← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 163

Sashe 84

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai de kuma ai yiwa Fateeman haka bashine mafita ba, domin koda abun yatashi mata mijinta ze iya yin maganin matsalar ai tunda shi ba 'a yi masa komai ba.

Sai de duk da haka ta wani guri batun Munniran ze iya samun kason maki mafi girma idan aka gangara 6angaren yawan bu'katuwa da kuma sashin gazawa.

Ta iya yiwuwa hakan ya ta6a zaman lafiyarsu idan mijin yaga ji da yawan bu'katan Fateeman ze iya nuna gazawarsa wanda ta nan babban matsalan zai iya bayyana harma ya illata farin cikin dake cikin zamankewarsu....... lallai Munnira tayi tunani me kyau.

Anty na cikin wannan tunanin se Munnira ta katse ta da fa'din

" _Anty kinsan iskancin dana sa akayi musu kuwa_ ?

Da kai Anty ta bata amsa alamar " _a'a_ ".

Murmushi Munnira tayi sannan tace " _Mahmud bashi da daman taimakon Fateemah koda jarabarta ta tashi_ _saboda shi bashida anfani, tsakaninsa da ita sai de kallo Anty, kinga idan_ _abun ya isheta dole zata nemi mafita mafitar danasan bazai wuce tace_ _araba auren sun ba, kinga dazarar auren yarabu sai inkoma insa adawo wa_ _Mahmud da lafiyar mazantakarsa sai muyi aurenmu dashi, ko kuma ince ya aureni ni zan iya_ _zama dashi ahakan tunda ita ta'ki kinga bayan an 'daura auren sai lafiyarsa ta dawo ni_ _kuwa zama daram Anty sai ke sai jikoki"_
Ta 'karashe maganar da dariya.

Anty ma murmushi tayi da farko dataji batun Munniran akan Mahmud hankalinta ba 'karamin tashi yayi ba amma 'karshen labarin sai ya wanki wancen 'din tunda taji komai zai dawo normal daga baya sai taji ranta wasai.

" _lallai kanki naja 'yan mata shiyasa nake 'kara sonki ai, dan nasan ki akwai kishin kai, sai dai kuma fah karki kuskura wannan abin yata6a min lafiyar yarona dan kinsan mutuncinsa kenan_ _ako'ina_ "

Wani dariyar 'keta Munniran tasaki kamar wanda Anty sa'ar ta ce,
Sannan tace

" _Haba Anty,ni da nake farautarsa dan anfanin kaina taya kuma zan bari gangancina ya illata sa, komai da kike gani akan tsari nake yinsa kuma kafin ayi aikin sai dana tabbatar da cewa za'a iya rabashi da hakan_ _aduk lokacin dana bu'kata kinga kuwa ai ba abin damuwa_ _anan_ ".

Anty kuwa tamkar wawuya haka take binta da idanu domin gaba 'daya ta tsinke da lamarin yarinyar gani takeyi tamkar wannan tamafi uwarta shu'umanci, amma tsabar haukan Anty bata ji ko 'diris aranta cewa wannan ba kalan auren 'danta Mahmud bane sai ma taji 'karin 'kwarin gwiwa akan Munniran.

Ita kuwa Munnira
tana gama fa'din maganar ta mi'ke tsaye tare da gyara zaman rolling 'din dake kanta tace

" _Yauma ni kinga son ganinshi nakeyi wallahi shiyasa ma kika ga na fito_ _da sassafen nan office 'dinsa zani gara tun wuri mu fara_ _fahimtar juna tunda gab muke da zama_ _abu 'daya_ "

" _Aikuwa da gaskiyarki_ "
Anty tabata amsa gami da fa'din, " _inkinje ki dawo dan Allah kafin ki wuce gida akwai sa'kona_ "

" _Toh Anty bazan_
_ma da'de ba_ _zandawo_ "
Munnira tayi maganar tana nufan 'kofar fita daga parlourn.

