← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 163

Sashe 20

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hun haahh"
yace yana kallonta,itama da mamaki tabi abincin da kallo sannan ta kallesa.

"Open your mouth mana"
Yafad'a da seriuos tune

Sai da ta kalli mummy tukun sannan ta kalli Abbas sai ta ga dukkansu babu wanda hankalinsa yake wurinsu.

Bud'e bakin tayi yasaka mata abincin.

Abbas kuwa duk abinda ya faru yana lure da shi,sai da yaga zata kalleahi ne kafin ya maida kansa k'asa tamkar tun zamansa awurin bai kalleta ba........bata san tun d'azu yake lura dasu ba, jiyayi tamkar ransa zai fita ajikinsa data kar6i abincin,jiyayi ya gagara natsuwa sam,"innalillahi yake ta fad'i azuciyarshi bai san dalili ba amma sai yaji ya tsani wannan scene d'in.

Take tunanin baya ya fad'o masa arai,irin yadda yake kula da ita shima yake bata abinci abaki,yau ga wani daban ya fanshe shi..........

Haka yaci gaba da bata abincin ita kuwa kamar jira takeyi daman abata sai kar6a takeyi
mummyn kam cewa tayi "aikuwa aiki ya sameka Mahmud indai wannan ce"

Maganar tata ce ta dawo da Abbas cikin hayyacinsa sai alokacin ya lura ashe Mahmud cigaba da bata abincin yayi ko kunyarsu bayaji.

Shikuwa Mahmud zuciyarsa d'aya yake bata,dan yasan is not a crime tunda sistern shi ce.

Spoon kusan biyar takar6a a hannun Mahmud sannan tace ya isheta.

Wani uban tsakin da Abbas yaja harni ma na tsorata da ita,sai dai sa'an shi d'aya azuciyarsa yayi shiyasa babu wanda yaji.

Cak ya mik'e tsaye ransa amatuk'ar jagule amma babu wanda zai fahimci hakan sai wanda ya sanshi sosai,saboda yanayin yariga yazame masa jiki,shiyasa babu wanda yagane halin dayake ciki.

Ummansa kad'ai ke fahimtarsa aduk halin dayake ciki sai ko Daddynsa.

D'akinsa yawuce direct yana shiga ya hau fincike riga kamar ita ce tamai laifin.

Bayi ya shiga ya watso ruwa ya fito dayake yana ta fad'in "la haula wala kuwwata illah billah"acikin zuciyarsa tunda abin yafaru sai hakan yasa yad'anji sassauci.

Kwanciya kawai yayi agadon dake d'akin sa cikin sa'a kuwa sai bacci ya d'auke sa.

Yayin da Mahmud yake can zaune da mummy Teemah kuma tashiga dan shirin zuwa islamiya.

Fitowa tayi da hijab d'inta ahannu tace "toh mummy na shirya yau wazai kaini"?

"Je ki d'auko kud'in adaidai ta ajakata"cewar mummyn.

Har Teemah ta juya da nufin zuwa d'akin mummy sai Mahmud yace ta dawo zai kaita.

"Dauko wanda zaki dawo dashi toh"mummyn tasake fad'i

Mahmud d'in ma sake cewa yayi "bari zan d'auko ta mummy idan sun tashi"

"Karfa a takura ka Babana"mummyn tafad'a tana kallon sa

"Haba mummy akan d'an wannan d'in"
Shima yabata amsar maganar tatta yana murmushi

Teemah hijab d'inta tasaka ranta fari k'al dan dama ta tsani hawan adaidaitan dan bata samu ma da wuri gashi ana zabga rana.

Koda suka fito kuwa Mahmud sai da ya lek'a d'akin Abbas da niyan sanar masa da fitar tasu amma sai yaga ma yana bacci.

Hakan yasa ya fito suka tafi abinsu.

Kamar yanda yafad'a d'in kuwa ana tashi yawuce ya dawoda da ita gida.

_Comment share and_ _vote pls_ 🤞🏻

*Salmern ku ce* 😍
[10/2, 5:55 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Fake friends are like shadows, always near you at your brightest moments but nowhere to be seen at your darkest hours.

🅿 *19*

Mahmud shegen surutu ne dashi, gashi baya da bak'unta sam gashi da iya jan mutun da hira hakan yasa awannan fitar da sukayi da Teemah har sabo ya shiga tsakaninsu na ban mamaki.

Tun daga ranar shiyake ajiyeta a school ya kuma d'auko ya dawo da ita gida da yamma ya ajiyeta a islamiya kuma.

Tare suke zama suyi hira haka abinci ma bai fasa bata ba kamar yanda ya fara tun farko sai ya mik'e kawai da haka, dan suna zama a kan table zai fara bata sai yaga tace mar tak'oshi kafin yaci shima, wani lokaci har d'akin sa take zuwa dan kawai suyi hira idan taga Mahmud d'in bai zo nemanta ba,idan akayi rashin sa'a kuma ranar yana d'akin Abbas sai fatattako ta tmdawo tana ture-turen baki tana mita,mummy najinta kuwa aja bakin har sai tayi kuka.

Koda lokacin shiga CAMP d'in Mahmud yayi ma Abbas ne da Teemah suka rakashi,Teemah harda d'an guntun hawayenta tana ta mar shagwa6an wai zai tafi ya barta shikuwa Mahmud yanata mata dariya.

