← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 163

Sashe 94

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" _i don't care Ummah, shi 'din lokacin da_ _abubuwan sukayi ta faruwa yana ina?, da ace an samu_ _nasarar cutar da ita Ummah da ya za'ayi, nifah banga abin damuwa_ _anan ba dan tausayi ina jin tausayinsa mana amma gaskiya_ _bazan sake barin yarinyar nan ta zauna tare da muguwar matar nan ba, domin_ _amanar ta aka barmin, koma menene zatayi tayishi tagama anan babu inda_ _zataje_ "

" _Muhammad_ !!
Ummah tafa'da tana kallonsa.

Juya kai yayi ya tare ta da fa'din
" _bazaki gane bane Ummah, wallahi na_ _tsani matar nan, ki fahimce dan_ _Allah Ummah, wani lokaci fah jinake kamar inje_ _in sa akamamin ita nayi ta dukanta har se_ _ta suma......amma bazan iya ba, bazan mata haka ba_ _saboda darajar_ _Mahmud_ , _albarkacin 'dan data haifa take ci_ _awurina da kuma Abbah in badan_ _haka ba da ni ka'dai nasan me zan_ _mata.... kiyi ha'kuri Ummah amma gaskiya yarinyar nan bazata_ _koma ba koda kuwa me ze_ _faru_ "

Ummah kam shiru tayi tana kallonsa yanda yasata agaba da masifa, amma bata wani yi mamaki ba dan tasan abinda ke cikin ransa yake fa'da mata and kuma tasan iya gaskiyarsa kenan dan haka tayi shiru tana sauraransa.

Yana gama maganar ya tashi ya wuche zuwa 'dakinsa da ido kawai Ummah tarakashi har ya shige ta daina kallonsa sannan ta dawo da idanunta gabanta.

Koda ya koma ciki ma tunani ne duk yabi ya ishe shi, sosai yake jin haushin Anty tare da Allah wadai da halinta, at d same time yana tausayawa Fateemah, cikin haka ya tuno da abinda yafaru 'dazu a wajen dinning, yasan halinta sarai tana dai-dai 'dinta ma bata bawa abinci daraja ba balle kuma ance tana cikin damuwa ai se ahankali.
Shiyasa ma yaga duk ta rame ta lalace.

Wayarsa ya 'dago ya 'kira layin Hannah.

Hannah na 'ko'karin shiga wanka taji 'karar wayanta, zuwa tayi ta 'daga tare da yin sallama.

Ciki-ciki ya amsa mata tare da fa'din " _Hannah me kikeyi_ _ne pls_ ?

Sai da ta 'daga idanu sama ta kuma juya su kafin tace " _wanka zan_ _shiga Yayah_ "!

yace
" _Okay, akwai abinci_ _agurinku_ _ko_ ?

" _Ehh sai na Teemah ne wanda bata ci ba_ "

cewa yayi
" _Yauwa ki bata ta_ _kawo min_ _yanzu_ "

Hannah da mamaki tace
" _Toh, amma Yayah baka ci abinci 'dazu_ _ba_ ?

Be bata amsar tambayarta ba kawai sai yace da ita
" _hope kinji me nace_ _ko_ ?

Da sauri ta bashi amsa da fadin
" _Umm naji_ "

Be sake magana ba ya yanke 'kiran kawai.

Bin wayar Hannah tayi da kallo sannan ta 'karaso wurin Teemah tace " _Yayah yace wai ki kai masa abinci inajin tsutsar ciki ke damunsa, 'dazun nan fah yaci abinci_ _amma kiji wai a'kara kai masa wani_ "

Teemah tuni tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka tace " _Hannah ni kuma zankai masa dan Allah_ ?

" _nima haka yace min ko baki ji ba sanda nace masa_ _wanka zanshiga, ki daure ki kai masa yanzu zaki dawo ai_ "

Hannah tana maganar tana 'ko'karin 'dauko mata plate 'din abincin.

