← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 163

Sashe 43

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ta tambayeshin ma be ko nuna alamun yaji ta ba sai data 'kara maimaitawa sannan ya 'daga mata kai alamar ehh shi 'dinne.

Take sai 'yan shagwa6anta suka motsa mata ta ha'de rai ta tura baki gaba yanda tayin sai ya 'kara mai data 'yar 'karamar yarinya.

Murmushi yayi aransa yace " mai hali kenan".

Azahiri kuma sai yace mata " me kuma yafaru naga kin 6ata rai ohh aren't u happy 2 see me?".

Sai ta 'daga kanta sama.

Waje ya fito da idanunsa tare da fa'din " saboda me"?

"Bakai bane ka tafi ka manta dani?"

" ohh sorry sis who told that na manta dake?, Allah kullun kina raina kinji"

Idanunsa akanta yake maganar da dukkan kulawa amma sai ta'ki yarda tawani karya wuya irin ita bata yadda ba 'dinnan.

" toh shikenan tunda yanzu nazo bashikenan ya wuche ba"?

Sai ta jijjiga kanta alamar "a'a".

Daya rasa yadda zaiyi da ita sai 'daga hannayensa duka biyu yakamo kumatun ta dashi, jijjiga kan yayi yana murmushi yace " stubborn head 'dinnan har yanzu yana nan ko?.

Yanda yayi 'din ita kanta yabata dariya amma sai ta juya masa baya tana dariyar 'kasa-'kasa.

A'dan nesa dasu kad'an ta hango wata 'kawarta dasuka fara 'kawace lokacin da aka fara waec, ta yaba da hankali da nutsuwa irinna yarinyar shiyasa ma bata yi mata mugun hali ba irin yadda tajewa sauran 'kawayenta.

Tana ganin yarinyar sai tafara tafiya da nufin 'kiran ta taga yayanta.

Takunta biyu kafin tayi na uku taji Abbas ya 'kira sunanta " FATEEMA" cikin wannan lion voice 'dinsan nan me ratsa mata zuciya.

Take ta tsaya cak tare da waiwayowa ta kalle shi, ahankali ya tako ya iso inda take tsayen, shima ya tsaya.

"Tafiya zakiyi ki barni anan?"

Da sauri ta jijjiga kanta.

" toh menene"?
ya sake tambayarta?.

Kasa magana tayi awannan lokacin domin irin kallon da yayan ke mata ya banbanta dana kullum, jikinta duk taji ya mutu sai kawai tayi 'kasa da kanta.

Bata zata ba sai taji yasa hannunsa yakamo hannun ta nadama ya bu'de yasa ka mata wata takarda sannan ya maida hannun ya rufe mata.

Da ido tabi hannun nata da kallo yayinda ta matse hannun nata gam-gam ta ri'ke takardar da kyau dukda bata san ta menene ba amma tanaji ajikinta tamkar takardan nada wani kyakkyawan muhimmanci arayuwarta.

Sai daya sake mata hannun ya maida nashi 'daya cikin aljihu yayinda 'dayan ke sau'ke daga gefensa kafin yace mata " zan tafi Fateemah inada aiki a office banida isheshen time yanzu "

Dasauri ta 'daga kai takalleshi sai yayi murmushi yace " sai munyi waya".

Yana fa'dar hakan yajuya yakoma mota be ko sake waiyowa ya kalleta ba, yana shiga kuwa driver yaja kamar daman jira yakeyi ashigo.

Ita kuwa mamaki hanata motsawa yayi saboda data ganshin ko dawasa bata kawo cewa ze koma dawuri haka ba.

Har suka 6ace daga wurin bata sani ba, tana can tana tunani.

Lokacin da runanin ya tsaya kuma koda ta kalli inda taga yayin gani tayi babu kowa.

Dasauri ta 'daga 'kafa ta taho gudu gudu ko zata ganshi amma ina bata ga kowa ba illah 'kuran wata ba'kar mota data hango awajen gate tana shirin fita.

" wai dagaske ne......yah Abbas ............kuma ka sake komawa".?!

