← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 163

Sashe 40

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Lokacin da aka fara zana waec kusan tare Mahmud da Teemah suke yi dan baya ta6a barinta tayi karatu ita kad'ai ko exam d'inma zataje tare suke tafiya.

Ana tsakiya da waec d'in ANTY tasake hura masa wuta akan yadawo gida haka nan tunda already yagama service d'insa toh zaman me kuma yakeyi, tace masa ya dawo gida wai afara maganan aurensa da Munirah.

Tambayar ta yayi cewa "wani maganar aure kuma ?.

Dan shi shaf yama manta da batun tun sanda yadawo nan, bai sani ba ashe abin har yanzu yana ran Anty.

Koda ya tambayetan haushi taji bata bashi amsa ba sai kawai ta yanke k'iran daga 6angarenta tacigaba da masifah.

Acikin kwana biyu tak'ira shi yafi sau a'kirga kuma duk akan maganar ne, daya ga haka sai ya 'kira Abbansa yayi masa bayani.

Abban nashi ma cewa yayi ya koma gidan kawai tunda haka mahaifiyarshi keso shi yasan mai zaiyi akan maganar auren.

Bai 'ki maganar Abban ba amma yace masa sai an gama weac zaizo, daga lokacin zuwa agama d'in yakama kwana tara kenan ya rage.

Dahaka sukayi sallama da Abban nasa kowa ya yanke 'kiran.

Mahmud wannan karan kokad'an bai bari Mummy ta san da labarin ba, dan yasan tana sani zata sashi agaba sai taga yatafi itama kafin hankalinta ya kwanta,bawai dan ta gaji da zamansa tare dasu ba " a'a " kawai wai dan kar ashiga hakkin mahaifiyarsa ne.

Tun kafin a kammala waec kuwa yafara shirye-shiryen tafiya gida, kwana biyu bayan waec d'in ya shirya yatafi wannan karan kam shirinsa na barin garin ne gaba d'aya, saboda da wuya ya sake dawowa, duk wani abu da yyake nashine na buk'atarsa ya tattare su haka yatafi ya bar kowa da k'ewarsa agidan.

*****

Dawowar Mahmud Lagos shiyafi komai faranta ran Anty dan tana ganin kasancewar sa tare da ita shine zai sa burinta yayi saurin cika, musamman ma yanzu da take ganin yin auren nasa shine zai sa ya rabu da son rayuwa awurin Khadija, tunda idan da aure akansa ai bazai yi gigin son tafiya wani gari yabar iyalinsa ba.

Adole take sa shi ya shirya ya ziyarci Muniran batare da yaso ba, kuma wannan shine karo na uku kenan dayake zuwa wajen Muniran, sai dai abinda Anty bata sani ba shine zuwan nasa ba anfanan su yake da komai ba saboda a duk sanda zai baya fad'a mata wata magana daban face sake jaddada mata dayake akan baya kaunarta and he can't even marry her saboda bata dace dashi ba.Maganar arzi'ki bata ta6a had'asu ba.

Antyn ce da kanta tasa Mahmud ya sanar da Abbansa cewa ya samu matar aure wai aje ayi masa tambaya, afad'ar Antyn
wai in itace tayi ma Abbab maganar tasan ba amincewa zaiyi ba kuma zaiga kamar ra'ayinta bana Mahmud d'in ba. Shiyasa take so shi yaje dakansa yayi bayani.

Nan ma da 'kyar Mahmud ya yadda ya amince akan zashin d'in har sai da yaga ranta na shirin 6aci kafin nan ya amince da zuwa d'in.

Da farko kafewa yayi akan shi bazai iya ba, ita tayi magana wa Abban nasa mana ai ba dole sai shi dakansa ba, kuma dagangan ya ya kafe akan hakan saboda yasan tana tsoro yanzu bakamar da bah, bazata iya fad'an ba shiyasa shima ya kafe akan hakan.

Dayaga rantan ya 6aci kafin ya amince akan zaiyi magana wa Abbahn saboda shi wannan mitan ya tsana bakomai ba, itakuwa Anty babu abinda yafi birgeta akan tayita k'ananun maganganu......aganinsa fah.

Ranar wata talata da dare around 8:00pm yaje yasamu Abban bayan sallar isha'i,
Abban ma na ganinsa ya fahimci akwai abinda ke damunsa, domin jikinsa sanyi k'alau ya shiga gurin Abban, zuciyarsa duk ba dad'i don ya tsani yarinyar can bai san me yasa ba, gashi mahaifiyarsa ta nace akan dole sai ita zai aura, infact shi auran ma ba yanzu ya shirya yi ba gaba d'aya.

Zuwa yayi ya zauna akusa da Abban ya gaida shi, shiru ne yabiyo baya bayan Abban ya amsa gaisuwar cike da kulawa.

Mahmud rasa ta inda zai fara yayi bai san yanda zai fara fad'ar maganar ba, dayake asali Mahmud shirgin mata bai dameshi ba, shi sam bashi da matsala dasu, aganinsa mata damuwa ne sosai su, ko lokacin da ya ke higher institution d'insa ma inka ganshi da mata toh friends ne ba komai ba, kwatsam sai gashi yanzu mahaifiyarsa ta 6ullo masa da maganar aure alokacin da shi sam bai shiryawa hakan ba, amma babu yanda zai yi dolensa ya kar6i maganar kodan darajar da take dashi na mahaifiya agareshi bazai bada ita ba, yayi alk'awarin cewa da iznin Allah sai ya nuna cewa shid'in d'aah ne, kuma na halak cikakke.

Ido Abban ya tsura masa da dukkan kulawa yana kallonsa , sosai ya fahimci d'an nasa na cikin damuwa sai yayi gyaran murya ya fuskanci Mahmud d'in da kyau sannan yace masa " yah akayi ne Babana"!.