" _ungo ki kai masa_ "

Kar6a Teemah tayi ta kama hanyar fita.

" _'Bangaren yamma zakiyi 'kofarsa ce ka'dai zaki fara gani agabanki_ "
cewar Hannah dake tsayen abayan Teemah.

Teemah kam fita tayi ko waiwayowa batayi ba ta fice daga 'dakin
tana jan 'kafa kamar bazata ba, tariga tasan halinsa sarai bawani abincin da ze sake ci tunda baya cin abinci sau biyu lokaci 'daya 'kilan kawai wani abin ne yasa shi cewa takawo masa.

Da sallamarta ta shiga 'dakin nasa taje ta ajiye abincin akan 'dan 'karamin dinning 'din dake 'dakin nasa me kujeru biyu kacal.

Tana shirin juyawa ta tsinkayi muryarsa yana fa'din " _kawo min_ _nan_ "

Komawa tayi ta 'dauko sannan ta kawo masa tana ajiyewa shikuma yana mi'kewa yake fa'din " _zauna kici ina zuwa yanzun_ _nan_ "

Hawaye kawai taji ya gangaro mata, kamar tasa hannu aka tayi ihu dan takaici, dama tasan bacin abincin zaiyi ba, da ta san cewa ita ze sa taci ma da bazata zo ba.

Kusan mintina biyu tana zaune da abincin agabanta, tana share hawaye, dataga ba yanda zatayi kawai sai ta bu'de tafara ci ahankali sanin halinsa datayi akan hakan, dan tunda yace taci toh matu'kar bataci ba baze ta6a barinta ta tafi ba, dan haka sai ta ringa ci ahankali take turawa bakinta harta jita dam, daga nan ta tsaya da cokalin ahannunta, tana jiran fitowarsa.

Ashe watsa ruwa yaje yayi sai da ya shirya kafin ya dawo parlourn cikin kayan baccinsa me birgewa jikinsa na tashin sayayyan 'kamshi.

Zuwa yayi ya zauna tare da ha'de hannayensa wuri guda yasata agaba yace mata " _ya dai_ ?

" _Na'koshi ne Yayah_ "
Muryarta na rawa tayi maganar.

Baya yayi ya jinginu da jikin kujera dan yaga ba laifi ta 'danci ka'dan sai yace " _U can leave, amma fah ki kiyaye kina cin abinci akan lokaci dan duk ranar dana_ _dawo na ga baki canja ba wallahi zan sa6a miki ne, bana son yawan_ _kukan nan da damuwa kuma, ko shi Mahmud 'din ce miki yayi ki dinga yi_ _masa kuka idan_ _ya rasu_ ?

Da kai ta bashi amsa alamar " _ah'ah_ "

Sai kawai yaci gaba da da fa'din
" _Ya kamata kisani Mahmud is now no more, baze ta6a dawowa ba, is better ki nutsu ki san_ _abinda ya dace ba ki ringa damun mutane da kuka da damuwa_ _ba, zan bawa Abbah_ _ha'kuri akan tahowarki dan nasan beji da'din hakan ba, sannan_ _idan nadawo naga kin saki jiki ni da kaina zan kaiki Lagos 'din ki dubo_ _su har wurin Mummy ma duk zan kaiki amma sai naga kina jin_ _magana tukunna......_ _clear_ "

Ta gya'da kanta tare da furta " _yes_" ahankali.

" _Toh gudnight_ "

Daga nan be sake kallon inda take ba ya maida idanunsa kan television.

Tashi tayi ta fita zuciyarta fal farin ciki, musamman dataji yace zai kaita gurin Mummyn ta, ai gaba 'daya sai ta manta da komai.

Hannah ma sai da ta fahimci farin cikin dake kan fuskar Teemahn data tambayeta kuwa take ta sanar da ita yanda sukayi da Abbas 'din.