Kamar ta fasa ihu haka taji amma kuma bazata iya ba.

Tana tsaye bata bar wurin ba taji ana mata horn sai tajuya dasauri takalli wajen zatonta shine yadawo amma sai taga motar gidansu ne wannan 'din.

Mummy ce ta bu'de motar tafito ta nufo ta dasauri domin yanda taga Teemahn abin ya 'dan bata tsoro.

Mummy na isowa inda take kawai tafa'da jikinta tayi lamo, sai da mummy ta 'dan bata 3mins tayi backin up kafin ta 'dagota ta tsayar da ita agabanta sannan ta tambayeta " me yafaru?.

" mummy Ya.....yah.. ne "
Tayi maganar tana nuna hanyan gate.

" wani yayan me kuma yafaru dashi?"

Mummyn tafa'da tare da jijjiga ta da 'dan 'karfi.

" mummy yah Abbas ne......yatafi.....
Tana gama fa'dan hakan sai ta fa'da jikin mummyn tayi shiru.

Mummy data fahimci 'yartata sai kawai tabarta ayanda take ajikin nata taringa bubbuga bayanta har tasamu ta d'an dawo daidai kafin tasamu da 'kyar ta lallesheta har se da taga ta warware sannan takama hannunta suka shiga ciki.

Tun daga lokacin Fateema bata 'kara yin wani abu da kuzari ba yayinda mummy kuma take jin bada'di tare da tausayin 'yartata.

Tana tsoron kar dai ace yarinyar nan soyayya ce takamata domin kallo 'daya zaka mata ka fahimci badaidai take ba, inkuwa hakane ai ta shiga uku!, yaza tayi ta iya sada Fateemah da farin cikin ta, idan yazamana shi'din ba haka bane azuciyarsa?".
Domin tasan it's hardly ace mutun kaman Abbas yaso Fateemah, kai Allah ma ya sauwa'ke Alla ya kiyaye ya tsare mu da sharrin zuciya.".( Ameen)

Atare suka koma gida koda aka tashi a wurin......ahankali Teemah ke tafiya tamkar mai tsoron taka 'kasa mummy kuma na bayanta itama tana binta ahankali .

Jijjiga kai mummy tayi data ga Teemah ta nufi 6angaren da 'dakinta yake daga shigowanta parlourn ko tsayawa bayiba ta wuce abinta.

Babu komai atare da ita sai mayafinta da kuma wannan takardan da Abbas ya bata, tun lokacin da yabatan har yanzu bata canja masa ri'ko ba bata kuma bu'de taga miye aciki ba.

Tana shiga 'dakin ta tura 'kofar ta datse da makulli sannan tacire head 'din dake kanta tayi jifa dashi akan gadon tare da mayafin baki 'daya tana niytan cire rigar ne taji hannunta da abu, da sauri ta bu'de hannun tare da kallon shi da wuri domin sai alokacin ta tuno da cewa Yah Abbas ne yabata takardar.

Amma saboda ri'kon ' karfi datayiwa takardan ga kuma gumin hannunta da yake gimtse tsawon lokaci, su suka had'u suka narkar da takardan a hannunta.

Da6as ta zauna abakin gado idanunta nakan hannun nata koda tayi 'ko'karin raba takardar da hannunta sai taga ya 'kara yagewa.

Duk iya 'ko'karinta naganin ta fahimci abinda takardar ke 'dauke dashi takasa saboda daidai inda akayi rubun daidai wurin ne yafi samun matsala.

Dolenta ta tattara ta cire da me 'dan girma da wanda
ya raki6e ahannun nata ta ajiyesu acikin side drawernta.

Sannan tacire doguwar rigar dake jikinta yarage daga ita sai pant, underwear da bra, ahakan takoma takwanta rigingine akan gadonta.

Ita kanta bata mecece damuwarta ba, haka kawai sai take jin ta wata iri, tamkar bata da ishashshen lafiya.

Nocking 'din 'kofa taji anfara yi kawai sai ta mi'ke ta nufi bayi batare da ko cire ragowar kayan dake jikinta ba, towel ma ahannu tashiga dashi bayan ta jashi akan 'kofar bayin.