*****
Mahmud kam lokacin daya shirya fita aiki exactly be sa6a lokaci ba yakan yawaita barin gida 7:30 dayake sai 9:00 ake bu'de kamfanin nasu so yana samun time yayi komai atsanake.

Ko yau 'din ma haka yayi shirinsa cikin wata arniyar shadda gezna milk colour, Fateemah nata binsa da idanu domin ita yau 'din gaba 'daya bata jin da'di, fargaba ne yacika mata zuciya da batasan kona menene ba, hatta ga6o6inta asake take jinsu, duk abinda Mahmud yakeyi da idanu kawai take binsa.

Break fast ma yau tea ka'dai taha'da masa ita kam tasha ma sam ta gagara shine dai yasha ka'dan sai ya tashi da niyyar tafiya, itama mi'kewa tayi dama already mayafinta yana ajiye agefenta sai kawai tafara warware shi.

Ganin hakan yasashi tsayuwa saroro yana kallonta sai data gama warwarewan kafin yace mata " _yau fah ba inda zakije, agida zaki zauna tunda kin'ki ki sanar dani_ _dodon dake hanaki zama, kuma ma kinga yau friday ne bazan da'de ba zandawo 12:00_ _za'a rufe office ki_ _zauna agida kijirani_ "

Fateemah najin hakan tafara masa kuka dayake daman acike take da damuwa so kamar jira take yayi maganar kawai tafara masa kuka tana fa'din "wallahi ita bazata zauna ba.

Yayi -yayi ta sanar dashi matsalan amma ta'ki, sai kawai taci gaba da kukanta, haka Mahmud ya6ata tsawon lokaci yana bata baki da lallami akan ta ha'kura ta zauna agida amma ta'ki.

Daga 'karshe kawai ya ha'kura yasata agaba yace toh suje a lokacin ma har 8:01am tayi.

Haka suka kulle 'kofan suka nufi inda motarsa take.

Har yayiwa motar key sai ya tuna ashe ya baro jakansa aciki wanda ke 'dauke da dukkan muhimman abubuwansa na wajen aikin.

Fita yayi yakoma ya 'dauko jakar wanda ya barta anan kan cough inda ya zauna dan rarrashin Fateemah.

Gurin motar ya koma ya bu'de baya ya ajiye jakar duk da idanu kawai take binsa.

Be shiga motar ba taga yasake komawa cikin gidan can bayan mintina biyar sai gashi yafito da 'dan saurinsa yashiga yace " _kin wani ha'da min Tea me sa fitsari sai da na koma na yi kafin naji dama dama_ .

Kauda kai kawai tayi dan batasan me zata ce dashi ba damuwar ta ma ka'dai ya isheta.

Horn ya dannawa Gate man 'dinsu dake daga can baya yana duba flowers 'din gidan.

Da gudu yazo yafara 'ko'karin bu'de gidan, kafin ya 'karasa tura gate 'din ne sai Mahmud yasake ce mata " _inajin kamar nayi mantuwa aciki wallahi, kuma fah bakomai bane tsaban yanda kika_ _rikitani ne da rigimarki yasa nake ganin haka_ ."

Shiru tayi masa yanzun ma shima kuwa sai ya shareta yaja motar yayi gaba dai-dai inda gateman 'din yake ya tsaya kamar yanda suka saba kullum suka gaisa sai de yau Mahmud yaciro ku'di ya dan'ka masa ko jiran godiya be yiba yaja motar suka fita.

Sai da suka hau kan titi kafin ya 'dan kalleta yace
" _inajin nextweek fah zan koma katsinan nan, se ki shirya tafita bakince_ _zaki_ _rakani ba_ ?

" _Umm_ "
Tace a'kasan ma'koshi.

" _toh sai ki fara shiri domin da mota zamu_ "

'Dan sake fuska tayi ka'dan tace " _zamu har Abuja ko_ _Yayah_ "

" _Insha Allahu, ko ni banje ba ke zaki je_ "
ya bata amsa atakaice.