Murmushi kawai Hannah tayi tare da jinjina masa aranta tasan yana yin duk hakan ne dan yaga 'kuncin Teemahn yaragu.

Wani lokaci takan ga kamar Teemahn na da sa'ansa domin Yayah yakanyi mata abinda bakowa ke samun hakan daga gareshi ba, bata san dalilin sa ba amma tana jinjinawa dangatar dake tsakaninsu.

*****
Washegari 'karfe bakwai ya bar gidan yayi tafiyarsa ya koma Rivers state, Umman ce ka'dai tasan da fitarshi itan ma atsatstsaye yazo yayi mata sallama yafice.

Tasan halinsa sarai yanzun yana hakan ne dan kar tasake yi masa magana akan Fateemah shiyasa yayi hakan ita kuwa yanzu ta riga ta saduda barinsa zatayi taga iya gudun ruwansa tunda kam yace Fateemahn amanar sa ce ita, toh nata kallo ne.

*Masoya Abin alfahari ina yin ku sosai da sosai wallahi nima, bazance muku komai ba dan bani da bakin gode muku all i know is that kuna sani farin ciki...... addu'o'in ku nasani walwala, Allah ubangiji ya bar minku ya sada ku da dukkan alkhairinsa.*

~WANNAN SALMERHN NAYI MUKU FATAN ALKHAIRI~

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍

[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated to my sister Khadeeja Usman Allah ya bar min ke._

*Bismillahir rahmanir raheem*

_A good heart and a good nature are two different issues, A good heart can win many relationships, But a good nature can win many good hearts._

🅿 *70*

Kwanan Fateemah biyu agidan sannan ta 'dan saki jikinta, Daddyn Abuja ma daya dawo sosai yayi farin ciki da zuwanta dan ko shima bawani da'di yaji da barinta da akayi acan ba kawai de yayi shiru ne saboda al'amarin ahannun matan yake, yanzu kuwa da ya ganta ya kuma ji labarin cewa Abbas ne ya kawo ta ai shikenan gaba 'daya sai ya manta ma da haushin Abbas 'din daya keji ya ringa sa masa albarka.

'Ko'kari sosai Hannah keyi wajen ganin ta mantar da Teemahn damuwar da take ciki, saboda bata barinta zama shiru sai de in tatafi makaranta wanda makarantar ma dan ya zama dole ne shiyasa lokuta takance da ita badan tana zaman 'dakin rasuwar mijinta bama da se ta ringa rakata makarantar ai.

Teemah kam baki take ta6ewa ta yi shiru, dama yanzu gaba 'daya ta canja wannan rashin jin duk babu shi ta dawo wata salihar 'karfi da yaji, wani lokaci idan tana abu se kaga kamar ba ita ba.

Haka abinci ma yanzu bata ci da wasa 3square meal 'din nan duk basa wuceta takanyi 'ko'kari taci a'kalla kamar spoon goma koma fi akowani lokacin cin abinci, Ummah sosai take jin da'din canjawar tata musamman data ga yanzu tasaki jiki har tana cin abinci batare da an takurata ba.

Damuwar ma duk ta rage shi yanzu ta barwa zuciyarta, addu'ah kawai take masa akowani lokaci musamman idan tayi sallah toh sosai take 6ata lokaci waken yi masa addu'ah wanda a lokacin ne tafiya yin kuka sai de ko Hannah bata bari ta fahimci yanayin data ke shiga.

Tana waya dasu mummy da Anty akai-akai, inda mummy kanta da taji cewar Teemah ta dawo Abuja sai da ta sau'ke ajiyan zuciya da can 'din ma kawai ta daure ranta ne tare da yiwa Anty kawaici, amma tunda ta koma Dubai sai taji zuciyarta ya kasa nutsuwa sai take ganin kamar Antyn zata iya sake cutar da Fateemah tunda tana gabanta.
Chapter 94 · 0% Book details