Abbas haushin hakan yaji, sosai abun ya sosa ransa har ya gagara juran ganin abinda Teeman takeyi dan Mahmud zai shiga CAMP ai baisan lokacin daya sa hannu ya finciko ta da k'arfi ba, bai tsaya ko'ina ba sai daya danganta ta da cikin motar ya tura marfin ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima ko takan Mahmud d'in ma bai k'ara bi ba.

Idan kagan shi zaka yi zaton ko gajiya yayi da abinda Teeman keyi shiyasa yayi hakan, kamar dai yanda Mahmud ma tunaninsa ya tsaya iya nan.Hakan yasa yabi bayansu da murmushi yana k'ara jinjina hali irin na Abbas d'in sam baisan wargi.

Abbas kuwa takaici ne yagama cika mas kwakwalwa, suna shiga cikin motar kuwa ya d'aga hannu ya sake mata wani rankwashii mai azabar zafi dan ya yishi ne a zuciye, amma sai ya waske da fad'in cewa bata da kunya ita kokad'an, wai 'yar k'arama da ita sai fitinan tsiya.

Bata fahimci mai yake nufi ba, amma zafin abinda yamatan sai yasata kuka,kukan tafara da d'an sauti dan abin biyu yazame mata ga missing d'in yah Mahmud ga kuma zalinta da akaci abanza.

Takuwa k'iyin shiru da gangan ma taketa yin kukan da sauti aranta take cewa aikuwa zaka ga fitina yau d'in nan ganin idonka.

Bai k'ara kallon inda takeba balle ya kulata sai da yaga kukan bana k'are bane kafin yayi parking agefen hanya da k'arfinsa sannan ya kalleta yace
"Zan 6a66allaki anan wallahi idan bakimin shiru ba idiot"
yafad'a yana wani zaro idanu

Shiru tayi cak kamar anyi offing switch dayake daman kukan na isaknci shiyasa tayi tsit da wuri dan sosai ta tsorata da yanayinsa na yau d'in acikin ranta tasake fad'in "ashe dai ni zanga fitinar bashi ba."

" _Banza jarababbiya_ "
Yafad'a lokacin da yake k'ok'arin tada motar aranta ta amsa da "wallahi badai ni ba kam sai dai kai"

Tana fad'a tawani kau da kai gefe kamat wata jaruma.

Dayake bajinta yayi ba shima sai bai kulata ba.

Tuk'in ya cigaba dayi batare da ya d'auki hanyar da zata sada su da gida ba.

_Waziri ibrahim_ ya nufa ita kuwa sai ware ido takeyi da mamakin yaushe yasan unguwar kuma mai ya kawo su hanyan nan d'in, kodan ma ai bai san gari ba ba mamaki 6atan kai yayi"duk aranta tayi wannan tunanin.

Hakan yasa da gwanintan ta tace "yayah nan fah ba hanyar gida bane"

Hannunsa ya d'ago da niyar gwa6eta a baki sai tayi saurin yin k'asa da kanta ta 6oye fuskar atsakanin cinyoyinta.

Hakan datayi ne ya kwaceta sai shima ya maida hannun nasa kan stairy tare da fad'in "nonsence".

Tafiya kad'an ya k'ara sai ya sa hannu ya d'ago wayarsa yayi dialling wata no.

Baiyi magana ba sai kawai "uhm" dayace yana fad'in hakan kuwa ya cire wayar akunnan sa tare da ending call d'in sannan ya ajiye wayar a gefensa.

Parking taga yayi a k'ofar wani gida,minti biyar mai kyau basu k'ara ba sai ga wata y'ar kyakykyawar budurwa tafito daga cikin gidan tana zuba murmushi.

Shikuwa yana ganinta ta fito sai shima ya bud'e motar ya fita ya tareta suka had'u a tsakiya.

_vote & comment pls_ 🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 5:57 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Fake friends are like shadows, always near you at your brightest moments but nowhere to be seen at your darkest hours.

🅿 *20*

Yarinyar kam masha Allah ba dai kyau ba,Teemah k'ura mata ido tayi tana ta kallonta har Abbas d'in ya isa gareta.Sai alokacin nr ta d'auke idonta daga kan yarinyar.

Saitin yarinyar Abbas ya tsaya sai ya zamana Teemah bata hangota kok'ad'an dan duk tsawon Abbas ya kare ta,sai dai bakin gyalen yarinyar da iska yake ta kad'awa shi kad'ai Teemah ke iya hangowa game da yarinyar.

Amma tun fitowar yarinyar Teemah ta lura yarinyar "A" ce afagen kyau, hak'ik'a kyau kam Allah ya bata ba laifi,taso tayita ganin yarinyar har tasamo abin kushewa amma sai Abbas yayi mata yaawah yayi babakere ya rufe ta gaba d'aya sai bayanshi kad'ai Teemah ke iya hangowa bata san meke gudana a tsakaninsu ba, ba kuma tajin akan abinda suke tattaunawa.

Rasa abinda zatayi tayi aranta takejin kamar tafita taje inda suke tsayen taji mai suke fad'a amma tsoro ya hanata dan tsan inta kuskura tamasa badaidai ba tilabta zaiyi shikam baruwansa balle ma yanda taga yau d'in yake 90% tasan babu abinda zai hanasa dukanta.

Kalle kalle tafara acikin motar kamar wanda yau ne tafara shiga cikinsa,ita kanta batasan mai take nema ba cikin haka kuwa idanta ya sauk'a akan wayarsa dake ajiye agefen inda ya tashi.

Karambani yasata ta d'auko wayar, cikin sa'a kuwa wayar bata shiga security ba tana bud'ewa taga akan k'iran da yayi d'inne wayar take haryanzu
Chapter 20 · 0% Book details