_Toh fah readers sai ku mammatso kusa domin jin yanda ha'duwar Mahmud, Munnira da kuma_ _Teemah_ _zai_ _kasance_ ........za'a kafta🤞🏻

~Taku akullum Salmerhmd.I heart u all masoyana.~ 🥰

_Comment, follow, Share and Vote@_ ~Serlmerh-md~

*Salmerh ce* 😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

Dedicated 2my lovely fans da ke ~whattsapp~
~facebook~ &
~Wattpad~
Inayinku sosai nima,
Allahu ya bar 'kauna.

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_True friends are not the ones who are there when it’s convenient. True friends are there when it’s not._

🅿 *65*

Sa'kon gaggawa ne ya iso musu cewar kayan da za'a kawo musu a Lagos za'a sau'ke su so sai aka wakilta Abbas akan zuwa kar6o kayan, dama da farko maiduguri za'a taho da kayan direct sai kuma aka samu wani matsala inda dole sai de a sau'ke a Lagos sai suje su 'dauko.

Ko ka'dan Abbas be kwana da niyyan tafiya ba amma da asubar fari aka sanar dashi lokacin ma yana zaune dafe da kansa bayan farkawar da yayi daga bacci da mafarkin Fateemah sosai mafarkin ya tsaya masa aransa, wai tana ta kuka saboda tarasa hanyar zuwa ko'ina ne oho, duk inda tabi de sai taga gurin yah mata duhu gashi wai tana ganinsu agabanta sun kewaye ta, a wurin akwai Mahmud, yaga Hannah, Antyn Mahmud yaga Daddy ma da kuma wasu mutane kimanin biyar da be sansu ba, amma inda akwai hanyan 6angaren Mahmud ne, Antyn Mahmud, wata da be santa ba da kuma shi kanshi, so take ta wuce amma tarasa ta ina zatabi, cikin wa'yancan ukun duk inta bi 6angarensu duhu ke mamaye gabanta, dalilin haka sai ta sake sakin kuka tana yarfe hannu, shi ka'dai ne kawai 6angarensa be yi mata duhu ba, amma ko data biyoshi 'din sai hanyan yayi mata nisa sosai yanda zai yi mata wahalar cimmasa shi kansa ma nisan yayi mata tana hangoshi yayinda har hannunsa yake mi'ka mata dan ta kama amma bata iya kamawa, hakan sai yasa taci gaba da kuka tana fa'din " _Yah Abbas_ !
_Ya...... Abbas_ !!
Yana san taimaka mata shima amma sai ya kasa, Mahmud kuwa daganin tana bin inda Abbas 'din yake tana 'kiran sunan shi sai shi kuma ya juya bayansa yana murmushi, taku 'daya biyu zuwa uku yayi sai ya 6ace 6at suka daina hangoshi sai haske ya mamaye gurin gaba 'daya tare da wani lumshi me 'kayatarwa.

Dai dai 6acewar Mahmud 'dinne Abbas ya farka daga baccin yatashi ya zauna dafe da kansa yana sake bitan mafarkin dayayin tare da juya al'amarin acikin ransa, yarasa ma'anar mafarkin gaba 'daya, abu 'daya ya iya fahimta shine Fateemah na bu'katar taimako arayuwarta sai de be san dalilin da ze kawo hakan ba.

Yana cikin tunanin mafarkin ne sai ya samu sa'kon tafiya zuwa Lagos, wanda yazo masa a bazata a kuma dai dai lokacin da ze fi bu'katan hakan, haka ya tashi yayi komai cikin hanzari ya gama shirinsa tsaf.

Su shida suka tafi , jirgin 'karfe 6:30am na safiyar ranar juma'ah suka bar Maiduguri zuwa Lagos.

Sai dai kuma cikin rashin sa'a sai da suka isa Lagos suka sake tarar da sa'kon cewa sai zuwa yamma zasu iso dan haka sai suka nemi gurin da zasu huta kafin yamma amma sam basuji da'din hakan ba.
Chapter 84 · 0% Book details