ya kasance gaskiya ne.

Abbas na office yaga 'kiran Hannah, bai san dalili ba amma haka kawai sai yaji zuciyar sa ta tsinke bawai dan basa waya ko bata 'kiran sa ba ah'ah, dan ko jiya ma sun gaisa da ita a waya amma haka kawai yau 'din ya tsinci kansa da fa'duwan gaba ganin 'kiran ta.

'Dauka yayi sannan ya kai kunnan sa, ba halin sa bane fara yin magana idan zaiyi waya matu'kar bada iyayen sa bane amma yau 'din sai yaji bakin sa ya furta sallama.

Muryar Ummah yaji ta amsa sallamar tare da fa'din " Muhammad kaji kunya kai kam"

Kai Abbas ya sosa duk da bai san laifin sa wurin Ummahn ba da har ta fa'di hakan amma sai yaji shi wani iri sai yace.
" Afuwan Ummah, barka da war haka" Ummah bata bi ta kan gaisuwar tasa ba sai cewa tayi
"Ina 'yata take?"
Amsa ya bata da fa'din
" tana gida Ummah ni na fita aiki ne".
Ummah sake cewa tayi
"Ina fatan dai lafiya take?"
Sai yace "Ehh Ummah lafiyar ta 'kalau"
" to masha Allah, yaushe zaka dawo min da ita gida dan gaskiya banaso ta haihu cikin inyamuran nan?"

Cike da mamaki ya zaro idanu tare fa'din " haihuwa kuma Ummah? waye ya sanar da ke ciki gare ta?"

D'an 6ata rai Ummah tayi tace da shi " Ni bana son shashanci Abbas tambayar ka nayi answer me kawai".

Abbas sai ya lumshe idanu tare da shafo kansa sannan yace " Ummah ki bari watan haihuwar yayi mana sai in kawo ta...".
Tun ma kafin ya idasa rufe bakin sa Ummah ta tareshi da fa'din " ban amince sam kama canza shawara"

Shiru yayi yana jin wani iri a zuciyar sa tare sa tunanin yadda zai 6ullo mata, Ummah kam ganin yayi shirun ne yasa ta fa'din " ni dai ina jira nan da 2weeks in ga 'yata a gefe na, in ba haka ba kuwa zaka sha mamaki na Muhammad, domin da kaina zanzo har Rivers 'din in 'dauko ta".
Ummah na gama fa'din haka ta yanke wayar ba tare da ta jira jin na bakin sa ba, dan ma abin ya ha'du mata da farin cikin jin labarin cikin shiyasa ma masifar batayi tsayi ba.
Abbas kam da kallo ya bi wayar tare da mamakin inda Ummah tajiyo wannan labarin, yasan in ba Teemah ba babu wanda zai sanar da ita tunda kam shi babu wanda ya fa'din mawa.

Lokacin daya koma gida sai ya tarar da ita har tayi masa abinci mai 'dan sau'ki, tuwon semo tayi da miyar egussi, sosai yake ya bawa 'ko'karin ta ta wannan fannin, domin shi ka'dai yasan yanda yake ji a duk lokacin daya tarar ta tanadar masa abinci koda kuwa wani iri ne sosai yake appreciating, dan ya fahimci bata wasa da abincin sa musamman data san cewa ba ya cin komai a waje so bata ta6a barin sa ya nemi abinci ya rasa ba, ko da kuwa mai sau'ki tana matu'kar 'ko'karin yi masa kuma yana yabawa da hakan.

Haka idan ya dawo a kullum tana 'ko'karin ganin ta tayashi rage kayan jikin sa, a yana hana ta ma amma dole kullum bata barin sa, hatta wanka da wasu abubuwan idan ya kama duk tana taya shi, shima kuma ba laifi lokaci-lokaci ya kan yi mata massaging 'kafafuwan ta dan wani sa'in yana 'dan yin kumburi ka'dan.

Sai da ya kammala da cin abincin kafin ya dube ta yace da ita " Ummah ta 'kirani".
Teemah na jin haka sai ta zaro idanu waje tana kallansa, take sai ya gane rashin gaskiyar ta sai kuma tace " me tace maka kuma?"

