← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 163

Sashe 107

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbas kam suman zaune ne yaso kama shi dan be ta6a tsintan kansa acikin irin wannan yanayin ba, be ta6a kallon surar mace azahiri irin hakan ba, macen ma kuma Fateema, idanunsa be ta6a cin karo da abu makamancin hakan ba, 'kirjin ta ya kura wa idanu dake sanye cikin jan bra mai kyan gaske, ajiyan zuciya ya sauke tare da kawar da idanunsa gefe itama Teemah adai -dai lokacin sai ta motsa ka'dan dan sosai taji alamun sauyi atattare da jikinta iska taji na hura ta amma saboda 'karfin alluran dake yawo ajininta yasa bata wani yi motsin na kirki ba ta cigaba da baccinta.

Tashi yayi yaje cikin kayan sa ya 'dauko rigar polo ba'ka na aikinsa ya dawo inda take, yanzun kam hawowa gadon yayi gaba 'daya yafara 'ko'karin saka mata rigar, a hankali, idan yaga kamar zata motsa sai ya dakata da abinda yakeyi sai ta kuma yin luf sannan yake cigaba da sawa kamar me dressing wa jinjirin da ba'a so ya tashi a bacci da haka har yagama mata, shi kansa mamakin kansa yakeyi yanda har ya iya tsayawa ya 6ata lokacinsa wurin sanya mata kaya duk kuwa da cewa hakan ba'kon lamari ne agurinsa amma a hakan sai da ya sa mata.
Shida kansa ya san Fateemah dabance a rayuwarsa, bata da me kama koka'dan azuciyarsa.

Yana gamawa kuwa aransa ya furta " _tubarkallah-masha_ _Allah_ " tare da shafa gashin kanta ahankali,
Dan yadda rigar ta matu'kar amsan jikinta ya kuma 'kara fito mata da asalin kyaunta da haskenta kamar ace nata ne, baran ma da ya ha'du da ba'kin skinny trouser 'din dake jikinta ai ba magana, sosai Abbas yaga 'karin hasken ta ya zarce na baya.

Abbas kam shashancewa da kallon ta yayi ya mori wanda suka wuce shi ma abaya, shi kansa yasan Fateemah mace ce, mace ce da kowa ni 'da namiji zaiyi sha'awar kasance wa da ita.

Ya godewa Allah aransa yafi sau a 'kirga saboda kawai mallaka masa ita da yayi amatsayin mata.

Abbas 'dinku kam kasa jurewa yayi lokacin da idanunsa suka sau'ka akan bakinta, sai ji yayi kamar an fizgeshi ya ran'kwafo da kansa zuwa dai-dai fuskarta, bakinsa ya ha'da da nata ya bata light kiss asaman la66an ta.

Yana cire bakinsa kuwa yaga ta turo bakinta gaba tare da juyi zuwa 'dayan 6angaren.

Sai da ya lullu6eta kafin ya tashi yana murmushi ya koma kan stool 'dinsa ya zauna.

Tsawon mintina talatin yana zaune wurin agabanta kamar mai gadin ta, sannan ya koma parlour anan ya tarar da tarin missed calls awayarsa har da na Daddy, Ummah da sauran abokansa.

Abokansa kam dama yasan dole zasu neme shi dan be yi sallama da su ba ya taho abinsa, amma be bi ta kansu ba, sai yabi bayan 'kiran Daddy, shima na Daddyn be shiga ba wanda hakan yasa ya gane cewa tafiyar su zuwa Lagos tayi nisa kenan.

Sai da ya 'kira Ummah yace da ita yana bu'katar ruwan tea ta amsa masa da toh sannan ta tambaye shi jikin Fateemah yace da sau'ki yasanar da ita cewa sun dawo ma already suna gida.

Godiya wa Allah Ummah tayi tare da fa'din tana zuwa anjima toh tadibo ta.

A silent ya saka wayar bayan sun gama magana da Ummah tare da ajiyeta agefensa, sam be yi niyyan zuwa ko'ina ba dan haka yayi zamansa a parlourn yana gadin farkawar ta.