Ba ita fito a bayin ba sai kusan 5:00 hakan ma dalilin tunowa da sallar la'asar 'din da batayi bane shiyasa tafito dasauri.

Tana fitowa kuwa idanunta suka sau'ka akan wannan kwalin da Abbas ya ajiye ma da tun shigowanta bata lura dashi ba sai yanzun.

Sallar dake gabanta ne ka'dai ya dameta adai dai wannan lokacin, dan haka kallon arziki ma kwalin be samu ta nufi wurin kayayyakinta ta 'dauko wanda take son sakawa ta sakashi sannan ta shimfi'da dadduma tare da zunbula hijab ta tada sallahnta.

Comment, vote and share pls🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi masoyana*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

“Time is free, but it’s priceless.
You can’t own it, but you can use it.
You can’t keep it, but you can spend it.
and once you’ve lost it you can never get it back.”

🅿 *37*

Koda ta idar bata bi takan kwalin ba har yanzu, kwanciyarta kawai tayi sai dai tana kwantawan mummy ta fa'do mata arai kawai sai ta mi'ke da hanzari tatafi wurin mummyn dan tasan dole zata damu idan tajita shiru.

Murmushin 'karfin hali ta 'ka'kalawa fuskarta yayinda ta tunkari inda mummyn take, koda mummy taganta ahakan kuwa sai ta 'dan ji dama dama.

Murmushin tayi itama sannan tace
" yanzu kuwa nake so na aika aduba minke sai kuma gashi kin fito"!

Batayi magana ba sai da ta 'karasa kusa da mummyn ta zauna kafin tace " kaina ciwo mummy sosai"
tayi maganar tana wani yatsine fuska tare da dafa goshinta da hannunta 'daya.

" haya niya ai, bari anemo miki magani kisha zaki d'anji daidai".

Mummy tayi maganar tata cikin kulawa sai ta 'kara da fad'in " ki koma 'daki ki kwanta ki 'dan huta idan ankawo maganin sai kisha ".

Kai Teemah ta 'daga alamar " toh tare da mi'kewa tsaye ta kama hanyar 'dakin nata.

Koda takoma 'dakin kuwa kwanciya tasakeyi, so take tayi bacci amma sam sai taji takasa yin baccin ma fuskar Yayanta ka'dai ke yimata gizo tana ganin tamkar bashi 'din bane dagaske tagani.

Wayarta da tun safe take ajiye a gefen mirror itace tayi 'kara alaman shigowan sa'ko kuma 'karan ne ya yanke mata tunanin yayantan datakeyi.

Kuma sai alokacin ma ta tuna da wayarta saboda tunda tafara shiri bata 'kara bi takan wayar ba sai da tagama shiryawa ne ta 'dauko wayar ahannunta ta kashe selfii bayan tafito da nufin tafiya wurin graduation d'in sai kuma ta ji ri'kon wayar ya dameta shine ta aiko aka ajiye mata ad'aki.

Toh shiyasa bata 'kara bi takai ba sai kuma yanzun dataji wayar tayi 'kara.

Ahankali ta tashi taje ga wayar bawai dan 'karar sa'kon dataji ba " a'a " kawai jii tayi tana bu'katan ganin cikin wayar tata da ta 'dau tsawon awanni batare da sun gana ba.

Dawowa tayi ta kwanta rigingine kanta nakan pillow yayin da 'kafafun ta ke ajiye akan katifa ta wani had'esu guri d'aya.

Koda ta bu'de wayar sa'kon Mahmud tafara cin karo dashi a fuskan wayar ga dukkan alamu shine sa'kon da ya shigo 'karshe 'dan mintina 'kalilan dasuka gabata .

Bud'e sa'kon tayi domin ganin me aka rubuta mata .

" wai nayi laifi ne bansani ba? "
Haka taga anrubuta

Sai tayi reply da " haba laifin me zakayi kuma yayah"!
Chapter 43 · 0% Book details