← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 163

Sashe 125

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~MOST READ~ 👇🏼
*KUNGA DA YAWA NAYI MUKU KO?TOH HARDA NA GOBE NAYI , IN DA RAI KUMA SAI SATURDAY MU HADU IDAN ALLAHU YA KAIMU, IN KUMA NASAMU* *DAMA BA MAMAKI KUGA UPDATE* .

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

I _dedicated this page to my fellow *Wattpadians and Whatsapp fans* , Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa tare daku comment 'din ku addu'o'in ku, tare da conversation 'dinku na matu'kar 'karamin karsashi, wannan page 'din kyautar kune👌🏻_ .🥰

*Bismillahir rahmanir raheem*

_I learn that life is a book, every day is a new page, every month is a new chapter and every year is a new series._

🅿 *84*

Kwana biyu bayan hakan Abbas ya koma Rivers dan dama hutun 1week aka bashi, kafin hakan kuwa sun sha drama da Daddyn Abuja akan tafiyar, Abbas ya so su koma tare da matar sa amma Daddyn Abuja ya hana shi, dan cewa yayi baza'a tafi masa can wata uwa duniya da yarinya ba, salon aji da'din cutar da ita acan ba, shi be yadda da zaman sun ba har yanzu yana ganin kamar Abbas mugun hali zai yi tayi mata, amma idan tana kusa da su toh abin zai zo da sau'ki kuma dole ne ya rin'ka kulawa da ita ko dan ganin idanun su ma.

Daddy gani yake kamar a bayan idanun su Abbas zai na zalintar ta ne kawai, shiyasa yace tukunna sai yaga yanayin zaman nasu kafin ta bishi.

Shi kansa daddyn cewa yayi bazai bar Abbas 'din yaringa daukan tsawon lokaci ba dole zai na zuwa duba ta.

Abbas be iya musu ko jan magana ba dan haka sai ya yi shiru kawai amma ba wai dan ransa ya so hakan ba, ya so ya sanar da Daddy babbah saboda yasan shi ka'dai ne zai sa Daddy amincewa amma kuma nauyin sa yake 'dan ji yanzun kuma ma dan kar Daddyn nasa yaga kamar yana jayayya ne da maganar sa shiyasa kawai ya fasa.

Ya dai 'dora hope 'din sa akan Teemah da tunanin ko zata yadda itan tace zata bishi, amma ko daya zo ya same ta da batun sai ta nuna 'kin amincewar ta sai ma tace zata koma gidan Ummah kawai idan ya tafi.

Bai san dalilin ta na 'kin amincewan ba, amma ba 'karamin haushi yaji ba yasan da ita ta amince toh da Daddy ma zai yi shiru akan lamarin.

Ai kuwa shima Abbas yace babu inda za taje agida zata yi ta zama ita ka'dai tunda bazata bishi ba.

Sosai ta tsorata da zaman da zata yi a gida ita ka'dai 'din saboda tuna baya da tayi, amma sai take ganin da ta bishi 'din gara ta zauna agidan in yaso idan ya tafi sai ta koma abinta ai baze sani ba.
Sosai Teemah ta 'dauki abin wasa.

Haka har Abbas ya tafi da haushin ta ha'di da kewar ta da zaiyi azuciyar sa.

*****
Anty ma a cikin week 'din ta bar kano ta koma Lagos, yanzu kam zuciyar ta fes ba wani damuwa, bata da burin cutar da kowa aranta illah taga ta gyara tsakanin ta da ubangijin ta ta kuma gyara lahirar ta, gidan ta ma ba 'daya da kishiyar ta ba amma bayan ta koma Abbah ya kawo amaryar sa har gida suka wuni tare dan Abbah kansa zuwa yanzun ya yadda da cewa Anty ta yi nadama ta gaskiya ta gyara halin ta gaba 'daya ta canja su daga munana zuwa kyawawa musamman daya ga yanda taje har Abuja musamman saboda Fateemah shiyasa ma batare da fargaban komai ba ya bar amaryar sa tare da ita.

Anty ma a'dan zaman nasu ne ta fahimci cewa kishiyar ta irin alkahiri ce mai sanyin hali, dangin albarka, tariga ta 'dauri aniyar kar6an kaddarar ta aduk yanda tazo mata, ta yarda cewa zata zauna zaman amana da kishiyar ta, cikin aminci da salama shiyasa ma bata damu ba ta budewa Anty Sadiya zuciyar ta gaba 'daya.

Haka kishiyar ta ma bata nuna mata komai ba suka ha'de kansu tamkar 'yan uwan juna, kowa ya ri'ke matsayin dayake kai.

Raba kwanakin su sukayi kamar yadda dukkan ilahirin masu kishiya keyi wato kwanaki bibbiyu.

*****
Ummah ma taso Abbas ya koma Porthacourt da matar sa sai Daddy ya hana, tayi ko'kari sosai wajen ganin ta gyara abin amma be yiwu ba, bayan haka kuma sai tayi tunanin ko Teemahn zata dawo gida ne kafin ya dawo, sai kuma Abbas shima ya yi nasa ikon ya hana.

Mamaki Ummah tayi sosai akan hakan kuma sai ta tambayi Teemahn ko tayi masa wani laifi ne tace ah ah wai dan ta'ki binsa ne shiyasa, Ummah batayi mamaki ba dama tasan sai da dalili kafin zaiyi hakan dan tasan baze yi purnishing 'din ta akan laifin Daddy ba, tasan yayi hakan ne dan yayi purnishing 'dinta akan 'kin amincewa binsa da tayi, Ummah sam hakan beyi mata da'di ba, aganin ta tunda abaya nema ake yayi auren amma ya'ki har sai da akayi masa za6i, Alhamdulillah kuma sai ya kar6i za6in nasu da hannu bibbiyu toh me yasa kuma ba za'a bar shi ya nutsar da hankalin sa wuri guda ba, me yasa baza'a barshi ya tafi da iyalinsa ba ko dan ma sha'kuwar su ta 'mara 'karfi.