Daga shi Abbas har ita babu wanda ya halacci taron walimar, inda kuwa babu laifi walima ta 'kayatar fiye da zaton mai karatu, gurin ma ka'dai abin kallo ne dan idan kaga yanda aka tsara gurin dole sai ya birgeka komai fari akayi decoration 'din wajen gwanin birgewa, ga wasu shahararrun malaman musulunci da aka gayyato maza da mata inda suka ja hankalin mutane akan ha'kuri da zaman takewar aure, ga 'dumbin jama'ar al'ummar musulmai da suka halatta suma ba 'a cewa komai, Ga Hannah ma da tawagar ta agefe guda suma ba laifi yawa ne da su, zakayi mamaki idan ka kalli ayarin 'yan CAPTAIN ABBAS FANS 1&2 suma agurin suna ta rawar kai abin su afa'dar su wai bikin nasu ne,'dai-'dai kun cikin su ne ke zaune aguri 'daya, wasu ko fuskar nan babu walwala, musamman ma masoyan CAPATIN na ha'ki'ka da suke jin cewa za'a musu kishiya, su kam har banson ganin fuskar su dan ko ka'dan babu walwala, sunzo ne da niyyar ganin kalar amaryar Abbas 'din amma basu samu dama ba dan Cpt. abbas ya 6oye amaryarsa ya hana su ganinta, basu sami ganinta ba kuwa har taro ya watse gaba 'daya.

Ummah da kanta ta kawo masa Tea 'din inda tasame shi zaune a parlour, taso ganin Teemah amma Abbas yace bacci takeyi dan haka sai kawai ta tambayi yanayin jikin ya sanar da ita cewa ba laifi jikin da sauki, tace "toh Allah ya sauwa'ka" daga nan ta tafi da zummar sake dawowa ta dubata idan ta tashi.

Mummy naso taga 'yarta taga halin datake ciki dan rabon su da ganin juna tun da rana data hanata 6uya a'daki, zazzabin nata ma labarin sa tazo taji bayan sun wuce asibiti ta kira layin Teemahn kuma ba'a 'daga ba, tana so taganta amma nauyin ganinta tare da Abbas 'din sai ya rinjayi 'kudurinta dole ta sanyawa ranta ha'kuri zuwa gobe idan Allah ya kaimu.

Bayan sallar maghrib Hannah tazo da sallamar ta ta gaida shi tare da fa'din " 'dazu ka kirani Yayah?

Yana kishingi'de cikin kujera be ko kalleta ba yace

" meyasa toh sai yanzu zaki zo?

"Ayyah Yayah muna wajen walima ne fah alokacin shiyasa"

Sarai yasan 'karyane dan haka sai ya jijjiga kansa ya kauda kan daga barin kallon ta yace ki 'dauko wa yarinyar nan kayan baccinta inajin zata bu'kace su"

Taso ta tambaye shi wacce yarinyar amma tsoron yanayin dayake ciki ya sanya ta ta ja bakinta kawai tayi shiru ta fita.

*****
Teemah kam bata tashi ba sai 'karfe tara kusan da quarter ma sannan ta farka, ahankali ta bu'de idanunta sai kuwa taga duhu, bata tashi ba sai ta fara lalu6en Hannah a gadon hannu da 'kafa amma bata jita ba, " Hannah!

" Hannah!!

ta kira sunan ta har sau biyu, jin shiru yasata ta janye bargon dake jikinta ta sau'ko daga gadon tamkar zatayi kuka, tana shirin barin 'dakin sai taga haske ya gauraye ilahirin 'dakin gaba 'daya.

Juyawa tayi sai caraf suka ha'da idanu dashi, zaro ido tayi waje tare da rufe bakinta da hannayenta duka biyu wanda sai alokacin kuma ta fahimci a inda take.