Shiru yayi shima ya zuba mata idanu.
Duk da bawai yau ne karo na farko da Ummah ke 'kiran sa ba, kusan kullum sai sunyi waya da Ummah hatta ita Fateemah ma suna waya dukkan su da ita amma yanzun kallo 'daya zakayi mata ka fahimci ta shiga wani yanayi da jin 'kiran Ummah.
Maimakon ya bata amsar tambayar ta ah ah sai yace da ita
" mara kunya....ai na lura tunda kika samu cikin nan kika zama mara kunya kuma shine har da sanar da Ummah cewa kinyi ciki ko?"

Kai ta kawar gefe tace " Ni fa bance mata ina da ciki ba".
Sai yace " To a ina ta samu labari?"
Shiru tayi masa tana 'kara ha'de goshin ta.
Sai shine yaci gaba da fa'din
" Ni dai let me tell u...idan kika kuskura kika haifamin baby mara kunya ko kuma mara son makaranta ni da kene".
Hawaye ta fara tare da mi'kewa ta shige cikin bedroom taje ta zauna dirshan a 'kasan tiles tana zubda hawaye, ji take ranta babu da'di a duk lokacin da Yayah ya ambaci makaranta ko kuma yayi mata gugar zana da hakan, ta so ta yi 'din kamar yanda ya bu'kata amma sam takasa shigar da shi cikin ranta domin koka'dan babu niyyan a zuciyar ta, shiyasa ma ta ha'kura, amma a kullun addu'ah takeyi Allah ubangiji ya cire masa abin a ransa shima ko zata huta da mitar sa akan hakan.

Abbas ma tashi yayi biyo bayan ta a 'dakin yazo ya zauna daga gaban ta ya fuskance ta, bai bi ta kan kukan nata ba illah tambaya da ya jefa mata inda ya sake fa'din " waye ya sanar da Ummah cewa da ciki a jikinki ai nasan kece kika fa'din mata".
Ya 'karasa maganar tare da 'dage gira 'daya sama.

Teemah kam da muryar kuka tace dashi " Ni dai bani bace sai ko in Hannah".
Sai yace " ita Hannah a ina taji labarin ?"
Teemah shiru tayi kawai tayi 'kasa da kanta wani hawayen na gangarowa, sai shine yaci gaba da fa'din " ai kema kin san tsakanin Hannah da Ummah dole ne idan taji sai ta gaya mata, gashi yanzu tace wai dole sai dai in maida ki Abuja wai bata son ki haihu a nan"

Yanayin da ya 'karasa maganar ma kanaji kasan ransa baya son tafiyar koka'dan, amma sai tayi 'ko'kari wajen ganin ta ri'ke kukan da take yi tace dashi " duk 'daya ne ai Yayah da can da nan 'din ba wata matsala".

Muryar sa da sanyi yace " kenan kema kinfi son can 'din ko?"
Itama a hankali tace " ah'ah fa Yayah ba haka bane....".
Sai ya tare ta da fadin " .......haka ne mana, kin fi son ki tafi ki barni ko tausayina bakiji ko?, yanzu fa idan ba kyanan komai ma ni zan rin'ka yi hatta abinci ma babu wanda zai na dafamin......".

Bai ma 'karasa maganar ba ta sanya kuka inda cikin kukan tace " Yayah to ya zanyi ni kam, Allah inajin tausayin ka amma ai kaga Ummah ce da kanta ta nemi hakan ba yadda zamu yi ne shiyasa".

Hannun ta ya kamo cikin nasa hannun yana murza 'yan yatsun ta cikin natsuwa yace " kawai kice mata ke ba yanzu zaki koma ba in taji daga bakin ki i'm sure zata ha'kura".

Kai Teemah ta jijjiga masa tare da fa'din " Allah ni kam bazan iya ba Yayah, Ummah ce fa".

Shiru yayi yana kallon ta ko da wasa bai son abin da zai raba su, sam baya son tayi nesa da shi amma kwatsam rana tsaka Ummah ke 'ko'karin shiga tsakanin su, bai san yadda zai yi ba amma gaskiya yana jin tamkar hakkinsa za'a shiga akana hakan, gashi ma tun kafin ranar tazo ya fara shiga wani hali na damuwa.
Chapter 147 · 0% Book details