← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 163

Sashe 115

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hisnul Muslim ta 'dauka cikin takardun data gani a drawern 'dakin tafara karanta azkar 'din safiya da maraice bayan shi sai ta 'kara dana kwanciya bacci kafin ta kammala ma sai bacci yaso yaci 'karfin ta, a hankali ta mi'ke agadon ta kwanta take kuwa bacci ya dauke ta.

Lokacin da Abbas ya tashi ze daga parlourn har ya le'kata sai yaga baccin ta takeyi, hasken 'dakin ya kashe mata ya bar dim light kawai tare da ja mata 'kofar ya wuce nasa 'dakin.

*10:30pm*
Ta farka daga baccin kamar an tsikare ta ta tashi ta zauna tabi ilahirin 'dakin da idanu, tana gama fahimtar inda take wato a'dakinta kuma ita ka'dai ai sai ta tashi tafice da sauri ta bar da'kin, Allah sai ya taimake ta hasken parlour na nan be kashe ba.
Amma Teemah bata tsaya nan ba ta wuce 'dakinsa, 'kofan abu'de yake dan haka kawai sai ta tura ta shiga da 'yar siriryar sallamar ta.

Zaune yake a bakin gado farar singlet ce ka'dai ajikinsa da dogon wando, system 'dinsa na agabansa inda ya bada dukkan hankalin sa akai yana dubawa, 'kafarsa 'daya na tsaye yayin da 'dayar kuma take tankwashe ya zauna akai.

Sallamarta ce ta sa shi 'dagowa ya kalle ta da mamaki dan kuwa yasan tayi bacci tun tuni kawai sai ya ganta yanzun kamar an koro ta.

👎🏻
*Duk wacce taji aranta kamar cewa wannan SALMERHn* *bata kyautawa... pls badan niba tayi min afuwa saboda Allah, ni kaina nasan bana kyautawa amma* *abubuwa ne dayawa suka sha kaina, koda banyi typing* *ba amma wallahi kullum kuna raina ba'a son raina kuma nake muku jinkiri ba* , *ba yadda zanyi ne kawai* .........
~FATAN ZAKU CIGABA DA MIN UZURI DA HA'KURI HAR MU KAI GA CI.~

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce* 😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_My 'kungiya on top_ 🤞🏻
_This page goes to u *DBWA* i heart u mutane na._ 🥰

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Anyone can make u happy by doing something special, but only someone special can make u happy without doing anything._

🅿 *80*

Hankalinsa da idanunsa ya mayar kanta ya tsaya 'kare mata kallo, yau riga da wando ta sanya ajikin ta, yariga yasan zancen daya kawota amma duk da haka sai ya jefa mata tambayar
" _ya akayi_ ?

" _Babu komai_ " itama tace masa atakaice.

Cewa yayi
" _Toh me ya hana ki bacci har yanzu? ko rigimar da saura ne bata 'kare ba_ ?
Yasake jefa mata wata tambayar.

Goshi ta ha'de tawani yi kicin-kicin da fuska tace dashi
" Ni bana wani yin rigima.....kuma ma ai baccin nake ji ne yanzun shiyasa nazo dan inajin tsoron 'dakin can 'din"

Ido ya zaro waje akanta yace
" _Kullun ne wai ke kike jin tsoron_ ?
_Come on... go back to ur room kiyi addu'ah ki kwanta_ "

'Kafa ta fara bubbuga masa cikin shagwa6a take cewa " _ni wlh tsoro nake ji ni ka'dai_ ....

Yatsan sa 'daya ya 'dago ya nuna ta dashi yace " _bafa na son iskanci ...da 'din da wa kk kwana da zaki tsiro min da wannan iyayin yanzu_ ?

Kuka ta sanya mishi yanzun tana 'kara maimaita " _ni wallahi tsoro nake ji kuma ai ko da ma bani ka'dai nake kwana ba_ _da Hannah ne_ !

Kwafa yayi yana kallon ta kamar an matsi bakin sa sai ya sake fa'din " _kafin itan kuma fah_ ?
Shi adole tsare ta zaiyi da fa'din hakan.
Teemah kuwa cikin kwanciyar hankali ta bashi amsa da fa'din
" _ni da Yayah Mahmud_ "!

Take Abbas yaji wani mugun bugu azuciyarsa, ransa gaba 'daya yaji ya 6aci atake sai ya rintse idanun sa, wani mugun kishine yataso masa a zuciyarsa ga wani tunani na daban daya 'dar su aransa, sai ma yake ganin kamar da gangan ta ambaci sunan Mahmud 'din dan ta 6ata ransa.

Sam shi beyi tunanin zata ambaci Mahmud alamarin ba, he thought da can baya zata yi magana akai dan shima tunanin sa yatafi ne a lokacin datake gida a Damaturu, wancan lokacin kam yasan ita 'dayan ta take kwana kuma dashi yaso kama ta.

Be iya jura ba sai da ya dafe kansa tsabar yanda yake sara masa, 'kasa yayi da kansa ya sauke idanun sa akan system 'din dake gaban sa, tamkar wanda yaga abin tsoro aciki ko kuma system 'din ne yayi masa laifin sai ya rufe ta da 'karfi.

Kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke tsaye bai ko sake kallon inda Teemah take tsaye ba ya shige bathroom.

Teemah kam binsa tayi da idanu domin bata san me yasa shi canjin mood cikin 'kan'kanin lokaci haka ba, amma ganin har ya shige be kula ta yasa ta tafi a hankali tayi kwanciyar ta.

Abbas haka da kayan jikin nasa bai ko rage ba yaje ya kunna shower akansa, zuciyarsa, nutsuwarsa da tunaninsa duk suka caku'de suka dagula masa lissafin sa gaba 'daya.