Be kulata ba sai ya kawar da kansa gefe duk kuwa da cewa yaji da'din yanda yaga ta tashi garau da ita, amma be nuna hakan afili ba, sai ya wuce ta ya nufi bayi ya dan watso ruwa sai alokacin ne yaji nutsuwar yin wankan ya shige shi, tun 'dazu yake so yayi amma ya kasa sallah ka'dai ke sashi barin inda take yana idarwa kuwa baya 6ata lokaci ako'ina yake dawowa yaci gaba da gadinta, dama burinsa be wuce ya ganta ta warware ba.

Yana shiga bathroom 'din kuwa sai itama ta wuce parlour da hanzarin ta da niyyar barin 'dakin, amma sai ta tarar da 'kofan arufe da lock, mamakinta kuwa be wuce na yanda akayi tazo nan 'din ba ga kuma wata riga ajikin ta dabata san daga ina ta sameta ba.

Kan stool 'din dake wajen dressing mirror ta koma.ta zauna tana jiran fitowarsa domin ya bu'de mata 'kofa ta tafi.

Abbas ma yaso ya 6ata lokaci a gurin wankan amma daya tuna cewa bataci komai ba sai kawai ya hanzarta ya fito in less than 15mins.

Shima yana fitowa direct gaban dressing mirror ya nufa dan ganin yanayin jikinsa yi yayi tamkar be ganta ba sai ma murmushin mugunta daya sake yi tare da kwar da kansa.

Dama yasan zata nemi hanyar fita shiyasa ya sakawa 'kofan lock kafin ya baro parlourn tun da wuri.

Towel 'dinsa 'daure a 'kugun sa ya fito, da farko Teemah rintse idanu tayi data ga ya nufo inda take ahaka, amma daga baya data gaji da rufe idanun sai ta bu'de su ahankali ta sau'ke su akansa.

Abbas duk yana lura da ita amma be tanka ta ba.

Ita kuwa akan cikinsa ta sau'ke idanun ta, ta kuwa 'kurawa jikin nasa idanu ta na kallo har zuwa 'kirjin sa.

Tasaba ganin Yaya Mahmud ahaka amma yau da taga Abbas sai ta ga tsarin halittarsa ba iri daya 'daya data Mahmud ba, sosai yanayin jikinsa ya birgeta yanda jikin ya wani mummur'de ga wasu parks da ya ajiye sai take jin sha'awar ta6awa, amma bazata iya ba dan tasan halinsa idan ta ta6a shi 6a66allata zai yi wannan Yayan kam, kan ta 'daga zuwa fusakarsa, suna hada idanu sai ya 'dage mata gira tare da fa'din " _ya dai_?

Kau da kai tayi gefe da sauri tace " _ni ina so in tafi ne"_

" _Zuwa ina kenan_ ?
Ya tambaya batare da ya kalle ta ba.

Amsa ta bashi da fa'din
" _D'akin mu, gurin Hannah..._ "

Taranta yayi da fa'din " _can 'din yafi nan ne_ ?

Bata bashi amsa ba sai kawai ta tura baki gaba tayi fuskar kuka.

Ko kallan inda take Abbas bai sake yi ba yaci gaba da sha'anin gabansa.

Teemah kan kukan shagwa6a tafara yimasa ka'dan-ka'dan, Abbas still 'kin kulata yayi sai daya ga kukan na shirin yin yawa ne sannan ya waigo azafafe ya dubeta yace " _for god sake ni na hana ki tafiya ne? Kije abinki mana ko na 'daure ki ne.._ ?

Da turarren baki cikin shagwa6a ta furta " ' _kofan fa arufe da lock ai na duba 'dazu_ "

Goshi ya dafe kamar ehh dagaske ya manta ne sai yace " _muje in bu'de miki_ "

Gaba yayi aransa ya furta " _zanyi maganinki ai_ "
Itama sai ta bishi abaya har zuwa parlourn, yana budewa kuwa ko magana bata sake yi ba ta fice abinta.

Tura 'kofan kawai yayi da gangan ya barta abu'de dan ya san zata dawo.

Ai kuwa ko bedroom 'din be gama shiga ba yaji ta dawo da saurin ta har tana shirin wuce shi.
Chapter 107 · 0% Book details