Ahankali ya d'aga kai ya kalli Abban nasa suka ha'da idanu take sai yayi gefe da kansa kamar mace tare da k'ak'alo murmushin k'arfin hali.

Da k'yar ya samu ya tattara bayanan dake bakinsa ya dunk'ula ya furta "Ab...bah wai dama maganan yarinyar da zan aura ne, wai ko za'a je ayi tambaya".

Murmushi Abban yayi sannan yace "Mahmud ba dama, wai ko za'a je ayi tambaya ko kuma kana so aje ayi maka tambaya?

Murmushin yakuma yi batare da magana ba.

" babana yau d'in kai ke yin abu kamar mace!?

" hmm toh a ina yarinyar take?

Abban ya sake tambayarshi.

Ahankali ya kwatantawa Abban nasa,daga yanda yake maganar sai Abban ya fahimci abin sam baya ran Mahmud d'in musamman daya tuno ranar da Antyn ta maresa akan wata yarinya,sannan ranar da Mahmud d'in ya 'kirasa alokacin dayake damaturu akan maganan auren da Anty take yawan yi masa harma ta uzzura masa yadawo gida duk akan maganar ba shakka wannan duk tilastawar Maryam ne, ni kuwa bazan ta6a tilastawa yarona abinda baya so akan wad'anda bama sanin asalinsu yayi ba.

Lokacin da Mahmud yasanar da Anty cewa sun gama magana da Abban kuma ga abinda yace ji tayi kamar ta goyashi saboda farin ciki.

Tayi zaton ai Mahmud d'in zaiyi mata taurin kai ne yak'i zuwa amma kuma sai yaje, hakan kuwa ba k'aramin farin ciki yasata ba.

Abbah binciken yayi kamar yanda ya fad'ad'in yayinda binciken ya d'aukesa kusan sati kafin ya gama gamsuwa da duk wani abinda yake son sani game da wannan family d'in.

Bai sanar da Mahmud ba ya k'yaleshi, yana so ne yaga ko Mahmud d'in zai zo dakansa yasake tambayarsa idan yaga shiru ko yayah ,yasani cewa matuk'ar da yaddansa a auren to shi zaifi kowa rawar jiki dan ganin an kammala komai dawuri inkuwa bahaka ba ma'ana bai sakeyin magana ba toh kenan shima be wani damu da maganar ba kenan rashin damuwarsa da maganar kuma na nuni da cewa baya ra'ayin abin har ransa.

Hakan ya sanya Abbah yayi gum da magabar shima yana jiran yaji daga Mahmud d'in.

Rashin ha'kurin Anty yasanya ta kasa ha'kuri da taji shiru babau wanda yasake bi takan maganar sai ta tuntu6i Abbah da maganar shikuwa yace mata bincike yake yi tukunna har yanzu, ita a ganinta tunda Mahmud yariga yayiwa Abbansa magana ai itama zata iya yi masa maganan irin kamar Mahmud d'in ne itama ya sanar da ita.

Bata wani damu ba saboda ita kanta bata san asalin tarihin 'kawartan ba shiyasa koda Abban yace zaiyi binciken bata damu ba.

*****
Teemah kuwa tana can sun gama hutun interval d'in dake tsakanin waec da Neco d'in har sun fara Neco yau suke na biyu,tun kafin ayi nisa tafara missing d'in Mahmud domin tasaba karatun dashi sosai yake highlighting d'inta akan wasu abubuwan da bata ganesu, yanzu kuwa babu shi, sai dai tayi ita kad'ai, dayake Daddyn ya sai mata waya a satin daya gabata, arana ta uku tana tsaka da karatun data ji ba sugar sai ta 'daga wayarta ta ta 'kira Mahmud tayi ta masa complain akan ita fah bata ganewa tunda yatafi take shan wahalan karatun gashi kuma ya'ki dawowa.

Lalla6anta yayi tayi yana bata ha'kuri a itakuwa tayita masa shagwa6a,ahakan ya tambayeta inda bata gane ba d'in data fad'a masa sai yayi mata bayani ata'kaice yanda zata gane.

Shikenan kusan kullum in tana da exam sai sunyi waya dashi a haka har aka kusan kammala Neco d'in .

2 days to candidate d'inta Daddy suka rabu da Abban Mahmud A lagos basu ma gama abinda sukeyi ba amma daddyn Teemah yace zai dawo gida saboda graduation na Teemah yana so ya halatta.

Anan Abbah yayi mata fatan alkhairi harma yace badan akwai aiki agabansa ba da shima zai je shi, Daddy ne yace bakomai ai addu'ar ma ta wadatar, sai Abban yace duk da haka ma insha Allahu idan yasamu lokaci ko bayan graduation d'in ne zaije musamman ya ziyarcesu.

Farin ciki ne sosai yacika ziciyar Daddy dan yajima baiji irin hakan daga bakin abokin nasa ba, so yana jin hakan yasan ikone kawai na ubangiji dayake kawo 'karshen duk wani al'amari inma me kyau ko akasin haka.

Ko da yaje gida kuwa bai sanar da mummy ba saboda yana son koda Abban Mahmud d'in zaizo toh zuwan ya zamewa mummy na bazata, kar kuma ya sanar da ita yanzu cewa Abban zaizo zuwan kuma yak'i yiyuwa duk dama ba'a fatan hakan, amma kuma idan hakan ya faru zai kasance ne kamar shine ma'karyaci a idanunta.

_Comment vote and_ _share pls_ 🤞🏻

(4 those that missed Abbas insha Allahu next page zaku jishi )😃

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Sometimes u have 2 4give & 4get,4give them 4 _hurting_ & 4get that they even _exist_ .

🅿 *35*
Chapter 40 · 0% Book details