Aranan da ya tafi Ummah ta 'kira Abbas akan zaman Teemah ita ka'dai agida 'din tace masa ai be yiba tace yayi ha'kuri Teemah ai yarinya ce kar yana biye ta akan wasu abububuwan tunda yasan bazata iya ba, shi kam rufe ido yayi yace da Ummah abar ta kawai, akwai security aciki da wajen gate babu komai insha Allahu, yace Ummah ai kowa ma haka take zama agidan auren ta so ba wani sabon abu bane, Ummah taso tayi convincing 'dinsa amma Abbas yakasa fahimtar ta dolen ta tabar shi akan ra'ayin sa kawai sai ta tura Hannah akan su zauna tare.

*****
Teemah yanzu hankalin ta a kwance yake bata da damuwar komai, duk kuwa da cewa Abbas ya hana ta zuwa ko'ina amma hakan be dame ta ba, yace ta zauna a gidan ta bai yadda taje ko wajen gate ba, suna zaman su da Hannah lafiya domin Hannah na taya ta surutu sosai ta 'dauke mata tunanin komai dan Hannah ba dai surutu ba, lokacin zuwa makaranta sai ta tafi, in sun gama lectures sai ta dawo gida.

Suyi fa'da suyi da'di dan Hannah akwai tsokana na fitan hankali.

Abbas tunda yatafi yau kwanan sa biyu amma sau 'daya tak ya 'kira ta shi' din ma da tunanin ta ya ishe shine ya 'kira ta dan kawai yaji muryar ta, Teemah kuwa gaishe shi tayi tare da tambayar sa ya ya isa.

Jiya yai muryar ta ras hankalinta akwance lokacin datake tambayar tasa bata tare da wata damuwar komai.

Bai amsa maganar ta ta ba sai ma ya tambaye ta yace " _wato ke bakya missing 'dina ko_ ?
Dan ransa yakasa yin ha'kurin bata damu da rashin sa ba.

Shiru tayi masa bata yi magana ba, sai dariya datakeyi 'kasa-'kasa, sosai Abbas yaji haushin hakan sai ma yaga kamar farin ciki take yi daya bar ta a Abujan dan haka shima sai ya kashe 'kiran kawai ya dafe kansa.

Teemah kam bata damu ba taci gaba da walwalar ta bata 'kara bi ta kansa ba haka shima.

Tana waya da su Anty da Mummy harma da Daddyn ta ha kama maman Amal itama suna waya akai-akai musamman dataji cewa Teemahn tasake yin aure ma sai ta ke yawan bata shawar wari wa'dan da bazasu cutar da rayuwar kowa ba,
Anty ma kullun maganar ta kenan guda 'daya shine ta kula da mijinta ta kula da hakkin da ke kanta, kuma ta daina rashin ji da taurin kai.

Sosai maganganun sun yake tasiri azuciyar ta musammman sai dai bata san ta yanda zata yi handling wasu abubuwan ba dan ta fahimci Yayahn 6au'da'd'de ne.

Amma data ga ya 'kara kwana da wuni be 'kira ta ba sai abin sai ya fara damun ta, da kanta ta fahimci bata kyauta masa ba.

Wasa-wasa kusan kwana biyar bai 'kirata ba sai dai Hannah ce ke yawan sanar da ita cewa ai Yayah ya 'kirata data na school kusan kullun hakan Hannah ke sanar da ita, amma idan tana gida bata ganin yana 'kiran Hannah, kuma Hannah bata ta6a cewa da ita ya neme ta ba ko yace a gaida ta ba abin na 'daure mata kai sosai.

Hannah kuwa bata san cewa basa waya ba da yake ba'a gida take wuni ba, sai dai itama daga baya tafara yiwa Teemah mitar bata ta6a ganin suna waya da Yayah ba shin basa missing juna ne ko kuma sai abayan idon ta akeyi.

Teemah "hmm" kawai ta ce da ita, dan ita kanta zuwa yanzun tafara shiga ru'du, missing 'din sa takeyi sosai shi kansa, muryar sa, fitinar shi, touches 'din sa da komai nasa.

So ma take ta ganshi gaba 'daya dan ba 'karamin missing 'din sa takeyi ba, tunanin sa kullum na damun ta musamman ma idan taje bacci da dare.

Sau tari idan ta tuna da Zahran sa takanji ba da'di har zuciyarta, inda take sai taji hankalin ta yakasa kwanciya wani sabon tsanar yarinyar take ji na tsarga mata.

Hannah ma da kanta ta fahimci Teemah ba daidai take ba a kwanakin nan dan tafiya ganin ta cikin tunani amma data ga bata sanar da ita meke faruwa ba sai itama bata tambaye ta ba.

Ranar daya cika kwana bakwai da tafiya ranar Teemah na kwance da dare takasa bacci sai juyi take yi, Hannah har ta gama waya da Bilal ta kwanta har ta 'dan yi bacci ta farka garin yin juyi sai ta ga Teemah zaune idanun ta biyu lokacin kuwa sha 'daya da kusan rabi na dare, batayi mamaki ba sai ma tausayin Teemahn daya kama ta.
Chapter 125 · 0% Book details