Banda emergining rayuwarta da Mahmud babu abinda ke zuwa ransa alokacin, rayuwarta na baya agidan Mahmud yake tariyo wa har sai da ya kasance shine babban damuwar sa alokacin, shi kansa yasan ba dai-dai yake aikata wa ba amma zuciyarsa ta kasa yadda da cewa 'kaddarar su kenan bayan yariga yasan hakan ne nd he can't change it, he cant even erase d fact that ta ta6a zama gidan wani da sunan aure, kishin hakan ne ya hana zuciyarsa sakewa, shai'dan yariga ya yi masa mugun hu'dubar da ba za ta amfane shi da komai ba.

Shi kansa Abbas yasan kuskure ne hakan saboda babu amfani tuna irin wannan passed 'din musamman ma daya kasance yanzu Mahmud is no more but ya kasa goge hakan azuciyar sa, muguwar sa'kan nan ta ri'ke mashi zuciya sosai tana kuma sake haifar masa da zazzafan kishin Fateemah aduk lokacin da hakan yazo ransa.

Shi kansa ya'ki yake da zuciyarsa akan hakan mafi yawancin lokuta yana burin ganin ya dai-dai ya tunanin sa, rayuwar auren su ta 'dau hanya, amma kafin faruwar hakan sai gashi da bakin ta ta sake tuna mishi cewa wani ya mallake ta kafin shi, kenan wannan passed 'din ba zai ta6a barin rayuwar su cikin sau'ki ba, rayuwar ta da Mahmud yasan azuciyar ta ne ba zai ta6a iya kankare mata ba amma me yasa sai ta furta masa da bakin ta?

Haka ya bar shower nata zuba akansa kusan 1hr yana tsaye guri guda batare da ya motsa ko da 'dan yatsan sa ba, da 'kyar ya samu ya saita tunanin sa da taimakon kalmar innalillahi wa innah ilaihi raji'un dayake maimaitawa ya samu har ya watso ruwa tare da 'dauro alwala ya fito.

Lokacin da ya fito ma har tayi baccin ta Teemah kam cikin natsuwa batare da damuwar komai ba.

Kallo 'daya yayi mata ya 'dauke kansa, sai daya sa kaya kafin ya shimfi'da dadduma ya tada sallar nafila kamar yanda ya sabayi kullun, shafa'i da wuturi ya 'kara a kai sannan yayi zaman ro'kon mahallici haka ya dinga jero addu'o'i akan Allah ya kawo masa sauki cikin al'amuransa ya daidai ta tsakanin zaman sa da iyalinsa in har hakan shine alkahirin dake cikin rayuwarsu gaba 'daya, kuma ya jikan Mahmud yasa mutuwa hutunsa ce.

Bayan da ya idar ma be tashi akan dadduman da wuri ba, sai da yaji ya dan nutsu kafin ya tashi a awurin.

Ji yayi kamar yakoma parlour yayi baccinsa a acan, amma sai yaga rashin dacewar hakan kuma daga yanzun baya son yadinga bawa shai'dan 'kofar da zai ringa gina musu katanga tsakaninsu dan haka sai ya tako zuwa gaban gadon ya tsaye nesa ka'dan da ita yana me sake koran shai'dan azuciyarsa.

Su hajiya Teemah sarkin birgima har ta juya tafara bararraje wa, jiyayi yana son ganinta sosai be yiwa idanunsa rowa ba kuwa ya 'karaso 'bangaren da taken tare da zama agefen ta yana me kusan ta kansa izuwa gareta, gashin ta dake tsefe ne duk ya baje mata afuska saboda fitan da ribbom 'din dake kan wanda ta 'daure dashi yayi.

Tunawa yayi da rigimar ta tun tana 'yar karamar ta bata son kitso sam, yasan hakan ne sanadiyyan zuwa hutu daya keyi acan Damaturu, wasu lokutan idan yana can shine zai zauna ya tsefe mata kan da lallami wataran kuma har sai ya siyo mata tarin choculates kafin take zama, tun be iya tsifan ba har ya zo ya koya da kyau yana mata a weekend.
Idan za'a yi kitson ma sai an kai ruwa rana kafin asamu ayi, bayan haka kuwa idan taga kitson akanta sai tafi kowa iyayi da yanga dashi.

Har ta girma bata son kitso, kullum kanta atsefe, Mummy kanta tayi tagaji 'karshen ta haka ta ha'kura ta 'kyale ta har abin yabi jikinta. Hakan kuwa be sa gashin ya lalace ba, domin yana nan ne kamar mara zuciya tana dai yin saloon akan lokaci amma babu kitso, gashi ba'ki kullum yana shai'ki ban sani ba ko dan kasancewar ta tsakiyan fulani ne ko kuma nata halittan ne haka oho.

Hannu yasa a hankali ya tattara mata gashin gaba 'daya zuwa tsakiyar kanta kusa da goshin ta anan yasa ribbom 'din ya 'daure mata gashin, dan yasan anan kam kowani irin bacci zatayi bazai ta6a takura ta ba.

Idanunsa ya tsayar akan fuskar ta ya tsaya 'kare mata kallo musamman 'dan 'karamin bakinta na rashin kunyan nan.

Da yatsan sa ya shafo bakin a hankali sannan ya maida hannun nasa gaban goshin ta yana 'dan shafa 'kananun gashin dake gaban goshin a hankali ta yadda bazama tasan ana ta6a jikin ta.

Abbas ya kai kusan 15mins agaban ta sannan ya tashi ya koma 'dayan gefen ya kwanta shima yasata agaba yana kallon ta a haka bacci yayi awon gaba dashi.
Chapter 115 · 0% Book details